MATUKAR INA RAYE

Matukar Ina Raye 4

by @mrsisham12

MATUKAR INA RAYE
(As Long as I’m alive)


Writer — MRS ISHAM
                 *** whatsapp.


Page 04


Aiki take taya Ummanta, amma gabaɗaya a tsarge take. Duk ta ji dirin mashin ko mota sai ta tsorata. Ba ma ita kaɗai ba, hatta su Ikilima duk a tsorace suke. Gani suke yi za a zo har gida a kwashe su.

Umma na lura da su, magana ne kawai ba ta yi ba, domin ta san Waheeda da shegen musu kamar boka. Ko a shekara tana tambayarta ba za ta taɓa gaya mata gaskiya ba. Gara ma su Rabi, idan suka ji matsa za su yi magana. Amma banda Waheeda kam. Da zarar ta fara ƙarya tana rantsewa, kai ka ce zallar gaskiya ce ke fita daga bakinta.

Kowa yana gyara kayan sana’ar da yaransa za su fita da su. Babu wanda yake kula wani, kowa harkar gabansa yake. Kasancewar Baffah ya sakar musu komai kamar ba shi ne ya ajiye su ba, ya sa duk suke neman kuɗi sosai yadda za su rufa wa kansu asiri.

Kowa na yin abin siyarwa ya ba ɗansa da safe su tafi bakin hanya su sayar da kosai da kunu. Da rana kuma awara, sai dare wasu su yi awara, wasu kuma doya da sauran su. Duk wanda ya kasance ranar girkinta ce, ita ce za ta yi cefane da kuɗinta ta ciyar da gidan, har ma da shi kansa Baffah.

Yaran gidan gaba ɗaya suna talla, amma Umma ta ƙi fir. Ta ce tana so Waheeda ta yi karatu sosai. Ba ta so a ce Salma ta kakare, Waheeda ma ace haka ta kasance da ita. Tana da burin Waheeda ta yi karatu mai zurfi. Shi ya sa ta cire ta daga makarantar gwamnati ta mayar da ita makarantar private.

Ganin haka da su Mama Sadiya suka yi, sai su ma suka mayar da yaransu makarantar private ɗin.

Karar fakawar babur suka ji a ƙofar gidan.

Zuwaira ta ce,

“Laaa, dama yanzu nake maganarsa a raina. Wallahi yau duk bai leƙo gidan ba.”

Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo yana murmushi. Har ƙasa ya gaishe da su Umma. Bayan ya miƙe ne ya zauna. Su Rabi suka gaishe shi, yana amsawa yana kallon fuskar Waheeda da ya hango damuwa ƙwarai a kanta.

“İkon Allah, Umma! Yau kuma me yake damun wannan rigimammiyar ’yarki?”

Taɓe baki Umma ta yi tana surfa waken suyar, ta ce,

“Ado ai ka fi kowa sanin halinta. Babu abin da aka mata. Iskancinta ne kawai ya motsa, take ta haɗe rai kamar wata gunki.”

Dariya Zuwaira da Salma suka sanya jin Umma ta ambaci “gunki”. Shi kansa Ya Ado sai da ya murmusa kafin ya ce,

“Hajiyar rigima da bakin hali, yau kuma me aka yi miki?”

“Yaya Ado…”

Ta kira sunansa a sanyaye.

Sharrr… sai ga hawaye ya fara zarya a fuskarta.

Cikin maida hankali a kanta ya ce,

“Tashi ki zo. Zo ki faɗa min, wane isashen ne ya taɓa ki yanzu nan? In ba sa kashi.”

Tana zuwa kusa da shi, ta ƙara volume ɗin kukanta.

Da mamaki duk suka zuba mata ido.

Cike da takaici, Mama Jamila ta doka tsaki.

“Allah dai ya wadaran naka ya lalace! Wai in ba sarganci ba, ina wannan katuwar da kukan banza? An sangarta yarinya sai iya shege take tsulawa mutane. Ku dai bi a hankali, kar ta kwaso muku abin da ba za ku iya ba.”

Duk da Umma ta ji zafin maganarta sosai, sam ba ta nuna ko a fuskarta ba. Sai ma aikinta da take yi, ba ta ko ɗago ta kalle ta ba, balle ta tanka mata.

