ZAREN KADDARA

CHAPTER [27

by @hindatuauwal

in slow motion yakejin sautin kaww na amsakuwwa acikin kunninshi,shikanshi neman abinda yakatsemai maganan dayakeyi yakasa yarda bintuce taɗora hannunta afuskanshi da sunan mari,

magananta yafarkadda ƙwaƙwal wanshi hotun data tafi,

"haryanzu lalace wata bekai namiji yadakeniba,kasani dukana shine ƙarshen kuskurenda zakayi mafi girma acikin rayuwarka"

besan yazaro belt ba yazabgamata asanda takai ƙarshen zancentaba seyanzu dayaji ƙaran ihunta,kalamanta na ƙarshene kaɗai abinda keshawagi acikin kwanyan kanshi,

sam kunnuwanshi basajin sautin kukanta,idanunshi basaganin ƴar farar baturiyan dayake duka,gashi yakama hannayenta duka biyu yariƙe,yasa ƙafanshi yatake nata,

kaman daga sama yaji saukan tagwayen marika,harseda ƙwaƙwal wanshi tatafi hutun taƙaitaccen lokaci,

"sakarmun ƴa mutumin banza kawai"

yaji diran sautin muryan acikin kunnuwanshi,ga hannunshi da'ake ɓanɓarewa,se alokacin idanunshi suka sauka akan Paa,daya tallafo Bintu jikinshi sekace zemaidata ciki,nantake yazaro wayanshi,betsaya ganin mezeyi da itaba yahaye sama abinshi,

yarigada yagama yanke hukunci yagama wannan auren,shikaɗai yasan emotional abuse ɗinda yahaɗiya awurin Bintu,she's so stubborn,yana shiga ɗakin yaɗauki biro da paper yadatse igiyoyi 3n dasuka haɗasu wuri ɗaya,

kaman yanda yabarsu haka yasamesu,sam bekalli fuskokinsuba balle yaga reaction ɗinsu,takaddan yamiƙama Paa yanafaɗin,

"takaddan sakinta ne gobe zan aikomata da kayanta seka turomun address ɗin inda za'akai"

haryajuya daniyyan komawa inda yafito yaji sallaman maza,kallonsu yayi seyaga ƴan sandane,fuskokinsu kaɗai zesanar dakai basada mutunci,

"ga mara mutuncinnan kutafi dashi harse rananda princess tagadaman faɗin abinda za'aimai"

"Paa kabarshi akwai lokaci"

ba'iya mahaifintaba hattashi Muhammad ɗin sedaye mamakin jin yanda muryanta tafito adake,

ko lafiyan Bintu ƙalau mahaifinta baya mata musu akan abinda tace bataso balle yanzu da'idan duniyan tace tanaso yamallakamata zebata donkawai tasamu sauƙin abinda takeji,

beƙara cewa komaiba yakamata suka fice,kai tsaye asibiti sukaje,doctor ye treating ɗinta yabata bedress tareda albishirin tanada ciki na 2wks,

koda yagayamata mele baki tayi tana faɗin,

"kuɗauki takaddan ku'ai kamai dashi tomorrow da safe"

haka ko akayi Muhammad na fitowa da safe zeje wurin aiki ɗan saƙon Bintu yabashi takaddan yatafi abinshi,

jiyayi zuciyanshi naneman shigewa cikinshi,calculatorn dake cikin kanshi yahau lissafin rananda cikin yasamu,

2weaks indai 2weaks ne dai dai yakeda rananda tafara zuwa makaranta,

nantake sheɗan yasakamai kokonto,ko cikakken 2month ba'ayiba?yagama yarda da cikin banashibane,amma zejira zuwa rananda zatahaihu,indai tanimeshi tagayamai zegayamata shi ɗaa banashibane,domin yarigada yasan halinta tanada sabo da maza kaman karya,

nantake yaɗauki zancen yawatsa abayan zuciyan shi,se'aloka cinnema yakira Mamy yagayamata yasaki Bintu,

"Allah shi kyauta"

kawai tacemai takashe wayanta,yasan ba'iya maganan kenanba,zatabarine harse rananda yaje zarian sannan tabuɗemai cikinta,shikuma bazebata wannan damanba don seta huce zeje,

*** kwanan Bintu 2 a harmony aka sallameta,Paa yemusu bucking ɗin jirgin da zetashi a washegari,dama don ita yazo,

tun friday dayakirata kaman yanda yasaba yaji tawuni lafiya,tana ɗauka seta fashemai dakuka,hankalinshi inyayi dubu to yatashi,jiyayi kaman yetsuntsu yazo nigeria,daƙyar yalallaɓata tai shiru bayan tagayamai abinda kefaruwa cikin kuka,

shiyacemata kada ta'uni agidan,taje gidan ƙaninshi tazauna,shima yananan zuwa kuma zeyima tufkan hanci,shine yanashiga yaga yana dukan mai ƴa,

