AMARYAR GADO

CHAPTER 8

by @xayyeesherthulhumaerath

AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026

Jan hankali: Wannan littafi ƙirƙirarriyar riga ce da aka saka wa kowace ƙaddara da ke cikinsa suna. Kada wani labari ko sirri da aka bayyana a cikinsa ya sa a fassara shi da rayuwar wani na gaske. 

Gargaɗi: Haƙƙin wallafar littafin na marubuciya ce kaɗai. Ba a yarda a juye shi zuwa wani harshe, ko a canza shi zuwa sautin murya (audio) ba tare da rubutacciyar yarjejeniya ba.

SHAFI NA TAKWAS

Shiru ya yi yana kallon gefe don bai san amsar da zai ba ta ba ma.

Farida ta ce, “Kun gani ba? Irinsu ne masu dumama benci. Su zo class su zauna suna claiming ‘big guys’, su cika mutane da surutu, amma da zarar an kwankwasa ƙwaƙwalwa, ka ji babu komai a ciki—fanko.” Tana karasa faɗin hakan ta fice daga class ɗin.

Ba ƙaramin kunya da takaici ba ne ya kama Sufyan. Yana jin kamar ya nutse a ƙasa, musamman yadda ya ga ’yan class ɗin suna ta magana ƙasa-ƙasa, wasu na kunshe baki suna dariya.

Habib ya ce, “Sufy, ta gama damu fa wallahi. Ta ci tuwo a kanmu.”

Tsaki Sufyan ya yi ya ce, “Ba ka san yadda nake ji ba. Zuciyata na tafasa. Ai ni ba ma wannan ba akwai hanyar da zan iya ramawa, babbar damuwata ita ce; kar watarana ’yan school ɗin nan su san cewa ita matata ce. Yadda nake ta capacity ina zaɓar irin matan da zan kula, balle ma a kai ga batun soyayya, aka gano cewa matata ce, ai tawa ta kare, aji down Wallahi.”

Habib ya sheƙe da dariya ƙasa-ƙasa ya ce, “Wannan fa na faɗa maka. Ba wanda zai yarda cewa matarka ce. Ina laifi ma ace mamarka ce, ai ya fi sauƙi.”

Surutun da Sufyan ya ji a bayansu ne ya sa shi hamɓarar da Habib da nufin ya yi shiru.

“Kai, ka san akwai ƙanwata fa, a 200 Level take, ai ta ba ni labarin matar nan. Miss Farida ake ce mata. Wai kasan tun da take kullum cikin hijabi da nikaf take, ba wanda take bari ya ga fuskarta fa. Kuma wai duk girman nan nata budurwar ce fa.”

Na kusa da shi ya ce, “Hehe, kana wasa ne? Ni ma na santa fa. Ka san mu komai a makarantar nan mun sani. Mummuna ce ta ƙi karawa, shi ya sa take rufe fuskarta ai. Yoo, in ba haka ba, ta yaya za a ce budurwa kuma ’yar boko tana rufe fuska haka?”

Suka sheƙe da dariya. Na ukun ya ce, “Gaye, dama wannan kayar ai duk wanda zai ɗauke ta, jahadi ya yi, bare ka ga irin wa innan sun fi maida hankali wajen yin rayuwar ey yane. Ba ruwansu da zancen aure fa.”

Na farkon ya sake cewa, “Ai kuwa ka ce mu shirya watarana za a iya damawa damu.”

Tashi Sufyan ya yi yana cewa, “Kai dalla, mu fita. Jin zancen bogazarcen nan ƙara bata min rai yake.”

Habib ya tashi, binsa ya yi cikin sigar tsokana ya ce, “Faɗa gaskiya dai, Sufy. Ko haushi ka ji ana  antaɓo maka mata?”

Tsayawa Sufyan ya yi, ya bishi da wani mummunan kallo. Sai ya durƙusa ƙasa ya ɗauki dutse ya jefa masa. Kaucewa Habib ya yi yana dariya.

“Daga faɗan gaskiya suna zancen wani zai yi jahadi, ba su san ga ka nan ba. Babban jarumi. Wayaga bera da damisa!”

Ya ƙara sheƙewa da dariya.

Tafiya Sufyan ya yi ya bar shi a wajen. Yana ci gaba da dariya, Habib ya bi bayansa da gudu.

“Jira ni mana, Sufy! Angon bogaza!”

Habib na karawasa Sufyan ya  daga kai ya kallesa ya ce,”Yanzu kai don Allah ko a cikin mafarki aka ce maka na ji haushi akan Farida za ka yarda?”

Habib ya girgiza,”Aa fa kasan kawai tsokana ce ai ni da na san irin matan da kake so kuma me za ayi da ita? Ai kawai kaddarace.”

Sufyan ya gyada kai,”Ahto ni ka ga batun tana sabga da maza ma ai daidai kenan, ta yi harkarta kawai nima inyi tawa bai dameni ba.” 

Ya karasa maganar yana daga kai suka hada ido da Farida za ta wuce ta shiga office din HOD, binta ya yi da wani mummunan kallo ita kuwa yi ta yi kamar bata gansa ba ta wuce abinta.

