ZAREN KADDARA

CHAPTER [17

by @hindatuauwal

"Sadauki kashemu zakayine?ubanme kake kallo haka"?

Sam yakasa ɗauke idanunshi daga bigirin datake ko kallon Nawaila beyiba balle yasaurareshi yabuɗe ƙofan ye ficewanshi.

Kai tsaye yashiga gidan betsaya wani tinaniba yasakai yashiga tsakar gidan.

Atsaye yasameta atsakar gidan wurin mai awara ga mutane maza da mata itakaɗai yakashe da ido.

Kallonta yakeyi babu ko ƙiftawa,yanda kasan ambashi kwangilan yin hakan.

Atsaye take amma setaji duk da tsargu,tanajin kallonda yakemata ako'ina najikinta.

Batasan wannan kallon batasan irin nau'in idanunshiba amma tanajin yanda suke mata rami agaɓban jikinta.

Ƴar ƙaraman muryandake kantane tashiga sanarda ita datai nesa dashi samm babu alheri ataredashi.

Batasan jikinta naɓariba sedata miƙa hannun zata karɓi awaran,bashiri tajanye hannunta zuciyanta tashiga bugawa kaman zata faso allon ƙirjinta tafito.

Tanufi hanyan ɗakinsu dasauri kaman zata wuce ƙafa funta,sotakeyi taimai nisa tadaina jin abinda takeji.

Ƙwaƙwal wanta da zuciyanta basutaɓa yanke hukunci cikin ƙankanin lokaciba irinna yau.

Shiɗin ba alheri bane tai nesa dashi shikaɗaine umarnin data samu.

"Na nawa zaka siya?"

Siddiƙa tafaɗi tana kallonshi.

Batareda yajuyo yakalletaba ya'amsatada

"Kisa mata wani"

Hannu yazira 'a aljihu yaciro 1k yabata,

Cigaba yayi da tsayuwa koze sake ganin tafito,yarigada yagama rasa tinaninshi da natsuwanshi tun lokacin daye tozalida ita.

Ta tafida zuciyanshi sa'ilinda yaganta akusadashi,tafi kyau akur-kusa haka.

Komai nata yafi kyau da tsari datake tafiyada sassarfa,betaɓa sanin yanada kwaɗayiba seyau dayaganta akusadashi.

Da gangan yakai hannunshi yataɓata don yasamu sauƙi amma hakan besamuba sema ƙaruwa da yayi.

Besan tsawon lokacin daya ɗauka atsayeba sedayaji ƙura nacikamai ido yaɗaga kai yaga hadari baƙin ƙirin,batareda ya motsaba aka fara yayyafi.

Jiyayi andafashi yajuyo yaga Nawaila me awaranma tashige cikin wani kafe itada tsirarun customers ɗinta.

"Kai wai lafiyanka "?

Hannu yasa yafara yamutsa gashin kanshi,yacije leɓenshi baki yabuɗe daniyyan magana sekuma yeshiru,yasake kallon ƙofan ɗakin tukun yajuya yakama hanyan fita.

Nawaila yabi bayanshi cikeda mamaki,akujeran mezaman banza yazauna.

"Sedaipha muje gidansu Wadata because driving bazeyuwuba ruwa akeyi sosai daƙyar nake ganin hanya."

Nawaila yafaɗa yanajuya kan motan zuwa layin gidansu Wadata,packing sukayi sannan suka shiga cikin part ɗinshi.

Tundaga balcony sukaji waƙan dake tashi,Sadauki yafara rawa dai dai da kiɗan dayake tashi,yanda yake taka rawan cikeda ƙwarewa zaka rantse da iya rawan aka haifeshi.

Yana shiga palon yaɗau sowa,sunan Kangiwa kawai ketashi,yashiga tsakiyan fili yaname cigabada rawanshi me burgewa da jan hankali.

Wata yarinyace tamiƙomai cup,maƙoshinshi abushe yake tunda yasanya ido akanta yaji maƙoshinshi yabushe,wani irin bushewane dabayada alaƙa da ƙishin ruwa.

