CHAPTER[51
Tana kaiwa nan tafice abinta,a balcony tahaɗuda Mardy dazata shigo,
"Lafiya,meke faruwa,wacece waccan tafita"
Mardy tajero musu tambayoyin alokaci guda,ganin hankalinsu suduka atashe.
Se alokacin wasu hawaye masu zafi suka ciko idanun Asma'u, taceda Mardy,
"Matar Alh.Mujahid ne tazo jan kunni"
"Metace muku"
"Bakomai"
Ummah tafaɗi cikin sigan abar maganan.
Mardy naji nagani haka Ummah tahana Asma'u taceda ita komai,don aganinta bakomai bane face zafin kishi.
@@@
Ahankali take takowa cikin palon,sanye takeda wata material maroon colour,tayafa belt ɗinshi akanta,jakanta rataye akafaɗanta nadama,Mardy nagefenta.
Wayatta dake riƙe a hannunta tahau ruri,sunan Alh.Mujahid tagani zane a screen ɗin wayan tana kallon wayan har ta tsinke.
Yau kwanaki 2 kenan dazuwan matanshi,kuma tun safiyan ranan da sukai wayadashi besake kirantaba balle yazo.
Sallama sukaima Ummah suka fito, zuciyan Asma'u ta doka sanda idanunta suka haskomata Alh.Mujahid tsaye ajikin motanshi,ga Abba suna gaisawa.
Jitayi kaman takoma,amma seta dake ta ƙarisa wurin,
"Ina kwana"
Tafaɗi murya acukule,sa'ilinda suka iso inda yake,itama mardy gaidashi tayi sannan takoma ciki,tajira Asma'un,shima Abba ciki yashige.
Alh.Mujahid yagyara tsayuwanshi agaban Asma'u dake tsaye kanta aƙasa,
Takashe interlock da ido,kaman mena zartanshi,kaman meson gano wani abu daga ƙarƙashin wurin.
"Dafari dai iname baki haƙuri tun rananda Badi'a tazo gidannan naso inzo amma Badi'a ta kulleni agida. Yanzuma daƙyar nasamu na fito"
Kalamanshi baƙaramin ƙonama Asma'u zuciya yayiba,
Muƙutt!tahadiyi wani abu meɗaci,daƙyar tabuɗe bakinta muryanta tafito.
"Kaima tsoronta kakeji kenan"
"Batsoro bane kiyaye wane,nafar kodai dole ka lallaɓa matanka idan irin wannan al'amarin yataso.
Saboda asamu alallaɓa ayi komai lafiya,amma ita har ta'isa tahanani aure,ko ta hanani yin abinda naga dama,
Ni!haba 'ai!!nafi ƙarfin wata mace tajuyani,ita kanta tana ganin fuskana tsora...
"Munafuki,algungumi!kai kam Mujahid kaji kunya,yanzu nanne meeting ɗin dakacemun zakaje,
Nace nanne wurin meeting ɗin"
Badia'a tafaɗa tana ƙarisowa gabansu,
Nantake jikin Alh.Mujahid yahau kakkarwa,ye wani tsamo tsamo,yana kyafta idanu kaman jaɓa tafaɗa akunu.
"Mekake gayamata"
Ta tambaya tana tsareshi da idanunta,
"Dama,dama,nazone na...
"Yazone yaƙaryata magan ganunki,yace yafi ƙarfin gidanshi,hasalima tsoronshi kikeji"
"Ƙarya kazo kake mata kenan,to bari intsinka ka,innuna mata kai bakomai bane"
Taƙarshe maganan tana sauke yatsunta biyar akan fuskanshi.
Ido Asma'u taware tana kallonshi, sotakeyi taga matakin daze ɗauka amma setaji shiru,
Hasalima kanshi aƙasa yake,jikinshi nacigabada ɓari.
Cikin tsawa Badi'a tace,
"babu kai,babu ita,kajini"
Kai yagyaɗa mata batareda yaɗago kanshiba.
"Shiga mota"
Tasake faɗi cikeda umarni.
"Mekefaruwa"
Muryan Adam dake ƙarisowa packing lot shida Abba yatambaya.
Kaman batasanda zuwan wani wurinba takafe idanunta acikin na Asma'u da babu komai se zallan tashin hankali.
