Chapter[01
*No 14 BAKIN FADAMA,ZARIA LOCAL GOVERNMENT,KADUNA*
Aure abune dakowwa keso shiyasa idan mutum zeyi aure seataru atayashi murna da fatana alheri.
sedai akowani zaman aure akwai ƙalubalen dayake cikinsa ko wasu maaurata sunada nasu ƙaddaran kamanni zan iya cewa aure sine yazamo silan zuban hawayena.
ya canjamun ƙaddaran rayuwana koda wasa bantaɓa zaton bazanyi rayuwan farinciki agidanaba.
inatausayama macenda mijinta yakasance mara tsoron Allah zinane ko jaraba?!..nakasa ganewa ayanzu zaɓi yana hannuna farinciki ko rayuwan ƴaƴana!!
idan har nafita nabar gidannan to bama kawa rayuwan ƴaƴana zesamu matsala bazan'iya cewa gakalaba amma inada tabbacin duniya zatai alawadarai da halayensu da dabiunsu to
"saiki zauna baƙinciki ye ajalinki?!..ciwon zuciya ko hauka dole asamu ɗaya"
wani sashi nazuciyanta kefaɗi cikeda rauni.
hawayen dabatasan rananda zasu daina zubaban mata banesuka samu daman zubowa asaman fuskanta sedai batadamu data sharesuba.
agogone yabuga ƙarfe 2:00pm nadare wanda yedai-daida turo ƙofa.
megidanne yashigo dubada babu wani tsoro ko shamaki ataredashi kaman ƙadangare haka yalafe ajikin bango batareda yarufe ƙofanba hannu tasa taliƙe hancinta sakamakon gurɓacewan iska da akasamu.
anatse tanufa ƙofan ganin yana yunƙurin yin'amai yasanyata kamashi takaishi bayin dayake cikin ɗakin.
amai yahauyi kaman ƴan hanjinshi zasu fito tabakinshi.
akullum mamaki takeyi akan meye abinso ashan giya?bayan wahalan dasukesha idan sunshashi ga zubadda ƙima gakuma tarin zunubi a'addinance.
dakanta takamashi takaishi ɗaki jin ana wanke bayin yasanyata zama taname dafekanta.
kuka takeyi akan makoman rayuwan ƴaƴanta idan sungirma.tasani dole watarana se ƴaƴanta sun zubadda ƙwalla fiyeda nata.
da ƙyar taiya miƙewa takwanta agefenshi badon tai bacci taji daɗiba sedon tasamu tamiƙe gobe daƙarfinta idan Allah yayarda.
_***_
Zaune take akan sallahya tanajan carbi, tanajin kakauniyan Adam dayake tafaman kaikawo kaman wani ɗiya mace.
Mahmud ne yashigo ɗakin bakinshi ɗaukeda sallama muryanshi atausashe.
zama yayi abakin gadon yana kafeta da ido adduan tashafa tagyara zama taname fuskantanshi dakyau bayan tagaidashi yaamsa tacigabada faɗin
"Abban Adam roƙonka zanyi akan abinda nakeroƙanka akodayaushe bazangazaba wurin gayama bamuda lokaci ayanzu,
rayawarmu banamubane face na ƴaƴanmu duk abinda zamu aikata yakamata muɗaga ido mudubesudomin sune madubin rayuwanmu.
wallahi aduk sanda kadawo awannan yanayin nabuguwa atsorace nake saboda kada wani dagacikin ƴaƴanmu yaganka,
idan mutane sukazo akan kacimusu kuɗi jikina harɓari yakeyi wajen biyansu donkadawani dagacikinsu yaji,
nakasa sakin jiki dakowwa agidannan saboda kadawatarana musamu matsala suimun gori ƴaƴanmu suji sedai kash!!!duk wannan ƙoƙarinnawa seda Adam yasankomai do...
"khadija!!"
Mahmoud yakatseta cikin tsawa da hargowwa ƙwallan dasuka cikamata idone suka samu daman zubowa yacigaba damagana.
