CHAPTER [20
Besan yashigo palonshiba seda sukai ido huɗu da ita,da sauri yajanye nashi idanun,yasanta yanzu zatahau karanta mood ɗinshi kaman mekaranta novel.
Kai tsaye tarungume shi,nannauyan ajiyan zuciya yasauke, ahankali tafara shafa bayanshi alaman rarrashi tana huramai iska akunninshi kaman wani ƙaramin yaro.
Abinda yake nimane yasamu sedai bayason raba damuwanshi da ita dubada lokacinda ze'aikata son ranshi benimi taimakontaba.
Hawayene suka hau mai tsere afuska.
"Komai zeyi dai-dai"
Jin waɗannan kalaman yasanyashi kasa riƙe kukanshi kaman wani yaro ƙarami,yaru ƙunƙumeta kaman zemaidata jikinshi suzama abu guda ɗaya,
riƙon dayemata behanata shafa bayanshiba,jin yana sauke ajiyan zuciya yasanyata kama hannunshi tazaunar dashi.
ruwa taɗauko 'a freezer da glass cup ta tsiya yamai ruwa tabashi,amsa yayi babu gardama saboda bushewanda maƙoshinshi yayi,gawani abu dayemai tsaye aƙahon zuci.
yana shanyewa yaji ƴan hanjinshi sunyi wani irin yamutsawa da ƙarfi,dagudu yamiƙe yashige bathroom ɗinda ke palon yahau kakarin amai,duk da babu komai acikinsa sedaya gama tsaf ta taimakamishi yaɗauraye bakinshi.
ganin bazeiya hawa up-stairs ba yasanyata kaishi ɗakinta,sanyine yaratsashi nan take yahau kakkarwa,blancket taɗauko tarufamai,
waya taɗauka daniyyan kiran likita taji yariƙe mata hannu,idanunshi alumshe ganin yanda ya yaye blanket ɗin da ɗayan hannunshi yasanyata gane abinda yake nufi.
ƙarisawa tayi gareshi yarungeta tsam ajikinshi,muryanshine yadaki dodon kunninta.
"yamutu Nawan Sadauki yamutu"
yadasa aya yana sakin gunjin kuka,gaban tane ye mummunan faɗuwa ba shiri takalli cikin ƙwayan idanunshi.
"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un"
tafaɗi hawaye narige-rigen sauka akan kuncinta.
"don Allah kimun faɗa kice wani abu,nasani niba uba bane nagari,nime son zuciyane da son kansa,anyama inna mutu zansami rahaman Allah?
oh nagane seyau nagane dalilin dayasa ubangiji bebani wasu ƴaƴan ba,yasan bazan iya kulawa dasuba,guda ɗayama nakasa,na tabbata baƙin cikin mune yakashe shi,aranan damuka haɗu na ƙarshe naga yanda tsana na yacika zu.."
rufemai bakinda tayi yasanyashi yin shiru.
Asafiyar data gabata duk wani mutum dayike cikin familyn Kangiwa yatashine da kalannashi damuwan da tashin hankalin,haƙiƙa kalaman Saleem yazaburaddasu daga zaman son zuciyan dasukayi tsawon shekaru 22 dasuka gabata.
*Adam*
Zaune yake akan sallahyan daye sallahn Athuba,hannunshi riƙeda alqur'ani yana karantawa cikin dishashshiyar muryanshi dabata fita.
muryan Baba lecturer yaji yana rangaɗa sallama tareda sauran ƴan uwan mahaifinshi,beko motsaba seɗaga kai dayayi yakalli agogo dake maƙale ajikin bango.
7:00am bashiri yamiƙe tinawa da yayi behaɗama ƴan uwanshi abun karyawaba.
"'ina kwananku".
ye jam'i wajen gaidasu alokacinda yafito palon,ko tsayawa beyi su amsashiba ye shigewanshi kitchen,be kulada ƙamshin abincin dake tashi tun apaloba seyanzu daya shigo yaganta tana girki,
"'ina kwana yaya"
Asma'u tagaidashi cikin sanyinta,amsata yayi yana kallon fuskanta daye jajir alaman tasha kuka,ga idanunta dasuka tasa alaman bata samu bacciba se'ayanzu yatina ganin dayemata apalo itada su Mubeen.
tausayin sune suduka yadiranmai,ƙaddara tahaɗasu cikin yanayi mewuya,tayadda bazasu iya gujemataba.
"Assalamu Alaikum!yaya ina kwana"
Mubeen daya shigo yafaɗi alokaci guda batareda yabari an amsashiba.
"Mubeen gaisuwan zanfara amsawa ko sallaman"
dariya yayi,suduka ƙoƙarin kauda damuwan abinda kedagulamusu zuciya sukeyi cikin kusancin dasuka samu atsakanin su.
"wai me'ake ceccewane tashin dariyanku har ƙofan kuyanbana"
Mubeena da shigowanta kenan tafaɗa,Adam yagimtse dariyan dayakeyi yanuna tada yatsa yace,
"karki sake cewa komai sekin koyo sallama"
kunnuwanta takama tana marai-raice fuska alaman ban haƙuri,Adam yakauda kanshi gefe.
