ZAREN KADDARA

CHAPTER [21

by @hindatuauwal

Mardy ba baka sekunni,komai aka cemata yi takeyi burinta ɗaya shine ayi agama asallameta.

seda sukai hour ɗaya suna abu ɗaya sannan akace tasauko, doctor suhaima tai mata se anjima suka fito.

office ɗinta suka dawo doctor Bilkisu da Mahmud sunan azaune.

"Alhamdulillah wata kam an auna arziƙi,wallahi shiyasa ake yawan gayama iyaye cewan sudaina barin ƴaƴansu suna haura garu,bishiya,ɗaukan kaya masu nauyi,da tsallaka manya manyan ramuka dasauransu.

because halittan ƴa mace halittace me rauni,me buƙatan tattali da kiyayewa,kuskure kaɗan ze'iya jawo mata matsala.

wanɗanda acikin kuskuren shine barin abubbuwan da ake cewa subari suna wakanuwa.

mubamu hana yarinyanki yin miki aikiba amma kibarta tai miki abinda baze cutarda itaba,ni bance waɗannan ayyukan zasu sa ƴanki tarasa budurcintaba amma zetaimaka sosai wajen sanya budurcin ƴanki yasamu rauni tayanda abukaɗan zeku sanci gun tazama perfect woman.

but idan ana kiyayewa sekaga idan irin haka tafaru ansamu sauƙin maida ƴan mata zawarawa batareda aureba,ko samun ƴaƴa saboda fyaɗe lokaci guda duk da yadanganta dayanda abun yazo.

daga ƙarkedai ina tayaku farinciki har yanzu mardiyya tananan 'a spacking lady Insha Allah mijinta shizemaidata perfect woman.

yanzu zan rubuta muku wasu ƴan magun-guna dazata rinƙa sha,sannan zanyi deparing ɗinku zuwa scattering department don aduba ƙwaƙwal wanta.

jin ta ambaci scattering yasanya idanunshi ƙara girma saboda tsoro,tashin hankali na tasomai tun daga kan babban ɗan yatsanshi har mid brain ɗinshi,yashiga rabama gangan jikinshi tako ina,fankan dake cikin office ɗin behanashi yin gumiba.

doctor suhaima takalleshi taname miƙamai takaddan magani da kuma na result ɗin dubata da akayi.

ganinshi awannan yanayin yasanyata tambayanshi cikeda kulawa.

"mlm lafiya meya faru"

se alokacin Mardy data duƙarda kai tana kukan farinciki tareda godema Allah taɗago.

mahmud yabuɗe bakinshi dake rawa kaman yanda ilahirin jikinshi ke rawa,da roƙo megirma acikin muryanshi bayan roƙon dayemata.

"don Allah likita karkicemun ƴata tahaukace bazan iya jurewaba"

yaƙarke muryanshi nasauka ƙasa alaman tahowan kuka.

doctor tai murmushi asanda take miƙewa,ruwa taɗauko mai acikin freezern dake cikin office ɗin,

tazubamai a glass cup tabashi bamusu ya'amsa yasha,sedaya numfasa sannan doctor tabuɗe bakinta cikin salo na kwantar maida hankali.

"wato bakomai yasa nace hakaba sedon fyaɗe abune dayake faruwa cikin yanayi na tsoro da firgici,yahai farma zuciya ciwo da wanda abun yasamesune kaɗai zasu 'iya bayani.

sukance har yanzu ba'a samu kalman dazezo kusada abunba balle ye bayaninsa,wannan tsoron da firgicin kan haifarma ƙwaƙwalwa ciwuka kala-kala.

kaɗan daga cikinsu akwai tsoro,fargaba,rashin bacci,rashin ɗan-ɗanon baki dasauran su,wanda idan ba'a ɗora mutum amaganiba sekaga hawan jini,depression,ƙeƙasan zuciya tayanda zasu rasa mercy ɗinsu,hawan jini mehawa ƙwaƙwalwa kai tsaye ko wasu cututtukan dasuka shafi ƙwa-ƙwalwa takama mutum.

shiyasa duk macenda irin haka yasameta to tarinƙa ganin likitan ƙwa-ƙwalwa."

