BABI NA TAKWAS
"Ke Rubaah wani d'an iskan ne kika bar wa ƙwanukan can, da kika gama cin abinci kika bar su a cikin d'akin da zai fito miki da su?."
cewar Zaliha data fito daga d'akin su ta zo ta tsaya a kanta.
Rubaah da ke zaune tana bitan hadda da aka basu a islamiya, sai da ta kai karshen aya kafin ta d'ago tare da yiwa Zaliha wani kallo a kaikaice kana ta yamutsa fuska tare da faɗin
"Ai ban ce ki fito da su ba, ki barsu idan na gama zanje na d'auko su. idan kuma kin gaji da ganin su a gurin sai ki fito da su."
ta mai da kanta ga alkur'ani ta cigaba da karatun ta.
Zaliha ta dungure goshin ta tare da rike kugu tana fad'in
"Ke kin isa ma kice a barsu sai sanda kikayi ra'ayi kafin ki je ki fito da su, waye sa'an ki da zai fito miki da su?
jimin ƴar rainin wayon yarinyar nan.
sabo da ga d'akin ya dawo gurin wanke-wanke dole ki bar ƙwanuka ciki, dallah tashi ki je ki fitar mana da su daga cikin d'aki."
Rubaah ta rufe kur'anin tayi huf zata mike,
tana fad'in
"Ki sake dunguri na ki gani idan ban ɓalla yatsar ba.
anki aje a fito da su me zakiyi? d'akin da ko shareshi ma baƙwayi...."
suka had'a ido da Mama.
Mama tayi mata ido kan ta koma ta zauna.
ta koma tazauna,
tana turo baki gaba,
tayi kwafa tare da girgiza kai tana tauna lips d'in ta gami da harar Zaliha.
"Wlh ni d'an banzan duka zan miki. inci uwar bakin rashin kunyar nan taki, in ni sa'arki ce."
cewar Zaliha tana hararar ta.
"Ke Rubaah taso ki je ki fito da kwanunan."
Mama ta faɗa tana nuna mata hanyar d'akin.
Rubaah ta kunbura baki ta mike tana cigaba da hararar Zaliha,
ita kuwa Zaliha tsaki taja ta wuce gun wanke-wanke dama zuwa ta tattaro kwanukan ne bazatayi ba,
dan yau mamarsu ce da girki, ta mata gori a d'aki Rubaah tana yiwa mamanta wanke-wanke har ta tayata aiki ranar da ba makaranta,
sukuma sai sun ga dama suyi mata, zasu bar mata abin gori.
shine Zaliha'n ta fito yin wanke-wanken...
Rubaah ta kwaso kwanukan ta fito da su tana cigaba da kumburi.
d'akin da basa gyara shi ma sai sufi kwana nawa basu share saba,
wani lokacin sai ta zo kwanciya ta share Dan bazata iya kwanciya cikin datti ba.
tana zuwa gurin wanke-wanke ta dangwara mata kwanukan ta juya tana yin kwafa. cikin kunkuni ta ke faɗin.
"Sai kace wani dakin zinari ɗakin da ko shara ba a yi."
"In kika zage Ni ne kawai bakin ki zaiyi jini."
"Bakuna suyi jini dai."
tayi maganar tana komawa in da ta tashi, sabo da Mama ta kafe ta da ido ta hana ta ramuwa yadda ya kamata, sai kumburi take tana huci.
"Ya Allah ka shirya min ita."
cewar Mama a zuciyar ta....
Da misalin karfe 5 da rabi Rubaah ta dawo daga islamiyya.
ta shige d'akin Mama ta iske ta tana waya, da sauri ta karasa in da Mama take jin tana fad'in
"Ya su Mashkur."
ta kwanto jikin Mama tana cewa
"Adda Ramlat ina yarana?."
daga cikin wayar Ramlat ta ce
"Autar Mama har an dawo daga makarantar, yaranki kad'ai zaki tambaya ban da ni, yaushe zaki zo?."
"Sai an yi hutu."
"Dan Allah kizo a weekend."
"Nifa wanann gidan naki yanzu ba son zuwan sa nake ba."
ta fad'a tana mikewa tsaye ta soma cire uniform d'in jikinta tana yamusa fuska da maga cikin wuya,
da alama wani abun take fad'i.
Mama ta harareta tana fad'in "Ke kam Allah ya shirya ki.
Ramlat zata zo a karshen mako.
Daga cikin wayar Ramlat tayi murmushi tana faɗin
"To Mama Allah ya kaimu."
Mama ta amsa da Amin kana ta ɗaura mata da nasiha kamar yadda ta saba.