"I'm sorry yaya"
"no! yaya bayajin saƙon ban haƙuri da safe"
Faɗin mubeen yana ƙunshe dariyan data tasomai,
baki ta turo sotakeyi yakalleta amma yaƙi seta ɗare can cabinet tace
"Aunty Asma'u ina kwana"
amsawa Asma'un tayi fuskanta ɗaukeda murmushi.
"nidai bazan'iya komaiba banida lafiya amma inda ɓaran magi da yankan albasa akawo"
murmushi Asma'u tayi tanajin yanda Mubeen kebata amsa.
ahaka sukayi abin karywan suka gama,kaman yanda suka saba suka ɗauki kayan abincin sedai yau ba'a palo suka ajiye kayan abincin ba cikin bedroom ɗinsu Mardy suka shiga.
***
Tunda aka kira sallahn Athuba tafarka,motsin Abba dataji yahanta motsawa,ada ganin komai takeyi kaman amafarki amma yanzu data farka taga Abba tagaz-gata komai.
sedaya fita sannan tasauko taje taɗauro alwallah tai sallah,tana idarwa takoma gado,ita kaɗai tasan abinda takeji se macenda ta tsinci kanta a'irin wannan halin.
ko doctor Bilkisu data shigo lumshe idanunta tayi tanajin lokacinda takoma take sanardasu tana bacci.
suna ajiye kayan hannunsu suka ƙarisa inda take kwance,fuskanta Adam yafara taɓawa yaji ba zazzabi sannan yakalleta sosai yace
"yajikinnaki"
Cikin sanyin murya ta'amsashi da faɗin"da sauƙi,ina kwana"
yanajin yanda sanyin maganan ta yataɓashi,har zuciyanshi yake jin abinda yasameta,da yasan yanda zeyi daya dawoda abinda ke jikinta jikinshi kodan tasamu sauƙi.
hannunta yakamo soyakeyi yalallasheta amma yarasa kalaman dazeyi amfanidasu,dazaisa tafahimci saƙon abinda yakeso,sedai yagaza samun ko kalma ɗaya don duk kalman datazo bakinshi gani yakeyi tayi ƙan-ƙanta.
tunda taji yayi shiru taɗago kanta,idanunta tasanya acikinnashi ta tariƙesu tsayin lokaci har yakaima tana karantan abinda ke cikinsu,base yace komaiba tarigada tagama fahimta.
"nafahimta"
tafurta muryanta ɗaukeda wasu irin emotions dabata taɓa zaton ɗan adam ze tsinci kanshi acikiba.
idanunshi dake cikin nata suka ƙara girma alaman mamaki tukun suka fara sheƙi alaman taruwan ƙwalla.
"I will cry"
tafurta ataɓare tana karya kai kaman wata yarinya me feeder.
dasauri yagir-gizamata kai yana ɗauke ruwan hawayen da ƴan yatsunshi biyu. hannunta dake cikinnashi yakama bamusu tasauko,mubeen yazubamusu ariash ɗin da ƙwai,mubeena tahaɗamusu tea.
kallonta kawai zakayi kagane tana cine badon yana mata daɗiba,Adam takalla daye wani irin so cool dashi,hawaye masu zaphi suka cika gurbin idanunta.
"kar hawayenan su zubo don Allah"
kai tagyaɗamai tana ƙoƙarin maidasu ko don farincikinsu,ko don surage damuwan da tasakasu.
bayan sungama Mubeena takwashe kayan takai kitchen,Baba lecturer yakirata takwashe wanda suka zuba musu.
doctor Bilkisu tashigo suka gaisa ta 'umarcetada ta tashi tasanya hijjab,bamusu tamiƙe taɗauko hijjab ɗin tafito.
Mahmud yatashi suka nufi asibitin A.B.U shika,tagate ɗin baya suka shiga,kai tsaye office ɗin doctor suhaima suka nufa dama tun da Baba lecturer yace yakamata akaita asibiti likitan mata tadubata.
***
Bayan sun gama gaisawa taimata bayani komai tareda treating ɗinda taimata adaren jiya.
"muje ko!"
doctor suhaima tafaɗa fuskanta cikeda murmushi,batace komaiba se miƙewa datayi,amemakon sufita taƙofa setaga tabuɗe wani ƙofan daya sadasu dawaje suka ɗanyi tafiya da befi na mintina 10ba.
segasu sun iso wani wuri kaman ba'a sibitiba,ye kyau sosai asaman glass ɗin anrubuta treating and emergency.
doctor suhaima tatura ƙofan suka shiga cikin palon,nurses suka gani birjik har dama likitoci.
doctor suhaima ta umarcetada cire hijjab ɗinta kafin tahau siririn gadon me haɗeda wasu irin electronics.
Masu karatu kuya haƙuri mutsaya anan semun haɗu a chapter 21
Dafatandai labarin yaƙayatar daku,wannan littafin gaba ɗayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui mana comment sannan kui sharing a group group naku.
Taku Hindatu Auwal
Se anjima.........
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
®By Hindatu Auwal
HIKAYA WRITERS ASSOCIATION
ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN
FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only
WhatsApp:
AREWA BOOKS:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
________________________________________