SOMEONE'S HEART DESIRE(Abinda zuciya ke so🤩)
Page 21
by @smauta
Kamar yadda wuni da lokaci sukan shude a kuma lokaci kankani yadda rayuwa da rana takan juya daga safe zuwa duhun dare haka yau ranar lahadin karshen mako ta kama wacce tayi daidai da watan adam biyu a birnin ikko lahadin da tayi daidai da ranar da zaya ziyarci mahaifar sa kamar yadda alkawalin ta ma Abby duk bayan wata biyu zaizo,tsugunne yake gaban akwatin sa yanata hada kaya kamar yar mace dan adam mutum ne mai tsafta komai nashi tsaf daure yake da towel kugunshi yagama hada akwatin shi tsaf parlor ya jawo ya ajiye shi ya koma ciki duk wani abu na electronics ya hau disconnecting dan zai samu kimanin sati daya a garin kano.............
Isowar adam gida keda wuya Sarah ta cukukiye yayan nata tana murnar ganinshi a ranar da zaya tafi haka ya rabu da kanwar shi tana kuka cikin bakin cikin rabuwa da dan uwanta,mamace tace ke sake shi dalla ya zauna sufyan ne ya dauko shi dama ya ida shigowa da akwati shi suka gaisa da mama ya bigi kafadar adam yace mazaaaa zan bace adam ya kalleshi da kyau zaka bace ina?sufyan yace ahhh mai iyali har sai an tambayi ina zayaje wannan sai kai ai😂😂😂Mama kuwa tayi karaf tace yawwa sufyan gayamashi dai so yake saimun mutu bamuga tsatson shi ba,ga kannenshi duk mun auras wannan ma data rage inaga ina itama sai tayi adam na gidan....
Sufyan ya kara fadada dariyar shi yace aa mama dan Allah karki mana wannan fatar 🤣🤣kanne nata mana overtaking gskia a dakata da bikin Sarah nan ajiramu,ajiraku a ina kullum ina kuka fito aiki ina zakuje aiki inji ya gayamaka rashin mutuncin daya shukaman bayan tafiyar sa,diyar yar uwata na samo mashi yarinya natstsa amma ya rufe ido ya tatama diyata wulakanci wai akwai wacce zai aura nidai banganta saidai ko aljana ta aureka ko adam,kaiii mama aljana kuma mama,yo eh mana inba mai iska ba wake abinda kakeyi Abby ya dauremaka gindi da zaya daka ta tawa wlh da tuni an daura auren nan da ummuna lagos kawai zan turota in yaso ka kawoman gawar ta..............
Sufyan yace ahhh mama bazaayi haka ba,aure lokaci ne zaiyi ni dakaina zanzo in kawo maki tsegumin mun samu mata mama aitamana addua,inayi kuma zan kara mama nizan wuce tsaya kuci abinci mana sufyan, Allah mama alhamdulillahi ya kalli adam na wuce sai anjiman ko Allah ya huta gajia,har bakin mota ya rakashi suna firar su sufyan yaga yadda adam yayi kyau yayi wani irin fresh tabbas wannan tafiyar dayayi alkhairi ce ya tuno lokacin da ya dakko tsanewa ya tsamure saboda tunani amma a wata biyu gashi har ya maido jikinshi ya yarda kam idan kana cikin damuwa to ka dagama inda damuwar taka take kafa da yardar Allah sai kaga canji..............
Yau dan aljanna zai dawo wurin lily tuna ta tashi take kalkale gida competition ya tashi ta gyara can tayi wancan girki kuwa saida tayi masa kusan kala ukku rayuwa take gudana a gidanta zaman farin ciki da soyayya mai karfi da mijinta,har 8 no dare bai shigo ba ta kirashi harta gaji sai wuraren 10 taji shigowar shi a lokacin ta cika tayi fammmm,yasan yayi laifi Shima da fara'ar shi yashigo gidan yana kiran yar kwain tashi lily lily mar'atussaliha tana zaune akan dinning inda yake bata kalla ba har ya iso inda take ya ajiye ledar hannunshi ya kalleta da kyau sannan yace mai kyau bata fushi,lokaci daya annurin lily ya haska har fararen hakoranta suka bayyana......................
Kwance take akan jikin dan aljanna tace mashi dan gobe inason zuwa gida, kallonta yayi sosai zuwa gida ina gidanki kibari saina koma wurin zainab yadda zakije ki wuni a gidan badan ranta yaso ba ta hakura daganan salon firar nasu ya canza zuwa wata zazzafar soyayya da har yanzu lily jikin ta bai ida sakewa da ita ba🥲kuka take tana bashi hakuri amma yau zafin ya samu nama idan har ban manta ba tun aurensu yauce rana ta ukku da mu'amala ta aure tashiga tsakanin su🙄🤨🤨🤨🤨🤨jama'a dama nace har yanzu akwai irin mazan nan.............
A duk ranar da wani abu zai shiga tsakanin lily da mijinta tana tashi da karuwar son mijinta sosai da har takan iyajin a rayuwa ba abinda zai iya rabata da dan aljanna duk wani jin dadi na gidan duniya a gidan mijinta tana samun shi,yau girki zai fita hannunta duk batajin dadi kawai ranta nata raya mata yanzu duk abinda takeyi da mijinta itama haka zai koma yayi da waccan sarai yagane kuncin da takeyi abinda da tsohon hannu haka ya zauna yanata lallashin lily har saida ya shawo kanta,wani irin deep romance ya bata kafin ya barta wanda zai kwana biyu tana tunawa da dan aljannar ta tsoho mijin yarinya indai soyayya ce kubar masu😁😁...............
Mama wai dan Allah kiran me kikeman kamar makauniya kullum girma kuke amma kasa kukeci kai mama bafa wani abu bane lily ta kirani wai gatanan zuwa gida kwana zatayi ma,adam dake kwance kan 3 seater kirjin yace rassssss,mama tace kwanan uwar wa da gidan mijinka lily fa batada hankali duka yaushe akai auren har an fara fita,Sarah tace cab mama lily aiko tana fita nan ne kawai batazo ba amma yana barinta tana fita,a ran adam yace kaga illar auren tsoho su saki mata sakaka freedom din yawo da bata samu anan ba shi can yabata mtswws.............
Tace kuma dan Allah kimata gurasa wai diyar baba nason gurasa ke rufeman baki marasa kunyar banza,Sarah tayi daria kai mama kika sani ko dagaske take dan Allah kiyi mata mana,yaushe zatazo ne yanzu taceman zata gama shiryawa saita fito Allah ya kawota lafiya,adam rumtse idon shi yayi kamar mai bacci dan wannan maganganun da sukeyi kamar ana diga mashi dalma a tsakiyar ka haka yakejin su ba wanda ya kula dashi mama tashige kitchen Sarah ta koma sama abinta, shi kadai a parlor tun tunani na mashi dadi har ya daina,tsulum ya mike kofar da zata sadashi da sashen abbyn su nan yashige bai zame ko ina ba sai kan kujerun dake jere a makeken dakin abbyn yayima kafadar shi masauki a wurin........