CHAPTER [30
kukanda Sameera tasane yasanyata maida hankalinta gareta,lokaci guda tana kamota jikinta,
"Mamy kicemai karyatafi,kicemai yadawo"
Ƙwallan dayake tattalin zubowansune suka silalo saman fuskanshi,ye saurin buɗe motan yashiga,daƙyar yasamu ya'iya controlling hawayenshi,sedai zuciyanshi duk babu daɗi,
mintina 30 suka iso,Ishaq nataredashi har aka gama shigarmai dakayanshi,seda komai yazama normal yatabbatar babu wani abu dazai buƙata kaman yanda Mamy tasanyashi sannan yemai sallama,
su 4ne aɗakin kacal,sedai sanda yaje mutane 3n gabaɗayansu sungama shirya kayansu,
kasancewanshi shiɗaya aɗakin yabashi daman jera komai nashi a muhallinshi,koda yagama ankusa sallahn magrib,
har lokacin kobi takan abincin da Mamy tazubomai akula beyiba,bayajin yunwa sekewan gida dayake damunshi,
yana gefen gadonshi yana ƙarema ɗakinnasu kallo,komai neat gwanin sha'awa,fata kawai yakeyi musulmaine masu halin ƙwarai,
Ƙofan da'aka turo yasanyashi kallon wajen,matashin saurayine da shekarunshi du-dudu baze wuce nashiba,
wankan tarwaɗane,meɗaukan ido da sheƙi,yanada doguwar fuska da jerarrun fararen haƙoranshi,kayan sport ne ajikinshi wanda yake nunida daga filin ball yadawo,
idanu yazaro yana faɗin
"sannu_kokaine room partner ɗinmu dabaka ƙarisoba"?
yanda yake magana kaɗai ya'isa yanunamaka yanada surutu,
kai kurum Sadauki yaɗagamai,fuskanshi cikeda murmushi,
zama yayi agefen nashi gadon dake kusada na Sadauki,
"thank God!amma naji daɗi,dama se'addu'a nakeyi akan Allah yasa wanda zezo musulmine,
ni sunana Khalid Bello Nawaila,amma anfi kiranada Nawaila,daga zaria nake,kaifa?"
"Mukhtar Usman Kangiwa"
"indian boy"?
Nawaila yatambayeshi yana ɗage gira ɗaya,
dariya Sadauki yayi,yanda Nawailan bayada wahalan sabo yemai daɗi,
kai yagir gizamai alaman"a'a"
"faɗi gaskiya kodai bakason koyamun indian cine"?
yanayin yanda yemaganan yasanyasu yin dariya suduka,
cikinshi yaɗan murza yana yamutse fuska yace,
"I'm feeling hungry"
dariya Sadauki yayi yana nunamai coolern dayazo da abinci,ido yafiddo,
"amma kataimakeni wallahi,dama tinanin yanda zanyi insiyo abinci nakeyi,bayan nagaji and gashi ban'iya girkiba"
yaƙarisa maganan yana buɗe abincin,ƙamshin abincin yadaki hancinshi,ya lumshe ido,
"tun kafin inci abincin nasan zeyi daɗi kaika girka"?
"'a'a but na iya girki"
"ok sauko muci"!
