ZAREN KADDARA

CHAPTER [18

by @hindatuauwal

"Address ɗin gidansune,fyaɗe nai mata,acikin hour damuke ciki ayanzu,hukunci nake buƙata irinna masu laifi kamana,I mean amatsayina na ɗan ƙasa.

Afagen doka ta musulunci nasani anabuƙatan shedu uku,waɗanda suka gani azahiri,bawaɗanda suka gani awani abuba,suka sance baligai kuma masu hankali idan ba'asamuba to atambayi wanda ya'aikata.

Malamai sun rabu zuwa gida biyu wasu sukace se antambayeshi sau uku,ya'amsa batareda tilasta,barazana ko gushewan hankaliba.

Wasu kuma sukace sau ɗayama yawadatar matuƙar yanacikin hayyaci,Saleem nai mata fyaɗe"

Sedaya dasa aya sannan yakalli fuskanshi,mamaki yagani zane 'allon fuskanshi idanunshi nabinshi da kallon tuhuma,ayanda yakejin jikinshi saura ƙiriss ya sare!bayaso yalumshe idanunshi yaje iyakan numfashinshi kenan aduniya.

Shiyasa yaraɓashi zewuce dasauri yakamo hannunshi,bayajin ƙarfi ajikinshi sedai akwai azuciyanshi da tazama dutse amemakon gari,shiyasa bashida rauni.

Saleem ye saurin bin bayanshi atsaye yahangoshi abakin canter yana rubuta statement koda yaƙariso amemakon yaga biro seyaga pencil ahannunshi da drowing paper.

Betaɓa sanin Sadauki nada talents ba seyau,yana kammala drowing ɗin beautiful lady ɗin yasauke numfashi menauyi,

se alokacin Saleem yabuɗe baki daniyyan yin magana amma seyaga Sadauki yalumshe idanunshi da alama jirine yake ɗibanshi dubada yanda ye ƙasa jikinshi yasaki,shida sauran ma'aikatan wurin sukai saurin tallafoshi.

Tunda Saleem yake betaɓa sanin akwai soyayyan Sadauki azuciyanshiba seyau kuma ayanzu daya ɗoramai nauyi megirma.

Direct A.B.U Teaching hospital yakaishi yasan bazewuce anan yake ganin likitaba,suna zuwa aka karɓeshi yatsaya aƙofan ɗakin,kiran Samyra ne yashigo tundaga ringing tone yasan itace.

Ɗauka yayi hankali atashe tafara magana,

"yaya ankawomuku case ɗin accident"

"Meyafaru"

yabuƙata farashin damuwanshi na hau hawa.

"Sadaukine_yaya sadaukine"

Jiyakeyi kaman anajanyo zuciyanshi aduk sanda taja numfashin kukan datakeyi.

"Karki damu ganinan ataredashi,anjima zankiraki take care "

tunda yafara magana bebata daman yin maganaba,yana kuma rufe bakinshi yakashe wayan.

*Ummah Khadija*

Zaune take akan gadon asibitin,idanunta nakaphe akan Adam da bacci yaɗaukeshi un expected,seruwa akeyi kaman da bakin masaki,agogo takallah 4:00pm.

Agogon dake kantane yasanar daita raguwan awannin dayaragemata.

Agobene zata tsaida haƙurin datai shekaru 22 tanayi,agobe litinin tana nufin komai,mafarin sabbin abubbuwa acikin rayuwanta.

acikintane zata rufe babin data buɗe cikeda burika masu yawan gaske,rayuwan farinciki tareda iyali masu albarka.

segashi agobe hatta *iyalan* zata yafesu,shiyasa take kallon fuskanshi dayake bacci ayanzu cikeda natsuwa.

Batada tabbacin intabashshi zeƙara yin bacci mecikeda natsuwan haka,kaman yanda batada tabbacin zata iya yinmai abinda yakeso shida ƴan uwanshi.

Dazarar tacigabada zama da mahaifinsu to wataran zuciyanta bugawa zatayi duk da sungayamata cewa yaran banashi bane sedai takasa yarda.

Sosukeyi tarayu dasu zatai hakan donsu,har bayan zuciyanta takejin matsayan zancenta,tarigada tagama yanke hukunci zata rayu donsu sedai batasaniba kozasu fahimci hakan.

Sam bazata rayuba matuƙar tacigabada zama a'inuwa ɗayada mahaifinsu,shiyasa tagayama Yaya Najib yaje yasameshi yagayamai tagama wannan auren,itakaɗai tasan emotional abuse ɗinda tahaɗiya,shiyasa dayadawo yasanar da ita zekawo takaddan sakinta nanda gobe inbahakaba zehaɗashida hukumane kawai.

Motsinda Adam yayine yasanyata dai daita natsuwanta.

"Harkagama masorin"?

"Banyi masoriba"

Ya'amsata yana mutsitstsike idanunshi.

"Kiyarda banyi masoriba"

Ummah Khadija tai dariya taname cewa"ka tsargu kenan"

Ye miƙa asanda yake bata amsa"kwana biyu bana samun baccine shiyasa"

"Yakamata kaga likita"!

"No gabashi nayi yanzuba"

Shiru taimai tana maida akalan zancen zuwa wani sashin.

