Matukar Ina Raye 3
by @mrsisham12
MATUKAR INA RAYE
(As Long as i’m alive)
Writer — MRS ISHAM
*** whatsapp.
Page 03
Sake da baki da hanci Uncle Abba ya tsaya kallanta, jin uban ihun da ta ratsa tamkar wacce ta ga mutuwa. Yau ya ga ikon Allah da idonsa. Tun da yake, bai taɓa ganin iya shegenta da malamai suke magana a kai ba sai yau. Ya dai san ba ta da kunya, amma bai san abin nata ya kai haka ba.
Har da ɗora hannu a ƙirji ya ce,
“Yau ko kukan jini za ki yi sai kin yi bayanin nan. In kuma ba haka ba, to tabbas kina ƙara wa kanki hukunci ne da kanki. Da farko na yanke bulala hamsin zan miki, amma idan kika kuskure na ƙirga biyar ba ki fara ba, to kin ja wa kanki bulala har ɗari… Ɗaya!”
Ya soma ƙirgawa, yana kai wa biyar cif ya tsinci Waheeda tsaye a gaban aji, daidai inda yake tsayawa idan zai musu bayani. Ta ɗan yi mui-mui da baki kamar mai son yin magana, daga bisani ta fara bayani cikin tsantsar Turanci ba tare da tangarɗa ba.
Da ta kammala, sai ta ɗan ja numfashi saboda tsawon bayanin da ta yi, sannan ta ɗora da Hausa,
“Bari in muku ƙarin bayani yadda za ku fahimta. Iyali na nufin rukuni na mutane da ke zaune tare, wato iyaye da ‘ya’yansu.
Gida shi ne ginshiƙi, shi ne asali, shi ne makaranta ta farko. Idan gida ya gyaru, al’umma ba za ta lalace ba.”
Ba iya Uncle Abba ba, har Principal da malamar sun girgiza da Waheeda. Fuskokinsu cike suke da mamaki da al’ajabi. Sun kasa yarda wai Waheeda ce ta yi bayanin duk abin da aka koyar da su. Ba su yi tsammanin haka daga gare ta ba, domin duk wanda ya santa ya san wacece Waheeda a cikin makaranta. Tofa, ya san katuwar dakikiya ce wadda ba ta gane komai.
Ashe kuwa a zahiri ba haka abin yake ba. Suna mata kallon biri ne, alhali tana musu na ayaba.
Kusa da ita Uncle Abba ya matso, har lokacin mamakin bai gama sake shi ba.
“Waheeda, wa ya koya miki duk wannan?”
Cike da tsiwa ta furta,
“Wa zai koya min in ba kai ba? Duk abin da ake yi a cikin aji na iya komai, kuma na san komai. Kawai dai ban cika maida hankali ba. Ni ba na son rubutu. Makarantar ma a dole nake zuwa. Na fi son in fara soya kosai a ƙofar gidanmu ina samun kuɗi.”
Sai ta kira shi a marairaice,
“Dan Allah ka sa a kore ni a bokon nan. Ni ba ƙaunarta nake ba.”
Murmushi Uncle ya yi. Principal kuwa ya girgiza kai, domin ya fahimci cewa idan ba a ɗauki mataki da wuri ba, tabbas za ta wargaza rayuwarta da kanta. A yanzu ya fahimci tana da wata irin baiwa, amma idan ba ta samu tsayayyen mutum da zai tsaya mata ta yi karatu ba, to rayuwarta za ta durƙushe. Ga shi ita da bakinta ta faɗa cewa ta fi son fara soya kosai fiye da zuwa makaranta, kuma maganar ta fito ne daga ƙasan zuciyarta.
Karasa shigowa ajin Principal ya yi. Nan take ɗaliban suka miƙe tsaye, suna haɗa baki wajen cewa,
“Good morning, Sir. We’re happy to see you. Welcome to JSS One.”
Murmushi ya yi musu, sannan ya ce su zauna. Bayan sun zazzauna ne ya dubi Waheeda, daga bisani ya maida kallonsa kan su Ikilima.
“Idan kun koma gida, ku sanar da Yayanku ko kuma mahaifiyar Waheeda S. Baffa ana nemansu a makaranta gobe.”
Cikin ladabi Ikilima da Rabi suka amsa da,
“To, Sir.”
Abin da ya sa Principal ya yi haka kuwa shi ne, ya san idan ya ce Waheeda ta kira masa ’yan gidansu, to fa ba za ta taɓa kiran su ba.
