SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)

Page 20

by @smauta





Shekaran jiya abokiyar zaman lily tadawo daga kasashen waje yau ita kuma lilyn da kanshi alhajin ya dauketa yakaita main house domin ya hada kan matan shi,bayan zama ya wakana daga lily sai uwar gida ta kalli lily tsaff yarinya karama shakaf tace lily naam ummi dan haka yaranta ke kiranta dashi,hakanan matar alhaji taji son lily a ranta,ahhh gaba kya tsine.............




Inaso ki dauki a matsayin kawa kuma yar uwa abokiyar shawara koda ba kowace shawara ba amma yazama mun hade kanmu mun ciyar da mijinnmu gaba duk da nasan na girmemaki ko ince nahaifeki ma,sirrin gidanki sirrin ki ne ba komai ake kwashewa a gayama uwa ko uba ba wani abun yanason kaida kanka kayi nazari ka gano mafita sai abu gagarumi ake fada duk da nasan anmaki wannan nasihar nima zan kara dan yanzu kin shigo wata rayuwa da abayaba irinta kikai ba,ki natsu ki kula kisa lura duk wani canji ko sauyi da zaki gani a gidan auren ki kizama mai hakuri karki gigita ko ki budema mutane sirrin ki a rayuwar yanzu sirrinki naki ne........






Dan Allah ki rike amana kizama yarinya tagari wadda miji zaiyi alfahari da ita kinji ko lily tace eh nagode ummi,kinyi makaranta kuwa ko business kikeyi lily tace ehhh nayi nagama service business kuma gskia banida interest akai bansan matsaloli,ummi tayi Daria tace gskia kam muma gamu a ciki munata fama saidai alhamdulillahi idan kika saba yanada dadi zaman hakan nan bayayi ki kara shawara dai kinji ko,nagode ummi haka ummi taitajan lily da labari har magriba alhaji bai dawo ba koda ta idar da sallah kiranshi tayi taji shuru sai yake cemata ai tunanin shi ma nan zata kwana dan yaga alamun hade mashi kai zasuyi hahaha 😄 kasan fa yanzu da wuri nake bacci nidai ka dawo ahhhhh cema hajia a baki mota daya a gidan nan ki koma gida,yanzu dan Allah bazakazo ba mar'atussaliha kiyi hakuri gobe da sassafe zanzo wurin ki sai lokacin ta tuna da mai mata take aure fa yau zaa fara raba girki wani abu taji ya taso mata ta fito parlor kan waya ta is keta tajira tagama,lily alhaji ne yace ki dauki mota ko driver ya maidaki aaaaaaaa noo badamuwa zan karasa dakaina ba nisa,har gaban motar ta rakota sukaima juna bankwana lily ta cilla kan motar sai gidan ta..............





A bangaren ya adam yau satin shi daya a lagos kuma zaman garin ya masa dadi yayi abokai a compound dinda yake na office dinsu wallahi har jikinshi ya fara dawowa sai yar damuwa kadan wacce baa rasa ba,ba abinda ke damunshi aikinshi yake hankali kwance kullum zaiyi waya da iyayen shi da abokan amanar shu har suna tsokanar shi gandar yarabawa ta anshe shi,ilai yau din ma yana kan hanyar shi ta komawa gida a motar da office ta bashi ya kira galaxy yane tazuru mai Lasisi kaifa iskancin ka yawa gareshi,galaxy ne yace masa kuma wlh dazu nayi tunanin kiranka na tuna kana office nace bari in bari magrib tayi nasan ka koma gida,yeah ya ake ciki ya kano?kano normal ba dadi bakanan kabarni da dan iskan nan kaima dan iskan ne ai................






Maganar project din nn naka daka fara kasan shi gini baiso a farashi a tsaya kuma ga damuna,katse shi adam yayi yace nifa na gayamaka wannan gidan ko maganar shi wlh banso kunayiman plan dinda nayi akanshi Allah baiba galaxy bazan iya rayuwa da kowa a gidan nan ba wallahi shiyasa kaga na kyale ginin nan,zan sa a samo dillalai zan saida shi idan yaso in samu wani wuri is saya amma for now Idasa ginin nan ba nawa bane zai tasoman da wani ciwo ne kawai wanda ya fara warkeman zaisamun ciwon kai da damuwa ne,kai dallah dakata Shima galaxy ya katseshi wai lily itace kadai mace diyar gwal ce da komai akai magana kace bakada interest wallahi ko zaka mutu wannan gidan baa saidashi ya yarinya tana gidanta tana jin dadin aure kai kana fama da sonta na banza da wofi karya kake wallahi,bari kaji in gayamaka tun muna mu biyu adam ka cire son wannan yarinya a ranka idan akace ma yanzu ciki gareta karka gardandata, rumtse ido yayi jin maganar ciki innalillahi waiinana ilaihir rajiun ya ke furtawa a ranshi ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba galaxy adam kasa tukin yayi ya faka gefen titi saida galaxy yai mashi kaca kaca,wulakanci da yayi masa da maganganun da ya gayamasa akan lilyn kawai yaji lokaci daya nan take kuma soyayyar lily kamar an mashi kurciya da ita,hakanan ya fara tuno rayuwar shi ta baya da abubuwan daduk ya aikata..........





Lallai so balai ne amma a yanzu Allah ya kawoma adam karshen nashi