"banajin yunwa"
"bawani nan sedai idan nima bakaso inci"
jin haka yasa Sadauki yasauko,Nawaila yazubamusu,sunaci gabada hira,
suna kammalawa suka tattare kayanda suka ɓata,suka ɗauro alwallah acikin toilet ɗinda ke ɗakin,suka nufi masallaci,
lokaci lokaci suna tsayawa Nawaila yagaisada mutane,donshi yayi sati wurin biyu kenan dafara zuwa,
bayan sun fito sallah suka nufi hall,kaman yanda al'adan makarantan yake,aduk ranan asabar da daddare ɗalibai zasui wanka,su sanya duk kalan suturan dasukeso,suje hall gamasu buƙatan kallo se akunna musu t.v,ga masu buƙatan rawa se akunna musu suma,
tundaga bakin hall ɗin yafara rawa,dagashi har Sameera gwanayene tawannan fannin,babu waƙan dazata fito dabasu iya rawantaba,wasu lokutan idan sukaga rawan da akaima wata waƙan sesuce rawan beyiba,dasunada dama ba'abinda zehanasu buɗe makarantan koyarda rawa,
batareda wani baƙunta ko kunyaba Sadauki yashiga hall ɗin,rawanshi kawai yakeyi tamkar besanda wanzuwan wasu mutane awurin bayanshiba,
darewa sukayi suka bashi fili,kallonshi kawai sukeyi cikeda burgewa,ganin yanda yake rausaya jikinshi kaman babu halittan wani abu waishi ƙashi acikin tsokan naman jikinshi,
uwa'uba kyawunshi,kankaceme wurin gaba ɗaya yaɗauka,nacikin hall ɗin seficewa sukeyi suna kiran nawaje,suzo suga wani kyakkyawa,
ba Sadauki yatashi agunba,seda akatashi,mutane se miƙomai hannu sukeyi suna gaisawa,
don haka agajiye suduka suka dawo ɗaki,basu tsaya yin komaiba sukabi lafiyan gado,
_***_
sosai yakejin daɗin zamada Nawaila,yanada kirki matuƙa,yanada hankali,tsafta,sannan uwa'uba ɗan ƙwalisane wato gayu,
sedai yayi noticed abubbuwa guda biyu atareda Nawailan,
da daddare bayataɓa iya bacci seyasha wasu ƙwayoyi,sannan yaluradashi baya farinciki,yakanyi dariyane kawai batareda wani shauƙiba,
haka kawai yakejin yadamu dahalinda Nawailan yake ciki,yanayine badayaji akan kuwwa se makusantanshi,
***
acikin sati 2 kacal yagama yagane kan makarantan,yanayin rayuwar da ban bancin mu'amala,yanayin jama'a dagayare dakuma jinshi maban banta,
raguwan abokan zamansu christianne,basa shiga harkansu kokaɗan,don haka zamannasu seyemusu daɗi,tskaninsu dasu se hye-hye,
***
kaman koda yaushe idan sundawo daga uzurorinsu,zaune suke suduka akan gadajensu suna hira,
suduka dariya sukeyi saboda labarin da Nawaila yake bashi,sedai kaman kodayaushe dariyan kawai yakeyi batareda wani shauƙiba,
dukda kasancewanshi mutum marasan tambayan mutane agameda halinda zuciyansu ko rayuwansu take ciki,amma seyakasa kauda kai akan Nawaila,hakan yasanyashi cewa,
"da'alama kana kewan gida dayawa"
"meyasa kace haka"
Nawaila ya'amsa yanamaida hankalinshi gabaɗaya kan Sadauki,
"murmushinka baya kaiwa cikin idanuwanka"
"haka rayuwan ɗan boarding yake"
"dole akwai wani aɓoye abayan wannan ɗan boarding ɗin"
"maiyiwuwa amma banaganin na fahimceshi yanda yakamata,"
yaɗan tsagaita kaman baze ƙara cewa komaiba sekuma yacigaba,
"wasu lokutan kafin kafahimci kanka dole seka kalli kanka tacikin idauwan wani,bana taɓa iya samun wannan kusancin da kowwa"
"meyasa?bazaka iya aminta da kowwabane"
"ban amince dakowwaba,saboda bawanda yataɓa niman hakan daga gareni"
suduka shiru sukayi naɗan wani lokaci,gefe ɗaya kuma Sadauki ne kenazartan abokinnashi,
akwai wani irin raɗaɗi ataredashi,baya tan tama akan zuciyan Nawaila cike takeda raunika masu ciwo,yana ganin yanda magan ganunshi suka fama maisu,
"meye wannan?"
Sadauki yasake tambaya asanda yaga yaɗibo tablets ɗinda yakesha acikin envelope,
ƙwayan yasaka aƙasan harshenshi,yalumshe udanunshi yana tsotsa,tamkar dukkan wani natsuwa nashi natattaraneda ƙwayan,
asannan Sadauki har yafiddaran jin wani abu daga gareshi,
"ƙwayace"
Sadauki yakalli Nawaila daye maganan,har yanzu idanunshi nanan alumshe,idan bakasaniba sekace bashi ye magananba,
"meyasa zakaita shanta bayan bazata iya magance maka ciwon dake ƙirjinkaba?"
