SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)
Page 18
by @smauta
Koda Sarah ta iso dan aljanna na shirin ficewa daga gidan fira sukayi sosai ya tafi dakyar lily tabar shi ya fice da sharadin kafin sarah ta tafi zai dawo,kekuma na dawo kanki ya ake ciki sarah tace normal amarya har kinyi cikar dakin console dinda ke parlourn ta kalla ke dan Allah dagaske kodai ma ciki gareni Sarah,Sarah tace ahh karki tmby kaza hanyar rafi,ki tmby kanki idan kinada shi ai kinsani…………….
Banida shi ma tsokanar ki nake kanwata waye kanwar taki?saratu mana ko ba kece gabana ke dan ubanki ko banyi aure ba na girmeki balle yanzu dana taka turba irinta manyan mata,sarah ta kwashi shewa tace sai dake lily wani farrr tayi tace gani fa to ya son ran naki,kiyi kiyi kicema yasir ya fito dakun gama service kema ki samu tabarakin aure yar nan,ke bansan iskanci ungo nan babani ce ta kawo ta fara ciro mata magunguna a leda…………
Wannan tafasa shi zakiyi da dumi kishiga ciki tsawon minti talatin wannan kuma dukkansu da madara ko nono safe da rana tace dan Allah kisha tasan halinki da magani,yatsina fuskar ta tayi kamar maijin warin kashi tace nifa banson shaye shayen magungunan wlh,sai namiji ya nace maka yanzu ma da yaya nake samu in warce kaina inaga inashan wnn abubuwan zan kwatanta de……………
Nikam akwai abinda ke damuna,Sarah tace menene wlh na kasa maganar da kowa sarah menene dallah kinsan ya'yan dan aljanna dukkansu sunzo gidan nan kinga yadda suke girmamani aunty sama aunty kasa wlh harda mamarsu nayi waya ranar faran faran kullum dan aljanna courage yake bani akanta yace batada matsala amma na kasa yadda karfa ta hada baki da yaranta suyiman shigo shigo ba zurfi Sarah,ahhh haba bazasuyi ba duk bala'in nan naki ai nasan kema ba kyalle bace ana cemaki kule kike cewa casssssss casssssss cacassssss………
To Allah yasa dai kinsan tsaffin matan nan makirai ne amma ina daidai da nata makircin idan zaman lafiya nima zan rungume shi hannu bibbiyu idan akasin haka shima zan rungume shi hannu bibbiyu na banza ma na siya fada balle na gidana kedai Allah ya sawake,Sarah tace Amin,bana ma tunanin akwai wata matsala lily dan da akwaita yaran nan bazasu shiryo suzo maki ba kowa na ma'aurinta su ballo suzo,anyi dacen su In Shaa Allahu,ahhhh a yadda sukazoman indai haka zamu tafi gaskia basuda matsala muje daki kiga tsarabar da suka kawoman……………
First born din nashi fa bakiji maganganun da yayiman ba wlh naji dadinsu yace su basuda mtsl da duk wadda mahaifinsu zai kawo shiyasa koda ya nufo su da maganar aure fatan alkhairi sukai masa haka mahaifiyarsu mafarin kiran nata kenan ma muka gaisa bakiga yadda takeman fara'a s wayar nan ba tace nan da 1 month visa ta ke karewa zata dawo wai ashe show room gareta sarah matar nan tasha kwana shiyasa bata kula mijinta tanacan ƙasashen waje kwaso kaya,nidai gskia da irin wnn kudin gwara babu sarah in saki mijina sakaka in tafi neman duniya ina dalili…………….
Harda kari da hakan yasa wlh lokaci guda dan aljanna yashiga raina har ga Allah inajin tausayin shi rashin iyali matsala ne,aike gakinan ya samu matar gida a rike miji 🤣🤣🤣daria tayi ahhh na rie kammmm dan ma🙂↕️🫣🤐🤐🤐🤐bakina alaikum dakinji bayanai banison ji ma ki rike abunki, gaskia kin gode wannan kaya designers lily kalli ko takalmin fa kingode Allah de ya kara hada kanku lily yasa gidan zamanki ne na har abada amin yar uwa dan Allah muje kiman wainar fulawa wlh idan nayi ban iyaci……………
Ke wai kodai dagsken kin kamu, Allah ko sarah nashiga ukku daga zuwana sai ciki nabani ni lily,ke mene na banuwa shege kikayi da ubansa ni wasa ma nake maki wlh,ai baki kama da mai ciki yo shima kullum haka yake ceman wai na cika kwadayi kodai ciki gareni to kije asibiti mana ki tabbatar,banfa zuwa wata asibiti idan ma shine Allah raba lafiya😂😂tunda kikazo kinyi period eh mana nayi ko sati baayi ba to gskia bashi bane sainan gaba washhhh naganki da ɗa wane suna za'a saka mashi ko yaya Adam zakima takwara………..