Kai yagir gizamata alaman a'a,fuska tamarai raice kaman zata fasheda kuka,ye murmushinda yaƙara fitoda natural beauty ɗinshi.

Bakomai yakeshaba idan yaje wuri irin wannan,yakarɓa yakai bakinshi yana ɗan ɗana,cock ne amma seyaji ɗan ɗanon nashi yasauya,kallonda takemai yasanyashi zuƙewa batareda yashiryama hakanba.

Photon yarinyan da ko sunanta besanibane yashiga gilma mai indifferent sheet,tamanne aƙirjinshi tasamu wuri tayi ƙane ƙane.

Jiyayi hannunta namai yawo awurare maban banta,hannu yasa yatureta,beson komai besan kuwwa,itakaɗai yake buƙata,karo nafarko da zuciyanshi tarinjayi ƙwaƙwal wanshi.

Yanajin suna tambayanshi inda zeje amma yemusu banza,yanada tabbacin koyabuɗe bakinshi sautin muryanshi baze fitoba,komai nashi yadaina aikin da akasanshi dashi yakoma ambatonta.

-----

4:15 Mahmud yafarka,Asma'u tamiƙe takira doctor Bilkisu,nantake tadubashi,duk da jininnashi besaukaba haka yadage se'an sallameshi.

Batada yanda zatayi don yamatsa,ga Asma'u duk tatakure don ko abincin data aikomatadashi bataciba,sauƙin tama ta tahoma su Nadr da madaransu.

Hakanan tasallameshi,sebayan tafiyansu sannan taga ledan maganinsu Nadr dasuka siya ga wayan Mahmud shima,sakawa tayi ajakanta tana ƙudurcema ranta inzata tafi gida seta kaimusu tunda duk hanyan ɗayane.

♦♦♦

Tabayan layinsu me adai datan yasaukesu,gashi lokacin har anfara yayyafi,shiyasa suka shiga taƙofan baya wanda kai tsaye zesadaka da sashin Inna.

Ruwanda aka kece dashi lokaci gudane yasanyasu shigewa ɗakin Inna.

_***_

Da duk taku ɗaya dazeyi dayanda bugun zuciyanshi yake ƙaruwa cikeda antisituation,filin tsakar gidan bakuwwa shiyasa yasamu daman shiga ɗakin dayaga tashiga ɗazun.

Ido 4 sukayida Mardy dake kwance akan doguwar kujera har yanzu atamfan ɗazune ajikinta,hasalima tinani takeyi akanshi,tsari takenima daga gareshi.

Tamiƙe dasauri ganin haka yasanyashi ƙarisowa gabanta,bayaso ta taphi,soyakeyi taita zama ataredashi suka sance a'inuwa ɗaya,yanajin yanda kallonta kaɗai kesamar maida natsuwa aciki da wajen duniyanshi da tun haihuwanshi yake ahargitse.

Daskarewan jini,tsinkewan zuciya dana zaren tinani suka diranmata lokaci guda,sotakeyi tagudu amma ƙafafu wanta sunƙi bata haɗin kai se zuciyanta dayake gudu akowani gaɓa najikinta.

Tana kallonshi yarungumeta,tarumtse idanunta da ƙarfi gaba ɗaya gaɓɓan jikinta sundaina aiki,tanajin yanda yashiga ƙoƙarin cimma burinshi takowani hali.

Dayana cikin hayyacinshi dayaga roƙonda takemai tacikin ƙwayannin idanunta,wani irin uncord momentne yaratsa.

Kaman ansamai paused haka yaji sanda kiran sallahn magrib yaratsa kunnuwanshi,ga wani tsawa daya cika ɗakin me tafida walƙiya.

Idanunshine suka shiga cikinnata,se ayanzu yaga saƙon dayake cikinsu sedai aikin gama yarigada yagama,dukda bayacikin hayyacinshi sedai hakan bazezama excuse agareshiba,balle kuma 'ita.

Akan idanunshi eyes balls ɗinta suka cikada wani'irin yanayi,kafin sukafara ƙyalli alamun hawaye,ze iya rantsuwa tun zuwanshi duniya betaɓa jin muryanda tafito da tsana megirma kaman ta taba.

