ZAREN KADDARA

CHAPTER [42

by @hindatuauwal

Zamewa yayi akan kujeran,yaduƙa asaitin fuskanta,handkerchief ɗinshi yamiƙamata,

Bamusu takarɓa,hawayen fuskanta tashare,sedai har yanzu batayarda sunhaɗa ido dashiba.

Muryanshi taji cikin yanayin dabatai zatoba,

"Queen inada Mama da Baba,sedai banida ƙanni,nikaɗai iyayena suka haifa,daga tasowata har yazuwa girmana ina sha'awan ace inada ƙanni,

waɗanda zasu tsokaneni na tsokanesu,na ajiye kayayyakina suɗauka sui hidima dashi,mui wasa da dariya,muje wuraren shaƙatawa alokacinda muke cikin nishaɗi,sedai bansamuba.

Queen kinada ƙanni,nikuma inada iyaye,mai yuwuwa Allah yahaɗamune dan muzamo zuri'a daya."

Batasan taɗago kantaba sedataga idanunta acikin na Kabir,

Wannan shine karo na farko da idanunta suka shiga cikin nawani kuma har natsayin wani ɗan lokaci.

Sallamanda Mubeena yayi abakin ƙofa yasanyasu ɗauke idanunsu daga cikin najuna.

Kabir ye saurin miƙewa yakoma inda yakeda zama tun ɗazu.

Tren hannunta ta'ajiyesu agabansu,sannan tagaida Kabir,cikin fara'a ya amsata sannan yaciro kuɗin da bazece konawa bane yamiƙamata wai tasha sweet,daƙyar Mubeena ta amsa.

Drinks ne,se ruwa,da snacks da sauran kayan motsa baki,

Drinks ɗin yazuba acikin glass cup yamiƙama Asma'u yana ƙasada kanshi kaman yanda akema sarakuna.

Amsa tayi muryanta ɗaukeda murmushinda takeyi tafurta,

"Nagode"

Anan wurin soyayya meƙarfi tasamu matsuguni azuciyan Asma'u da Kabir,

Musayan kalamai suka cigabada yi,besan lokaci yaja harhakaba seda sukaji ana kiraye kirayen sallahn azuhur,

Daƙyar ya'iya mata sallama,yanajin kaman karyatafi.

*NO 144 ISMAIL ROAD,FULANI LOCAL GOVERNMENT*

Kwance yake akan make-ken gadonshi,bacci yakeyi hankalinshi kwance,

"Abba!"...

Karamar muryanta tafaɗi cikeda gajiya,

"uhmm!!"

Yafaɗi yana yamutse fuskanshi batareda yabuɗe idanunshiba,

Little takarya kai,ataɓare tace,

"Abba katashi,Abba"

"Uhm little kibarni"

"Abba katashi ka kaini makaranta"

Idanunshi yabuɗe kaɗan yakalleta,sanye take cikin uniform ɗinta,tayi kyau kamar kullum,kamanninta da Asma'u yasake cika idanunshi asanda tawaromai idanu.

Tana cewa,

"Abba karka sani nai latti katashi"

"Little give me 5 minute more"

Miƙewa tayi daga zaunen datake agefenshi tahaye kan ruwan cikinshi,tana jawo hannunshi tana magana,

"Tun ɗazu Momma ta tashi har tagama break fast,amma kai Abba..."

Kumatunta dayaja yasanya sauran maganan nata maƙalewa ama ƙogwaronta,

Bayada yanda zeyi,dole yamiƙe don yasan halinta,bazata kuma barinshi ye sukuniba seyabar baccinnan.

Dasauri yashiga bayi yewanka,yana fitowa yaga Jamila har taciromai kaya ta'ajiyemai.

Nan da nan yashirya cikin wata dakakkiyar shadda sky blue wacce aka fisanida meruwan sararin samaniya,anyimata ɗinki sumfurin tazarce da aka ƙawatashida ɗinkin hannu.

Takalmi merufi yasanya bayan yafesa tirarenshi na max and spenser,

Yana fitowa palon idanunshi suka haskomai iyalinshi,farincikin shi,fatanshi da komai nashi arayuwa.

Ayanzu shekaru 5 kenan dafaruwan komai,shekarunda suka sauya rayuwanshi gaba ɗaya,wasu shekaru dayasami ciwo arayuwanshi,ciwonda har kwanan yau yakasa warkewa balle yamanta wanzuwanshi.

Sedai ayanzu ba'abinda zece ga Allah segodiya,koba komai ayanzu yanada wata mace datake matuƙar sonshi,take matuƙar ƙaunanshi tareda tayashi jinyan ciwukan dake ƙirjinshi.

Itada family ɗinta gabaɗaya sunyi ƙoƙari sosai wurin nunamai rayuwa,shi iya karanta tauhidi yayi,sukuma sunkoyamai yanda ake amfanida tauhidin 'a aikace.

