CHAPTER [46
Wani abune yatokare mata maƙoshi,Allah yagani ta tsaneshi,batason ganinshi,batai auneba setaji wasu irin hawaye masu zafi nabin fuskanta.
Nantake yaruɗe,yabi duk yadiririce,Allah yagani bayason kuka,balle kuma kukan mace,macenma wacce yake matuƙarso fiyeda komai,wacce ze'iya bada rayuwanshi don ganin batai ƙunciba.
Amma wai shi dakanshine yasanyata kuka,haushin kanshi dakanshine yakamashi,shima kaman zeyi kukan yace
"Don Allah kidaina kuka"
Kaman jira takeyi ye magana sekawai tabuɗe baki tashiga kuka kaman wata babyn roba mai batir,
Jikinshine ye sanyi,duk yanda yaso ye magana da'ita bazata yardaba,sekawai yamatsa gefe,tashige cikin gida.
Yafi minti 10 atsaye,yana tinanin abinda bazece kona mene neba,wani yaro yagani zeshiga gidan yakirawoshi,yabuɗe bayan motanshi yaɗauko ledan siyayyan dayemata yabashi yakaimata.
*
Seda ta tsaya 'a garden tasha kukanta sanrai sannan tashiga ciki,
Asma'u kaɗai tagani 'a palon tana kwance,dayike yau bataje makarantaba batada lectures,
Zama tayi akan kujera tana sauke numfashi,
Asma'u tace,
"sannu dazuwa"
"Yawwa Ukty"
Seda Asma'u tamiƙe daga kwancen datake sannan taga idanunta dasukai jaa,alaman tayi kuka,duhun fatanta yaɓoye yanayin fuskanta.
Cikeda kulawa Asma'u tace,
"Ukty meyasami idanunki"
Hannunta Mardy takai tamurza idanunta kaɗan tana bata amsada
"Kwarone yafaɗamun a'ido,amma yafita,wai inama Ummah takene"?
"taje maƙota barkan matan Suraj"
"Allah..."
"Assalamu Alaikum"
Matashin yaron ye sallama akofan palo amsawa sukayi,
Mu'azzam yashigo yana miƙama Mardy ledan,
"Wai gashi inji wani aƙofar gida"
"Wuce kamayarmai kace nace banaso"
Juyawan yayi,Asma'u ta taroshi,ta'amshi ledan tana cewa,
"Kaji Mu'azzam jeka abinka"
Bamusu yajuya,
Asma'u takalli Mardy datai kicin-kicin da fuska,kaman wacce aka aikomata da saƙon mutuwa,
Ba mardy ba,hatta ita kanta ada ta tsani wannan Sadaukin,amma ayanzu soyayyan dayake nunamata yasanyata tafarajin tausayinshi,jiranda yemata kaɗai ayau kafin tadawo ya'isa yanunama soyayyan dayake mata bakaɗan bane.
Tafi kuwwa sanin Mardy bazata taɓa sonshiba don zuciyanta tarigada tarufe tun dagakan Zaid,sedai yakamata'ace tadaina wulaƙantashi,
"Ukty"!
"Please indai akanshine karkice dani komai"
Kaman yanda Mardyn tabuƙata haka Asma'u taja bakinta tai shiru.
*NO 56 TABARAKALLAH KANO*
Tsaye take abakin palon tana ɗagama Alh.Zanna dake ƙoƙarin fita 'a mota hannu alaman bye-bye,bata sauke hannun taba sedata daina hango motanshi megadi yamaida gate yarufe.
Kaman jira takeyi yafice,nantake murmushin da kekan fuskanta ye ƙaura,asalin mood ɗindake cikin zuciyanta yabayyana akan fuskanta,
Dasauri tanufi sashenta,kai tsaye bedroom ɗinta tashiga,tabuɗe wardrobe taɗuko wata leda,
Ko tsayawa buɗe ledan batayiba,tasa hannu tayagashi,dogon hijjab da niƙaf suka bayyana,ɗauka tayi tasanya,
Tafito daga gidan batareda ta tsaya taɗauki motantaba,abinda zatace bata taɓa yinshiba tun bayan aurenta da Alh.Zanna,
Tana isowa bakin teey-teey tasamu me adai daita taɗauki drop zuwa asibitin mlm Aminu Kano.
Me adai-daitan nasauketa tashige ciki dasauri sefaman waige waige takeyi tamkar wata mara gaskiya.