Juyawa ya yi ya fita.
Uncle Abba ya dubi ajin ya ce,
“Okay class, sai mun haɗu gobe. Yanzu malamar English ɗinku za ta shigo. Waheeda S. Baffa, go and sit down.”
Waheeda, da ta cika tana batsewa tun lokacin da Principal ya ce yana son ganin iyayenta, ta haɗe rai tana jan tsaki a ƙasan ranta. Ta wuce gurin zamanta ta zauna. Su Rabi kuwa sai magana suke yi mata, amma ita ko kallon arziki ba su samu daga gare ta ba.
Ƙarfe sha ɗaya aka buga bell ɗin fita break. Kuɗin da Baba Karami ya ba su ne suka nufi wata matashiyar budurwa da ke zaune a bakin gate tana siyar da awara. Robar awararta na gabanta, ga yara sun yi mata caa suna dafifi.
Da suka isa wajen, Ikilima ta yi saurin cewa,
“Kam buuu… wannan uban layin ma za mu samu siyan awarar nan kuwa? Ki ga yaran nan kamar wasu mayu, duk sun wani dabaibaye ta.”
Rabi ta dubesu ta ce,
“To mu haƙura kawai mu je mu siya wani abin mana. Mu ma ai ba dole ba ne sai awara za mu ci ba. Ga can mai siyar da wainar fulawa, ga kuma kankarar kuka.”
Waheeda ta galla mata uwar harara.
“Ke, idan su za ki siya, ga nan hanya. Mu kam awara za mu ci. Bari ma ki gani.”
Tana gama faɗin haka ta fara dube-dube. Ai kuwa cikin sa’a ta hango wata matacciyar kadangare da ta mutu har ta soma kumbura. Leda ta sanya a hannunta, sannan ta je ta ɗauko kadangaren.
A firgice Rabi ta yi saurin cewa,
“Waheeda, me za ki yi da wannan mushen kadangaruwan?”
Wani irin mugun murmushi ta yi da ya kawata fuskarta.
“Yarinya, tsaya ki sha kallo.”
Yaran ta nufa. Ta samu bayan wata yarinya da ke bin layin siyan awara, ta aza mata mushen kadangaren a bayanta. Daga nan ta ja baya, ta runtse idanunta, sannan ta fasa wani uban ihu kamar wacce ta ga dodo.
“Wayyo! Ga kadangare a jikinku! Sun mamaye ku!”
Ai, kan kace kwabo, yara suka fasa ihu suka fara gudu. Cikin ƙanƙanin lokaci wajen ya rikice, kamar wani mugun abu ne ke faruwa. A garin gudun, wasu sai faɗuwa suke yi a kan junansu.
Yarinyar da Waheeda ta ɗora wa kadangaren kuwa, tana taɓa bayanta ta ji wani abu. Wani irin ƙara ta sanya, sannan ta zube ƙasa sumammiya. Babu wanda ya bi ta kanta; kowa ta kansa yake a garin gudun.
A cikin ruɗanin ne aka yi ball da robar mai awara, awarar ta watse a ƙasa gaba ɗaya.
Su Waheeda na ganin haka, suma suka shiga cikin masu gudun. Daga nan suka arce zuwa aji.
Rabi, da ta gama tsorata, ta ce,
“Yau mun shiga uku, mun lalace! Ni dai Allah yana gani babu ruwana. Waheeda ce silar komai. Yanzu ki ga hatsaniyar da kika tayar, dan kawai kina son ki ci awara. Gashi kin sa kanki a bala’i.”
“Kanmu dai, ai har da ku.” Ta faɗa tana harararta.
Zaro ido duka su biyun suka yi, jin abin da ta faɗa.
“Kar ki mayar da mu ’yan iska. Mu muka ce ki ɗauki mushen kadangare ki ɗora wa yarinya? Ga shi ta faɗi, kila ma ta mutu.” Ikilima ta faɗa tana ɗaukar jakarta.
Su ma suka ɗauki nasu jakunkunan, suka bi ta hanyar baya wadda aka hana bi. Duk da an toshe ƙofar, haka suka kama ginin suka tsallaka, domin ginin bai da tsayi sosai, shi ya sa ba ya ba ɗalibai wahalar hawa.
Haka suka wuce gida suka bar makaranta, ba tare da sun san abin da zai biyo baya ba.
“Kai! Ina za ku je?”
Suka ji muryar wani namiji daga bayansu.
