MATUKAR INA RAYE

Matukar Ina Raye 2

by @mrsisham12

MATUKAR INA RAYE
(As Long as I’m alive)


Writer — MRS ISHAM
                 *** whataspp.



Page 02



“Gidan uban wa za ki je da wannan safiyar? Kuma wannan kururuwar me kike yi har kika cika kunnen mutanen unguwa?” ya tambaye ta yana zazzaro mata idanunsa masu haddasa mata tsoro.

Cikin rawar murya ta ce,

“Ina kwana, Baba Karami…”

Harara ya watsa mata, sannan ya ja ta ƙiiiii zuwa cikin gida kamar ana jan kayan wanki, yana cewa,

“Da ban kwana ba za ki ganni a nan ne, shegiya mai kama da mayu”

Duk fitsarar Waheeda da rashin kunyarta, sai ta yi tsit tana matsar hawaye kawai, tana addu’ar Allah Ya rufa mata asiri kada jikinta ya gaya mata da wannan sanyin safiyar.

Da babbar muryarsa ya yi sallama a cikin gidan. Mama Sadiya da Mama Jamila, waɗanda suke surfa waken alalen tallar Zuwaira, suka ɗago suka dube shi kafin su amsa.

Fuskar Baba Karami babu yabo babu fallasa. Ya gaishe su ba tare da ya kai dubansa kansu ba.

Su Rabi ma suka gaishe shi, kowa ya shiga rigar nutsuwarsa.

“Lafiya lau? Ya Labiba?” Mama Sadiya ta tambaye shi.

“Tana lafiya,” kawai ya amsa yana shigewa ɗakin Umma, har lokacin yana riƙe da hannun Waheeda.

Rabi da Ikilima suka yi dariya suna bin bayanta da gwalo, domin sun san da zarar Baba Karami ya kama Waheeda, to babu shakka za ta sha faɗa ko duka.

“Barka da safiya, Umma.”

Murmushi Umma ta yi da ganin babban ɗanta. Sai da ta gyara masa wajen zama kafin ta ce,

“Ka zauna mana.”

Tana kallon Waheeda da yake riƙe da hannunta.

Ya zauna sannan ya sake hannunta.

“Kun tashi lafiya? Ya matar taka take?”

“Lafiya lau, Umma. Tana gaishe ki.”

Umma ta ce,

“Masha Allah. Ya wannan sanyin?”

Ya amsa,

“Ana sanyi kam Umma. Allah Ya ba mu ikon wuce shi lafiya.”

“Ameen.”

Waheeda kuwa tana tsaye a gabansu tana zazzare ido, jira kawai take su shagaltu da hira ta samu damar tserewa.

“Umma, me ya hana yarinyar nan zuwa makaranta? A ƙofar gida fa na same ta tana ihu, jikinta futu-futu kamar mahaukaciya.”

Umma ta girgiza kai cike da takaici ta ce,

“Iskanci ne kawai, Babana. Ka san halinta,da safen nan ma faɗa suka tayar ita da ’yan uwanta a kan wanke kwanuka. Sam Waheeda ba ta jin magana. Abin takaicin ma shi ne rashin son zuwa makaranta. 

Tun da Salma ta gama secondary, ita  sai ta samu tayi karatun,amma ina abu ya ci tura. Idan na gaji da biyan kuɗin makaranta, kawai zan cire ta ta haɗa kai da Salma su riƙa talla.”

Waheeda ta yi saurin cewa,

“Eh wallahi Umma, dama haka kawai ki ka yi. Ni ma dama na gaji da makarantar nan. Gara kawai in fara soyar ƙosai a ƙofar gida.”

Daga Umma har Baba Karami, kallon Waheeda kawai suka tsaya yi cike da mamaki.

Nan take Baba Karami ya miƙe ya riƙo ta, sannan ya kai mata wani rankwashi mai zafi a tsakiyar kai.

“Wato ke yanzu kin zama isasshiya kenan ko? Yaushe ma kika fara makarantar har za ki ce kin gaji, za ki fara talla? Makarantar da ake tura ki ba gata ake miki ba. Yara nawa ne suke yawo a titi suna fatan samun damar karatu irin taki, amma saboda tsabar rashin ji da iya shege kina ɓata mata kuɗin makaranta da na tara. To za ki ci gidan ku kuwa”

Yana gama faɗin haka ya duba cikin ɗakin, sai ya hango tsohuwar igiyar cajin Salma. Nan take ya ɗauko ta ya fara zane Waheeda da ita.