*Ummah Khadija*

tunda suka shigo gidan gabanta yashiga faɗi har suka shiga ɗakin mama,mutanen gidan suka shigo sukaimusu sanda zuwa.

aka sanya ɗaya daga cikin ƙanninta dabasu riga sunyi aureba tasakemata ruwan wanka takaimata cikin bathroom ɗin dake cikin ɗakin.

tana fitowa wankan taga flate da ƙoshiya asamanshi,se cup da jug,tabuɗe jug ɗin taga kunun gyaɗa dayasha madara se ƙamshi yakeyi,flate ɗin kuma fatan kuskusne amma nashuwaka,se kayan ciki.

sedata kimtsa sannan tazauna taci abincin don favorite food ɗintane,data kammala takwashe takai kitchen sedata wanke sannan tafito.

tanufi waɗɗakan Mama zuciyanta cikeda tarkacen tinani kala kala,da sallama tashiga,Mama dake tsaye abakin drower ta'amsata.

tazauna abakin gadon,muryanta narawa alaman tahowan kuka akodayaushe.

"Mama don Allah kiyahaƙuri nasan najamiki abin kunya kuma nazubar miki da ƙima da mutunci,

bansaniba ko Baba dabaya raye zeyafemun saboda nasaɓama wa'azin ku,ako dayaushe kuna tina tardani abin kunyane idan aka saki mace,

shi aure bautane duk abinda yabaki kihaɗiye kishanye sedai kun manta akwai ban banci tsakanin auren da dana yanzu,narigada nayi haƙuri iya yanda zan'iya.

mahmud raina yake nima,baƙin cikinshi ze'iya kasheni!Mama don Allah,inaso inshaƙi iska nadaban da wanda nake shaƙa yanzu."

Mama tai gyaran murya sannu ahankali kamalalliyar muryanta yaratsa masarrafan jin ummah khadija

"khadija kowani abu yanada dalilin faruwanshi,kowani aure yanada nashi ƙalubalen,bazan tilastaki akan sekin koma gidan mahmud ba amma zan baki shawara amatsayina na uwa.

shin idan kinrabudashi kinsan halin wanda zaki aura anan gaba?mazannan ba tukwane bane balle ki ƙwan ƙwasa kisan na ƙwarai,tunda aka haifeni nake karatun ɗana miji har yanzu danake tsaye agabanki bangamaba.

naga cases kala kala arayuwata kuma kowani namiji da kalan halinsa,haka yanada nashi kalan method ɗin daze hargitsama matanshi lissafi,akullum cemusu nikeyi sui haƙuri kinsan meyasa saboda nima haƙuri nayi danaki mahaifin.

kince akwai ban banci 'a tsakanin auren da dana yanzu,bazaman aurenne akwai ban banci ba iyayenne akwai ban banci.

khadija wallahi gwara mijinki akan mahaifinki tunda ƙazantan dabaka ganiba tsafta,shiko naki mahaifin har gida zekawo mace da waɗannan hannayennawa danida abokan zamana mukema karuwanshi girki,kuma se abinda sukace sunaso sannan zamu girka.

idan kuma bakiyiba yadakeki,kuma yazageki agabansu,idan kikaje gida ko sauraron abinda yemiki baza'ayiba balle abarki kinumfasa za'a tasoki agaba adawo dake gidan mijinki,idan yana gidan abashi haƙuri,acemai se haƙuri mata se haƙuri,idan bayanan agayama uwar mijinki.

shin mu iyayenmu basa son mune?ada haka muka ɗauka seyanzu nagane so akeyi mui zaman auren,gata akemana batareda mun saniba,da'ace awancan lokacin munzubarda arziƙinmu munje munyi wani auren to ƴaƴan wasu zamu raina bayan mun watsadda namu yaƴan.

narantse da Allah mahaifina betaɓa zagin maceba amma Allah yahaɗashida siriki kalan mahaifin ki,tayaya shima mahaifinki Allah baze jarabceshiba?maza na kuskuren muzgunama ƴaƴan wasu har sui kuka wasunsu suce Allah ya'isa,suna ganin bakomai bane basusan Allah ko ze'isar ɗinba.

ayau kwanakinki 7 'a asibiti,adaren jiya wani yeƙoƙarin yinma mardiyya fyaɗe,shin idan kika barsu mezefaru?kinsandai ba saurayin daze aureki sedai memata ko wacce matanshi tamutu,inma kinsamu mijin kenan don tozon saa beciwoba balle kuma daɓuri.