Waaaaa,keeee ni har mantawa nake da wani ya adam na baro kurkutun kaddara da ina can kullum sai munyi fada kamar zamu tada gidan nan😂😂😂inda mutum yake nan ake ganinshi duk waye waye na da mama wlh ban taba cewa agaida shi ba,kuma kinsan ya kusa 2 weeks kwance ba lafiya gida anyi anyi yaje asibiti yaki ciwo sosai baya iyacin abinci sai abu liquid lily tace wai ya adam din niko mama bata gayaman ba kullum fa sai munyi waya daria ta kwashe da ita tace alhakinane ke binshi amma na yafe mashi😂…………….
Alhakinki ai duk abinda yayi maki ke kike ja wlh ya adam mutumin kirki ahhhh sarah wlh na yarda ranar da nayi gudun hijira na tabbatar da halin kirkin shi,dariya sukayi har suna kashewa Sarah tace kai lily kin dade kina bala'i da rayuwa kin dade kina gana mana azaba😂😂 wlh yanzu gidan tsit da baki nan ba wani bari bari,kammm sai kace wata yarinya eh mana kullum fada caaaaaaa mama tayi abby yayi shiko ya adam ai albashi ne kullum sai kun yi ta………….
Bawan Allah ya huta shima da halina shima idan kin koma gidan ki ce ina gaisheshi da jiki kuma kice mashi wai ko kayan wanki aka kawo gidan miji a nemeta balle yar adam,ni nabar gaba dashi na girma wlh yanzu na wuce da iyawar shi,iyyeh lily ya adam kwarai shikuwa dan nasan abinda shi baisani ba,mene kika sani share kawai yarinya,to badani ba wnn sakon naki kirashi da kanki ki gayamashi,hahahahhahaha waaa niii nadai kirashi in mashi ya jiki badan halin shi ba wlh…………….
Aishi matsalar shi baisan abun arziki ba ma da idan zaki tafi inada wani cowleg da nayi mashi pepper soup nasan yanaso amma da kince nice nayi ba sha zaiyi ba😂😂asara ma zakiyi ko gida idan kece kikayi pepper soup ba sha zaiyi ba tunda ya ganki kina murar nan kin fyace majina kina motsa pepper soup yake kyamar soup dinki😂😂😂🥹💔……………………
Sai kace shi tsaftar gareshi duk dagiyace ranar ɗaurin aure ma bakisan me yamun ba kwace lbrn yadda sukayi a daki tass taba sarah labari daria take har tana rike cikinta ina turaren yana nan na taho dashi wlh sai ranar da zanzo gida in shafo shi yanzu dai da aurena ba yadda zaiyi dani😂😂lily ba ranar da zakiyi hankali kedai indai gurin wannan ne ban hankalta koda auren nan saina gallaba mashi,duk abinda yamun abaya wanda ban rama ba yanzu zan ramashi a inuwar aure nake ba damar a tabani eheeeee……………..
Yinin ranar haka suka karar dashi da firar gida duk abinda ya faru bayan auren lily a gidan sarah ta bata lbr itama duk abinda ya faru a nan din taba sarah labari sai gab magriba sarah ta fito zata tafi firrrr lily tace batasan wnn ba,itada tafiya sai dan aljanna ya dawo yaushe zai dawo?sai 8 kina nufin duk ina cikin gidan nan to wallahi badani ba,bako zanyi wani reverse tayo yaushe kika fara zance tunda kikayi aure ai dama na gayamaki bazan fara fira ba saikin tashi dan haka zakizo ki addaba mana kinsan yasir ba magana ba yanzu ma ba tsira yayi ba inada number wayar shi fa😂🤣🤣………..
Yi hakuri karki kirashi nidai tafiya zanyi lily wani marairaicewa tayima sarah duk dan taji tausayin ta tayi kamar bata ganta ba uwayen chocolate ta kwaso mata ta bata wnn sunyi yawa wlh kullum sai ya kwasoman su nima nan sunman yawa karsu lalace,ki dibar ma wannan tazurun yayan naki kice inji ni mama dai nasan bazata sha ba shiko yanashan chocolate to gatanan dai yasha albarkacin mijin kanwar shi🤣🤣🤣🤣a rayuwa ban taba ganin wanda ya raina ya adam irin ki ba lily,wlh gobe ma zan kirashi in mar ya jiki gojojo kenan dayanada mata duk bai huta ba yai kwance gida ba lahiya duk rashin aure ne……………….
Sarah kodai kamariyya ma zamu hadashi da ita,keni ba ruwana shika shikan iskancin ki saida safe ta bude kofar ta fice suna dariya………
PLEASE AND PLEASE LIKE, COMMENT,SHARE JAZAKALLAHU KHAIR🙏🥹....SM AUTA TAKU CE💃💃 MU HADU A NEXT PAGE THIS BOOK IS FREE WANNAN LITTAFI KYAUTA NE……