CHAPTER [13
*Hajiya Munari*
Zaune take agaban jangudo,hannu yaɗora akan case ɗin da takawomai nakuɗin.
Yatsunsa yaɗora akan zip ɗin jakan dazimman buɗewa nantake iska meƙarfi yacika ɗakin.
baiya rufin ɗakinba hatta ginin ɗakin jijjiga yakeyi,hjy Munari tarumtse idanunta ƙam hanjin cikinta na yamutsawa don tsoro,hakan yahaifar matada zufa gamida ɓarin jiki.
Banda jangudo daya gyara zama da alama yasaba dawannan yanayin dukda atsorace take hakan behanata jin abinda yafaɗa atsawaceba.
"Basumutuba?ya'akayi haka?"
"Sedafa nafara ƙirga mutanen motan naga suncika sannan nabama Duna umarnin shanye jininsu,sannan akai ɓaddakama yazama hatsarin mota"...
Shiru da'alama yanasauraron maganane,jin yafara ɓaɓɓaka dariyannannashi yasanyata buɗe idanunta ahankali.
Hakan yedai daida sa'ilinda yakecewa"to hakanma yayi Iziddyn nidai taɓarayina banda matsala kuma zangin dayamusu sharaɗi kuma dole abi"yaƙarke damai fadanci.
Begamaba wannan guguwan yasake tashi irinna ɗazu,seda ɗakin yakoma dai dai sannan tasamu natsuwa yasaukar mata.
Muryan jangudone yaratsa masarrafan jinta batareda zato ko tsammaniba.
Baiya rantsuwaba hatta qur'ani zata iya dafawa akan bata taɓa jin muryanshi akausashe irin hakaba,
"ajiya munyi aiki nida Duna,sedai ansami matsala ba Hamrah bace acikin motan,seyanzu Iziddyn yake sanardani.
Yazo wucewa yaga munyi aiki kuma aikinnamu beyiba,sedai tun adaren yemaganin matsalan tahanyar kashe ita Hamrahn yasanyamata ciwonda yasajeda mutuwan fisabilillah,
itakuma yarinyan yatoshemata ƙwaƙwalwa dawasu jariran aljannu,tayanda bazata taɓa iya tina asalintaba dakomai nata dayawuce abaya.
Sedai shi Iziddyn ɗin yafaɗi abinda yakeso abiyashi dashi ladan wannan aikin.
yanada buƙatan abinnemai cikakkiyan budurwa daranta kuma idanunta abuɗe, fa'idan wannan aikin natareda samun nasara akan aikinda yayi akan Husnah.
Domin yanda budurwannan bazata iya tina komaiba balle tai tinani akai haka tinanin Husnah dayagabata zekasance.
Sharaɗin shine kuzakuyi wannan aikin dakanku,kuma idan kukaƙiji bazaku ƙiganiba."
Tunda yafara magana idanunta kekafe akanshi tako ina zufane keketomata,baki tabuɗe daniyyan yin magana amma setakasa sakamakon kallonda yemata yaname cewa
"Babu sauƙi babu rangwame acikin wannanaikin,yarage naku,kuyi ko kuƙiyi.sakamako nadaga abinda kuka aikata"
Batada nayi hakanan tamiƙe taimai sallama,wayanta taciro acikin hand bag ɗinta daƙasdin kiran hjy Mainah tasanarda ita halinda akeciki.
Kaciɓiss tayi da saƙonta natabar ƙasan,zuciyanta naluguden bugu tafara kiranta,sedai dayafara ringing seya katse alaman tasata a black list.
Hannu taɗora aka daniyyan runtuma ihu sekuma taɓugeda bushewa da dariya,badon komaiba sedon tinawada tayi hjy Mainahn tamantada ATM ɗinta ahannunta wanda tabata taje taciro kuɗinda zatakawoma jangudo.
Nantake tashige motanta zuciyanta wasai,kaitsaye gidanta tashige bayan megadi yabuɗemata gate.
Murmushi tasaki da alama wannan karon nasara natareda ita acikin tafiyannata.
takalli yarinyan da take tsaye tanajeramata kayan abinci'akan dining zuciyanta tarayamata.