akullum mu matan hausawa ƴaƴa kedannemu,amma inkika lura ubangiji baya maida haƙurinmu da juriyanmu abanza,yakan da ɗaɗamana tahanyan ƴaƴayenmu suzama bangwayen jinginanmu,sanyin idaniyanmu,

sekiga komai kaman ba'ayiba,sedai kabada labari yarigada yawuce,shikanshi mahaifinnaki ina yake?

banbaki labarinnan don kirainashiba sedon kisan akomai narayuwa bake kaɗai bace,wallahi idan kikaji halin mijin wata bazakiso kiƙara jiba,kuma tananan tana zaman haƙuri,haka rayuwa take kafiwanine wani yafika.

kiyi tinani nanda anjima,yakira yayanki Najib sunyi magana da ƙanin babanshi zasuzo anjima za'akiraki aji tabakinki."

laɓɓanta suka natsu awaje guda sa'ilinda tarufe bakinta tana kallonta don ganin reaction ɗinta.

ummah khadija tadafe kanta cikeda rashin sanin madafa,kalaman Mama take ɗauka tana ɗorawa amizani.

yunƙurin fyaɗe!ƴattace akai yunƙurin yinma fyaɗe,dalilinnan kaɗai ya'isa yasanyata komawa gidan mahmud.

tinanin randa za'aimata me gaba ɗaya nasa numfashinta barazanan ɗaukewa,abinda tafi tsana aduniya shine yake yunƙurin samun ƴanta,

abinda idan yasamu wata yarinya takeji inama tanada halin ɗauketa takaita wani duniyan taɓoyeta,tayanda babu wani abu dazeƙara taɓata balle yahar gitsamata lissafi

shine yake ƙoƙarin samun ƴanta,shin menene amfanin ta aduniya,tanacan tana haukan banza wani naƙoƙarin rusamata duk wani tanadi nata na rayuwa.

"innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,astagfirullah,Allah muntuba,Allah kayafemana,Allah kawanke zukatanmu,Allah ka tsaida waɗannan jaraba woyin 'iya haka...."

takai ƙarken addu'an tana sakin gunjin kuka.

*Saleem*

12:00pm na ranan laraba tai maine aƙofar gidan daya sanya sergent yazo yanimomai bayanai akan zanen da sadauki yayi 'a police station jiya.

karona farko dayake jin kunyan haɗa ido dawani tun kafin yaganshi,wani irin bugawa zuciyanshi takeyi dabaiyi kamada faɗuwan gababa,halinda zuciyanshi take ciki ayanzu ta ta'allaƙaneda kuskurensu nabaya.

tunda Sadauki yabuɗe bakinshi da kalmomi 4n ƙarshe yaji komai yahautsinemai,notinda besan da zamanshi akan shiba yaji yakwance,kusa kurensu yake gani acikin idanuwanshi miraratan.

shiyasa yatarasu yagayamusu Sadauki yamutu,yaga tashin hankalin dayakeson gani acikin ƙwayannin idaununsu,yaga yanda suka tashi daga zaman son zuciyan dasukayi tsawon shekaru 22 sunayi,

suduka yaga yanda danasani yarufesu kaman ƙaton bargo,shiyasa yaƙi zuwa asibitin sekawai yabada umarnin adawo dashi police station aɗauki statement ɗinshi asakashi abayan kanta tunda bayada lafiya......

"assalamu 'alaikum"

sallaman mahmud yatsamo saleem daga kogin tinanin daya faɗa,kallonshi yayi tacikin tabarun daya sakaye idanunshi aciki,besan jikinshi na kyarmaba sedaya ɗago hannunshi sui musabiha yaga yana rawa ahankali.

"sunana saleem zaid kangiwa,D.P.O anan police station na fada,akwai wasu ƴan tambayoyi danakeso inmaka inbazaka damuba"

"bakomai"

faɗin mahmud bakuma don babu komai ɗinbane sedon be'isa yagujema tambayoyin ɗan sandanba.

Masu karatu kuya haƙuri mutsaya anan semun hadu a chapter 22

Dafatandai labarin yaƙayatar daku,wannan littafin gaba ɗayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui mana comment,sannan kui mana sharing a group group naku

Taku Hindatu Auwal

Se anjima........

*ZAREN KADDARA*

*حبلاالقدر

®By Hindatu Auwal

HIKAYA WRITERS ASSOCIATION

ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN

FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only

WhatsApp:

AREWA BOOKS:Hindatu Auwal

PHONE NUMBER:***

________________________________________