"Ɗagani"

Komotsi gazawa yayi,tai amfanida hannayenta duka biyu tureshi,tayunƙura with empty emotions and promise's fayau takejin kanta.

Bedroom ɗinsu tashiga taɗauki zani taruphe jikinta,tana nan atsaye abakin drower idanunta kafe akan sitirunta,sotakeyi tafahimci wani abu koya yane.

✨✨✨

Kaman amafarki haka yake ganin komai,addu'a yakeyi akan ubangiji ye gaggawan farkaddashi daga wannan mummunan mafarkin.

"Kyanshi ace duk na mijin dayema mace fyaɗe to 'a kasheshi,kisane yadace dashi."

Muryan Mamy yacika kunnuwanshi,ze iya rantsuwa akan yanajin sautin muryanta acikin ɗakin,tamkar ayanzu take maganan.

Wayanshice tahau ringing,yajawo jeans ɗinshi yana zaro wayan daga aljihunshi,Samy love shine sunan dake yawo 'a screen ɗin tareda tambarin ƙato-ton love.

Ɗauka yayi ko sallamanta be'amsaba,yajefamata tambayan da dayaketa faman yinma kanshi.

"Samy mafarki nakeyi"?

Yanajin yanda hankalinta yatashi sedai yanacikin yanayin da baya fahimtan komai,komai zesamu muhalline a'inda yadace matuƙar yasamu amsanshi.

"Samy kigayamun gaskiya mafarki nakeyi"?

"Dagaskene am....."

Betsaya jin ƙarshen zancannataba yakatse wayan.

"Kasan ada koɗan waye yema ɗiyar wani fyaɗe to se'an fidda haddin Allah akanshi? shiyasa mutane ke kiyayewa amma yanzupha hmmm!"

tasauke numfashi cikeda takaici.

Miƙewa yayi jiki ba ƙwari,hasalima jikinshi ɓari yakeyi kaman wanda masassara yakama,atsorace yakama tafiya,yamantada wani halitta waishi mutum balle yaji tsoronshi.

Tsoron ubangijinshine yacikamai zuciya,tsoron kada yamutu da dattin dayake jinshi acan cikin naman jikinshi,dattinda babu wani sabulu ko so-son dazeje kusada gun balle yawankeshi.

"Allah natuba! Allah karka kasheni batareda anwankeni tahanyar haddiba"

Faɗi yake yana mai maitawa da muryanshi dayake can ƙasan maƙoshi,

kokaɗan bayajin ruwan dayake dukanshi,tafiya kawai yakeyi yanason zuwa inda za'a wankemai wannan dattin.

kafin numfashin shi dayake sama sama kaman wanda asthma ɗinshi yatashi yaɗauke.

Idanunshi dake gani dishi dishi yarufe da dukkan abinda yemai saura arayuwanshi yake tafiya ayanzu,har ya'iso police station ɗin,

yana shiga yabuƙaci ganin D.P.O,kamannin shida D.P.O ɗinnasu baya buƙatan tamabayanshi daga inda yafito,ko dun yanada kyau fiyemada D.P.O ɗinne oho!

Wanda yashiga sanardashi bejimaba yadawo,yemai jagora,yana shiga suka haɗa ido,bedamuda reaction ɗinda ke kan fuskanshi ba yaƙarisa bakin table ɗinshi yarubuta address ɗinshi sannan yarubuta raping.

Yanajin kallonda Saleem yakemai,bedamuba don ayanzu bashine agabanshiba,sedaya ɗago yazubamai jajayen idanunshi,muryanshi can ƙasan maƙoshi yafito......

Masu karatu kuyahakuri mutsaya anan,semun haɗu a chapter 18

Dafatandai labarin yakayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya,kudai kuimana comment sannan kui sharing a group group naku.

Taku Hindatu Auwal

Se anjima.....

*ZAREN KADDARA*

*حبلاالقدر

®By Hindatu Auwal

HIKAYA WRITERS ASSOCIATION

ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN

FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Group

WhatsApp:

AREWA BOOKS:Hindatu Auwal

PHONE NUMBER:***

________________________________________