Ɗiyar talaka ƴar ƙauye wacce iyayenta basu taɓasanin inda take aikiba tunda bataje gidabama,bama ajima da ɗaukotaba,abinda zatagayama wacce taɗaukota bazebata wahalaba.
Dawannan mafitan datasamu cikin sauƙi tashige ɗakinta,abari yahuce shiyake kawo rabon wani,da zafi zafi ake dukan ƙarfe hakan yasanyata kiran numbern Sambo.
Shiɗin yakasance mutumne wanda takesanyashi yake burnemata dabbobi manya da ƙananu shida yaranshi aduk sanda jangudo yabuƙaci hakan.
Koda tagayamai batasamu matsala dashiba,nan take yagayamata inda za'ai aikin da misalin 12:00pm.
Jitakeyi kaman ansaukemata wasu manyan kaya masu nauyin gaske dasuka farama rayuwanta barazana nawanzuwan tashin hankali,amma ayanzu datasamu mafita setajita sakayau.
_***_
12:00pm
Hajiya Munari takunna motanta,mai gadi yabuɗemata gate,Samirah nazaune akujeran me zaman banzatana waro idanu.
jitakeyi kaman tai fuffuke tabar cikin motan,can ƙasan ranta jitakeyi kaman kwananta yaƙare aduniya,sam hankalinta yaƙi kwanciya ahaka suka miƙi hanya tunsuna ganin gidaje haryakaima sejephi-jephi takeganin gidajen ahaka harsuka riski daji.
Tanaso taimata magana akan inanenan?shin nannne anguwan datace zata rakata?! buɗe bakinta yedaidaida tsayuwan motan.
Wasu majiya ƙatti tagani kowannensu yana riƙeda manyan touch light masu matuƙar haske,hjy Munari ta umarceta da tafito bamusu tafito.
Jitayi ɗaya daga cikinsu yafincikota kafin tagama fahimtan abinda yake faruwa taganta sheme sheme acikin ramin dasukai mai haƙi irinna ƙabari.
Idanuntane suka ciko taph da hawaye,koba agaya mataba tasan wani abune mara kyau zesameta nantake kewan ƴan uwanta yakamata,bata taɓajin haushi da tsanan kasantuwanta talaka kuma ƴar kauye irin yauba.
Don shine yajawomata mutuwan dabatasan sunan dazata sanyamaiba,Saukan ƙasa ajikinta yasanyata ware idanunta akan hjy Munari dake tsaye hankalinta akwance.
Wani janyawu tahaɗiye,muryanta adakushe tace
"menai miki dana cancanci wannan hukuncin?shin laifine danna kasance me'aiki aƙarƙashinki?koko laifine danna kasance talaka kuma ƴar kauye"?
Shiru hjy Munari tayi batareda taɗauke idanunta akantaba,hannayenta taɗaga hawaye nagan garomata daroƙo megirma acikin muryanta
"ya Allah naroƙeka kabimun haƙƙina,bansan kotaya yaba amma Allah kasa nazamto rai naƙarke dazata salwanta ta dalilin wannan baiwan ta.."
Maganan nata yakatsene sakamakon ƙasanda yarufe fuskanta,idanunta akafe akan saman al'arshi dayacika da baiwan ubangiji na wata da taurari masu haske.
Har akagama rufe Sameera takasa ɗauke idanunta akanta,tanajin yanda magan ganunta suke taɓata girmansu nazauna mata,daƙyar taiya janye ƙafafunta tashige motanta.
*MAHMUD*
Da sallama yashigo cikin ɗakin,mahaifiyanshi yagani itakaɗai azaune akan kujera se Asma'u dake zaune a'inda yabarta.
yazauna a jikin kujeran datake zaune sotakeyi suhaɗa ido amma yahana hakan faruwa.
Gyaran murya tayi kafin tace"Mahmud waɗannan ƴaƴan waye?"
Awannan lokacin datai tambayan ba abinda take muradin ji samada yaƙaryata maganan mutane,wallahi ko ƙarya yemata zata yarda.