Sufyan ya yi kwafa,”Ni fa sai yau na kara sanin an gama bata min rayuwa wallahi, Habib zo muje ka ga.”
Binsa Habib ya yi suka je suka tsaya ta bayan motar Farida, ya yi shiru yana zurawa motar ido.
Habib ya ce,”Sufy yane? Kace inzo kuma ka tsayar damu anan, wannan ba motar Farida ba ce?”
Sufyan ya girgiza kai,”Ita ce, yadda yau ta disgani ta sosa min zuciya ita ma sai na yi mata kwatankwacin abun da zai sosa mata rai.”
Habib ya ce,”Me kenan?”
Sufyan ya ce,”Matatar man zan toshe, yanzu ka leka ka tabbatar babu mai ganina.”
Leke Habib ya fara yana zare ido kamar sabon munafuki, Sufyan ya ya tattara ledojin pure water da wasu tarikice ya samu ya tura.
“Yawwa ai in ta san wata bata san wata ba mu fiske kawai.” Sufyan ya fada.
Suna cikin tafiya Habib ya ce,”Kai ma fa kasurgumin mugu ne, yanzu in motar taki tashi mata ya kake so ta yi?”
Sufyan ya yi dariyar mugunta,”Ohon mata, ita ta sani.”
Suna daga gefe suna kallo dake sun gama lectures din ranar har Farida ta fito ta shiga motar.

Tana tafiya ganin garin ya hade da hadari yasa suka tashi daga student garden din da suka zauna.
Tuki Farida take cikin sauri ganin ruwan sama da daf da barkewa an fara yayyafi tazo daidai tsakiyan titin School din motarta ta cirke, ta yi ta yi motar nan ta tashi ta ki motsawa, ta fita daga motar zata duba kenan ruwa ya barke kamar da bakin kwarya, ga shi ba kowa a wajen sai ita daya, haka ta bude gaban motar ruwa na dira akanta tana dubawa amma bata ga matsalar komai ba hakan yasa ta koma ta kara kokarin tada motar amma sam taki alamar motsawa bare tashi.
Zama ta yi cikin motar ta rasa mafitar da zata bille mata, gashi har a lokacin ko a mota babu masu wucewa, ganin ruwan ba na kare bane kara karfi yake yi hakan yasa ta tashi ta kara fita ta gwada tura motar, gabadaya karfinta ta tattara ta tura motar, tana turawa ta shige da sauri ganin alamar zata tashi sai kuma taki, sau uku tana hakan motar taki tashi ta gama jike shakaf ga wata irin gajiya da ta game ilahirin jikinta. Hango wata mota da ke zuwa ne yasa ta jingina gaban ta ta motar tana daga masu hannun neman taimako. Sufyan ne da ya zo daidai inda take sai d ya sauke glass ya tura kansa ya kara mata kallo sama da kasa.
Har ta bude ido zata mai magana ganin shi ne ta gagara cewa komai.
Sai da ya tabbatar ta gansa shi dinne tukunna ya ja motarsa ya wuce abunsa.

Habib ya ce,”Ta bani tausayi kuma fa wallahi.”
Sufyan ya wurga masa wani mummunan kallo yana tuki,”To ai za ka iya sauka ka taimaka mata.”
Habib ya bude baki,”Ah ni awa ai kawai muje mutumina.”

Garin Jos da ruwa 5&6 har  yamma ta fara tsalawa ruwan nan ake Farida tun tana kokarin komawa motar ta gwada kunnawa har ta sadakar rawar ɗari take tana tsaye ta takure tana daga hannu ganin ruwan ya fara sauki motoci sun fara yawo jifa-jifa, ko kallonta basa yi suke wucewa abunsu, wani mai bakar mota ne ya tsaya.

Fitowa ya yi, sai ta ga ashe HOD ɗin su Sufyan ne. Ya tambayeta me ke faruwa da motar, ta faɗa masa. Ganin yamma ta yi sai ya ce mata ta shiga motarsa ya kaita gida. Sannan ya kira mai gyaran mota a waya, ya zo ya duba motar.

Ganin ba ta da zaɓin da ya fi bin sa ne yasa ta shiga motar, ba don ta so ba.

Suna isa gidan, ta hango motar Sufyan a waje. Ya dawo, yana zaune a cikin motar, domin burinsa ya ga yadda za ta yi ta koma gidan. Ko fitowa daga motar bai yi ba har HOD ɗin ya sauketa, ta shiga cikin gida.

Sai fa HOD ɗin ya tafi, shi ma Sufyan ya ja motarsa ya bar unguwar.

Farida na shiga gida ta canja kaya. Zazzabi da mura suka rufeta, ta ɗauki magani ta sha, sannan ta shige cikin bargo.

Misalin ƙarfe sha biyu na dare, Farida ta jiyo hayaniya a falo. Abin da ya farkar da ita kenan daga barcin da ta samu.

Tana tashi ta fita, sai ta ci karo da Sufyan a bugu, shi da Falila suna rungume da juna.

Fara murza idanu Farida ta yi don ta tabbatar da abin da take gani gaske ne.

Falilah ta ɗaga kai tana nuna Farida, “Handsome, wannan fa? Ta tsaya mana a kai lafiya?”

Cikin muryar maye Sufyan ya ce, “Rabu da ita, yar wahalace, yar aikice. Tashi mu shiga ɗaki, kar a sa mana ido.”

Ya tashi, ita ma ta tashi. Suna tafiya kamar za su faɗi saboda mayen da ya kwashe su.

Farida ta tsaya cak, idanuwanta cike da mamaki da takaici. Ƙirjinta ne ya fara bugawa da ƙarfi, yayin da ta kasa ɗauke idonta daga kan Sufyan.

Ta kasa yarda da abin da take gani, wai Sufyan ne da irin wannan rayuwar duk irin tarbiya da gatan da iyayensu suka yi musu?”