BUDURWAR ZUCIYA

7-8

by @zahrasurbajo

Bayan tafiyar Alhaji maman nuravkwana tayi tana tunanin wacce yarinyace zatayi daidai da buƙatar alhaji,tunda ayadda yakemata bayani duk da ba fitowa yayi fili ya faɗa mataba,shi mutumne hariji,wanda yake da ƙarfin shaawa,to dole seta natsu yayin nema masa matar tunda tasan duk wacce ta bashi bazece baya soba tunda yana ganin girma da darajarta.

Zainab ƴar gidan malam hadi,itace tazoma maman nura arai,domin yarinyace kyakkyawa ta bugawa a jarida,gaa ƙaramar yarinya amma wayayyiyace bata wasa ba,duk da tana da tsiwa amma hakan be hanata girmama mutane,in kaga ta maka rashin kunya gonarta ka shiga.

Sosai zuciyar maman nura ta gamsu da yarinyar da kuma tarbiyyar gidansu,hakanne yasa washe gari da magriba ta kimsa ta nufi gidansu zainab ɗin tunda layinsu guda.
Da shigarta gidan asu taci karo da zainab ɗin wacce aka fi kiranta zee barazna zee fashion,aguje ta tsokano yayarta maryam.

Ayko bayan maman nura ta ɓoye tana dariya ita kuma maryam ta tsaya tana haki,tana faɗin "rufin asirinki kizo ki ciremin dan wallahi baze yiwu nida kayana ki fini iko dasuba"cewar maryam ɗin.

Sallamarmaman nurace tasa ummansu fitowa aɗaki tana amsa sallamar tana faɗin"murya najeji kamar ta maman nura,yau agidan namu"ta faɗi tana leƙowa.

"ba kama bace nice maman zainab,ashe kina ciki kika bar
Maryam zata fashemin kan ƴa?"cewar maman nura.

Murmushi maman ainab tayi tace"ƴar takice bata da gaskiya shiyasa na barsu ta caskalata,ace abu ba nakaba amma kadinga nunawa meshi ka fishi iko akai,ay kinga ansamu matsala"cewar maman zainab ɗin tana shimfiɗawa maman nura tabarma suka zauna.

Nan suka gaisa cikin girma da mutunci,maman nura ta gabatar mata da abinda ya kawota.
Nisawa maman zainab tayi sannan tace "zainab kuma maman nura bama maryamba,zainabfa gaba ɗayanta shekarunta 16 ne,sannan in banda tsokana da rashin kunya zainab ba abinda ta iya,tsakani da Allah yiwa zainab aure yanzu wallahi gangancine,kar aje asamu matsala tunda kinga yanada mata da manyan ƴaƴa"cewar maman asanyaye.

"akwai abubuwan dana duba gameda su duka naga zainab ɗin tafi cancanta da anemar masa,dan haka kar matansa da ƴaƴansa su saki wani tunani,wallahi ba abinda ze faru sai alkhairi,nide in har inada alfarma,agidannan to zainab ɗin nakeso abamu"cewar maman nura.

"kina da alfarma agurinmu maman nura,bari mahaifinta ya shigo yanzu se kuyi maganar dashi in har ya bashi wallahi ina goyon baya banida wani haufi ko kaɗan dan nasan bazaki taɓa kaimin ƴa inda zaa cuar da itaba"cewar maman zainab ɗin.

Nande sukai ta tattaunawa kan magana har malam hadi ya shigo,suka gaisa da maman nura cikin girma da mutunci.

Sanar dashi abinda ya kawota yayi,sosai yaji daɗin maganar sabida zee ɗauko mishi magar da takeyi Allah yay tawa da ita,sabida bata da tsoro,ko da waye faɗa ya haɗota yin kayanta takeyi,har ya gaji da kawo masa ƙararta da akeyi,uwa uba kuma Alhaji mahadi bayan kuɗi kowa yasan mutumin kirkine wanda baa buƙatar bincike yayin bashi aure.

"maman nura inde zainabce to ni mahaifinta na bashi,yasamu lokaci yazo ya ganta,Allah yasa alkhairi aka haɗa,"cewar malam hadi.