A tare suka juya, suka ga seniorsu ne, ɗan SS3, cikin uniform, hannunsa riƙe da bulala.
Ganin sun yi shiru ne ya sa ya ce,
“Kun yi shiru? Ina za ku je bayan lokacin tashi bai yi ba?”
Waheeda ta ce,
“Kabeer, don Allah ka rufa mana asiri. Na maka alƙawari, gobe zan kawo maka sabuwar bulala.”
Jin haka, Kabeer ya fahimci akwai abin da suka aikata, domin shi yanzu yake hanyar zuwa makarantar, saboda su ’yan zuwan rana ne.
“Me kuka yi?”
Da sauri Rabi ta ce,
“Me ta yi dai, mu babu ruwanmu. Duk ita ce ta ja wannan abin…”
Nan ta ba shi labarin komai.
Da mamaki yake kallonta, amma ganin yadda ta marairaice masa ya sa ya ji tausayi. Sai dai dole ya tsoratar da su, saboda gaba kada ta ƙara aikata irin abin da ta yi yau.
“Wai me ya sa ba kya ji ne, S. Baffa? Yanzu in yarinyar nan ta mutu, kin san ke ma kashe ki za a yi ko?”
Waro idanu Waheeda ta yi.
“Ni wallahi ban yi mata komai ba. Kawai dai na ɗora mata shi a saman himarta ne.”
“Hmmm… Ni dai na faɗa miki. In yar mutane ta mutu, to ke ma har gida za a zo a ɗauke ki da motar ’yan sanda, sojoji da manyan bindigu. Ko station ba za a kai ki ba, kai tsaye za a bindige ki a ƙofar gidanku.”
“Innalillahi!”
Tsabar tashin hankali, sai da Waheeda ta ji fitsari na neman zubo mata.
“Shikenan… tawa ta ƙare. Ni ma yanzu mutuwa zan yi. Kabeer, aradu, ban yi niyyar kashe ta ba. Ikilima, ai ke ma shaida ce ko?”
Ta faɗa a gigice tana kallon su Ikilima, waɗanda su ma zuwa yanzu hankalinsu ya tashi sosai, jin kalmar mutuwa da Kabeer ya ambata.
Ganin yadda Waheeda ta tsorata ne ya sa ya ce,
“Kar ki damu. Zan rufa muku asiri. Yanzu zan je makarantar, duk yadda ake ciki zan zo har gida in faɗa muku. In kuma gaskiya ta fito… to fa manyan motocin ’yan sanda ne za su zo su kwashe ku.”
Daura hannu a kai ta yi, sharrr! Sai ga hawaye wiwi suna zarya a fuskarta.
“Senior Kabeer, yanzu in suka kashe ni, ba zan sake kallon Ummanmu ba ko?”
Kai ya gyaɗa mata, tare da zaro farin handkerchief daga gaban rigar uniform ɗinsa ya ba ta, yana kallon fuskarta.
“Goge hawayenki. Yanzu ku tafi gida, zan je in ga me ke faruwa a can. Amma fa…”
Ya dakata da gangan domin ya ƙara daga musu hankali.
“Ku kasance a shirye.”
Yana gama faɗar haka ya juya ya tafi, yana dariya shi kaɗai. Yadda dukkansu suka shiga damuwa abin ya ba shi dariya, musamman ma Waheeda, wadda idanunta da hancinta suka yi jawur sosai.
Kamar wasu munafukai haka suka shigo gidan. Ko sallama babu. Kallo ɗaya za ka musu ka san akwai abin da ya dame su, musamman ma Waheeda, domin kowa ya san ba kasafai take yin shiru ba. Ko rashin lafiya take yi, da ƙyar bakinta yake mutuwa.
Umma na zaune a tsakar gida. Ta ɗago ta dube su, sannan ta danna wayarta ta duba lokaci, domin ta san sai ƙarfe biyu suke tashi.
“Kai, ya aka yi kuka shigo gida ko sallama babu? Kuma yanzu ba ƙarfe biyu kuke tashi ba?”
Salma ta tambaye su tana riƙe da buta, domin yanzu ta fito daga bandaki.
Shiru suka yi mata, kamar ba da su take magana ba. Daga bisani ma, Waheeda ta shige ɗakin Umma, ta bar su a tsaye bakin buɗe.
Mama Sadiya ce ta dubi ’yarta.