"Paa ba inda zani,idan lokaci yayi dakaina zanzo,"

"please princess inkaratu kikeji kinsan bakida matsala"

"no Paa kabari kawai"

taimaganan batareda tabashi ƙofan dazeyimata magiya ko lallashiba,hakanan Paa yatafi yabarta agidan ƙaninshi,

*BAYAN WASU WATANNI*

zaune take acikin mota,se jaririn dayake kwance akan cinyanta,dai dai da drivern dayake tuƙa motan sojane,sojanma da'akema laƙabida marphorl seda aka buɗe mata motan sannan tabuɗe idanunta da kallo ɗaya zakaimusu kasan ba'abinda yacikasu se zallan rikici,

ƙafanta guda ɗaya tafito dashi,sojojin dake ɗaya motan suka ƙariso gabanta,suname gurfananda mutumin dake tsilli-tsilli da idanu kaman ɓarawo ahannun mata,

idanunshi basui tozalida kuwwaba se Bintu Nazeer Mai Atamfa,har yanzu tana nan aƴar gayunta,classy woman.

sedai ma wanda yaƙaru,ga tabon sallahnta dayaketa sheƙi alaman haryanzu tananan da riƙon addininta,shiyasa akace idan kai shekaru baka haɗuda mutumba katambayeshi komai amma banda hali saboda hali zanen dutsene,

Bintu tai murmushi haryanzu intai murmushinnan mekaman koren furen flower sekaga tamkar babu wata mace wacce takaita kyau acikin duniya da wajenta,

zazzaƙan muryantane yaratsa masarrafan jinshi,

"darling!nasan kayi mamakin ganina ko?tom bashinda kacine zaka biya,gaɗanka ɗan sati biyu,ga matanda kadaka da cikin sati biyu,ga belt,"

taƙarke tana zaro belt ɗin dake ƙugunta,miƙewa tayi tsaye tamiƙama wanda ye driving ɗinta yaron nan take sodojin sukasa kaca suka ɗaure matashi tsaph,

Mamy nacikin gida akazo aka gayamata,inkaji ana batun shiri to hankali akwance yake,koda Mamy ta isa wurin Bintu tarigada tagama dukan Muhammad,

tabi Mamy da kallon 3saura anini,gamida mele baki alokaci guda taname umartan sojanda yamiƙama Mamy jaririn,taɗorada

"gayaron kunan,besha nonon mara tarbiyyaba,dangin mara tarbiyya basui mai huɗubaba,balle ragon suna,

idan baku amsheshi amatsayin ɗaba zaku'iya kaini kotu,ga address ɗinanan"

taƙarke tana saka public card ɗinta agaban rigan Muhammad,bata tsaya jin abinda zasuceba tashige mota suka wuce,

da taimakon ƴan anguwa akashigarda Muhammad ciki,koda sauran ƴan uwanshi suka dawo baƙaramin harzuƙa sukayiba,suka dage akan bazasu karɓi ɗaba kuma sesun bima ɗan uwansu hakkinshi,

shikanshi Muhammad ɗin yadage akan baze karɓi yaronba,daƙyar dasiɗin goshi Mamy tasanyasu sukabar maganan,da alwashin zata riƙeshi don koba aure atsakaninsu ita mai riƙema Bintu ɗane,

basada yanda zasuyi hakanan suka barmatashi, duk wani uzuri nashi basa ciki,kuwwa matsayanshi agameda yaronda Mamy taima huɗuba da Mukhtar na zuciyanshi,

duk yanda Mamy taso maganan yarufu amma hakan yaƙi samuwa seda kuwwa yasan Muhammad da ƴan uwanshi sunƙi karɓan Mukhtar,

haka raɗe-raɗin yaro shegene yadinga yawo 'a unguwa,

wasuma kai tsaye suka dinga yaɗa Muhammad ya'auri Bintu dacikine batareda yasaniba,shiyasa da asirinta yatonu yasaketa,

wasukuma suce da kwarto yakamata agidanshi shiyasa yasaketa,dayike ubanta babban ƙusane aƙasa shiyasa dole suka karɓeshi,

itadai Mamy tatoshe kunnuwanta akan magan ganun mutane,tamaida hankalinta wurin rainon mukhtar wanda takema alkunyada *Sadauki*,

*bayan wasu shekaru*

yarone ɗan kimanin shekaru 8 yashigo gidan, ƴar kantin dake jikinshi me matuƙar kyau da tsada ye phutu-phutu daƙasa,dasauri Mamy tamiƙe daga tabarman datake zaune,takamoshi

"Sadauki lafiya"

tai tambayan cikin tashin hankali,kaman dai kowace rana akullum akoda yaushe,jikannata bayasamun komai daga mutane da ƴan uwanshi yara se kyara da tsangwama,

Matsayinta a anguwan da darajan gidansu yasanyata yin shiru,tanada tabbacin akwai watarana dazatazo wanda sudukansu zasui danasanin abinda suka aikata.