“Dan Allah Baba Karami ka yi haƙuri, Ba zan ƙara ba. Umma dan Allah ki ce masa ya yi haƙuri. Wayyo Baffa na Ka zo ka ƙwace ni, Baba Karami zai kashe ni Yaya Ado”

Ta riƙa kwarara ihu,amma Baba Karami bai sake ta ba sai da ya mata lilis, ya ga bakin nata ya mutu, sannan ya rabu da ita.

Duk da ta ba Umma tausayi, sai dai ta yi biris da ita, domin ta san yar autarta sai da tsauri take jin magana.

Da Baba Karami ya fito tsakar gida, ya zuba wa Rabi da Ikilima ido. Su kuwa sun yi tsit a gefe kamar ba su san abin da ke faruwa ba. Tun da suka ji ana dukan Waheeda suka shiga taitayinsu, domin sun san idan ya gama da ita tabbas zai dawo kansu.

“Uban me ya hana ku zuwa makaranta?” ya jefa musu tambaya yana wurga musu mugun kallo.

Cikin sanyin murya Ikilima ta ce,

“Ba mu karya ba ne.”

Ya ce,

“Sai an karya ake zuwa makaranta? Wannan wanke-wanken da kuka tara ƙuda yana bi fa?”

Rabi ta ce a sanyaye,

“Ai yau wanke kwanukan Waheeda ne.”

“Ke zo nan!” ya kira ta.

Ta fito a hankali kamar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki.

Ya saka hannu cikin aljihunsa ya zaro naira ɗari biyu ya miƙa mata.

“Maza je ki sayo omo, ku haɗu ku wanke kwanukan nan, sannan ku wuce makaranta.”

Cikin sanyi ta karɓi kuɗin ta fita, su kuwa suka fara tattara kwanukan.

Duk Mama Sadiya da sauran ƴan gidan suna jin abin da yake faɗa, amma babu wacce ta kuskura ta ce komai, domin babu wanda bai shakkar Baba Karami . Yana da wani irin kwarjini da ke kashe musu duk wani tsaurin ido.

A daidai lokacin Salma ta shigo da ledar kamu da Umma ta aike ta saya. Ta gaishe shi tana ƙoƙarin sulalewa zuwa ɗakin Umma, sai ta ji ya kira ta.

“Jiya ke da wa na ga kuna hira?”

Ta ɗan matsa baya kafin ta ce,

“Amadu ne.”

Ya sake tambaya,

“Wane Amadu?”

Ta amsa cikin sanyin murya,

“Amadu ɗan gidan Malam Sani.”

Ya kalle ta ta gefen ido. Ita kuwa ta sunkuyar da kanta ƙasa, kirjinta na bugawa.

Zuwaira da ke gauraya ƙulun ƙosai kuwa addu’a kawai take Allah ya taimaki Salma kada Baba Karami ya ƙara magana, domin ya taɓa hana ta tsayawa da yaron, kuma duk sun san hakan.

Baba Karami ya ce,

“Yayi kyau. Zan je in same shi. Idan aurenki zai yi, ya fito kawai.”

Salma ba ta ce komai ba, ta juya ta shiga ciki tana sauke ajiyar zuciya.

Zama ya yi a kan jarka har suka gama wanke-wanken. Daga nan suka shirya cikin uniform ɗinsu na ƙaramar makarantar private da suke zuwa, su uku gaba ɗaya. A lokacin an gama dama kunu, an kuma zubawa kowa nasa a cikin kofi. Waheeda kuwa, duk da ta rantse babu wanda zai sa ta sha kunu, sai ga ta tana sha tana ta ɓata fuska saboda rashin jin daɗinsa.

Da suka tashi tafiya, ya ba su naira ɗari da hamsin kuɗin tara, sannan suka bar gidan. A hanya, Waheeda ba ta kula kowa ba domin har yanzu zuciyarta na cike da haushin dukan da Baba Karami ya yi mata.

Da suka isa bakin gate ɗin makaranta, mai gadi ya riga ya rufe ƙofar. Ya ce

“Na riga na rufe. Babu mai shiga yanzu.”