Tana jin zafin abin da suke aikata mata. Tana jin zafin yadda suke aibata mata yara, musamman Waheeda, wadda duka-duka ba ta wuce shekara goma sha uku ba. Ta rasa me yarinyar ta tsare musu da ko da yaushe ba sa taɓa faɗin alheri a kanta, sai sharri da munanan kalamai.

Da yake Umma ta kasance mace mai matuƙar haƙuri, ba ta taɓa tanka musu ba. Domin ta yarda cewa wata rana komai zai zama labari.

Ya Ado, da bai ji daɗin abin da Mama Jamila ta faɗa ba, ya ce,

“Haba Mama Jamila, wannan wani irin magana ne? Duka nawa Waheeda take? Komai take yi, duk cikin yarinta ne. Nan da wasu shekaru, ko an ce ta yi, ba za ta yi ba.”

“Sai kuma kai kanka ake ji wai mahaukaci ya hau kura.”

Ta faɗa tana barin gurin.

Ya girgiza kai yana jin babu daɗi a ransa. Ya san dole Umma ta ji zafin maganarta, amma da yake tana da kawaici ba ta nuna ba. Ya rasa yaushe gidansu zai zama kamar sauran gidajen da ake zaman lafiya. Ya rasa yaushe ne su Mama Jamila za su watsar da makaman yaƙinsu da kuma gaba da suka ɗauka da Umma.

Zaro kuɗi ya yi daga aljihunsa, naira ɗari biyar.

“To ya isa, dena kuka. Ga shi, ku je ku sayi abin da ku ke so, ku kawo min canji.”

“Kul Ado, dan Allah ku daina ba yaran nan kuɗi a haka. Kar ku ɓata su da son kuɗi. Yau da safe ma Baba Karami da ya shigo sai da ya ba su kuɗi.”

Murmushi ya yi ya ce,

“Au Umma, dama Sadam ya zo gidan nan da safe? Ai da na sani da na zo. Kin san fushi yake yi da ni saboda na ce ina son kanwar matarsa.”

’Yar dariya Umma ta yi tana girgiza kai.

“Allah ya shirye ka, Ado.”

“Yaya Ado, wallahi kuna mana wariyar launin fata a gidan nan. Rabon da ka ba ni kuɗi har na manta. Ku dai su Rabi kawai kuka sani.”

Cewar Zuwaira.

“Katuwa dake ni ne zan ba ki kuɗi? Tabb! Za ki shekara kuwa. Ikilima, tashi ki samo canji, sai ku ɗauki naku ku ba ni sauran kuɗina.”

“To, Ya Ado.”

Ta faɗa tana fita.

Cikin ƙasa-ƙasa da murya, yadda ita kaɗai za ta iya jinsa, ya ce,

“To yanzu faɗa min. Na san haka kawai yau ba za ki yi irin wannan nutsuwar ba. Dole akwai lauje cikin naɗi.”

Sai da ta dubi inda Umma take, ta ga hankalinta ba ya kansu, sannan ta ce,

“Ya Ado, za a zo a kama mu. Shikenan, kashe mu za a yi.”

Waro ido waje ya yi da mamaki.

“Waye zai zo ya kama ku? Me kuka aikata?”

“Assalamu alaikum.”

Ɗago kai suka yi suna kallonsa, domin babu wanda ya san da shigowarsa sai sallamar da suka ji.

Ai tuni ta fara tsilli-tsilli da idanu tana mannewa kusa da Ya Ado, domin ganin fuskarsa da ta yi ma sai da ta ji ’yan hanjinta suka kaɗa.

Sama-sama ya gaishe su, sannan ya miƙa wa Ya Ado hannu suka gaisa. Yana harararsa, shi kuma Ya Ado yana masa dariya, saboda ya san hararar ta mece ce.

“Meye na ga wannan uwar kiriniyar ta wani nutsu a gefenka? Ko wani abu ta yi?”

Baba Karami ya faɗa yana jawo jarkan ruwa da ba komai ya zauna.

“Ah ah, babu ruwanka da ita. Hira muke yi, tana ba ni labari ne. Kar ka sa mana ido.”

Tsaki ya ja, ya dubi Umma ya ce,

“Baffah bai shigo gida ba ne?”

