SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)

Page 16

by @smauta





A SAFIYAR YAU ASABAR NE ZAA DAURA AUREN FATIMA ISYAKU LILY DA ANGONTA ALHAJI NAJIB AUDU DALA………




Dalla wai ki tashi har 8 na safe fa,karki bataman rai sarah dama a hayake nake nan ban tashi daurin auren da sai 2:30 shine zan tashi tun 8 inyi ubanme wlh shiyasa ya adam idan yashige dakin nan yai gum yo wnn gado ai sunanshi kafi amarya kaishi🤣mtsww banza yar iska naji dai jeki wlh sai 10 zan tashi…………..




  
Ke wai zaki rike miji kuwa lily breakfast ya zakiyi ai dan aljanna bamai ciye ciye bane tanan bangaren na huta kuma baya fita da wuri sai 11 watarana ma sai 1 har munyi baccin mu mu more rayuwa,fita kawai sarah tayi daga dakin ita kuma tacigaba da shakar baccin ta gida fa ko ina ya dauki harama anata kacaniya…………….




Tun daren jiya baccin da adam ya kwanta haka ya tashi tsakar dare rutsum bai rumtsa ba,sallah yake shikanshi baisan iyakar ta addu'a taketa kwararowa saida asuba bacci mai dadi ya kwashe shi,bai farka ba saida kiran galaxy ya tashe shi,yane bacci kake ma eh wlh kasan ƙarfe nawa kuka umm 9 ba,dalla mike kaifa uban amarya kamata yayi kana gida yanzu kana taya Abby arranging gidan nan galaxy I cant wlh yaushe zaka zo anjima kadan ina tafe ok………….





Murgina kawai yake kan gado yana fiddo hotunanshi dana lily tun na yarintar su, yanzu shikenan nan da few hours tazama ta wani,tashi yayi zaune yace Allah idan auren lily shine farin ciki a rayuwarta Allah ya dawwamar ta da hakan nikuma kabani hakuri da dangana ka yayeman son ta so irin na soyayya da nake mata ka bani wacce zata mayeman gurbin lily a rayuwata ka saukakaman halin da nake ciki a yanzu da wanda zan shiga nan ga, Allah na roƙe ka da sunayen ka tsarkaka nimai laifine a gare Allah gani gareka ni adam idan har son lily zaizamar mun wata cuta ko jarabawa a duniya ka kawoman ita ciki sauki,kasakama zuciya ta hakuri da salama,ameeen ya adam😭😭😭😭……………….






Yadda ta kintata haka ta miken kuwa 10 ta tashi bata tsaya komai ba ta fada toilet din ya adam da komai nashi tayi wanka ta fito sarah na shigowa Allah ya tarfa ma garin ki nono wlh babani harta iso, sbd hawan bene ma yasa taki zuwa nan kiyi sauri ga mai makeup din nan har tazo fa…………





Duk jikin lily yayi sanyi likis tace yunwa nakeji babu wani abu inci kunun gyada Sarah ta debo mata da doya bata maci doyar ba kunun tasha sosai sannan ta mike tsaye ta kalli Sarah ina akwatin kayan nawa kawomun nan in shafa mai………








Dakin mama taje ta dauko mata akwatin,mai kadai ta shafa ta koma gaban mirror wani turaren adam da tun jiya kamshin shi yayi mata taje ta buda ta shafa a jikinta komai akan gadon ta watsar dashi a ranta tace Sarah zakizo kiyi duties dinki na kanwar amarya…………




Kasa ta sauko tana bi tana gaisheda yan uwa da abokan arziki da suka halarci bikin,babani na dakin mama ta shiga hajjaju makkatu ta madina masu kanshin zamzam babani tace yal mulki gwamnati bakisan kudi sai mulki an taso,ina kwana lafiya lau amarya kai babani harda ke……………






Ahhhhh eh mana mijin ma ai dani za'a tafi gidan nice kishiyar taki🤣lily tace lallai aiko da kafar ki zaki baroman gidan,nan babani ta shiga yima lily nasiha kan aure ta shigeta sosai dan bata san ta fara kuka ba,kuka take sosai har saida babani ta koma tana lallashin ta sannan………….






Inda kawayenta suke can ta wuce kowa da iskancin da yake mata daya bayan daya tana maida masu ansa bakin ta baya shuru kuma ba'a bin lily bashin magana wayarta ce ta hau ringing husna tace ko angon ne,wani farrr lily tayi tace kwarai da aniyar ki kuwa shine yarinyar nan kinci 2k………….






