ZAREN KADDARA

CHAPTER [4

by @hindatuauwal

"I Miss you more and more"

Itama mantawa tayida komai tarungume ɗiyarta.tana shafa bayanta cikeda so da ƙauna gamida kewanta.

"zakisha mamaki idan kika karyamun mata."

yanda yemaganam cikin sigan raɗa yasa bawanda yaji sesu dayayi dominsu.

dariya sukayi suduka tasaketa tai hugging ɗinshi titely,cikin hausanta dayasauya tace

"'inayi,'a'a beyiba nayikewanka "

"da larabci nakeso"

yanda tai magana dayanda shima yayi yasanyasu darawa,

"nan bawurin magana bane muje gida". Hamrah tafaɗa tanajanmata akwatinta guda ɗaya.

haka suka nufa motannashi ƙirar BMW fara mekyau da itah.

hira sukeyi sosai Asma'u naganin cigabanda akasamu akano.

ahaka suka iso ƙofan madaidaicin gidannasu.

packing yayi suka fito shima fitowan yayi dayike ajikin garejin dayake jikin gidan yake ajiye motannashi saboda tsakar gidan bayada wani yalwa kuma yana ɗaukeda rijiya se kitchen da bathroom dayake facing ɗinka inkashigo.

fanfo nacan wurinda akatanaza domin yin wankewanke da ajiye dosbin ɗin shara.

falon tabuɗe ƙamshin tira-ren tsinke da air freshener sukaimata oyo-yo talumshe idanunta taname tina yarintanta.

bawasu kayabane afalon zuwa madaidaicin dining ɗinda zesadaka da kitchen.

kujerune masu kyau nazamani sekayan kallo da ƴan decorations ɗinda baza'arasaba.

3bed roomne acikin palon, ɗakinda tai daudalan yarintanta Hamrah tanunamata tana cewa,

"kishiga kiwanka sekifito muci abinci."

"to"

tace tana shiga ɗakin.

kamandai yanda tasani ƙamshine abu nafarko dayemata sallama.

sesabbinkayan furniture's ɗinda suke tafaman ɗaukan ido.

bakomai yasa tagane sabbibane se ƙamshin dasukeyi nasabunta.

madaidaicin gadonta 6/6dayasha gyara da pink ɗin zanin gado takalla tana murmushin jindaɗi tareda yinma iyayennata addu'a acikin zuciyanta.

farin towel ɗinda keninke akofan bathroom taciro.

kayan dake jikinta tacire ta ajiye ainda yadace sannan tashiga bayin.

ruwan wanka tatara abaho tai wanka.

kiraye-kirayen sallahn la'asar datajine yasanyata fitowa ɗaure da alwallanta.

ganin akwatinta aɗakin yasanyata gane Nury tashigo.

kayan datagani akan gado taɗauka tawarware,doguwar rigace ta'atamfa,ɗinkin bawani mehayaniyan kwalliyabane haka itakanta atamfan tanada tsada daidai siyan merufin asiri.

seda tagama tsane jelan gashinta dayajiƙe wajen wanka sannan tazauna agaban mirror tai shapha.

doguwar riganta tasanya tanajin kewansu datayi na lulluɓeta.murmushine kwance akan fuskanta hartai sallahn ta'idar.

kaman yanda Nury tacemata azaune tasamesu apalon.

tana isowa suka miƙe suka nupha dining room dake ɗaukeda kujeru guda biyar.suduka suka zauna.

"mezakici"

Noury ta-tambaya tanabuɗe kulolinda kewurin,fuskanta ɗaukeda murmushi tace

"duk 'abinda kikeso"

daganan suka cigabada hiran yaushe gamo,tanabasu labarin makaranta da rayuwan saudiyya.ahaka harsuka kammala.

batayarda mahaifiyannata takwashe flates dasauran abubbuwan dasuka ɓataba.

wannan ranan naɗaya dagacikin ranakun dabazasu taɓa mantawa dashiba.

*ZARIA*

Agajiye yazauna akan kujera murmushi shimfiɗe afuskanshi,yana kallon Ummah Khadija daketafaman karɓan kuɗi.

wata matace tahankaɗo labule tashigo fuskanta bayabo bafallasa.

"Mahmud nanan.."

gaban Ummah yayanke yafadi daƙyar taiya cewa

"bayanan"

Ƴar sandan dake bayanta tace,

"wancan ai yaronshine ko"?

"Eh"

Matan takalleshi don bawanda zega Mahmud yakalli Adam yace baɗanshibane.

banbancinsu kawai Adam farine shikuma mahmud yanada duhun fata,

"tom zamu tafidashi idan yadawo seyazo police station ɗin sabon gari"

"bayin Allah wai mekefaruwane"

Ummah ta-tambaya cikin yanayi na tsoro da firgici."

"Idan kunzo police station ɗin kwaji"

Ƴar sandannan tafaɗa taname kama hannun Adam daniyyan tafiyadashi,

dasauri Ummah Khadija tariƙota taname zubda hawaye tace

"baiwan Allah kitaimakeni kigayamun indahalin rufe maganan anan semurufeta."

kallon Matan ƴar sandan tayi alaman tafada?! tanuna mata

"eey"

don dama tazoda ƴar sandanne don Ummah Khadija tabiyata kuɗinta kuma gashi taga alaman za'asamu nasara.