Ba tare da ta ɗago ba ta furta,

“Rabon sa da gidan nan tun safe. Da ya yi karin kumallo ya fita.”

Gyada kai ya yi, bai kuma cewa komai ba. Ya miƙe ya shige uwar ɗakin Umma.

Ganin haka ne ya sa ta fahimci yana son magana da ita ne a keɓance, bayansa ta bi.

“Yar Autar Umma, faɗa min su waye za su kama ku ɗin?”

Ya Ado ya kuma tambayarta, ganin yanzu daga shi sai ita ne babu mai jin su, tunda su Mama Sadiya duk ayyukansu suke yi.

Waheeda ta ce,

“Yau ne a makaranta kadangaruwa ya hau jikin wata yarinya, shi ne muka gudo gida.”

Zuba mata ido Ya Ado ya yi yana bin ta da kallon tuhuma. Ya san wacece Waheeda wajen neman magana. Tun yana jin maganar ya fahimci ita ce ta sa wa yarinyar kadangaren a jiki. In ba haka ba, ina ruwanta da guduwa?

Cikin sake kwantar da murya ya ce,

“Faɗa min gaskiya, ko dai kece kika sa mata?”

Ko rufe bakinsa bai gama yi ba ta daga murya tana cewa,

“In ni ce Allah ya tsi—”

Da sauri ya sa hannu ya toshe mata baki, ganin su Mama Jamila sun dawo da hankalinsu kansu saboda ɗaga muryar da ta yi.

“Dallah malama! Matsalata da ke ba a sirri da ke, mtsssw.”

Dariya Zuwaira ta sanya ta ce,

“Lallai Ya Ado, in dai sirri za ka yi da Waheedatu, ai gara ka je masallaci ka ɗauko speaker kawai ka faɗi abin da za ka faɗa.”

Ya murmusa.

“To kin ji ai, kowa ya shaide ki. Ke mace ce, ya kamata ki iya riƙe sirri, kin ji ko?”

Kamar da gaske ta gyada masa kai.

Baffah ne ya shigo gidan, hannunsa ɗauke da asuwaki. Gyaran murya ya yi yana nufar ɗakinsa.

Ya Ado ne ya gaishe shi, sai a sannan ya ankara da shi.

“Ah ah, Ado! Kai ne ka shigo kenan? To ya kasuwa?”

“Alhamdulillah, Baffah.”

Baffah ya yi murmushi ya ɗan tako zuwa gare shi. Ya Ado yana ganin haka ya san me Baffah yake buƙata, amma bai motsa ba sai da ya iso ya furta,

“Ado, ya kasuwar dai?”

Ya kuma tambayarsa a karo na biyu.

“Lafiya lau.”

Ya ba shi amsa yana ƙoƙarin danne dariyarsa.

“To madallah. Sannu Ado. Na ce ko zan samu na sayi goro a wurinka. Rabona da kuɗi ya fi sati, wallahi.”

Salati Mama Jamila ta rafka ta sake abin da take yi, ta miƙe tana tafa hannu.

“Gaskiya Baffah, ka ji tsoron Allah. Har kana rantse rabonka da kuɗi ya fi sati? Shi dubun da ka ba Gimbiyar taka yau, sata ka yi ko kuma tsintarsa ka yi a ɗakinka?”

Nuna ta ya yi da yatsa yana cewa,

“Wallahi Jamila, hawainiyarki ta kiyayi ramata. Zan ci mutuncinki fa! Wai saboda kina min baƙin ciki, ɗana zai ba ni abin arziki, da yake ke ba ki gaji arzikin ba, kina so ki hana ta? Tirr da muguwar halinki!”

Cokalo ɗaurin ɗankwalinta ta yi ya dawo gaban goshinta.

Ta ce,

“Ai dama ita gaskiya ɗaci gare ta. Sai in rasa da wa zan yi baƙin ciki sai da kai. Me kake da shi, me na sama ya ci balle ya ba na ƙasa? Ko ka manta kowa ciyar da kansa yake yi a gidan nan?”

Ganin za su iya tayar da faɗa har ya jawo hankalin maƙwabta, shi kuma ba ya so, sai ya yi saurin fito da naira ɗari biyar daga aljihunsa ya ce,

“Dan Allah Baffah, ka yi haƙuri ka rabu da Mama.”

