ZAREN KADDARA

CHAPTER[35

by @hindatuauwal

Adaren Asma'u batasamu bacciba segoshin athuba,daƙyar ta'iya tashi tai sallah,tana idarwa takoma gado.

bata farkaba se 9:00am,koda tafito Ummah kawai tagani sauran duk suntafi makaranta,

"Ummah ina kwana"

tagaidata idanunta kafe akan carpet ɗinda ke palon,

"lafiya ƙalau,yajikinnaki"

Ummah tabuƙata,

"ainawar-ware"

"Asma'u"

Ummah takira sunanta,

"Na'am"

ta'amsa batareda taɗago takalletaba,

"Asma'u!inaso kicirema kanki dukwani damuwa,kimanta komai,kidaina ƙoƙarin tina komai,

ubangijin mu yafimu sanin dalilin faruwan komai,don haka inaso kiɗaukeni amatsayin mahaifiyanki ba uwar riƙoba,kiɗauki ƴaƴana amatsayin ƴan uwanki,

duk abinda yadameki kizo kisanar min,nai miki alƙawarin zamu kitsa murufa da kunnin dama batareda kunnin hagu yasaniba,

bazan taɓa yafemikiba idan kika haɗiye damuwanki kekaɗai acewan bakida kuwwa,

muɗinnan ayanzu ahali gudane ubangiji yahaɗamu awuri guda,don haka komai namu yazama ɗaya,

damuwanmu,farincikinmu,dakomai namu,"

Tunda Ummah tafara magana hawaye kebin fuskanta,batasan wani irin ahali tafaɗoba,sedai tanada tabbacin karamcinsu baze taɓa barinta itada ƙanninta su wulaƙan taba,

tasan bazeyu tamanta komaiba,sedai zatai iya ƙoƙarinta wajen ganin tarungumi ƙaddaranta,

kallonta Ummah takeyi cikeda tausayawa,yanayin Asma'un ayanzu yana nuna zatajure komai rayuwa tazomata dashi,zata rungumi dukwani ƙaddara nata akowani yanayi,

batareda tace komaiba tamiƙe,dakanta tahaɗamata tea,dama ita tahanasu Mardy su tasheta,

taɗauko food flask ɗinda keɗaukeda doya da ƙwai,ta ajiye agabanta,

"Nagode"

tafurta tana ƙoƙarin haɗiye kukan dayake tasomata,

muryan Ummah taji asaman kanta,cikeda kulawa,

"kisha tea ɗin,idan akwai abinda bemikiba seki ƙaro 'a kitchen,and idan kinason bread shima yana can"

"Tom"

tafaɗi,tana ƙoƙarin ɗaukan tea spoon ɗin.

*Sadauki*

Tsaye yake agaban madubi,tirare yake fesawa ajikinshi,fuskanshi ɗaukeda murmushi,

yau sati 2 kenan dafaruwan komai,sedai kona daƙiƙa ɗaya bemanta Mardy ba,

yayi kewanta sosai,yayi kewan kyakkyawan fuskanta,besan yanda akayi soyayyanta yashiga zuciyanshi yazauna farar ɗaya hakaba,

wani irin soyayya yakemata mara limit balle iyaka,idan yace ga adadin sonda yakema watannan baiwar Allahn yeƙarya,abinda yakeji akanta yagirmi dukwani kalma,yafi ƙarfin so balle kuma ƙauna,

haƙiƙa soyayyan Mardy itace ƙaddaran zuciyanshi,yanada tabbacin ze'iya jure komai rayuwa tazomai dashi amma banda rashin Mardy,soyayyan Mardy ze'iya kaishi har lahira,

sallamanda su Sameera sukayi yasanyashi ajiye bottle ɗin,yana gyara wuyan T-shirt ɗin jikinshi,

kallonshi sukeyi cikeda tambaya,tun ada Sadauki gwanine wajen iya kwalliya dasanya tsadaddun kaya,

sedai kwalliyan yau!da farincikin dake kan fuskanshi yasha ban ban da lokutan baya,

"'ina zuwa haka"?

"wurin nuriyya zani"

"nuriyya"!!!

suka faɗi sunan atare,tamkar basu taɓa jin suna kalanshiba,

raɓasu yayi daniyyan tafiya tamkar bega reaction ɗinda kekan fuskansuba,

Sameera tariƙoshi tana dariya kaman yanda shima Nawailan yake dariya,

"Explain"

Nawaila yafaɗi yana sanya idanunshi acikin nashi,

kallonsu yakeyi,yasan halinsu,yasan kalan fitinansu,bazasu taɓa barinshi yafitaba harse yagayamusu,

"I mean mardy"

kai Sameera tashiga girgizamai kai alaman a'a,fara'an fuskanta nagushewa lokaci guda,

idanunshi dakekan fuskokinsu suka ƙara girma,bayason ganin yanayin dakekan fuskokinsu,bayason suce dashi komai,

"No!No Samy!I mean no,karkice komai!kaima haka"

ye maganan yana maida kallonshi ga Nawaila,

hannunshi dayake ƙoƙarin zarewa acikinnata tadamƙe tana ƙara kafeshi da manyan idanunta kalannashi,

"Bro kada kaje,kayahaƙuri kabarta,kaman yanda tagayama kainesa da'ita,tokai hakan,

saboda abinda kaimata babbane,laifinda kaimata mai tsayuwane azuciya,so pls leave her"

"Samy kuskuren dana aikata mata kawai tasani,amma batasan zuciyataba,

batasan kalan soyayyan danake mataba,batasan kalan abinda nakejiba,

mai yuwuwa idanna gayamata abinda nakeji,nanunamata kalan soyayyan danakemata wataƙill setayafemun,"!