"kudin zubi nakebin mijinki ₦70,000"

gwauron numfashi tasaki meƙunsheda abubbuwa mabanbanta.

jiki asanyaye tashiga ɗaki cikin kuɗin shinkafa taɗauko tabasu.

nan da nan gidan yaɗauka abinkada gidan yawa.

zama Ummah Khadija tayi tana sharce hawaye.

shima Adam ɗin zamayayi akusada ita cikin tattausan murya yace

"bansan mezanceba amma a'iyasanina ana aurene don raya sunnan Annabi to amma hakan bazesamuba harse ma'auratan sunacikin kwanciyan hankali sannan susamu daman samama iyalansu farinciki.

nasani kuwwa cemiki yakeyi kihaƙuri don ƴaƴanki sedai inhar haƙurinnaki yemiki yawa tobazamu samu farincikiba.

saboda dafarincikinki muke samun natsuwa,abinda nake nufi anan shine dakomai naki muke rayuwa."

hawayenda yakeriƙewane sukasami daman zubowa,hakan yasanyashi miƙewa dasauri.

kaitsaye shago yakoma wannan unin yayi shine cikin wani irin yanayi dababu kalman dazeyi adalci wurin bayyanashi.

shiyasa yadinga jinkanshi samasama,hatta mutanen dasuke tare seda suka fahimci haka.

*Mardy*

zaune take acikin motan se kawayenta Idayat da Fairuzah se uban gayya Marwan,

dakallo daya zaka gane kudi bamatsalanshi bane,dubada bewuce shekaru 22 ba.

"Dear zanwuce se'anjima"

Mardy tafaɗa tana ƙoƙarin buɗe murfin motan,hijjab ɗinta yajanyo yaname narke fuska kaman zeyi kuka.

ganin yanayin fuskanshi yasanyata dawowa tazauna tanabinshi dakallo mecikeda kulawa ganin haka yasanyashi sauke murya yanacewa

"gaskiya banson rabuwa dake yanzu pls kibari se'anjima"

"haƙuri zakayi nima ba'ason raina zanrabu dakaiba kawai banason nai latti dayawane aimun magana"

"kedai wlh Mardy anyi bush girl komai bazakiyi irinna wayayyuba"

faɗin Idayat,Fairuzah tacafeda,

"shiyasa wlh takebani kunya meye dunbaki koma gida dawuriba,yanzu kokaji sunsami freedom balle mutum,mutum ɗinma big Lady kamarki"

shiru tayi don batason wannan sunan dasuke kiranta dashi,shiyasama tafara kula Marwan.

dayabata wayama ƙin amfani tayidashi don batason surutun Ummah da Adam ga mahaifintada kullum bayida nasihan dayawuce karta dinga kula samari.

"Dear anjima zandawo da daddare"

marwan yafaɗa yanasakinmata life kiss ayatsunta,

dasauri tarumtse idanunta jikinta naɗaukan ɗumi don jitayi kaman yamannamata wuta sedai bazata iya hanashiba saboda ƙawayanta karsu kirata dasunan datafi komai tsana wato bush girl.

tunadukan datasha jiya yasanyata saurincewa

"no kabari mayiwaya"

murmushin jindaɗi yasaki,basuwani jimaba tafita tashige gida wanda sedataraka samarin kofar gidan da harara.

misalin 9:00pm Ummah Khadija tamike tashige ɗakinsu Adam duba kaji dama ɗakuna ukune a falon.

Mubeena datai bacci taɗauka daniyyan kaita dakinsu itada Mardy.tsayawa tayi cak! sakamakon abinda kunnuwanta sukaji.

"haba Dear yanzu photonki dakayan baccine bazaki turomunba.?wainikam anya kina sona?"

"mekakecewane haka?wallahi insonka fiyeda rayuwa dakanta"

marwan yadaƙile murya sosai yanacewa"

"Ƙarya kikeyi wallahi bakyasona"

Mardy taja numfashi kaman zatai kuka tace

"'idan dannaƙi turomaka photo nanekakecewa haka to zanturo amma please kanagani kagoge karka bari kuwwa yagani"

Ummah Khadija najin haka tashiga ɗakin idan tace maka tasan lokacin data ajiye Mubeena harta damƙi Mardy totayi ƙarya dukanta kawai takeyi tako'ina.

batasan kuka takeyi itakantaba sedataji tana shashsheƙan kuka kaman numfashinta zeɗauke.

zaman ƴan bori tayi awajen hannayenta dake ɓari kaman yanda jikinta keɓari taɗago takife fuskanta aciki,babu abinda kwa-kwalwanta keganewa balle tai tinani.

abudaya take tantancewa shine zafinda ƙirjinta yakemata sekanta dayakemata ciwo kaman zefaɗo,

kuka takeyi marasauti,kuka takeyi da dukkan abinda yemata saura arayuwanta,kanajin sautin kukan zakagane bakaramin ciwobane aƙirjinta.

Masu karatu kuyahaƙuri mu tsaya anan,semun haɗu a chapter 5.

Dafatandai labarin yaƙayatar daku,wannan littafin gaba ɗayanshi kyautane agareku masoya.

Don Allah kui mana comment,sannan kuimana sharing a group group naku.

Taku Hindatu Auwal

Se anjima........

*ZAREN KADDARA*

*حبلاالقدر*

® By Hindatu Auwal

HIKAYA WRITERS ASSOCIATION

ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN

FACE BOOK:

WhatsApp:ZAREN KADDARA HAUSA NOVEL GROUP

AREWA BOOKS:Hindatu Auwal

PHONE NUMBER:07943602834

______________________________________