Washe baki Baffah ya yi ya sa hannu ya karɓa.

“Ahhh! Allah ya yi albarka. Wannan abar arziki haka. To sannu Ado, godiya nake.”

Yana gama faɗin haka ya wuce ɗakinsa.

Girgiza kai Umma da Baba Karami suka yi, domin duk abin da suke faɗa suna jinsu daga cikin ɗakin.

Mama Jamila kuwa, in ba mita ba babu abin da take yi. Takaicinta shi ne Baffah bai biye mata sun yi ta daddaga jijiyoyin wuya ba. Sai ta ci gaba da surutunta ita kaɗai, babu wanda ya kula ta. Daga ƙarshe ta gaji ta yi shiru.

Ita kuwa Waheeda, duk abin da ake yi ta zuba musu ido ne kawai. Ta nutsu kusa da Ya Ado kamar wata ƙwarai. Ita kaɗai ta san me yake damunta. Amma duk da haka, duk lokacin da suka haɗa ido da su Ikilima, sai ta galla musu uban harara, kamar su ne suka sa ta aikata abin da ta yi.

An gama gyara waken suya. Har Salma ta kai niƙa ta dawo. Ana yayyankawa kenan suka ji ana doka sallama a ƙofar gida.

Dama haka gaban Waheeda ya buga. Haka kawai ta ji hankalinta bai kwanta ba da wannan sallamar da ake yi.

Ya Ado ne ya miƙe zai je, sai Baba Karami ya ce,

“Bari in ga waye yake wannan sallamar kamar yana bin mutane bashi.”

Ya fita ƙofar gidan.

Jim kaɗan sai ga shi ya shigo yana wurgawa Waheeda mugun kallo.

Ya nuna ta da yatsa.

“Wannan yarinya! Wannan yarinya! Anya Umma ba aljana kika haifo ba kuwa?”

Da Umma ta ji haka, ta san ta sake tsakulo mata wata fitina ce. Sai kawai ta zuba mata ido tana kallon yadda take wurwurga ido kamar wacce ta yi wa sarki ƙarya.

A hankali ta furta,

“Waheeda, me kika yi?”

Shiru ta yi tana kallon su Rabi.

Ganin haka ne ya sa Umma ta dubi su Rabi, su ma duk a tsorace suke.

“Rabi, me kuka yi?”

“Umma wallahi, mu ba ruwanmu. Waheeda ce nan.”

Cewar Rabi, muryarta na rawa.

Tsaki Baba Karami ya ja.

“Iyayen yarinyar da ta sumar a makaranta ne suka zo wai sun kawo ƙara. Sai kuma yarinyar da aka yi wa ɓarnar awara.”

Ya faɗa yana komawa ƙofar gidan.

Dariya Mama Jamila ta yi.

“Ohh, ikon Allah! Dan kuka kenan mai Jawa iyayensa bala’i.”

Umma ba ta kula ta ba. Sai mayafinta da ta yafa a jikinta, jin Baba Karami yana cewa mutane su shigo ciki, gudun kada maƙwabta su ji abin da ya kawo su.

Ya Ado kam ya kasa magana. Shi da Salma duk ido suka zuba wa Waheeda, wadda ta miƙe tsaye ta ɗauki buta da sauri, za ta gudu bandaki kenan.

Baba Karami ya yi saurin riƙo ta yana jefa mata harara.

“Gidan uban wa za ki da wannan butar?”

Cikin inda-inda ta ce,

“Kashi zan yi.”

“To sai dai ki yi a jikinki. Zo nan!”

Ya faɗa yana figota zuwa tsakiyar gidan.

Baban yarinyar ne, sai kuma wani matashin saurayi, da ita yarinyar da ta suma, ga kuma mai awara.