Dan aljanna wata ajiyar zuciya ya sauke yace mar'atussaliha busy bikin yasa aka manta da miji,fita tayi daga cikin mutanen sannan tace ban mance da mijina ba amma mijin dai yasani ina fushi dashi,nasani kyakkyawa bata fushi yar albarka aiman uzuri…………





To zan duba ingani idan da yiyuwar hakan idan babu kuma zaka ansa tuhuma ta ne daria yake sosai soyayyan lily na kara tsaga kowane bargon jikin shi da jijiya Allah yaimaki albarka amin ya rabbi,nan da anjima kadan kinzama mallakina mar'atussaliha……………




A koda wane lokaci ni mallakinka ce dan aljanna kai daya ido da zuciya ta ke gani duk wani ɗa namiji a duniya bayanka yake ban taba mashi kallon so indai akwai ka Allah ya baka ikon rikeni amana, kamar yadda nima na alkinta a raina zan so ka kamar yadda uwa keson ɗanta……………….





Nagode sosai masoyiya ta sai munzo nanda anjima kadan, Allah ya kawoman kai lafiya kuma cikin aminci mijina Amin ya rabbi ki kulaman da kanki In Shaa Allahu kullum ina kokarin hakan amma tunda yau ka bukata na yau zaifi na kullum haka suka kashe wayar da shaukin soyayyar juna,arrrrrrrrrrrrrrrrrrrrrr wlh soyayya tayi 🤣🤣…………………






Wai dan Allah adam meye haka sai kace mai wankan canza fata duk ka shanya mu nan 1 ce fa zatayi yaushe muka isa gidan, Sufyan yace wnn dan iskan wanka kamar mace yanajin su bai fito ba kuwa saida ya kyalle jikinshi tassss sannan…………





Kungam gulmar ko anje anyi gulmar ka ko kai zaka auri yarinyar nan iya wanke jikin da zakai kenan, galaxy yace ni bakin cikina daya ne ba biyu ba munaji muna gani za'a daura auren dawani bakai ba………….




Sbd mugun zurfin cikin ka,sai lokacin adam ya juyo yana shafa mai yace komai rubutaccene daga Allah galaxy kasan koda soyayyan nake da yarinyar nan idan niba mijinta bane wlh ina kallo zata auri wani…………..




Na maida ma Allah lamurana wlh ina addu'a kullum inajin wani peace a zuciya ta dan Allah karka tadaman ciwon da nasamu ya faraman alayen warkewa duk da banida tabbacin hakan……….




Sufyan ne ya tabo galaxy dan ya lura yana shirin maidama adam martani ne,shiru sukayi adam nata shirin shi a tsanake tsaf ya kammala……..




Tabarakalla Ma Shaa Allah,wata dakakkar wagambari skyblue ce ya saka taji ɗinkin babbar riga da yar ciki, complete din adon jikinshi skyblue ne da dark blue kama daga saman hular shi kayan jikinshi, agogo har direwa takalman kafar shi company Hermes sandals ne amma sun karbi kafar shi matuka,ga wani azababbe kamshi na tashi kai farat daya akace maku shine angon bazakayi gardama ba Allah yayi halitta adam namiji ne iya namiji mijin da kowace ke mararin kalar sa…………..






Mazaaaaaaaa wanka fa ya fita wani killer smile ya saki hannu ya basu suka rafke rafff irin ta abokai muje, Sufyan ne gaba adam tsakiya galaxy na baya haka suka fito dakin wata shahararrar jeef ta galaxy suka shige adam na baya a owners corner…………





Galaxy yace kai maza anya bokanka yau ba Sa'a ya baka ba,kaga yadda ka fita da fitar ka kodai dakai za'a daura ne,kanada matsala dani dai yau ko galaxy ahh noooo ina taya abokina kishi ne kawai,to ka bari dan zamu fara kishin haramci tunda matar wani ce………..





Sufyan dake tuki ya kalli adam ta mirror yashe goran miskili mai ban haushi ga sani wani lokacin kuma ga shagala,shidai uffan bai ce masu yana kame yanajin duk iya shegen da sukeyi mashi,hankalin shi na kan waya wani zane dayayi yakeso bayan bikin nan yayi presenting a office yake kara dubawa duk dan yayi keeping kanshi busy akan surutan nan nasu……………….



Madarar kyau kawata Allah ƙamariyya wlh,kai dole ma mu tsaya tsayin daka wlh miliyoyin kudi za'a ajemana,ba kuda matsala dan canji ne fa da dala ma za'a saye maku ni wata shewa suka dauka sarah ce itama ta fito cikin shigar ta ta alfarma taci makeup kanwar amarya lily tace mata……….




Yesssss yar 'U ta yasir sai dubu ta taru bansan iskanci kuma zaki fara ko dariya akayi dan duk wanda ke wurin nan inda sabo ya saba da halin lily kamariyya na'am wai ba'a daura bane saurin me kikeyi yanzu 2 din ta buga nanda minti talatin ukku ce ciff a kanku…………..