Kai tsaye office ɗin doctor Nafisa tanufa,
10:00pm yedai dai da tura ƙofanda Hajiya Mainah tayi bakinta ɗaukeda sallama,
Azaune tasameta akan kujera,tana duba wata patient,ganin Hajiya Mainah yasanyata sallaman wanda take gabanta,
Bayan tafita Hajiya Mainah tazauna akujeranda ke gaban table ɗin doctor Nafisa,
Batareda wani ɓata lokaciba tai mata bayani,doctor Nafisa ta umarceta da tashiga bayi ta taromata wannan ruwan mugunyan acikin wani ƙaramin bottle test,don akai lab ai gwaji.
Tana fitowa tamiƙamata,doctor Nafisa taɗauki waya takira wani mutumi dataji takirashi da Ubaid,
Bajimawa yashigo yakarɓi ruwan mugunyan yafita,
Tundaga fitanshi har zuwa lokacinda Ubaid yadawo zuciyan Hajiya Mainah besamu sauƙiba kona second ɗaya,
Result ɗin doctor Nafisa tabuɗe,tundaga kan fuskanta zakagane koma meye acikin takaddan tobame daɗibane,
Hakan yasa hankalin Hajiya Mainah yaƙara tashi,batace komaiba se idanunta dasukayo waje kaman jaɓa tafaɗa akunu.
Doctor Nafisa tagyara zama tukun tashiga gaya mata result ɗin,
"Hajiya kiyahamuri sakamakon test ɗinki yanuna kinkamuda cutan cancer,wanda yafaru sakamakon mu'amala dakikeyi tsakaninki da jinsinki na ɗiya mace,
Kuma cutan tayi ƙarfi tayanda magun guna bazasu ɗauke kiba sedai aimiki aiki"
"Yaushe yakamata 'ai aikin and menene rules ɗin aikin"
Hajiya Mainah tai tambayan muryanta adake,zuwa yanzu hawaye sunƙafe mata,dagaskene wani tashin hankalin yafi gaban aimishi kuka.
"Aikine dabayada matsala,don awuni ɗaya za'ayi kuma two days kawai zakiyi don muga kyan jikinki,se payment ɗin 500,000."
"A'ina za'ai aikin kuma yaushe"?
"Idan har kinbiya kuɗin aikin to yin aikin baze zama mewahalaba,"
"Account number ɗinki"
Hajiya Mainah tace tana kallon fuskan likitan da kallo guda zaka shaida son kuɗinda take dashi,irin sune likitocinda suka maida harkan lafiya yazama kasuwanci,kauda tinanin tayi agefe,tai mata transfer din kuɗaɗenta.
"Ok sunshigo,inaganin gobema zaki iya zuwa asibitin A.B.T.H SHIKA ZARIA,
Hajiya Mainah tayamutsa fuska tacikin niƙafinta,kaman zatace wani abu sekuma tafasa,tamiƙe tana amsamata da setazo.
*
Batasha wahala wurin yinma Alh.Zanna ƙaryan zataje gaisuwan uwar riƙonsu nagidan marayu acan katsina kuma bazata dawoba se'anyi uku.
Kuɗi yabata sosai tareda yinmata ta'aziyya,baicin ayyukama sunyimai yawa daba abinda zehanashi zuwa har can katsinan yemusu gaisuwa.
Washe gari tun 7:00am taimai sallama tafito amotanta,takama hanyan zaria,tuƙi takeyi ahankali amma bazatace anatseba,don shikam natsuwannan tarasashi,balle tai amfanidashi,
Wata mata tagani atsaye agabanta tajuyamata baya,sanyeda fararen kaya,horn tadanna mata amma matan tai banza.
Cikin ɓacin rai takuma danna mata horn ɗin,wannan karon tajuyo sedai ganin fuskanta da Hajiya Mainah tayi yasanyata sakin sitiyarin tana ambaton,
"HAMRAH"
Batai auneba sejitayi kanta yabugu da glass ɗin motan,kafin motan tai wani irin juyawa kanta yakuma buguwa a'inda bazatace ko inabane,duhune yagilma mata tacikin idanunta,daganan komai yeshiru.
Masu karatu kuya hakuri mutsaya anan semun hadu a chapter 47
Dafatan dai labarin yakayatar daku,kudai kui min comment,kununamin reaction dinku,sannan kui min sharing a group group naku.
Taku Hindatu Auwal
Se anjima.......
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
*By Hindatu Auwal*
*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*
*ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN*
FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only
WhatsApp:
AREWA BOOKS:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
___________________________________