Ko gaisuwa baban bai tsaya sun yi ba, ya soma da cewa,

“Na kawo muku ƙarar ’yarku ne. Da ace ban rarrashi zuciyata ba, da ‘yan sanda zan ɗauko a tafi da ita. In ba shaidanci ba, yar wannan yarinya har ta san ta iya tayar da tarzoma har ta sumar da mutum. To na ga saka ‘yan sanda a lamarin ba shi da fa’ida, tunda yarinya ce sa’ar ’yata, wadda na san ba za ta wuce shekara goma sha uku zuwa goma sha huɗu ba. Don haka ku ja wa ’yarku kunne. Nan gaba idan abu makamancin haka ya ƙara faruwa fa, ba zan yi haƙuri ba. Ba ni da mutunci wallahi. Wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe. Yauwa.”

Baba Karami ne ya furta,

“Dan Allah, bawan Allah ka yi haƙuri. Ba mu san abin da ta aikata ba sai yanzu da kuka zo. In sha Allah za mu ɗauki mataki a kanta.”

A masifance ya furta,

“Yooo! Ai ba za ta faɗa ba, tunda ta san rashin albarkar da ta aikata. Wannan ’yar taku kamata ya yi ku kai ta Dawanau na wani lokaci, ko za ta nutsu. Yauwa, ni dai na gama magana.”

Baffah, da ya fito daga ɗakinsa ne ya ji abin da yake faruwa. Da ya ji mutumin yana cewa a kai Waheeda Dawanau, sai ya ce,

“To kai ka kai ta mana. Ai ga ka ga ita, sai ka sunkuce ta ka kai ta. Ana ba ka haƙuri, kana sake tuburewa kamar ana zuga ka. In ka ga dama kar ka yi haƙuri, ka yi duk abin da za ka yi.”

Duk da mamaki suka zuba wa Baffah ido, ganin ya tsoma baki alhali ana ƙoƙarin kashe maganar, shi kuma ya fito zai ƙara mata fetur.

Gyada kai mutumin ya yi yana cewa,

“Ba shakka, gado ai ba karambani ba ne. A wajenka ta koyi duk wani iya shegen da take yi kenan. To ni, Alhaji Inuwa, daidai nake da ku. Dama saboda zuciyar Musulunci ne ya sa na yi haƙuri. Amma tunda ka ce in yi duk abin da zan yi, to ku ma za ku gani. Sai na nuna maka na fi ƙarfin wani ya taɓa min ’yata tilo ya zauna lafiya.”

Ya gama faɗa yana zaro wayarsa daga aljihunsa.

Umma ce ta yi saurin cewa,

“Dan Allah ka yi haƙuri. Kar ka biye ta na sa. Tun kafin ku zo gidan nan ka riga ka yi haƙuri. Kar maganganunsa su sa ka fasa aikin alheri. Kar ka manta Allah yana son mutane masu yafiya. Ni ce mahaifiyarta, kuma na maka alƙawarin irin haka ba za ta sake faruwa ba.”

Yana cika yana batsewa ya ce,

“To billahillazi ya ci albarkacin ki. Amma in ba da haka ba, da na nuna masa ni waye a garin nan. Kuma na faɗa, zan sake faɗa, ku ja wa ’yarku kunne tam.”

Yana gama faɗin haka ya figi hannun ’yarsa. Ko sauraron Umma da ke masa godiya bai yi ba, suka fice.

Kallon Baffah Baba Karami ya yi, rai a ɓace, ya furta,

“A gaskiya Baffah, abin da ka yi yanzu bai kamata ba. ’Yarka ce ta yi laifi . Duk abin da zai zo yana faɗa, in ba a ba shi haƙuri ba ai ba za a fusata shi ba.”

“To ubana, in ka gama yi min faɗan sai ka ɗauko ice ka rufe ni da duka kawai.”

Ya gama maganar yana fita daga gidan.

Mai awara ta ce,

“Saura ni. Dan ni gaskiya ba zan yarda ba a biya ni awarata kawai. Dan in na koma gida Babata duka na za ta yi.”

Ya Ado ya ce,

“Nawa ne kuɗin awarar taki?”

“Na naira ɗari bakwai da hamsin ne.”

Hannu ya sa cikin aljihunsa ya fito da naira ɗari huɗu da hamsin, domin su ne kaɗai kuɗin da ya rage masa a aljihu.

Ganin haka ne Umma ta warware bakin zaninta ta ba shi naira ɗari uku. Ya cika kuɗin ya miƙa wa mai awara.

Nan ita ma ta yi tafiyarta.