Hahahahaha ohhhhh wai dagske aure zanyi ko a'a wasa ne,daria aka kara dauka ina zuwa nan lily ta sulale tabar abokanta ta nufo dakin ya adam kanta tsaye ta banka kofar dakin bata zarce ko ina ba sai gaban mirror turaren nan na dazu ta bude ta kara shafawa🤣🤣🤣……………….






Koda ta rufe mamadin ta aje saita riko shi a hannun ta akwatinta dake bude ta kalla ta kalli gadon wai sarah bata gyara komai ba nufinta ina amarya ni zanyi aikin nan wannan turaren kuma wlh na sace shi ina son shi idan na tafi gidana na kira in nemi yafiya cilll zata jefa shi a cikin akwatin nata kamar daga sama taji muryar ya adam yace bani abuna yana mika mata hannu daga inda yake tsaye bakin kofar……………





Dagowa tayi taganshi tsaye cakkkkk wlh ba tsoro taji ba amma yau yayi mata wani irin kyau har sheki yakeyi ga sajen nan nashi luffff ya kwanta ko bakiji ba ,dan dan Allah kayi hakuri nasan baka gidan ne kuma inason turaren sai akace kixo ki sace shi?a'a ba sata nayi ba menene??????





Aro ne okay bring me,me kikeyi a dakin nan?wannan kayan na waye ya kalli yadda suka hargitsa mashi daki,ki tsaya ki gyara shi pin idan na dawo nagani a ƙasa wallahi ranki saiya baci,kuma idan kikaga abu kinaso tambaya ake ba dauka ba,kawai ya daka kwana ya koma inda ya fito,kodayazo compound din kowa ya hallara hatta ango da tawagarsa ta yan canji suna wurin fara buɗe taro da addu'a akayi………………





Tun lokacin kirjin adam ke dukan tara tara yana zaune kan kujerun da aka baza a compound din gidan nasu wuri ya natsu liman ya bada sanarwa ina waliyyin amarya ina waliyyin ango idan suna kusa su matso abby ne cikin fararen kayanshi ya matso kanen baban Alhaji najib shima ya matso kusa sukayi musabuha ta alkhairi…………….







Dubban mutanen dake wurin ne damu kanmu nan nan muka shaida ɗaurin auren FATIMA ISYAKU LILY DA ANGONTA ALHAJI NAJIB AUDU DALA AKAN SADAKI NAIRA MILIYAN DAYA LAKADAN BA AJALAN BA…………………




Lily na cikin kwashe kayan nan taji wannan sanarwar ai kayan ta watsar tayo waje inda kawayenta suke da gudu ke lafiya, Lafiya kuna nan har an daura auren wlh naji da kunnena haba nan suka tashi anata murna masu Allah sa alheri nayi kowa da irin tashi murnar………….






A tsakar gida kuwa hayani ta barke kowa na zuwa wurin wanda yasani domin ayi musabaha ta alkhairi,ango bakin nan kuwa bai rufuwa galaxy ne ya tabo adam muje gun abby ko kamar wanda kwai yayima dakwaye a ciki haka ya tashi koda sukazo wurin abby da fara'ar nan tashi ya ansa masu harda adam din dukka sukai mashi Allah sa alheri ya ansa yanajin dadi kasan ranshi yana tausayin babban dan nashi amma ya za'ayi kaddara ta riga fataaaa…………………….





Koda suka tunkaro alhaji najib wani tuƙukin bakin ciki ne ya taso mashi,dakyar ya saita kanshi ya bashi hannu sukai musabaha, Alhaji najib yashiga kuwa gabatar ma da abokansa adam din yayan matar daya aura ne idanun shi har rufewa sukeyi dakyar yake ansa su kawai na karfin hali ne……………..







Su galaxy na gefe ya tunkaro su Sufyan maza muje wurin mama ku gaisa mu fito kaina ciwo yake mubar gidan nan bansan hayaniya galaxy ne ya e a'a mama ko daga baya mun dawo muyi mata Allah sa alkhairi galaxy yayi hakan ne kuwa dan yayi backing abokinshi daga ganin amarya baisan tuni ya ganta ba kuwa,hakan yayi mashi bai ansa ba kawai ya sakai yayi gaba………….





Hular kanshi ya cire saboda ac motar ta zagaya mashi yadda ya kamata kanshi ya kama baisan lokacin da ya fara furta Ya Allah write for me a life that is pleasing to u,and a return to u that is beautiful keep me balanced and focused in my faith sourround me with what is good for me🙏and do not allow my heart to become distant after u become distant after u have guided it🙏………………


ASHA KARATU LAFIYAAAAA


                    WAYYO YA ADAM 

LILY ADAMS BAKI HALACCI BA😭🥹🥹🥹🥹🥹🥹😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭


PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏🥹...SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……