Haryanzu bai daina jin ciwon rashinsu Asma'u ba,akullum wannan ciwon yana danƙare aƙirjinshi,

Sedai ayanzu yayi sulhu dasu,tayanda yake rayuwa taredasu,batareda sunruguza sauran lokutan dayake dashi arayuwaba.

"Darling"

Yatsinci muryan Jamila acikin kanshi.

"Kinyi kyau sosai"

Yafaɗi yana bata wani side hug,sakamakon kallonda takemai cikeda tuhuma.

Baki tabuɗe zatai magana yesaurin sumbatan goshinta yana murmushi.

"Abba"

Little takira sunan tana kallonshi.

Goshi yadafe yana fesarda iska tabakinshi,yakamo hannun little yana cewa,

"Let's go"

Baki Jamila ta turo ganin yanda yake ƙoƙarin tafiya batareda yaci abinciba.

Tunkafin tai magana yatari numfashinta da,

"Innaje office zanci wani abu"

"OK!I love you"

Yasake faɗi don tasaki ranta.

"Love you too!bye"

Da haka sukai sallama cikeda soyayya da ƙaunan juna.

***

"Abba kullum seka sanyani latti"

Little tace asanda suke tafiya amota,idanunshi yaɗauke daga kallon ti-ti,yakalleta kaɗan yace,

"Sorry little Abbanki yana gajiyane dayawa idan yadawo daga office"

"To Abba kadaina zuwa office ɗin"

Tafaɗi cikeda yarinta,

Dariya yayi jin abinda tace kuma hakan yedai dai da isowansu gate ɗin makarantan.

Sedayaga shigewanta sannan yaja motanshi yawuce fuskanshi ɗaukeda murmushi.

*SADAUKI*

7:00am kaman kowace rana zaune suke 'a dining tabale suna breakfast,

Abby yakalli fuskan Sadauki dayake kurɓan coffee ɗinda ke cikin cup ɗin ahankali yanda kasan yana yanga ko jan 'aji.

Abby yasaki wani tattausan murmushi, kallon fuskan Sadauki kaɗai kansanyashi farinciki mara adadi,yakanyi alfahari yaji natsuwan rai kaman kowani mai iyali.

Amatakin dayake ayanzu arayuwa ba'abinda zecega mahaliccinshi se godiya,don ya'azirtashi da komai,yamallakamai komai,yamalla kamai duk wani abu dayake fatan samu arayuwa.

Irin wannan iyalin yake fatan samu,surayu da juna natsawon rayuwa,yaga jikokinshi ada bai-baye dashi,y...

Asanda tinaninshi yakawoshi nan seya tina maganan da sukayida Sheik Usman ayau da safiyar nan.

Don haka seyace,

"Su Yaya sunje sunyi maganada iyayen yarin yannan kuma anbaka izinin nima"

Jiyayi yakasa haɗiye abinda ke bakinshi,wani abu yatsirgamai tun daga maɗiganshi har tafin ƙafanshi,bebi takan fatan alherinda Ummy takeyiba,yaja kujeran dayake kai ahankali yamiƙe.

"Abby zanwuce office"

Muryanshi tafaɗi cikin wani irin yanayi mewuyan fassaruwa.

Suduka mamakine yakamasu,wanda yafito har akan fuskokinsu.

"Akwai wani matsalane"

Abby yatambaya,itakam Ramlat konace Ummy kaman yanda Sadauki yaraɗamata kasa magana tayi.

Se alokacin yagane abinda yaji ajikinshi yafito har akan fuskanshi, don haka seya ƙaƙalo murmushi yace,

"Bakomai"

"Katabbata""Sure"!!

Kai yajinjina musu yana murmushi,jin yanda sukai magana har suna haɗa baki.

Ummy tace,

"take care"

"You know it"

Ya'amsata yanabarin dining ɗin.

* * *

Tunda yashiga office ɗinshi yake tsaye kaman haƙori,wani abu nakaiwa da komowa aƙirjinshi,

Yasan kamata yayi ace yayi farinciki,ye godiya ga Allah daya bashi daman kaiwa wannan matakin.

Kowani namiji idan yatsinci kanshi a'irin wannan matakin farinciki yakeyi,sakamakon taka wani mataki daze kaishi ga mallakan abinda yakeso.

Sedai agareshi bahaka abin yakeba,shi tashi zuciyan ƙalubalenda kegabanshi kawai take haskomai.

Tsoronshi Allah,tsoronshi ganin fuskan Mardy ɗaukeda tsananshi,tun ashekarun baya daya haɗuda ita bayajin ze'iya rabuwa da'ita,balle kuma yanzu da soyayyanta tagama ratsa kowani jijiya da tsoka najikinshi.

Baya raba ɗayan biyu idan har yarasata to tashi rayuwanma rasata zeyi,z...

"Dude!"

Yariski muryan Nawaila 'a tsakiyar kai.