“Na gode, Waheedatu.”

Umma ta faɗa tana shigewa ɗakinta.

“Waheeda, ba kya ji sam me ya sa ne kam? Haka kike ganin ’yan uwanki suke yi? Yanzu kin ji daɗi da ran Ummanku ya ɓaci fisabilillah?”

Ya Ado ya yi maganar yana komawa ya zauna a inda ya tashi.

Hawaye kuwa wannan na bin wannan, domin ta san yau Allah kaɗai ne zai iya kwatanta abin da zai faru da ita a hannun Baba Karami. Ga shi ya damƙi hannunta, babu halin guduwa.

“Kneel down!” ya umarce ta.

Ta durƙusa a tsakiyar gidan, sannan ya je ya ɗauko wani katon dutse ya ɗora mata a saman hannaye. Daga nan ya koma ɗakin Umma ya bar su a waje.

Mama Sadiya kuwa sai watsa habaici take yi tana dariya. Ita kuwa Mama Jamila, ko ɗago kai ta kalle su ma ba ta yi ba; harkokinta kawai take yi. Har aka ci aka suɗe, aka gama komai, ba ta saka baki ba.

Salma ta ce, “Za ki ci ubanki ai, tunda ba kya jin magana. Yarinya kamar renon aljanu.”

Cikin shasheƙar kuka Waheeda ta ce,

“Ba dai ubana ba.”

“Sai na wa?” Salma ta tambaye ta tana ƙoƙarin miƙewa.

Cike da tsiwa Waheeda ta furta,

“Sai na wanda ya tsargu.”

Takalmi Salma ta jawo ta wurga mata. Nan take Waheeda ta fashe da kuka, domin dama kukan take son yi amma ba ta samu dama ba.

Ya Ado ne ya ce,

“Salma, ki rabu da ita mana. Bana son neman magana fa.”

“Ai ta iya jawa kanta raini. Kullum sai na faɗa mata ta daina shiga sabgar yaran nan amma ba ta ji.”

Cewar Zuwaira.

“To kenan ba zan yi wa kanwata faɗa ba kenan?”

“Can muku dai. Yanzu kun fi kusa.”

Ta faɗa tana ɗaukar bokitin ƙarfen da ta sa ruwan wanka ta shiga bandaki.

Umma kuwa, bayan ta shiga ɗaki, zama ta yi a bakin gado ta yi shiru, tana tuna rayuwar baya—lokacin da ta fara haɗuwa da Baffah.

Lokacin Baffah yana ganiyarsa da kuɗi, ga aure-saki. Farkon haɗuwarsu kuwa, ya zo gurin mahaifinta ne a Bauchi domin karɓar hayar gona. A nan ne ya fara ganin Umma, lokacin tana da shekara goma sha biyar a duniya, ta dawo daga makarantar allo.

Tun da Baffah ya ɗora ido a kanta, ya ji ya kamu da muguwar ƙaunarta. Kyanta ya ƙara rikita shi, ga ta fara jajir, wanke hannu ka taɓa.

Bai yi ƙasa a guiwa ba. Ya samu mahaifinta da batun yana son aurenta. Mahaifin Umma ya yi masa wasu tambayoyi, nan ya sanar masa cewa yana da mata biyu.

Bai damu ba, domin shi ma matansa huɗu ne. Ba tare da ɓata lokaci ba ya ba shi auren Umma. Bayan sati uku aka yi aure, aka kawo Umma gidan Baffah da ke Gombe.

Matan Baffah biyu da suke gidan nan hankalinsu ya tashi ganin irin macen da ya auro—fara, kyakkyawa, kuma ta fi su da komai.

Nan take kishi ya fara, suka fara tsangwama da hantara gare ta. Duk da haka Baffah na taka musu birki.

Su Mama Sadiya ba su fara shiga tashin hankali ba sai da suka ga Umma da ciki. Domin dukansu babu wadda ta taɓa haihuwa.

Nan tsanarta ya sake ninkuwa a zukatansu. Babu hanyar da ba su bi ba wajen ganin cikin ya zube, amma Allah bai ba su iko ba.

A haka har ta sauka lafiya, ta haifi ɗanta santalele, namiji mai matuƙar kama da Baffah. Ranar suna aka sa masa suna Alaramma Sadam, wato sunan mahaifin Baffah. Daga baya aka yi masa inkiya da Baba Karami.