"ki kara hakuri kiyi ta ladabi a gidan aurenki, dama yanzu dole ki zamo mai hakuri dan girma ya same ki, ki zauna da mijinki da abokiyar zaman ki lafiya, kiyi mata adalci kada ki tauyeta dan kina ganin ke tazo ta same ki a gidan,
Allah ya baku zaman lafiya da hakuri da juna."
Rubaah ta kumbura baki tana magana kasa-kasa
"Wannan Aminan 'yar rainin wayon ai Adda Ramlat ɗin ce ma ke barin ta."
tayi kwafa tana taune lips.
Mama ta girgiza kai,
sukayi sallama da Ramlat.
Mama ta harareta ta da idanun gargaɗi.
"An ce miki kowa irin ki ne, da idan an masa baya iya hakuri sai ya rama? ina rabaki fa Rubaah tam."
Rubaah ta kuma turo baki.
"Allah Mama dan baki san halin Amina'n nan bane."
"Shine me? ke ma haka ake fad'an halinki."
ta kumbura baki tana shagwab'e fuska.
Mama taki goyon bayan ta' tana bin bayan amaryar Adda Ramlat, tayi waje baki a ture dan tasan Mama bazata tab'a bin bayan ta ba, kullum a gun Mama itace mara gaskiya.
Mama tabi bayan ta da kallo tana girgiza kai. Allah ke nan mai halitta ya halicci Ramlat da Rubaah a tsatsonta masu hali mabambanta.
tausayin ɗiyarta Ramlat ya kamata, tuna sanyin hali da hakuri irin nata.
a gefe guda na zuciyarta kuwa tausayin Rubaah ɗin ce itama sanin halin rashin hakurin ta. halin Rubaah daya kasance na ba yafiya idan an taka ta, yakan sa Mama shiga tsoro da zullumi a ko da yaushe.
hannu biyu ta ɗaga tana jero addu'a ga ƴaƴan nata guda biyu a duniya. addu'o'in da ya zame mata jiki a ko da yaushe...
***
***
Bayan sallar isha, in da ta idar da sallar tayi bitar karatunta,
bacci sosai a idanunta,
ta gyara ta kwanta kan sallaya, aiko bacci ya tafi da ita.
kasancewar yau Mama ce da girki sai da ta gama duk aiyukanta ta kafin ta shigo d'aki.
ta dubi d'iyar tata da ke baccin ta cikin kwanciyar hankali, ta sauke numfashi a hankali ta furta
"Allah ka shiga lamarin ta."
bata tasheta ba sai da taje tayi wanka ta dawo, sannan ta karasa in da take ta bubbuga ta.
sam bata da nauyin bacci bugu daya ana biyu ta farka.
"Taso kije ki kwanta."
cewar Mama tana duban ta.
kai ta gyad'a ta mike a hankali ta
d'au Al'kur'anin ta, tayiwa Mama sai da safe.
har takai kofa kamar kullum Mama ta kuma yi mata gargad'in, kada taji bakin ta a d'akin su Zaliha babu ruwan ta da shiga tsafgarsu.
tana fita Malam Musa na kokarin shiga.
Habu daya fito daga kicin rike da kwanon tuwon sa.
ya ja ya tsaya idanunsa a kanta.
a hankali ta matsa gefe ta bawa malam Musa hanya tare da gaishe shi.
ya amsa da sauri yana haske fuskarta da tocilan hannunsa tare da fad'in
"Ina kuma zakije?."
idanunta da suke cike tap da bacci ta lumshe su ta kuma bud'e su lokaci guda,
ta kai d'aya hannun ta ta mussuke idon ya yin da d'aya hannunta ke rungume da kur'ani a kirjinta.
ta kad'a kwayar idanun da wani kalar yanayi tayi wani luuu da su, wanda hakan halittar ta ne, sai dai ga wanda bai san ta ba zai iya kiran hakan da sabar iyayi a ƴan shekarunta.
ta motsa lips d'in ta da bacci ya sa su yi mata nauyi ta ce
"Zan je na kwanta ne."
Habu daya mace a tsaye yana kallon ta, gaba ɗaya ya
tafi a kallon fuskarta da yadda take sarrafa kowani sassa dake kan fuskar nata. yawani haɗiye miyau. Yana gyara rikon kwanon tuwonsa daya kusa suɓucewa a hannunsa.
Da sauri Malam Musa
ya ce
"A'a me yasa ba ki yi kwanciyar ki a nan ɗin ba?."
ya bud'e labule da sauri ya shige ciki yana fad'in
"Maryam ai da kin barta ta kwanta a nan."
