SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)
Page 19
by @smauta
SOMEONE'S HEART'S DESIRE
WASHE GARI DA MARECE
Abby ne ya hango adam na fitowa compound din gidan tun daga nesa shima ya hango abby da tafiyar nan tashi kamar baison taka kasa ya kara wurin abby ahhh manya dibar fari jiki kam yayi lafiya dama Allah ya halicci mutum yace bazaici abinci ba dole kasha wuya,ya jikin abby da sauki kaci abinci?eh naci bakin ne ba appetite mama ta matsa kuma sai naci abinci…………
Adam kenan ka gode Allah iyayen naka na raye har kanada wadda zata matsa kaci din ma wasu neman hakan suke amma inaa,ko wannan wata niima ce adam,hakanne, Allah ya baka lafiya kadaina yawan zama ɗakin nan kmr yanzu haka ka fito ka dan zagaye gidan nan iya karfin ka zakaji jikin ya saki sosai,gabanka dai likita yace komai naka normal damuwa ce kawai ka dora ma kanka adam na rasa ta mecece…………
Saurayi kamar ka har kana kai gejin irin wnn damuwar, bansan menene a ranka ba kuma banaso ma in sani dan duk abinda yake saka cikin wannan halin muddin ni mahaifin ka nasan shi nima zai tabani amma ina so ka koma ga Allah shine maji rokon bawa a kowane hali ka shiga ka rike Allah shi ya saka maka kuma shizai yaye maka amma kayi yaki da zuciyar ka sosai adam kar ta jefaka a halaka,wacce daga baya zakazo kana dana saninta kaji……………..
Suna cikin firar su da abbyn mai dadi yanata kwantar mashi da hankali yaji kwatar damuwar da yake ciki ma ta fara raguwa wayar sa ta hau kuwwa kallon screen din yake sosai yanaso ya tabbatar da sunan wa yake gani,tunda sukayi candy aka siya masu waya yake da number amma flashing bai taba hadasu ba sai yau?kiran me take mashi kuma?abby na zaune baice masa uffan ba dan baisan wake kiran ba har ta gaji ta tsinke…………
Wani sabon ruri wayar ta dauka kamar maijin tsoron wayar ya shafa screen din yakai minti ukku kafin yace Assalamu alaikum,lily uwar karangadi ta ansa waalaika salam ina wuni ya adam,umm lafiya muryar shi a rarrabe yake maganar kamar yana tsananin tashin hankali ya jikin fine alhamdulillah Allah ya kara lfy Sarah ke fadaman bakaji dadi ba,ummmm itama duk bata saba wayar dashi ba da yanayin yadda yake respond dinta yasa tace sai da safe ok kasa cire wayar yayi a kunne abby kam kobai gaya mashi ba yasan wacece dan yaji muryar ta cikin wayar…………….
Yunkurawa abby yayi yace bari in shiga ciki kanshi ya jinjina kawai sai lokacin ya zare wayar daga kunnen shi wani sabon dafi ne ta sosa mashi daya dade yana jinyar shi,tsoki ya buga ya danna number tata a blacklist dan baya so ma watarana ta kara gigin kiranshi a wayar,duk ya zama wani sukuku dashi kalar fatar jikin shi baki ne amma rashin lafiyar nan dayayi ta kwana biyu sai yayi wani irin haske sosai kalar shi ta hutu ta kara fitowa muraratannnn………………
Lily kuwa yana kashe wayar tace kaji dashi danma bakada lfya ne kar ace ban kiraka a dinga mun dumin nan ana cewa ban girma ba,amma dame zaisa in kiraka kamar wani mai hangum sai wani ummm yake mani a kunne😂😂ya adam tashi yayi ya lallaba yadan fara zagayen gidan nasu kamar yadda Abby ya bashi shawara ilai kuwa sai yaji kafafun shi sun fara saki amma duk tafiya daya yanajin muryar lily har cikin kogin kanshi…………..
Ko yayi yunkurin yaki ce tunanin ta saiya kasa kiran magriba ya tsaida shi daga zagen duk yayi zufa jikin shi,dakanshi a ran nashi yake cewa ya samu lafiya,gida ya shigo ya tarar da sarah kwance a parlourn ita kadai,sannu da zuwa ya karfin jikin hajia saratu naji sauki ina mama kamar naga tashiga wurin abby,an kira sallah eh ya adam naji yanzu tashi……………….
Wanka yayi ya canza kaya ya fita zuwa masallacin dake nan layin su shine bai dawo gidan ba har akai isha yanata karatun Alkur'ani dandanan yaji zuciyarsa ta saki,a kofar gidansu yayi dailing number Galaxy yane gawa taki rami ko kaki ko kaso garon nan dana saya sai an daka man gumba,daria yayi yace kasha abunka dan iska kana ina gani kan hanya zanje majalisa,inason fitowa nima but bana iya driving ya kenan bani 20mnt sai inzo muje ko toh shikenan Nagode…………….
Lily ce kwance jikin dan aljanna yana shafa mata fuska fita suke cikin tsananin so da kauna,ya kalleta my wife ummmm,tunda aka kawoki gidan nan bamuyi magana ba,inaso ki saurareni dakyau lily,ni mutum ne mai son iyalin shi kuma mai kokarin ganin duk wani abu da kika bukata a doron duniyar nan muddin inada shi lily zanyi maki shi,duk dukiya ta taku ce banida wasu bayan ku………..
