ZAREN KADDARA

CHAPTER [47

by @hindatuauwal

Wata mata tagani atsaye agabanta tajuyamata baya,sanyeda fararen kaya,horn tadanna mata amma matan tai banza,

Cikin ɓacin rai takuma danna mata horn ɗin,wannan karon tajuyo sedai ganin fuskanta da Hajiya Mainah tayi yasanyata sakin sitiyarin tana ambaton,

"HAMRAH"

Batai auneba sejitayi kanta yabugu da glass ɗin motan,kafin motan tai wani irin juyawa kanta yakuma buguwa a'inda bazatace ko inabane,duhune yagilma mata tacikin idanunta,daganan komai yeshiru

*ASMA'U*

Tafe suke suna hira,kowacce cikinsu tana rataye da jakanta na makaranta,

Tsayawa sukayi awurin meraken dake farkon layinsu,gaisawa sukayi,kasancewan sun saba dashi kuma Kamilun bayada wata matsala.

Sanda guda suka siya,suka ɗan tsaya suna jiran yayanka musu,

Wata baƙar motace range rover tawuce,bakuma tai nisaba tayo rivers ta tsaya,

Wani dattijon mutum ma'aboci kamala da dattako yafito,sanye cikin manyan kaya,tun bai ƙarisoba ƙamshin tirarenshi yacika musu hanci.

"Assalamu Alaikum"

Yafaɗi cikin muryanshi mezurfi,

"Wa'alaikassalam"

Suka amsa suduka,

"Sannunku ƙannina"

Amemakon Asma'u ta'amsa seta ɗauke kanta,don yanda taga fuskanshi tasan zeyi surutu da iyayi,

Mardy ta'amsamai ganinshi babba,don zekai shekaru 35-37,kallo ɗaya zakai mai kashaida mutumne me natsuwa kuma da alama yanada rufin asiri ga wani irin exposure daya ratsashi,

"Ƙannina ina zuwa haka"

Yatambaya fuskanshi ɗaukeda ƙayataccen murmushi,

Sakin hannun Mardy Asma'u tayi tai gaba abinta,

Mardy taɗanyi murmushi tana amsashida

"gida zamuje se anjima,"

Bakuma ta tsaya jin mezeceba tajuya daniyyan tafiya,

Dasauri yasha gabanta yana cewa,

"don Allah zan'iya samun numbern wancan sistern naki"

Shiru Mardy tayi,Allah yagani bazata iya wulaƙanta wannan mutuminba,ko bata girmamashi don shekarun shiba,kamalanshi da kwarjininshi bazasu bata kofaba,

"Kayahakuri amma bamuda waya"

Bashiba hatta ita sedatai mamakin ƙaryan data sharamai,ganin tana shirin tafiya yasa Kamilu cewa,

"Hajiya Mardiyya kitsaya kikarɓi raken mana,nakusan gama yankawa"

"Idan kagama ka aiko mana dashi"

Mardy tabashi amsa batareda tajuyoba don har yanzu wannan Alh.yananan atsaye.

Lokacinda ta'isa gida Asma'u har tayi sallah,tanama cin abinci.

Allah yataimaketa Ummah bata apalon da batasan mezataceba.

"Ukty sanda zuwa"

Banza tai mata tai shigewanta ciki,kasancewan bata sallah yasa jakanta kawai ta ajiye tafito.

Asannanne taga Ummah azaune akujeranda ke kusadana Asma'u,

Kujera taja tazauna,

"Sannu Ummah"

"Yawwa!yagajiyan makaranta"?

Mardy tai murmushi tana amsawa da

"lafiya kalau"

Yunƙurawa tayi daniyyan tashi tazuba abincin Asma'u tai saurin miƙewa tana cewa,

"Ukty barina zuba miki"

Batace da ita komaiba,don bataso tai magana Ummah taji tai mata faɗa akan wulaƙanta mutane,tafiso tai mata ita da ita.

Kwanaki biyu da faruwan haka,misalin 4:30pm,

Asma'u na kitchen tana girkin yamma taji muryan Abba nakiranta,

Kallon Mardy tai dake yankan salad kunninta sanyeda earpiece tana wayada Zaid,

Sanin kotayi magana bazata jiyotaba yasanyata zare earpiece ɗin,dasauri takalleta,

Asma'u tace,

"girki zaki kulamun dashi Abba yana kirana"

"Tom"

Ta'amsata tana maida earpiece ɗinta,

Atsakiyan palo taganshi atsaye,dayike yau beje shagoba,yatashi bayajin daɗi,

Ƙarisawa tayi taduƙa agabanshi,cikeda ladabi tace,

"Abba gani"

"Kije ƙwargida akwai baƙonda yake jiranki inkin dawo zamui magana"

Kanta aduƙe ta amsada "to"

Ciki tashiga taɗauko mayafin doguwar riganda ke jikinta,fuskanta bata buƙatan wani kwalliya,don haka lips tick kawai tasa,tazira takalmi meɗan tudu kaɗan,se humra data mutstsika tafito.