Mama ta dube shi tana cewa
"A nan kuma Malam ai yau da gobe duk a can d'akin su Halima zata kwana, ko ka mance ne."
ya zauna bakin gado yana fad'in
"Na sha'afa ne, amma ai na sha fad'a miki in tayi bacci ki barta ta kwana ba sai kin tashe ta ba. ba'a tashin mutum a bacci irin haka musamman yana jin dad'in baccin ai sai gigin bacci ya kai shi wani gurin, ki kirata ta dawo ta zo ta kawanta, a Binta a nan ɗin."
Mama ta dube shi da mamakin ganin da iya gaskiyar sa yake fad'i
"Taya za'ayi mu kwana d'aki daya da Rubaah bayan ga ka nan, ai bazai yiwu ba. addini ma ya hana."
bombomi Malam Musa ya soma
"Eh ai komai ma zaki ce, tun da ni ban isa da ita ba. ai kullum nuna min iyaka ta kike sabo da bani na haifeta ba, to shike nan sai kiyi duk yadda kike so, tun da Ni ban isa na ce ga yadda za'ayi a yi ba."
"Haba malam, Rubaah shekarar ta sha biyar fa, taya za'ayi mu kwana d'aki d'aya da ita, ai sam hakan bai dace ba."
"Yanzu kam ko mai ma zakice ai tun da kin nuna min kasawa na a kanta."
Mama tayi sororo da mamaki, irin haka yasha faruwa sakanin su, sun rinka muhawara kan kwanan Rubaah a d'akin idan yana nan, idan tayi bacci kar Mama ta tashe ta ta barta ta kwana kawai.
sai dai sam taki ta bada goyon baya ko da kuwa zaiyi fushi.
wani lokacin takan zauna tayi ta tunani kan lamarin, tana son gane shin hakan da take idan ya ce ta kwana a nan ɗakin alhalin yana nan, idan ta hana hakan. rashin nuna halacci ne ga wanda ya nuna mata halacci ita da d'iyarta.
to amma fa tafi yarda kan kudirin nasa ba dai-dai bane, bai kyautu su kwanta d'aki daya da 'yar da ta fara tasowa ba bare Rubaah da ta kai shekaru goma sha biyar.
Mama ta jijjiga kai tana fad'in
"Allah ya baka hakuri."
Rubaah kam tuni ta wuce abin ta bayan ta kori Habu da hararar da ya sashi cin tuntuɓen daya kusa kifewa. bata ma san me ake ciki ba,
dan bacci ne ke azalzalarta..
Tun a daren wancan ranar Ramlat ta sanyawa zuciyar ta cewa, da yardar Allah bazata sake nuna masa bukatarta ba, ko da kuwa zai kashe ta ne.
zatayi ta addu'a Allah ya yaye mata.
Karfe 7 dai-dai ta kammala shirya yaranta.
ta dubi Mashkur data gama had'e masa boturan uniform d'in sa, ta ce
"Yi sauri kaje gurin Auntyn ku ka amto muku breakfast d'in ku, kada ku makara."
yaron ya fita da sauri kamar yadda ta umurce sa, ta janyo Muhsin ta karasa shirya shi.
jim kad'an Mustapha ya shigo rike da Mashkur,
numfashi ta sauke tare da amsa sallamar da ya yi.
"Sannu da zu."
ta fad'a tana d'auke idanunta daga kallon sa,
ta karasa shirya Muhsin.
ganin shi ya tuna mata da daren jiya da take jiyo sammabun shi a d'akin Amina, duk da ba wannan ne karo na farko da ta saba jin hakan ba.
"Ina kwana."
ta fad'a a taice.
ya amma yana fad'in
"Lafiya lau, kin tashi lafiya?
Auntyn su bata da lafiya bata samu tayi breakfast ba, ki shirya musu su samu su tafi kada su makara."
kallonsa tayi jin hakan ya d'an sosa mata rai, bata ce komai ba ta nufi kitchen d'in ta.
dan wannan ba shine farau ba, idan Amina ce da girki,
ba lallai ne tayi musu ba, dole ita mai 'ya'ya ta yi ko ita ce da girki ko ba ita ba.
ko da yaushe idan Amina ce da girki sai an kawo wasu uzururruka.
har ta kai bakin kofar kitchen d'in ta juyo ta ce
"Ina son zuwa na gaida Mama idan su Mashkur suka dawo daga makaranta."
yana amsa mata ta shige kitchen.
breakfast mai sauki tayi ganin lokaci na kurewa,
ta saka musu a lunchbox d'in su sannan ta had'a musu tea suka sha, ta rako su har bakin kofa kamar yadda ta saba, tana tsaye har sai da suka shige cikin makarantar...
Kafin su dawo ta gama shirinta tsaf bayan ta gama girki.
suna dawo wa tayi musu wanka suka ci abinci ta shirya su suka nufi gidan Mama........!
Mommyn Twins ce