Inaso dan Allah dan son annabi lily ki zauna da matata lafiya kar inji kar ingani kar wata fitina ta taso aceman daga wurinki take,ina shaidar hafsatu indai wurin hakuri ne tana iya bakin kokarin ta dani da abinda muka haifa saboda hakan yasa na zakiga wani lokaci tayi ƙaura ta kama harkokin ta duk da hakan na damuwa ta wasu lokuttan amma muddin na tuna irin abubuwan da take fuskanta ina kokarin ma in ƙara mata ƙarfin gwuiwa kan ta zauna a wajen………..
Saboda hakan ne yasa ma na kara aure banida niyyar aure ko sha'awar aure haduwa ta dake yasa naji zan iya natsuwa dake wata kila hakan yasa itama matata ta rage wata damuwar da take ciki,sai kinyi hakuri dani dakuma duk yadda rayuwa zata sauya inaso muyi zama na amana sirrinki sirrinki ne,kamar yadda matata take rikeman sirrina tsawon shekara da shekaru kusan ta wnn ina girmama hafsatu lily,kiyi koyi da halayen ta,kawaici kauda kai muddin kikai haka zakiji dadin zama dani kuma itama zakiji dadin zaman da ita matace wacce tun a duniya zanyi shaidar ta wlh batada matsala ina fata kema zaki zauna da ita tsakani da Allah?……………..
In Shaa Allah banshigo gidan ka dan kawo maka wata tangarda ko cikas a rayuwa ba,nashigo gidan ka da niyyar aure,zama kuma na har abada zanzame maka mata ta rufin asiri in kareka inda miji yake bukatar kariyar matar shi,inyi fada a inda mata ya kamata ta kare mijinta in kaunace ka kamar yadda manzon tsira ya kaunaci Nana A'isha fatana daya dakai kayi mana adalci karka raba daya biyu duk abinda kayi mata nima kayi kokarin yimani indai ka tsayu ka ginu akan adalci nikuma bazaka sameni mai tada maka husuma ba nayi alkawarin haka,nagode lily wani french kiss ya shiga aikata mata tana maida mashi martani da tsananin jin daɗin hakan……………..
Kai innalillahi idan a kafiran farko kazo wlh zakayi wuyar sha'ani duk yadda muka nuna maka tafiyar nan baci bace kana nan kwance rai hannun Allah saida kayi applying haka? tafiyar me zata amfane ka da ita?can bakasan kowa ba ko fira kayi damu,kana arewa sai kafijin dadin zama akan wata lagos har wata shida idan change of environment kakeso ka dauki hutu mana ka tafi wata kasar ka samu good 2 month amma sai Lagos kuma kasan can headquarters ne ba hutu kullum sai ka fita office………..
Duk lokacin da nake bukatar dawowa kano zan dawo fa batareda nasha wahala kamar contract ne zanje idan naga bazan iya ba zan dawo gida but for now ina da buƙatar yin hakan nikadai nasan me nake going through kuna ganina ne kawai, Sufyan yace abby ya sani?a'a yanzu muna hanya fa sukayi approving request din nawa idan na koma gidan zan sanar dashi dole in tafi Saturday ko Sunday naga a letter Monday sukeso inyi reporting,toh Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi……………….
Ameen cigaba da labarin su na matasa sukayi sai 10 galaxy ya sauke shi gida bakowa gidan nasu kowa yashige dakinshi yashiga duk wasu abubuwa dazai bukata ya fara sorting dinsu out,har kusan 12 na dare sannan ya kwanta da tunani kala kala a cikin ranshiiiii🥹🥹🥹🥹🥹…………………
Jimmmmm dukkansu sukayi mamace ta kalleshi kanshi a kasa tace ni gaskiya ban farin ciki da tafiyar nan taka,idan ka tafi banida wani babba namiji dazai tsayamun a gida kenan kazama dan kanka sai abinda ranka keso zakayi baka isa kayi shawara damu ba, Abby ya kalleta yaga bacin rai sosai ya sassauta murya maman yara kiyi mashi hakuri,duk namiji ba'a sanshi da zaman gida ba adam na'am abby banji haushin ka ko daya ba wlh kuma inada yakinin nasara na tare dakai amma daga yau duk abinda zakayi ka nemi shawarar iyaye, Allah yasa hakan shine alkhairin ka wata shida kamar gobe ce ga mai tsawancin kwana………..
Abu daya nakeso dakai duk bayan wata biyu zakazo ganin gida muddin kayi haka na amince,In Shaa Allahu abby zanyi kokarin hakan mama dan Allah kiyi hakuri abby ya ari bakin ta bakai mata laifi ba tashi kaje Allah yasa albarka Amin,da harara mama ta rakashi har ya fice,abby ya kalleta namiji idan yana cikin irin halin da adam yake ciki ƙaura yakeyi kuma koda adam baiyi kudirin haka wallahi kinji na rantse maki nayi niyyar daukar shi muje hutu zuciyar shi ta samu sauki ya samu salama,ke macece bakisan namiji yadda yakeji ba muddin bai samu abinda yake so ba kiyi mashi uzuri kuma kibishi da addu'a kawai………….
Mama ta numfasa In Shaa Allahu Abby,bansan yaushe adam ya fara irin wnn soyayyan ba,koda a mafarki akacema shikeson lily haka saina karyata amma kiri kiri abby kana kallo lokaci daya yaro ya susuce,ina sane na hana adam auren lily niba karamin mutum bane na ansa ma wani aurenta dan yana ɗana ina dauki diya in bashi wadda kullum basu zaman lafiya,kuma nayi mashi hakanne yadda gobe ko kwallon mangwaro yagani yana so to da gaggawa zai furta bazai kara bari yayi nauyin baki ba,da in masu aure kullum ana kaikawon kawoman kara ina hanyar zuwa rabon fada……………..