@@@

Tundaga nesa ta hangoshi tsaye ajikin motanshi,bata shaida kowayeba sedata ƙarisa gabanshi,

Shine dai mutuminda shekaranjiya yataresu awurin Kamilu me rake,mamakin yanda akayi yasan gidansu yakamata amma seta shanye.

Tagaidashi cikin sanyin murya,

"Barkanki da fitowa ranki yadaɗe"

Alh.Mujahid yafaɗi amemakon ya'amsa gaisuwan da Asma'u tai mai,

"Barkan kadai"

"Yakike,ya gida,ya ƙarin kyau"?!

Murmushi mesauti tayi,tana amsawada,

"lafiya ƙalau"

"Sunana Alh.Mujahid,ni ɗan kasuwane,inada matata guda ɗaya sedai bamu taɓa samun haihuwaba,

Maganan gaskiya Asma'u tunda naganki wancan ranan naji soyayyanki tashiga zuciyata,

Aranan natambayi me rakennan yagayamun gidanku,banyi ƙasa agwuiwaba naje nasami Baba,akabani izinin nima.

Saboda dagaske nakeyi,sonikeyi na mallakeki amatsayin matata,duk da nasan akwai tarin masoya bayanni amma zanso kibani dama"

Seye shiru,Asma'u tasaci kallonshi tawutsiyan ido,

"Soulmate"

"Uhm"

Asma'u ta amsa,

"Bakice komaiba,ko bakison mai matane"?

Dasauri tagirgiza kai tana murmushi, don talura yanada barkwanci da kuma zolaya,da alama bazeyi girmankai kaman nawasu masu kuɗinba.

"Am...

Ringing ɗinda wayanshi yafarayine yakatse maganan dazeyi,

Nantake yanayinshi yasauya,ame makon yaɗauki wayan seya kalli Asma'u yace

"kawo wayanki nasa miki numberna"

Bamusu tamiƙamai wayan,bayan yagama lodamata numbobin yamiƙamata wayan,

"Sweat heart zantafi semunyi waya"

Kai tagyaɗamai tareda cewa

"Allah yabamu alkhairi"

"Agaida Madam"

Tasake faɗi don karyace batai mishi karaba,

Amemakon yatafi seya tsaya yana kallonta harseda ta shige gida.

Da murmushi akan fuskanta tashiga palon,

"Ukty wannan murmushin love haka"

Cewan Mardy dake zaune,pillow taɗauka ta cillamata,Mardy takauce tana dariya.

Bayan sallahn isha'i tana zaune Mubeena tasanar da'ita Abba nakiranta.

Miƙewa tayi saboda akwai hijjabin data idarda sallah ajikinta,da sallama tashiga palonnashi,seda yace da ita tashigo sannan tashiga.

Azaune tasameshi akan carpet ɗinda ke palon,Ummah nagefenshi tana yankamai kayan fruit,

Abba yace,

"Asma'u yakukayi da baƙonnaki"

Kai tasunkuyar tana rasa mezatace,sekawai tai shiru tana matsa yatsunta kaman meyi musu tausa,

"Asma'u inaso kinutsu,kitsaida hankalinki kifahimci Alh.Mujahid,don banbashi daman zuwa wurinkiba seda nai bincike akanshi,tunda kantinshi anan cikin sabon gari yake,

Wato Asma'u shi Alh.Mujahid koda bashida arziƙi halinshi kaɗai ya'isa yasa a'aureshi,saboda mutumne me kirki,ga zakka,ga tausayin naƙasa dashi,

Wato ko waɗanda suke ƙasa dashi sunajin daɗinshi balle kuma iyalanshi,

Amma Asma'u bazan miki doleba,idan har bakyasonshi ki magana inbashi haƙuri,"

"Aini Abba banida tacewa awannan maganan,duk abinda kayi dai daine,banida jaa da magananka"

"To Alhamdulillah,indai hakane to gobema inazuwa zan sanardashi"

Ummah tace,

"nidai da ace so samune da'an haɗamana dana Mardy,kaga Asma'u tazama uwar ɗakinmu kenan."

Ummah taƙarshe maganan cikin sigan zolaya,

"Kai Ummah!nihar na'isa,kuma duk wanda ya aureni ai dole yemuku biyayya"

Asma'u tace cikin jin kunyan maganan Ummahn,

"To matan Oganmu Allah yakiyayeki ranki yadaɗe"

Yaƙarke maganan yana dunƙule hannunshi gamida jinjinamata alaman girmamawa,

Suduka dariya sukayi atare.

Masu karatu kuya hakuri mutsaya anan semun hadu a chapter 48

Dafatan dai labarin yakayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui min comment,kununamin reaction dinku,sannan kui min sharing a group group naku.

Taku Hindatu Auwal

Se anjima....

*ZAREN KADDARA*

*حبلاالقدر

*By Hindatu Auwal*

*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*

*ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN*

FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only

WhatsApp:

AREWA BOOK:Hindatu Auwal

PHONE NUMBER:***

____________________________________