CHAPTER[10
akan idanunsu aka fitoda ita zuwa theater room basufi 30mnt ba aka ƙara zuwa akawuce da ita zuwa ɗakinda zata huta.
shiga sukayi shida ita idanunta alumshe suke alaman bacci takeyi,fuskanta tayi fayau taƙara haske,nurse ce tashigo tabuƙaci kayanda za'asama jariran.
shida Asma'u sukaje suka ɗauko kayan acikin trolley ɗinta,suka sayi sauran kayan buƙata anan cikin asibitin.
Mahmud ne yabiya kuɗin theatern tunda yanadasu,akwai wani abu nadaban atareda jarirai iya kallonda zakaima fuskokinsu iya yanda soyayyansu da ƙaunansu zasu zauna acikin zuciyanka.
ganin dare yayi sosai yasanyashi cemata tazauna atareda ita shikuma zeje masallaci yajira.
"Asma'u_Asma'u!!"
can cikin kanta takejin sautin muryan Hamrah dake kiran sunanta idanunta taware akan fuskanta,tata fuskanta na washewa da murmushi,
"sannu Nury yajikinnaki"
"da sauƙi"
ta'amsata fuskanta ɗaukeda murmushi mesanyi.
"Asma'u"
takira sunanta tasigan dazata bata natsuwanta gabaɗaya,kasa amsawa tayi se zuciyanta datake dokawa wanda beyi kamada faɗuwan gababa.
Hamrah tasaki murmushin gefen baki wanda yaƙarama fuskanta cikan kyauda haiba,muryanta asanyaye tafito,
"kizamto me haƙuri da yafiya arayuwanki,kada kizamto ɗaya dagacikin mutane masu roƙo da son abinduniya.
kiriƙe martabanki taɗiya mace da addininki,kikasance mace mekamunkai bamai girmankaiba,akodayaushe kirinƙa gayama kanki rayuwanki banakibane kekaɗai.
komai zakiyi arayuwanki akwai waɗanda zetaɓa kobayan ranki,addu'a takasance makaminki,ambaton Allah yazamto sitiranki,duk rintsi dajin daɗi naduniya kadasu sanyaki kimanta asalinki naɗiyamace,musulma kuma hausa fulani.
don Allah naroƙeki kadarashin iyaye da ƴan uwanki najini yazamto makullin ruguza komai"
kantane yeshiru musamman zuciyanta,zaren tinaninta yatsinke ba abinda kekai kawo acikin kanta samada zantukan Nury,
"'ina abinda nahaifa suke"
se ayanzu Asma'u taɗago eyes balls ɗinta tasaukesu akan yarandake gefen Nury suna baccinsu hankali kwance,jiki amatuƙar sanyaye taɗaukesu tamiƙamatasu,kallonsu tayi na ƴan wasu daƙiƙu,fuskanta ɗaukeda murmushin dayagaza barin fuskanta takalli Asma'u tana cewa
"mene sunansu?"
"Nadr da Nadara"
dubanta tamaida zuwaga yaran,
"kiramun mutuminda yataimakemu"
"Tom"
tace tanufi bakin ƙofa kaitsaye,hannu takai dazumman buɗe ƙofan setaga ambuɗe taja baya tanagaida doctor Bilkisu da Mahmud wayan doctor ne yahau ringing tai picking tana jingina bayanta da garun ɗakin.
Mahmud yaƙarasa bakin gadon suka gaisa yaran tamiƙamai tanamai godiya taƙar ƙareda faɗin,
"Rayuwa tamkar littafi take,meɗaukeda shafuka maban banta,kaɗan daga cikinsu akwai farinciki da baƙinciki,rayuwa da mutuwa.
akwai abubbuwa dayawa damuke sonyi arayuwarmu sedai lokaci bayabamu daman hakan shiyasa ubangiji yakebamu daman yin wasiyya yakuma umarci bayin shi da'aka bama wasiyyan dasuyi iya ƙoƙarinsu wajen ganin suncikamai muradinshi.
banso ɗoramaka wannan nauyinba sedai banada wata dama bayan wannan dana samu ayanzu.
allonda aka rubuta yarigada yabushe.ba gogewa ba canjawa,zaren ƙaddara tarigada tahaɗe rayuwanmu alokacinda bamui zato ko tsammani ba ƴaƴa amana"...