"cikin tattausan harshe yaname kamo hannunta khadija wallahi bahakabane,wannan itace ƙaddarata kitayanida addua kan Allah ya yayemun nima baasanrainabane k....!!!
"Ƙarya kakeyi Mahmud Allah bayataɓa ɗorama bawansa abinda yafi ƙarfinshi balle kai son zuciya ne kawai yasa kazamo maƙaryaci mazinaci kuma mayau...!!!"
saukan Marin datajine yasanya sauran maganannata maƙalewa amaƙogaronta,
wani irin siiiii....!!!!takeji akunninta takasa yarda wai yau Mahmud ne yamareta kankaceme hawaye sun wanke mata fuska.
dayatsa yanunata akausashe yahau faɗin
"khadija karkiga ina lallaɓaki kiɗauka kowani shirme zanɗauka wallahi dagayau idan harkika sake kuskuren kiranada waɗannan mugayen sunayen hmmm!ye ƙwata kamun yaɗorada"kiɗora amizanin ƙwa-ƙwalwanki."
waniirin zafi takeji aƙirjinta daɓas tazauna tana kallonshi yaɗiba ruwa abokitin heater yawuce.
Adam dake sharan falo yaji komai idanunshi sunkaɗa sunyi jajir kaman garwashin wuta
yasharce hawayenda suka zubomai batareda yasan lokacinda suka zuboba yanajin tsanan Abbansu naɗarsuwa afilin zuciyanshi.
nandanan yahaɗamusu abin karyawa ƙanninshi guda uku yatada kowanne seda yakaimai ruwan wanka harbayi bayan sunyi shirin makaranta suka fito palo domin karyawa.
Mardy yakalla yace"takira ummansu "
fuska ta yamutsa tana kallonshi cikin ido tace
"gaskiya nina gaji gasu Mubeen nan"
ranshine yaɓaci nan danan yadakamata tsawa yana cewa
"bangadaman su Mubeen ɗinba seke zaki tashine kosena kare-rayaki."
baki taƙara turowa tana magana ciki-ciki
Zuciya taciwoshi besan lokacinda yaman garetaba.
dama meneman kukane aka jefeshi dakashin awaki,kuma tasan ubannata bayason laifinta sonta yakeyi kaman ranshi don tanada sunan mahaifiyanshi.
Mahmud dafitowanshi kenan daga ɗaki yaga Adam yadaketa betsaya tambayan dali-liba yakamoshi yakifamai mari kyawawa guda biyu.
yariƙo Mardy dake kuka kaman shima zeyi kukan yahau rarrashinta.
duk abinda kefaruwa Ummah khadija nagani dasauri taƙaraso wurin Adam dake tsaye gefen bakinshi har yafashe tafin hannunta tasa ashedan yatsun Mahmud dayakwanta ye jajir asaman fuskanshi abinkada farar fata.
jin hannun mahaifiyanshi afuskanshi yasa yaɗago yakalleta dasauri yasa hannu yasharemata hawayen tausayin shi dasuka silalomata batareda sanin taba.
Ahankali yabuɗe bakinshi sautin muryanshi yafito dawani irin sanyi naban mamaki
"Ummah don Allah kidaina kukannan banaso zaniya jure komai amma banda kukanki bakiji yanda nakejiba"
ganin taƙi kokallonshi yanyashi ɗora hannunta akan ƙirjinshi dai dai saitin zuciyanshi.
jin zuciyanshi nabugawa dasauri da dasauri yasanyata kallonshi atsorace,
dawani irin nisantaccen yanayi amuryanshi yasoma magana,
"'aduk sanda hawayenki kezuba haka nakeji 'idan kuma natina mahaifinane ye silanzubowansu se'inji tsanan...."
dasauri ta toshemai baki tana girgizamai kai,
idanunshi yalumshe batareda yace komaiba yarun gumeta.
*ZANNA COMPANY,KANO*
Zaune take acikin office ɗinta dayasha kayan alatu na more rayuwa.
kallo ɗaya zakaimata kasan ta-tada kai dawasu iyayen kuɗi.
sedai matsalan ɗayane shine damuwan daya lulluɓe ciki dawajen duniyanta kaman ƙaton bargo.