"Mamy idona"

muryan Sadauki yadawo da ita hayyacinta,hannunshi dayake murzawa aidon nashi tasauke tana huramai,

"Sadauki wai banace maka kadaina shiga harkan mutaneba,"

tafaɗi sanda take ƙoƙarin ciremai kayanshi,

"Mamy banje wurinsuba,wurin Sameera naje mui wasa shine su Saleem suka yardani aƙasa suna janmun kaya wai shege yayi gayu!

Mamy wai dagaske sunana shege"

"zomuje inƙara maka wanka"

cewan Mamy tana kamamai hannu amemakon tabashi amsan tambayanshi,

***

"Sadauki! Sadauki kafito kutafi makaranta ga Sameera nan najiranka"

Mamy take faɗi daƙarfi yanda Sadauki dake cikin ɗakinshi zejiyota,jin shiru yasanyata miƙewa tashiga ɗakin,azaune tasameshi abakin gado,yanashan mintin tsinke,

"Sadauki wai bakaji inamagana bane"

"Mamy bazaniba"

yafaɗi kanshi aƙasa,ƙarasowa tayi tazauna akusadashi,

"Sadauki"

takira sunanshi tana kamo hannunshi,hawaye tagani ciketaph da idanunshi,baki tabuɗe ye sauran taran numfashinta,hawaye nabin fuskanshi,

"Mamy bazaniba,banaso su Saleem su dakeni,sucemun shege!Mamy banaso"

"Sadauki kayahaƙuri,Allah yana tareda masu haƙuri,duk wanda yabikada sharri tokai kasakamaida alheri,duk wanda bayasonka kainesa dashi saboda karya cutardakai,asannu komai zewuce"

tai maganan cikeda lallashi tamkar dawani babba mehankali takeyi,

"Mamy tokice sudaina cemun shege"

yafaɗi hawaye nabin fuskanshi,

"Sadauki dani dakai bamu isa muhana mutane faɗin abinda sukesoba,amma munada ikon toshe kunnuwanmu tayadda duk abinda suka faɗa akanmu bazeyi tasiri azukatan muba"

da haka tasamu ta lallaɓashi yashirya yafito suka tafi makarantan,

@@@

da sallama yashigo palon,tundaga ƙamshin tirarenshi yagane kowaye,zuciyanshi tashiga bugawa dasauri dasauri,murya narawa yagaidashi,

"kai zonan"

yafaɗi adake amemakon ya'amsa gaisuwan dayemai,

jiyayi kaman yazura aguje don tsoro,sedai baze'iya gudunba don yasan koyagudu batsira yayiba,kaman me tafiya akan ƙwai haka yake takawa ahankali,

tsayuwanshi agabanshi yedai daida saukan wani abu kaman guduma afuskanshi,kafin yadawo hayyacinshi yaji yadamƙi kunninshi,

"kai dan ubanka menace maka"?

kanshi dayemai nauyi yashiga girgizawa hawaye nabin fuskanshi,yabuɗe bakinshi yanajin yanda fuskanshi ya'amsa dawani irin zugi metsanani,

sedai ƙunan kalaman dayakeson furtawa sun shafe wannan,besan dali-liba amma sau ɗari zega wannan mutumin dake gabanshi sau ɗari zeji ƙaunanshi da soyayyanshi dabesan daga ina kuma yaushe sukasami muhalli acikin tsokan naman dake ƙirjinshi,

"nidakai bamada wani alaƙa"

yafaɗi acan ƙasan maƙoshi,wani marin yasake sakinmai aɗayan gefen kuncin nashi,yasaki ihu yaname jada baya,jikinshi gabaɗaya naɗaukan rawa,

muryan Mamy yaji sedai yakasa tan tance ma'anan abinda take faɗi,yabuɗe idanunshi daƙyar yana saukewa akan Mamy data tallafoshi zuwa jikinta,

yana kallon bakinta namotsi,yarufe idanunshi dakemai zugi naban mamaki,

Mamy da dawowanta kenan daga maƙota barka taɗago Sadauki dake jikinta ganin yasuma yasanyata ɗago jajayen idanunta tasaukesu akan Muhammad dake zaune hankalinshi kwance tamkar besan wani abu nafaruwa apalonba,

Masu karatu kuya haƙuri mutsaya anan semun hadu a chapter 28

Dafatan dai labarin yaƙayatar daku,wannan littafin gaba ɗayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui mana comment ko kuma kununa mana reaction dinku,sannan kui sharing a group group naku.

Taku Hindatu Auwal

Se anjima.......

*ZAREN KADDARA*

*حبلاالقدر

*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*

ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN

FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only

WhatsApp:

AREWA BOOKS:Hindatu Auwal

PHONE NUMBER:***

_______________________________________