Tace"ba mariba idan kasheshi zanyi awurinnan be'isa yako motsaba balle yatanka,
Don haka yanada kyau kizauna keda tsoho da tsohuwa,da furfura da gashin gemu kunimi mafita.
Don auren mijina dai dai yakeda siyan ticket ɗin mutuwa"
Tana kaiwa nan tajuya fuskanta ɗaukeda ƙayataccen murmushi,
Numfashi Adam yasauke asanda Badi'a taja motan Alh.Mujahid suka wuce,
Bece komaiba yakama tsintsiyan hannun Asma'u suka koma ciki.
*SADAUKI*
Ledan hannunshi yacilla acikin motan,yaname gyara zamanshi acikin motan.
Key yema motan,kokaɗan bayajin ze'iya amfanida magungunan nan balle kuma shawar warinshi,
Yana shiga office ɗin idanunshi suka sauka akan Nawaila.
Bece komaiba yaƙarisa yazauna,
"Yajikinnaka"?
Muryan Nawaila yakatse zaman kuramenda sukeyi.
Sadauki yace,
"dasauƙi"
"Me doctorn yace"
Sedaya yamutsa fuska kaɗan sannan yabashi amsa.
"Yace jininane yahau,se chronic ulcer and ..."
Yaɗan tsagaita kaman bayason faɗin abinda ke shirin fitowa daga bakinshi.
"And seme?"
Nawaila yatambaya yana tsareshi da idanunshi.
"Kamanta kawai"
"Amma...
"Dude"!!
Yakatse shi dasauri yana miƙewa yashige bathroom.
Tsayawa kawai yayi yana kallon fuskanshi,tunda yadawo daga gidansu Mardy yakejinshi kaman wani artificial intelligence,
Jinshi yakeyi kaman bayada rai awasu gaɓoɓin najikinshi,dayawan wasu abubbuwan yanayin sune don kawai yasan anayi,
Badon yanada feelings ko interest akansuba,sedai dai dana seconds ɗaya yakasa mantawa da'ita balle kuma yacireta azuciyanshi,
Ashekarunda suka gabata idan wani yacemai zeso wata mace haka kai tsaye zeƙaryatashi saboda hango rashin yiwuwan hakan.
Kanshi dake ciwo yadafe,ga zuciyanshi dake barazanan fashewa,
Durƙusawa yayi agun hannunshi dafeda ƙirjinshi,ga wani irin tari daya tasomai lokaci guda,
Wani irin yawune yacikamai baki,ƙoƙarin miƙewa yakeyi amma yakasa,
Duhune yagilma mai tacikin ƙwayannin idanunshi,tukun ko wani gaɓa najikinshi yasaki.
Nawaila nazaune yaji ƙaran faɗuwan wani abu,tinaninshi bekaishi ko inaba se bathroom,
Aƙofan yatsaya yana knocking amma se yaji shiru,batareda tinanin komaiba yabude ƙofan.
Aikam idanunshi sukai mai mummunan gani,Sadauki ne akwance baya numfashi,
Ga jinin da besan kona meneneba yana fitowa tabakinshi.
Hankali amtuƙar tashe yasaɓashi akan kafaɗanshi,sedaya fito sannan mutane sukaga halinda C.E.O ɗinnasu yake ciki.
Yana isowa asibitin ko kyakkyawan packing be tsaya yiba yafito,
Batareda yatsaya kiran nurses ko jiran wild chair ba yasaɓashi yashiga dashi ciki.
Karɓanshi sukayi suka shiga dashi ICU,
Nawaila ye tsaye yana dakon fitowansu,imbanda faɗuwa ba abinda gabanshi yakeyi.
Abby ne yaƙariso inda yake,kallo ɗaya zakaima fuskanshi ka shaida tashin hankalin dayake ciki.
Masu karatu kuya hakuri mutsaya anan semun hadu a chapter 52
Dafatan dai labarin yakayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui min comment,kununamin reaction dinku,kui min sharing a group group naku.
Taku Hindatu Auwal
Se anjima...
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
®BY HINDATU AUWAL
*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*
ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN
FACE BOOK PAGE:@Hindatu Auwal Hausa Novels
WhatsApp:
AREWA PEN:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
_____________________________________