Bayan shekara guda, Mama Sadiya ita ma ta haifi ɗa namiji aka sa masa suna Ado.

Ado da Baba Karami tare suka taso. Duk da Mama Sadiya ba ta son alaƙarsa da Baba Karami, babu yadda ta iya, domin sun yi shakuwa irin wadda babu abin da zai iya rabasu sai Allah.

Idan suka je ɗakin Mama Sadiya , haka za ta riƙa tsangwamar Baba Karami. Amma Umma kuwa, haka take jan Ado a jiki kamar ɗanta na cikinta.

Bayan wasu shekaru, Umma da Mama Sadiya suka samu ciki kusan a lokaci guda. Har wannan lokacin kuma Mama Jamila ba wani labari.

Mama Sadiya ce ta fara sauka ta haifi mace, aka sa mata suna Zuwaira.

Bayan sunan Zuwaira, Umma ma ta sauka ta haifi mace, aka sa mata suna Salma.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya. Umma da yaranta suna fuskantar rayuwa iri-iri—wulaƙanci da rashin mutuncin kishiyoyi.

Babu irin abin da Umma ba ta gani ba. Kasancewar ta mace mai matuƙar haƙuri, duk abin da za a yi mata ba ta taɓa tanka ba. Sai dai idan abin ya ƙona mata rai, ta shiga ɗakinta ta ja yaranta a jikinta ta yi kuka sosai.

Tun Baba Karami bai da wayo, har ya fara fahimtar cewa Umma tana shan wahala a gurin su Mama Sadiya.

Da ya ɗan taso  kuwa, nan ne ya fara tsaya mata. Duk wadda ta yi wa Umma wani abu, sai ya tsaya a ƙofar ɗakinta yana yi mata zagin ƙare dangi. Har ma ya kan ce zai daki duk wadda ta kuskura ta tsaya masa.

Idan ya fara wannan rashin kirkin nasa, su Mama Jamila kan shige ɗaki su yi tsit. Domin har ga Allah, Baba Karami ba ƙaramin aikinsa bane ya hau musu ruwan duwatsu.

Ga shi idan yana yi, to Umma ce kaɗai take iya dakatar da shi.

Baffah kuwa, ba ya shiga cikin lamarin. Haka zai zauna a ƙofar gida yana ji, har ma makwabta su taru suna kallon abin da ke faruwa.

Su Mama Sadiya kuwa ba sa iya tunkararsa idan ya tsaya musu, saboda ba ƙaramin shakkarsa suke yi ba.

Yaro tun bai je ko’ina ba yake musu rashin mutunci saboda uwarsa. Ga shi da fuskar bosawa, a haka ya taso.

Ita dai Mama Jamila, sai dai bakinta ya kwace ta, domin ba ta da ‘ya’ya.

Ummah gaba ɗaya rayuwar gidan Baffah ta fice mata a rai. Ba ta da wani buri da ya wuce ta koma gaban iyayenta. Amma daga zaran ta tuna da yaranta guda biyu, sai hankalinta ya tashi. Ta san idan ta bar gidan, babu wanda zai kula mata da su. Rayuwar wulaƙanci kawai za su yi, domin ta jima da sanin kishiyoyinta sun tsaneta, sun kuma tsani yaranta.

Wannan dalilin ne ya sa ta yanke hukuncin cewa za ta yi zaman yaranta, domin tafiyarta ba ita ce mafita ba. Tana tsoron irin rayuwar da yaranta za su yi tana raye, musamman Salma da take mace. Gwamma Baba Karami da yake namiji ne.

Ta ci gaba da zaman haƙuri kamar yadda ta yi na shekarun baya, amma ta yanke shawarar ba za ta sake haihuwa da Baffah ba. Za ta rungumi yaranta biyu, ta kula da su, ta kuma ba su tarbiyya gwargwadon iyawarta.

Amma da yake ƙaddararmu ba a hannunmu take ba, Ummah ta sake samun ciki ba tare da ta sani ba. Sai da cikin ya kai wata huɗu kafin ta gane.