"Na tabbata Ummy ruwan sama yahanata dawowa."

Se alokacin yakalli ago-go

"oh! Allahna har lokaci yatafi haka"

"Kanata bacci aidole kace haka"

Miƙewa yayi yaɗauro alwallah yazo yajasu sallan la'asar,seda aka kira sallahn magrib ruwan yatsagaita,aikam sega uncle Taheer yakawo Ummy,Adam yemusu sallama yataho gida.

***

Yanajin yanda jikinshi ye sanyi naban mamaki,kalan sanyin yedaban dana zazzaɓi.

kaman kodayaushe da sallama yashiga cikin palon,azaune yasami Mubeen da Mubeena sunyi shiru-shiru.

Haka kawai jikinshi yabashi wannan shirun bana alheri bane.

"Lafiya naganku ahaka"?

"Yaya kaga Aunty Mardy ce se magana mukemata amma tai banza"

Mubeen yafaɗi damuwanshi nabayyana hatta cikin muryanshi,bece komaiba yanufi ɗakinnasu.

Atsaye yasameta takashe wadrope da ido da alama bata cikin hayyacinta,da isanshi inda take yasa hannayenshi duka biyun akafaɗunta,yagir-gizata da ƙarfi,nannauyan ajiyan zuciya tasauke,wani kasalallen murmushi yabayyana akan fuskanta,muryanta asanyaye tafito

"mafarkine!yaya zamu farka"

Akwai wani yanayi atareda Mardy daya kasa gane kona menene,kallonta yakeyi sosai,searching yakeyi kozega ƙanwarshi ajikin wannan yarinyan dake tsaye agabanshi.

"meyafaru"?

Kai tashiga girgizawa tabuɗe baki hawaye nataranmata.

"Yaya karka tambayan mafarkine kawai zamu farka!zamu farka daga wannan mummunan mafarkin"

Yanajin yanda kalamanta ke taɓashi girmansu nazauna mai,yabuɗe baki yakai saubiyar amma ba sautin daya fito,daƙyar ya'iya lalubo muryanshi.

"Mardy ba mafarki bane dagaskene kigayamun mekefaruwane"!!

Hannunshi ta ture da ƙarfi kafin yasan abinyi hatta ƙarisa dressing mirror,tadunƙule hannunta tadaki mirrorn yafashe,nantake glass ɗin yayanke mata hannu.

Sosai tai maraba dazafin dayakaimata ziyara,talumshe idanunta taname marhaban dashi don koba komai shi sabone yanzu yake ciwo,akan ciwonda zuciyanta yakemata na raunin daya sameta batareda tayi ƙoƙarin kare kantaba,yarigada yagama kasheta gangan jikinta kawai yabari 'araye.

Adam dasu Mubeen suka ƙariso wajenta hankali atashe,Adam yariƙo hannunta dayake zuban jini,Mubeena taciro ɗan kwalin kanta tabashi yaɗaure hannun,fizge hannun tayi akaro nabiyu tana jada baya.

Adam yadakamata tsawa yaname cewa

"Mardy bakyada hankaline?kashe kanki zakiyine"

"Mutuwa ai yarigada yakasheni tun ɗazu,fyaɗe fa yemun"

Taƙarke tana sakin gunjin kuka,kuka takeyi ƙirjinta kaman zebuɗe,kuka takeyi da'abinda yemata saura acikin duniyanta,kuka take jikinta na ɓari numfashinta har tsatstsayawa yakeyi.

Giɓinda rayuwanta yasamu kaɗai take gani acikin ƙwayannin idanunta,duk wani fata da sarai gamida burika sun rushe!sunbi iska tattareda lokacinda yafi kowani lokaci muni arayuwanta,

zafin fitan raine kawai zemantar da'ita wannan raɗaɗin,se ayanzu nauyin komai ke danneta,da ƙyar take iya shaƙan numfashi.

Su Mubeen dasukai suman tsayene sukai kanta,idanunta dake zuban ruwan hawaye suka rufe,kanta daye dumm!yacunkushe ye shiru,hannuwa takeji maban-banta da sautikan muryukansu kafin komai yafita daga kanta.

Ko motsi Adam gazayi yayi,kaman statue ɗin ƙanƙara haka yazama,kaman ansa baki antoshe wutan aci bal-bal haka tinanin shi yabushe acikin ƙwaƙwal wanshi,gadai idanunshi ƙuri akansu amma kanshi fanko yake awannan lokacin.

ga za'a gwadashi gani za'ayi zuciyanshi takusa bugawa,yana gani tai luw zata faɗi su Mubeen suka riƙeta,

agaɓan da ake zazzaɓin dake damun Mubeena ma ɓoyewa yayi ganin abinda kefaruwa megirmane.

Masu karatu kuyahakuri mutsaya anan semun hadu a chapter 19

Dafatandai labarin yakayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui mana comment sannan kui sharing a group group naku.

Taku Hindatu Auwal

Se anjima......

*ZAREN KADDARA*

*حبلاالقدر

®By Hindatu Auwal

HIKAYA WRITERS ASSOCIATION

ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN

FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only Group

WhatsApp:

AREWA BOOKS:Hindatu Auwal

PHONE NUMBER:***

________________________________________