"amma zata sanyani inyi bacci,batareda mafarkin abinda nakejiba,"
"gobenmu ta ta'allaƙaneda yauɗinmu,abinda muka zaɓa muyi ayau shike yanke hukuncin abinda zefarudamu agobe,zaɓin ba'a tsakanin mekyau da mare kyau bane,wannan sauƙi gareshi,
asalin ababen zaɓin rayuwa sune,mafi ƙarancin sharri acikin sharrika biyu,ko mafi alkhairi acikin alkhairai guda biyu,"
yana gama faɗin haka yajuya yakwanta abinshi,batareda yatsaya ganin reaction ɗinda ke kan fuskanshiba,
koda athuba dasuka tashi bawanda yanunama ɗan uwanshi wani abu agameda maganan dasukayi,
se bayan dawowansu daga masallaci suna zaune suna jiran ruwan wankan dasuka ɗora ye zafi,
"'inada sauran zaɓa atsakanin mekyau da mare kyau,
amma zaɓi atsakanin mafi sharri acikin sharrika biyu,ko mafi khairan acikin alkhairai guda biyu,
waɗannan sune zaɓuɓɓukan rayuwanmu,gayamun 'awani matsayi kaɗaukeni"
Sadauki ye shiru yana tinani,
"bakoda yaushene ake yanke hukunci da ƙwaƙwal waba,kayanke hukunci da zuciyanka,
"ɗan'uwa"
Sadauki yafaɗi,yanajin kalman na zamamai,tabbas beyi ƙaryaba,wannan shine matsayin da zuciyanshi tabama Nawaila batareda tai shawara dashiba,
hannunshi yakamo,yasakamai envelope ɗin,yaname cewa,
"dagayau bazan ƙara shan wannan abunba saboda ɗan uwana,ba iya shiba kome kagani wanda bakaso ataredani kagayamun zanbari,
amma inaso kaimun alƙwari guda ɗaya,shine bazaka taɓa barinaba har abada,"
kai yajin jina mai,yanamejin girman alƙwarin nabin ko'ina najikinshi,
*bayan sati 2*
ɗalibaine tako ina zazzaune tareda ƴan uwansu,suna hira cikin farinciki,kuwwa kaganshi awannan ranan zaka sameshine cikin annashuwa,wannan rana ita akema laƙabida visiting day,
zaune suke aƙasan wata bishiyan dalbejiya,iska me daɗi na kaɗasu,hira yakema Mamy kanshi bisa kafaɗanta nadama,
Sameera da Nawaila yahango suna tunkaro inda suke,hannunsu ɗaukeda popcorn,yanda suke hira atsakaninsu seka ɗauka sun ɗau shekaru da sanin juna,rantse rantsuwa bayau suka soma ganin junaba,bayau yagabatar dashi agaresuba,
hannu yakai cikin popcorn ɗin Sameera data zauna akusadashi,tai saurin janyewa tana dallaramai harara,
fuska yashagwaɓe yana karya kanshi gefe ɗaya,wanda Sameera tasan roƙonta zeyi,hakan yasanyata cewa,
"karma kasoma don bazan bakaba,cemaka nayi kazomuje amma kaƙi,"
kallonshi yamaida ga Nawaila,
"ina bayan ƴar uwata"
yafaɗi shima batareda yabari ye maganaba,
"marowata kawai"
"eey munji"
suka haɗa baki wajen faɗi,
Messenger ne yazo yasanarda Nawaila anakiranshi, hakan yedai daida ƙararrawanda aka buga wanda yake sanardasu ƙarewan lokacin ganawa da ƴan uwansu yayi,
anan Nawaila yemasu Mamy sallama,yatafi amsa kiranda akemai,shikuma Sadauki yabisu Mamy har bakin motansu,bedawoba sedayaga tafiyansu,
sallama yayi ba'a amsaba,yakalli Nawaila dake tsaye yajuyama ƙofa baya,ƙarasawa yayi inda yake seyaji yanacewa,
"meyasa bazaku dubeniba!meyasa bazaku gane ba'iya abinci da abin…,"
"Dude!"
Sadauki yakirashi yana dafa kafaɗanshi,
dasauri yajuyo,lokaci ɗaya yana ɗauke ƙwallan daya taru acikin kwarmin idonshi,
"meke faruwa"
"babu komai"
"shin alaƙanmu nabuƙatan hakane"?
Sadauki yatambaya batareda yaɗauke idanunshi akanshiba,
shiru Nawaila yayi kaman bazece komaiba,shikanshi Sadauki yafiddaran jin wani abu daga gareshi,sekuma yaji sautin muryanshi ɗaukeda wani irin nisan taccen yanayi maradaɗi,
Masu karatu kuya haƙuri mutsaya anan semun haɗu a chapter 31
Dafatan dai labarin yaƙayatar daku,wannan littafin gaba ɗayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui mana comment,kununa reaction dinku,sannan kui sharing a group group naku.
Taku Hindatu Auwal
Se anjima.........
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
®By Hindatu Auwal
*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION
ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN
FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only
WhatsApp:
AREWA BOOKS:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
______________________________________