Sedaya fara haɗiye abinda yakeji,yanimi wuri yazauna yana kallon fuskan Nawaila.

"Ashe su Baba sunje wurin iyayen Mardy"

"Uhmm!"

Ya'amsashi kaman meciwon haƙwara,yaname kunna system ɗin gabanshi.

Nawaila yace,

"yaushe zakafara zuwa taɗi"

Banza yemai yana kama aikin gabanshi,duka yaɗaskamai,Sadauki yadallaramai hararan wasa yana cewa,

"Leave me alone"

Tunda Nawaila yaji yace haka yasan baze saurareshiba,sekawai yamiƙe yabarmai office ɗinshi.

4:00pm yashigo gida,kai tsaye ɓarayinshi yashige,ye wanka,yashirya cikin wata boyle milk colour,anyimata ɗinkin hannu da zaren daye matuƙar dacewa dayadin.

Hula yaɗora akan lafiyayyen gashinshi dayasha gyara se ɗaukan ido yakeyi,sajenshi yakwanta akan fuskanshi se ɗaukan ido yakeyi.

Ga takalminshi mara rufi daya fito daga companyn vista,da kallo guda zaka gane matashine ɗan gayu,ɗan ƙwalisa,dayake kan lokacinshi,irinshi ake kirada end of discussion.

***

Yana isowa ƙofan gidan ye packing,taƙaramin ƙofa yashiga,ye tsaye 'a gate na biyu,yana addu'an ubangiji yakawomai wanda zekirawomai ita,don yasan koya kira wayanta baɗauka zatayiba.

Kallon sama yayi,yaga rana tayi shirin faɗuwa,gari yafara duhu,gani yayi anbuɗe gate,tukun wata mota ƙirar BMW tashigo.

Idanunshi suka haskomai wani dattijo mai kamala da dattako,ko acikin dubu yaga wannan dattijon zeshaidashi,saboda ƙaddara bata haɗa fuskokinsu cikin sigan dazasu manta junaba.

Cikeda girma-mawa yaduƙa yagaida Abba asanda yaƙariso inda yake,

Fuskan Mahmud ɗaukeda murmushi ya'amsa yana ɗorawada,

"Aibakata tsayuwa ananba,muje ciki se akirawo maka ita"

Cikeda kunya yabi bayan Abban,wani sashi na zuciyanshi na addu'an yanda mahaifinta ya yafemai,yasa itama tayafemai.

Palonshi Abba yakaishi,yafita ba jimawa sega Mubeena ɗaukeda babban trey,ta ajiye akan coffee table ɗinda ke palon,tana gaidashi cikeda girma-mawa.

Hannu yasa a'aljihunshi yaciro kuɗaɗenda besan adadinsuba yabata amma taƙi karɓa,sekawai yasakamata a trey ɗin don yasan zatagani.

Wayanshice tai ƙara alaman shigowan saƙo,buɗewa yayi yana maida hankalinshi gaba ɗaya gun saƙon,

hakan yasa beji shigowan Mardy ba,se ganinta dayayi atsaye ajikin garun ƙofan,hannunta naɗe akirjinta,tai tsaye,tsayuwa irinna sodoji.

Tayi matuƙar yinmai kyau acikin idanunshi, bazece agaba ɗaya rayuwanshi betaɓa ganin mace mekyantaba,

Sedai ita kaɗaice macenda takesanyashi yamance kanshi idan ye tozalida kyakkyawan fuskanta.

Duk da sanye take cikin hijjab green colour da akaima ɗinkin jalbab,wanda yarufeta ruph har ba'a'iya hango yatsun ƙafafunta.

Kewanta da soyayyanta suka rufarmai lokaci guda,hakan yasanyashi rasa kalman dazeyi amfanidashi wurin yinmata magana.

Duk da kuwa bezo wannan matsayin asauƙiba,besamu daman ganinta haka cikin ruwan sanyiba.

Miƙewa yay,idanunshi kafe akanta,batareda yasan mezece da itaba.

Idanuntane suka sauka akanshi,tai saurin ɗaukesu daga gareshi kaman wani naman ruwa ko wani abu datai kuskuren gani batareda tai zato ko tsammaniba.

Idanunta kafe suke akan tile's ɗinda ke wurin,laɓɓanta dasuke matuƙar burgeshi suka motsa,muryanta tafito ɗaukeda abinda yafi tsana aduniya.

Masu karatu kuya hakuri mutsaya anan semun hadu a chapter 43

Dafatan dai labarin yakayatar daku,wannan littafin kyautane agareku masoya,kudai kui min comment,kununamin reaction dinku sannan kui min sharing a group group naku.

Taku Hindatu Auwal

Se anjima......

*ZAREN KADDARA*

*حبلاالقدر

*By Hindatu Auwal

*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*

*ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN*

FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only

WhatsApp:

AREWA BOOKS:Hindatu Auwal

PHONE NUMBER:***

____________________________________