faɗuwan gaba,tsinkewan zuciya,da daskarewan jini yaziyarci dukwani halitta merai,numfashi da sanin yakamata lokaci guda.
tundaga kalman ƙarke data furta muryanta akarye basusake jin amon muryantaba,suna kallonta tamaida bakinta tarufe,fuskanta yacikada annuri,haibanta da kamalanta suka sake cika idanunsu,har ƙasan zuciyansu sukaji sanyayyiyar ajiyan zuciyanta,tajuya fuskanta zuwa sashinta nadama seyazama tajuyamusu ƙeya.
wani irin yanayine mewuyan fassaruwa yaratsa atsakaninsu,kukanda jaririn yatsanyara shiyadawodasu hayyacinsu,gaban gadon Asma'u taƙarasa da dukkan wani abu dayemata saura arayuwanta tabuɗe bakinta.
"Nury_Nury kitashi yana kuka"
shiru batako motsaba balle susaran zata amsa,danauyi megirma taɗaga hannunta tagir gizata luww taga tabiyota tai aziman rungumeta ajikinta.
shaph tamanta likitan nataredasu acikin ɗakin,hakan yasanyata buɗe baki tanafaman kiran sunan likita,seda Asma'u takira sunan likita sannan tadawo cikin hayyacinta.
ta taka zuwa bakin gadon kallo ɗaya taimata tasan Hamrah tarigamu gidan gaskiya,domin ta tabbatar setakai hannunta zuwa saitin zuciyanta,shiru taji tashafi fuskanta daye sanyi ƙalau sedai babu abinda yacanja nadaga murmushi,annuri dacikan haiban dake kwance akan fuskanta.
wannan gaɓan da akekai yanzu yafi komai wahala awurin likitoci.
ɗankwalin dake kanta taciro cikin ƙanƙanin lokaci tawar-wareshi tarufe ƙayatacciyan fuskanta.
jitayi zuciyanta naneman shigewa cikinta,daƙyar taiya jawo jarumta taɗorama kanta tabuɗe baki yakai saubiyar amma bakalman daye nasaran fitowa.
se idanunta datazubama doctor Bilkisu,amon muryanta taji kalaman nazarcewa cikin kunnuwanta suna ajiye kansu a'inda bazasu taɓa gogewaba.
"Allah yemata rasuwa"
shine kaɗai abinda yake shawagi amasarrafan tinaninta,wasu irin emotionsne suka tasomata lokaci guda,kaman ansa baki antoshe wutan acibal-bal haka tinaninta yabushe acikin ƙwaƙwalwanta.
tanajin wani abu dabatasan komene neba yana kwancewa dagacikin ƙwaƙwalwanta wanda takeda tabbacin har mutuwanta baze taɓa komawa dai daiba.
kaman wacce parilise yakamama ƙwaƙwalwa haka tazama,gadai idanunta ƙureey akanta amma kanta fanko take awannan lokacin.
batasan metakeji da abinda yakamata tajiba,itada butun butumi basada maraba,tana kallo Mahmud da doctor Bilkisu suka fita basuwani jimaba sukadawo tareda wasu maza guda biyu.
suka ɗauketa suka sanyata agadon dasuka shigo dashi sannan suka tura gadon zuwa waje,se alokacin talumshe idanunta,
"Nury tarasu"
shine kaɗai kalman dayaratso tatsakiyan kanta,kaman wacce aka tsikara haka tamiƙe dasauri tanufi ƙofa kaciɓiss sukayida doctor Bilkisu,
"muje ko!"
doctor tafaɗi,
kai kurum tajin jinamata,tana gaba tanabinta abaya ahaka har suka iso inda motanshi take.
Masu karatu kuya haƙuri mutsaya anan,semun haɗu a chapter 11
Dafatan dai labarin yaƙayatar daku,wannan littafin gabaɗayanshi kyautane agareku masoya,don Allah kui mana comment sannan kui mana sharing a group group naku.
Taku Hindatu Auwal
Se anjima........
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
® By Hindatu Auwal
HIKAYA WRITERS ASSOCIATION
ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN
FACE BOOK:
WhatsApp:
AREWA BOOKS:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
____________________________________