Maman nura godiya taita musu,inda ta jima agidan ha wajan ƙarfe goma da ike ba nisa zuwa gidanta.Tunda ko a abujar su baa cikin gari sukeba suna can karshi ne ba a ƙwaryar birninba.
Zamanta agidan seda ta raba faɗa tsakanin maryam da zainab ɗin yafi sau huɗu,kuma duk wanda zata raba ɗin ita zainab ɗince bata da gaskiya.

Washegari da misalin ƙarfe goma nasafe sukayi waya da Alhaji ta sanar dashi ansamo yarinyar,dan haka in ya samu lokaci yazo ya ganta dan ƴar unguwarsuce.

Sosai yay mata godiya inda yace mata daya taso office yau ta gidanta zai biyo.
*********
Da laasar ya dawo gida sukai masa sannu da zuwa kowa tai nata guri shima ya wuce ɗakinshi,wanka yayi ya,sauya kaya sannan ya fice cikin wata arniyar mota ya nufi gidn maman nuran,wacce ke zaman jiran isowarshi su wuce gidan su zainab ɗin.

Itako zainab acan gidansu ummansuce tasata agaba tanamata faɗa"zainabnki natsu dan Allah ki kama kanki kinga wanie zezo ganinki yanzu wanda in har,Allah yasa shine ze zama mijinki,to dan Allah karbkije gabanshi ki nuna halin,tarbiyyade dede gwargwado munamiki ainab amma in kika kunto wata tsiyar wanima zega baa miki tarbyarne"cewar umma.

"ni komai nayi agidannan ban iyaba ba gwanda in yi aurenaba in huta,wallahi ko kuturune ni auranshi zanyi in tafi inbar muku gidan tunda kowa be sona sede su anty maryam"cewar zainab ɗin tana turo baki gaba.

"muna sonki zainab tunda mu muka haifeki amma wasu cikin halayankine bama so,shine yasa koda yaushe ake miki faɗan ki gyara"cewar umma.

"yanzu umma soyayarce tasa ni zaamin aure baayiwa anty maryamba,ay kowa yaji ma yasan gajiya dani kukayi shine yasa kuke nan maraba dani,kuma tunda hakane wallahi in har akamin auren ninkuma sena bakumamaki tunda kunkullum kallon mahaukaciya kukemin"cewae zainab.

Wanka umma tasata taje tayi badan ranta yasoba tazo tasata tai kwalliya dan zainab annin ado ba baya bace kamar me aljanun kwalliya haka take dan duk sallah in ta idar seta maida kwalliyarta.
Sosai tayi kyau dan inba anceba bazaka ɗauka shekarunta 16 ba inka kalli cikar halittarta,kamar takai 18,

Suna zaune suka jiyo sallamar maman nura,ayko hannu biyu umma ta tarbeta ta shimfiɗa mata,tabarma suka zauna.

Nanfa akaita hira wacce kusan rabinta akan halayen zee ne.

Shiko Alhaji mahadi suna tare a mahaifin zee awaje suna magana inda ya bashi tabbacin ya bashi zainab ɗin sede yana roƙonshi da ya riƙe masa ita amana.

Sun ɗan jima tare kamin malam ya tura yaro ya kira zainab ɗin acikin gida,jin hakane yasa Alhaji komawa gurin motarshi ya zauna aciki,tunda dama abakin layi suke shida malam hadi ɗin kowa ya wue yana kallonsu hakane yasa ya koma mota dan ragewa kanshi idanu.

Zainab zuwa gun malam tayi,shi ya nuna mata inda Alhaji mahadin yake zaune acikin motarshi,sabida yasanshi sarai ba mutumin banza bane tunda yana yawan zuwa unguwar tasu wajanmaman nuran..

Cikin takun isa da ɗaukar hankali zee ta nufi motar gabanta na faɗuwa ganin haɗuwar motar,sabida kyan motar yakai lyau,shiyasa ta fara tunanin koma ɗan yankan kaine.

Tunda Alhaji mahadi ya hangota tana nufo motar tashi yakewa Allah kirari,domin zee ta mori iya tafiya yadda take ajiye ƙafartama kanshi abun burgewane.

Tunda ya fahimci itace zee ɗin tashi burarshi dake cikin wando ta fara harbawa da wani irin ƙarfi,dan ba ƙarya yarinyar tai masa,shiyasa harta ƙaraso inda yake be ɗauke idonshi akantaba.