yaƙarke maganan muryanshi nasauka,

"Dude!zaka'iya niman soyayyanta amma bazaka taɓa nasaraba,matuƙar kajemata dawannan fuskan taka,

Dude yakamata fa katina Mardy batasan komai agameda kaiba bayan kuskuren daka aikatamata,

don haka ayanzu dolenka kai haƙuri karaba Mardy dajinka da ganinka,har zuciyanta tasamu natsuwa,inyaso daga baya seka nunamata fuskanka alokacinda kasan takamuda ƙaunarka,

dukda banida tabbaci amma inada cikakken yaƙinin zaka samu rangwame daga gareta."

shiru yayi,yasan duk abinda suka faɗi gaskiyane,idanunshi yalumshe nantake fuskanta yabayyanarmai tattareda kallon tsanan datakemai,

nantake zuciyanshi tatsinke,jikinshi ye sanyi ƙalau,daƙyar ya'iya jan ƙafafunshi yakoma yazauna,gumi na tsatstsafomai takowani kafa najikinshi,

lokaci guda yana yanke hukunci danganeda magan ganun su Sameera,

kallonshi sukeyi cikeda tausayawa,irin wannan soyayyan ake kirada love at first sight,sedai tashi tayimai shigan gaggawa,haƙiƙa Mardy itace macenda tashiga zuciyanshi asa'a,kuma tamaida ƙofa tarufe garamm!

Ganin yanda suka koma gefenshi suka zauna cikeda damuwa hakan yasanyashi jin badaɗi,yasan yanda sukeson junansu,dayanda suke ɗaukan duk wani damunwan dayashafesu,

miƙewa yayi yana ƙoƙarin sakin ranshi tunda abinda yakeji yarigada yasamu wurin zama,

"ɗazu munyi wayada secretary,yakamata kaimana booking ɗin flight gobe muwuce,"

kai Nawaila yagyaɗamai,already yarigada yasan maganan,dama wani contract ne yakawosu sewannan ƙaddaran yafaru,ɗazu sukai meeting inda aka shaidamusu sunsamu Contract ɗin,

shiyasa Sadauki yeshirin zuwa wurin Mardy,segashi ayanzu komai yasauya,

@@@

Bayan Abby yadawo Sadauki yasanar dashi tafiyansu Abuja inda dama anan suke aiki a company ɗinshi na S.D.K Building & Construction Company.

sauran company's ɗinnashi kuma wasu yaɗora akai sukemai jagoranci,

seda yafara sallamada Sameera sannan yafito daga gidan,

dayike aranan zata koma gidan mijinta dayake GRA,dama mijinnata bamazauni bane,babban ɗan kasuwane,

yanada manyan shopping malls anan zaria dama sauran garu-garuwa,

@@@

Aƙofar gidansu Mardy ye packing,daga cikin motan yatsaya yana kallon gidan dawani irin nisantaccen yanayi,ga kewan Mardy dayasake lulluɓeshi,

"kai ɗan zomana"

yafaɗi asanda yaga wani yaro yafito daga cikin gidan,ƙarasowa yaron yayi zuwa jikin motan,

se'alokacin yafito,yabuɗe ƙofan baya yaɗauko manyan ledojin shopping ɗinda yemata,

cikin sauƙi yaron yagane Mardy,yabashi one thousand yasha ruwa,bejira fitowanshiba yaja motanshi yawuce abinshi,

*Mardy*

Zaune suke apalo suna hira,wanda gabaɗaya yata allaƙane akan tuwon madaranda Asma'u taimusu,

aƴan kwana kinnan da Asma'u ke girki aɗakin baƙaramin santi sukeyiba,don girkinnata akwai daɗi,yanda kasan wacce takaranci catering,

sallamanda akayi aƙofar ɗakin yasanyasu amsawa,matashin yaron yashigo hannunshi riƙeda manyan ledoji dasuke ɗaukeda tambarin Dubai shopping mall,

"wai gashi abama Mardy"

"inji wane"

Ummah ta tambaya tana ƙarema kayan kallo,

"nima begaya miniba,kawaidai yacemun inkawoma Mardy"

"kai anyama nan aka aikoka kuwa?"

"nan aka aikoni wallahi"

yafaɗi cikeda tabbatarwa,

"kaga Mubeen tashi kabishi muji"

Mubeen yatashi suka koma ƙofar gidan tare,

ko kallon kayan Mardy batayiba,balle tatanka,shan tuwon madaranda ke hannunta kawai takeyi,

ba'ajimaba Mubeen yadawo,

"Ummah munje bamuga memotanba,kuma Sadik yatabbatar munda wurin Aunty Mardy aka aikoshi,don harseda yafaɗi sunanta bayan suffantata dayayi,"

Ummah takalli Mardy datai musu shiru kaman ba'akanta ake maganaba,

"Mardy waye wannan"?

se'alokacin taɗago idanunta takalli ummah,tareda bata amsa,

Masu karatu kuya haƙuri mutsaya anan semun hadu a chapter 36

Dafatan dai labarin yakayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui min comment,kununamin reaction dinku sannan kui min sharing a group group naku.

Taku Hindatu Auwal

Se anjima......

*ZAREN KADDARA*

*حبلاالقدر

*By Hindatu Auwal

*HIKAYA WRITERS ASSOCIATIONS*

*ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN*

FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only

WhatsApp:

AREWA BOOKS:Hindatu Auwal

________________________________________