Waheeda ta turo baki ta ce

“Oho, Kar Allah ya sa ka buɗe. Ai ba ma son zuwa makarantar nan mu ke ba , takura mana kawai ake yi. Wallahi ba zan ƙara zuwa ba.”

Mai gadin ya girgiza kai kawai, domin ya saba da halinta da rashin kunyar da take yi kusan kullum.

Rabi ta ce

“Ah ah, ni dai babu ruwana. Wallahi gwara mu roƙe shi kawai ya bar mu mu shiga. In ba haka ba, idan mun koma gida Baba Karami zai soya mu da ran mu.”

Waheeda ta riƙe ƙugu 

“Aradu, Sai dai ya kashe ni, amma babu wanda zan roƙa. Tunda an rufe, gida zan koma ko kuma in je ruga in yi wasa da yaran Sulluɓawa. Ku dai idan za ku iya ku je ku roƙe shi.”


“Mu dai babu ruwanmu. Ki je ke kaɗai, ba za ki ja mana duka ba.” Cewar Iklima

Ta ƙarasa wajen mai gadi tana roƙonsa ya buɗe musu ƙofa.

A daidai lokacin wani malami ya zo zai shiga makarantar. Ya tarar da su suna ta roƙon mai gadi, Waheeda kuma tana gefe ta na faman kumbura baki.

Ya tambaya

“Me yake faruwa?”

Mai gadin ya amsa
“Sun yi latti ne, na ce su koma gida amma sun ƙi.”

Malamin ya dubi Rabi ya ce

“Ku garin yaya kuka yi latti, Rabi S. Baffah?”

Ta amsa a sanyaye
“Malam, da ƙafa muka zo kuma gidanmu yana da nisa.”

Sai malamin ya kalli mai gadi ya ce ya bar su su shiga, tare da yi musu gargaɗin kada su sake zuwa a makare.

Waheeda ba haka ta so ba, domin tana fata a hana su shiga gaba ɗaya. Amma da aka bar su suka shiga, kai tsaye suka nufi ajinsu na JSS 1B. Sun tarar da malamin Social Studies ya riga ya shigo. Suka yi excuse me sir, sannan suka shiga suka zauna.

Rabi da Ikilima suka fito da littattafansu suka fara kwafin rubutun da ke jikin allo, tare da mayar da hankali ga bayanin malamin.

Malamin yana koyarwa cikin nutsuwa domin ɗalibansa su fahimta. Nan idonsa ya sauka kan bencin baya, inda Rabi da Waheeda suke zaune. Ya ga Waheeda kawai ta zuba masa ido tana kallonsa da manyan idanunta ba tare da ta rubuta komai ba.

Ya ce

“Waheeda S. Baffa, stand up!”

Nan take duk yaran ajin suka juya suna kallonta.

Waheeda ta miƙe tsaye tana hararar sauran ɗaliban saboda yadda suka mayar da hankalinsu kanta.

Cikin nutsuwa malamin ya ce,

“Kina ganewa kuwa?”

Ta amsa ba tare da ɓata lokaci ba,

“Eh Malam, ina ganewa.”

Ya ɗan yi murmushi ya ce,

“Very good, Mu ga littafin Social Studies ɗinki.”

Waheeda ta janyo jakarta, ta buɗe ta, sannan ta fito da littafin ta ɗora a saman desk.

Uncle Abba ya zuba mata ido cike da mamaki, har ya rasa kalmar da zai furta. Duk ɗaliban ajin sun fito da littattafansu suna rubutu tare da mayar da hankali, amma ita ko alama babu. Tun da yake zuwa ajin ya lura cewa ba ta taɓa fito da abin rubutu ba, sai dai ta zuba masa manyan idanunta tana kallonsa kamar mai son gano wani sirri a jikinsa.

Da farko abin bai dame shi ba, amma daga baya ya tambayi sauran malamai game da halinta. Sai suka tabbatar masa cewa haka take a duk darussansu. Sun yi mata duka, sun yi mata faɗa, amma babu abin da ya canja. Sai dai ta zauna tana kallon allo kamar mai fahimtar komai, amma idan aka tambaye ta sai ta kasa ba da amsa. Har ma malaman Staff Room suka yanke cewa Waheeda ita ce mafi raunin fahimta a ajinsu.