“Rabi, kar ki bari in taso in same ki tsaye a nan kamar dusa. Ana muku magana kuna yi wa mutane banza. Me ya same ku? Duk kun dawo kamar kajin da ƙwai ya fashe wa a ciki?”
Kafin Rabi ta buɗe baki, Ikilima ta amsa,
“Mama Sadiya, mai gadin makarantar mu ne ya rasu.”
“Allah Sarki. Allah Ya jiƙan sa da rahama. Ai yadda kuka shigo sai kuka daga wa mutum hankali.”
Umma ta faɗa tana miƙewa, ta bi bayan Waheeda, Salma kuma ta biyo mata baya.
Tun daga bakin ƙofa suke jin sheshsheƙar kukanta.
Da mamaki suka kalli juna kafin suka zauna kusa da ita.
Umma ta ɗago ta zaunar da ita.
“Mamana, me kuma ya sa ki ke kuka? Ko don rasuwar mai gadin makarantar taku ne? Addu’a ya fi buƙata, ba kuka ba. Kin ji ko?”
Rungume Umma ta yi, ta ci gaba da kuka tana cewa,
“Umma, ni bana son barinki. Bana son mutuwa.”
“Wata sabuwa, in ji ’yan caca.”
Salma ta faɗa tana dariya.
Murmushi Umma ta yi jin abin da ta ce. Ta manta yaushe rabon da ta ga Waheeda a irin wannan yanayi. Tun wani zazzabi mai zafi da ta yi har take sambatu tana kuka, sai kuma yau.
“In sha Allah ba za ki mutu yanzu ba. Sai kin yi aure, kin haihu, har kin tsufa. Kin ji ko?”
Murya a sanyaye ta ce,
“To…”
“Yawwa, yar albarka. Yanzu tashi ki cire kayan makarantarki ki saka wasu. Dazun Salma ta wanke miki kala uku, ga su can kan igiya. Sai ki zo ki taya ni gyara waken suya da za a yi awarar yau.”
“Ummanmu, Adda Salma ta dauko min bibbiyu nake gani.”
“Ai ko million-million kike gani sai kin dauko kayanki. Ban da iskanci! In miki ciki, in miki zanin goyo, ai dadin sai ya miki yawa.”
Salma ta fada tana harararta.
“Yi hakuri ki dauko mata, ba ki ga yadda yau ta koma ba?”
“Wallahi Ummanmu, ke ce kike sangarta yarinyar nan. Shi ya sa take duk wani iskancin da take so.”
Ta karasa maganar tana fita daga dakin.
Ganin yadda Waheeda ta sunkuyar da kanta, ta kafe wandon makarantar tata ido, ya sa Umma ta fara zarginta. Haka kawai ta ji zuciyarta na bata akwai wani abu da take boye mata.
Cike da dabara ta ce,
“Yau babu neman Toskana kenan? Ko ke fa ki dinga nutsuwa. Kar ki bari ana kawo karar ki gida. Ki kame kanki, ki zauna babu ruwanki da kowa sai wanda ya kama. Ko dai kin yi wani abu ne, Mamana? Fada min.”
Da yake Allah ya zuba mata dan banzan wayo, ta san sarai Umma na son ta sha ruwan cikinta, sai ta yi saurin cewa,
“Ni yau babu wanda na tsokana. Ko su Rabi ki tambaya.”
Umma ta zuba mata ido na wasu dakiku kafin ta ce,
“Kin tabbata? Domin na san halinki sarai. Mutuwar mai gadin makarantarku ba za ta kashe miki jiki har haka ba. Sai dai ko akwai wani abin da kika yi, tsoro ya kama ki. In akwai, gara ki fada mini gaskiya tun yanzu, in san inda zan bullowa lamarin.”
“Kai Umma, ni fa gaskiyata kenan na fada miki.”
Tana gama fadin haka ta koma ta kwanta.
“To, ja’ira, sai ki tashi ki sa kayanki, ki bar mini dakina.”
Tana gama fadin haka ta fice, ta bar Waheeda ita kadai a dakin.
Salma na shigowa ta watsa mata kayanta tana nuna ta da yatsa.
“Wallahi ki shiga hankalinki da ni a gidan nan. In ba haka ba, sai na ja Baba Karami ya miki tsinannen duka.”
Ko ci kanta Waheeda ba ta ce mata ba har ta gama ta fita.
Ta canja kayanta, sannan ta fito cikin gidan ta zauna kusa da Umma. Ta sa hannu ta fara tayata gyara waken.
Don’t forget to comment and like 🥰❤️