"hajiya Mainah! what wrong with you"
ƙawanta Munari tafaɗa taname taɓa hannunta datai tagumi dashi.
Afirgice taɗago ganin ƙawarta kuma aminiyarta data zame mata ƴar uwa.
Hakan yasanyata jin dukwani rauninata yataso,hawayene suka cikomata ido,talumshesu tanajin yanda suke gangarowa har cikin zucinyanta.
"subhanallah hajiya Mainah menake gani haka?!"
"hamrah"
tafaɗa tanajin yanda ambaton sunan ta kaɗai yasanyata samun sauƙi danganeda halinda take ciki.
tun satin dayagabata har'izuwa yanzu dakuma sauran lokutan dasuka ragemata araye dukda batajin zatai tsawon rai saboda ƙaddaran dayasameta.
"wace_ce'ita"
hajiya Munari tatambaya cikeda kulawa.
seda tashaƙi iska tabasar sannan tabuɗe baki sautin muryanta tafito
"Matan yaron mijnane yau sati ɗaya kenan daye ciwo mun dawo daga super market mukabiya muka gaidashi.
naga mata kala-kala,haka nayi mu'amala damatan dabansan adadinsuba sedai 'itah!! Hamrah tadabance soyayyanta da buƙatan ta lokaci guda suka diranmun.
harga Allah naso namanta daitah kodan alfarman cikin dake jikinta amma wallahi nakasa da duk numfashin dazan shaƙa dayanda takeƙarasamun wuri tazauna azuciyana.
sau biyu ina zuwa daniyyan gayamata amma nakasa saboda wani abu daya girma kwarjini da haiba atareda itah narasa yanda zanyi."
murmushi Munari tayi meƙunsheda ma'anoni maban-banta.
tamiƙe tace "biyoni"
Hajiya Mainah batai gardamaba tamiƙe don dama zaman office ɗin yaisheta tunda dama tazo batai komaiba.
kasantuwan itace C.E.O.nakamfanin da mijinta yamallakamata shiyasa batanimi wani uzuriba,sectariya taimata adawo lafiya.
motan hajiya Munari suka shiga bayan hajiya Mainah tacema drivernta yakoma gida.
seda suka fara tafiya sannan hajiya Mainah tacemata inazasuje? irin dai murmushin ɗazu tasakeyi me ma'anoni maban-banta wanda yarigada yazamemata jiki.
"'inda za'asharemiki hawayenki"
taƙarshe maganan adai dai lokacinda sukai parking akofar wani gida dayakasance madai-daici abayangari,
Yanda hajiya Munari tashiga gidan kaitsaye batareda wani shayi koniman iziniba shize nunamaka baƙaramin sabo sukayi da koma waye mamallakin gidanba.
ɗaki ɗayane afilin tsakar gidan anyimai ginin ƙasa tareda rufin jinka.
suna'isa kofan ɗakin sukaji sautin dariyan wani mutumi muryanshi meamo yana cewa,
"hajiya Munari da ƙawarta hajiya Mainah"
Irin murmushin nandai taƙarayi asanda takalli ƙawartata,
ciki suka shiga suka zauna agaban wani baƙin mutum tittirnadashi,gashi mummuna wani irin muni dabata taɓa ganin wani ɗan adam da kalanshiba.
sanye yake cikin wasu kayan fatu da tsiraicinshi kaɗai suka rufe.
Masu karatu kuyahaƙuri anan zamu tsaya,semun haɗu a chapter two.
Dafatan dai labarin yaƙaya tardaku wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya.
Pls kuimana comment sannan kui sharing zuwa group group naku.
Taku Hinadatu Auwal
Se anjima.......
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر*
® By Hindatu Auwal
HIKAYA WRITERS ASSOCIATION
ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN
FACE BOOK:
WHATSAPP:ZAREN KADDARA HAUSA NOVEL GROUP
AREWA BOOKS:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
_______________________________________