Hankalinta, idan ya yi dubu, ya tashi. Nan fa, ba tare da sanin kowa ba, ta fara neman hanyar zubar da cikin.

Duk wani irin magungunan gargajiya da ake cewa suna zubar da ciki, babu irin wanda ba ta sha ba. Amma shiru, sai dai ta riƙa fama da matsanancin ciwon ciki, cikin kuwa ya ƙi fita.

A ƙarshe ta je asibiti domin ganin likita. Nan ta yi masa bayanin gwargwadon abin da za ta iya.

Likitan ya zaunar da ita ya fahimtar da ita hatsarin da ke tattare da cire cikin da ya yi ƙwari. Har ma ya ce za ta iya rasa ranta.

Idan kuma aka dace, za a iya cire cikin cikin nasara.
Ba tare da Ummah ta yi tunanin komai ba, ta amince.

Nan ya yi mata wasu allurai.

Bayan ta koma gida, cikin dare jini ya balle mata.

Hankali a tashe, Salma ta shiga ɗakin Mama Sadiya, inda Baffah yake a ranar. Cikin kuka ta sanar musu halin da Ummah take ciki.

Da suka shiga ɗakin, Ummah ta riga ta fita hayyacinta.

Nan suka kwashe ta a babur ɗin Baffah suka nufi asibiti.

Da suka isa, aka ba ta gado aka fara duba lafiyarta.

Ummah kuwa, wadda ba ta cikin hayyacinta, sai ta ga kanta a cikin wani irin daji mai ban tsoro da firgitarwa.

Dariyar yara ta ji tana tashi, haɗe da maganganu.

Ta bi sautin har ta je bayan wata bishiya ta tsaya tana leƙen inda yaran suke.

Yara ne da yawa, da za su kai kusan guda ɗari, maza da mata. Kowa yana wasa cikin walwala, sanye da fararen kaya.

Sosai ta shagalta da kallonsu.

Sai ta ji an ɗora hannu a kafaɗarta.

Da sauri ta juya.

Sai ta ga wani tsoho a bayanta yana mata murmushi.

A tsorace ta ja baya tana kare masa kallo cikin ɗar-ɗar.

Tsoho ne ƙwarai. Yana sanye da fararen kaya, hannunsa riƙe da sanda.

Ya zuba mata ido yana kallonta kamar yadda ita ma take kallonsa.

“Wanene kai?” Ta fisgo maganar da ƙyar.

Murmushin da ke fuskarsa ya ɓace lokaci guda, kamar ba shi ne yake yi mata murmushin ba.

Murya a tausashe ya furta,

“Ni ne mutumin da yake ƙoƙarin dakatar da ke daga aikata babban kuskure mafi girma a rayuwarki, Maimunatu.”

Ya kira sunanta a ƙarshe.

Mamakinta ya ƙaru jin ya ambaci sunanta kai tsaye.

Ba tare da ta fita daga mamakin da take ciki ba, ta ji ya ci gaba da cewa,

“Shin me yasa bil’adama ba sa gode wa Allah? Me yasa ko da yaushe suke ganin tsarinsu shi ne daidai akan na Mahaliccinsu? Me yasa suke da butulci?”

Shiru ta yi masa, domin ba ta san abin da za ta amsa masa ba.

Ga bugu da ƙari, ta ji tamkar an ɗaure mata bakinta da igiya mafi kauri a duniya.

Hakan ya sa kawai ta zuba masa ido.

“Kin gwada na farko, abin da ke jikinki ya ƙi fita. Kin sake gwadawa na biyu, nan ma ya yi gardama ya ƙi fita. Ba ki haƙura ba, haka kika yi na uku, nan ma ba ki samu biyan buƙata ba.

Me ya sa ba ki haƙura ba? Me ya sa kike da taurin kai, Maimunatu?”

Ya faɗa cikin ɗaga murya har sai dajin ya amsa da ƙarar muryarsa.

Har yaran da suke wasa gaba ɗaya suka dakata, suka juyo suna kallonsu.

Zuwa wannan lokacin, jikin Ummah rawa kawai yake yi.

Hawaye kuwa suna kwaranya daga idanunta, tana tuna yadda ta yi ta ƙoƙarin zubar da cikin.

Don’t forget to comment and like 🥰❤️