Ya karɓi littafin ya fara buɗewa. Abin farko da ya ci karo da shi ya sa ya ɗago ya kalle ta da mamaki.

Waheeda ta turo baki ta kauda kai gefe tana ta zunbure-zunbure.

Duk shafin da ya buɗe sai ya tarar da zane-zane iri-iri marasa ma’ana. Ya girgiza kai cikin takaici, sannan ya koma kusa da allo inda kujerarsa da wayarsa suke.

Ya ce,

“S. Baffa, come here.”

Ba ta fito ba sai da ta ce,

“Dalla ku daina kallona, Kun wani kura min ido kamar mayu. To aniyar moɗa ta bi randa… tuf! tuf! tuf!”

Ta faɗa tana taku zuwa gaban allo.

Ya umurce ta da ta durƙusa, sannan ya ci gaba da koyarwa. Bayan kusan mintuna talatin ya gama, sai ya dubi monitor na ajin ya ce,

“Je JSS 3 ki karɓo min bulala a wurin Uncle Sani.”

Ba ta jima da fita ba sai ga ta ta dawo ɗauke da wata zabgegiyar bulala ta miƙa masa.

Ya karɓa ya ce cikin fushi,

“Wato kun ɗauke mu marasa aikin yi ne saboda muna bata lokacinmu muna koyar da ku? Muna koyar da ku ne domin ku inganta rayuwarku, amma saboda hatsabibanci har akwai waɗanda ba sa mai da hankali, suna ta zane-zane a littafi”

Ajin gaba ɗaya ya yi tsit, kamar babu ko mutum ɗaya.

Ya ci gaba da cewa,

“Ko da ita kaɗai ce mai wannan halin, ba zan lamunta ba. Zan yi amfani da ita a matsayin darasi ga sauran ɗalibai.”

Da ta ga ya nufi inda take, sai ta miƙe tana ta rantse-rantse.

“Na rantse da Allah, Uncle, ba zan ƙara ba. Allah fatana baya son bulala. Don Allah ka yi haƙuri, kar ka duke ni.”

Ya ce yana warware bulalar,

“To me yake hana ki yin rubutu?”

Nan take hawaye suka cika mata ido ganin kaurin bulalar, kasancewar igiyar engine ce. Ta san idan ta sauka a jikinta, ba za ta manta da ranar ba.

Ya sake tambaya,

“Faɗa min, me yake hana ki yin rubutu?”

Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya ta ce,

“Ban iya ba.”

Nan take ɗaliban ajin suka fashe da dariya.

Har Uncle Abba sai da ya yi murmushi a ɓoye, sannan ya ce,

“Au, ba ki iya rubutu ba amma kin iya zana shirme? Iyayenki suna biyan kuɗin makaranta domin ki yi karatu ki sanya su alfahari, amma ke kin mayar da littafi wajen zane-zane marasa amfani.”

Cikin marairaicewa ta haɗe hannayenta a cikin hijabi ta ce,

“Ba zan ƙara ba, Malam. Idan na sake, ka yi min bulala dari da hamsin.”

Ya ce,

“To na ji. Ba zan dake ki ba, amma sai kin tsaya a gaban aji ki yi bayanin abin da na koyar yau, kuma sai ɗaliban ajin sun gamsu da bayaninki kafin zan kyale ki.”

A wannan karon dariyar da ajin suka yi ta fi ta farko. Kowa ya san babu ɗalibin da ya fi Waheeda rashin fahimta a ajin. Don haka ta yaya za ta iya bayanin darasin da ita kanta ba ta fahimta ba?

A bakin ƙofar ajin kuwa Principal tare da wata malama suna tsaye. Sun zo wucewa ne, amma ganin abin da ke faruwa ya sa suka tsaya suna kallon wannan ban dariyar da ke tsakanin Waheeda da Uncle Abba.

Waheeda ta sunkuyar da kai cikin sanyi ta ce,

“Uncle… ban iya ba. Ban gane komai ba.”

Cikin son tsorata ta ya matsa gare ta kamar zai dake ta, yana cewa,

“To ai kuwa dole ki sha bulala yau, tunda ba kya jin magana.”

Waheeda ta runtse idanu, sannan ta saki wani irin ihu kamar mai tashin aljanu.

“Wayooooooo! Umman Salma da Waheeda! Za a dakar miki ƴa da bulalar da ake dukan jakuna”