Amsan data fito daga bakinshi tasanya zuciyanta tai tsawan hadarin gabas na tsakiyan ogusta,jitayi kaman ankifar matada duniyan ta.
"Ƴaƴanane"
Daƙyar tahaɗiye abinda yake tasomata tai amfanida damanta naƙarshe daze datse zaren ƙaddaran daya haɗatada waɗannan ƴaƴan.
"Mahmud ko ƴaƴankane kahaƙura dasu tunda kanada wasu,ka kaisu gidan marayu don billahil'azeem idan hardangin Khadija sukaji to zama tsakaninku yaƙare,saboda cewa zasuyi zakaɗauko cutan zamani kashafamata"
"Inna ba khadija ba ko duk duniya zasu juyamun baya saboda waɗancan yaran bazan damuba,khadijah acikin duniyata take sukuma waɗancan yaran rayuwatane.
Don haka zan iya haƙura da dukwani abu dake cikin duniyata saboda nasamu natsirada rayuwata."
Acikin muryanshi takejin matsayan zancenshi,wannan shine iya gaskiyanshi.
Adam dake tsaye abakin ƙofa tun sanda Mahmud yafara magana yalumshe idanunshi.
jijiyoyin kanshi nakumbura da ɓacin rai metsanani,kai tsaye ɗakin Ummah Khadija yanufa batareda yakalli bigirin dasuke zauneba.
Zuciyarshice tabuga kaman zatafaso allon ƙirjinshi ta tarwatse,ruhinshi naneman arcewa daga gangan jikinshi.
sedai hakan behanashi ƙwalla waniuban ihuba yana kiran sunan Ummah Khadija dake kwance arigin gine idanunta alumshe babu alaman numfashi atareda ita.
Dama tun tuni zuciyanshi takegayamai yazo gareta,sedai bayada abinda zecemata tasamu sauƙi,yanzuma daga masallaci yadawo yashigo yaganta don baze iya jurewaba.
Ihun Adam da sunan Ummah Khadija dayake kira cikin ficewan hayyaci yasanya Inna da Mahmud,haddama sauran mutanen gidan dake dakon jin ƙiriss suhallara suka shigo cikin ɗakin.
Ruwa aka ɗibo aka fara yayyafamata 'amma kogezau batayiba balle tasan anayi.
Inna tasaki salati cikin gunjin kuka tana faɗin,
"shikenan Mahmud ka kasheta,ka kasheta da baƙin cikinka"
haka tadingi mai maitawa,
Mardy ceh tashigo jikinta sanyeda hijjab da 'alama sallah taidarwurinda Adam ke zauneyana dafe dakan Ummah Khadija taƙarisa da alama ma bayacikin hayyacinshi.
"Ya-ya... Yaya"!!!!
Jin yayi shiru yasanyata ɗiban ruwan dake gefenshi wanda akaima Ummah Khadija amfanida shi tawatsamai.nannauyan ajiyan zuciya yakawo yasaukeyakalli Mardy da idanunshi da kallo ɗaya zakaimai kashaida akwai matsala.
"Yaya muje asibiti"
Kaman wanda parilise yakama ma ƙwaƙwalwa haka yakejinshi,tun daga ƙasan ranshi yakejin akwai abinda yakamata yayi,miƙewa yayi akan ƙafafu wanshi yasa hannu yatallafota.
Adai-dai lokacinne Mubeen da Mubeena suka shigo dagudu fuskokinsu shaɓe shaɓe da hawaye.
Mahmud ne yataimakamai a wannan lokacin bedamuda komaiba suka sanyata amota kai tsaye se asibitin New City.
Masu karatu kuyahaƙuri mutsaya anan semun haɗu a chapter 14
Dafatan dai labarin yaƙayatar daku,wannan littafin gaba ɗayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui mana comment sannnan kui sharing a group group naku.
Taku Hindatu Auwal
Se anjima......
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
®by Hindatu Auwal
HIKAYA WRITERS ASSOCIATION
ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN
FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only
WhatsApp:
AREWA BOOKS:
PHONE NUMBER:***
_______________________________________