CHAPTER [53
Kallonta yayi da lumsassun idanunshi,tausayin tane yakamashi,ganin yanda duk tadamu,aranshi yakejin yakamata yaɓoye damuwanshi ko don ita. "Yawwa my love"
Ya'amsa asanda yake ƙoƙarin zama,don kwanciyannan ya isheshi,
Kamashi tayi tana cewa,
"kayi ahankali karka gotadda ruwan"
Pillow taɗauka tasamai abayanshi yanda zeji daɗin jinginan.
Da ɗan murmushi akan fuskanshi yace,
"Nagode"
Amemakon ta amsa setai murmushi tana cewa,
"mezakaci"?
Dasauri yace,
"bakomai"
Idanunta tazaromai cikin sigan karkaimun haka.
"Shikenan zanci"
"Tome zakaci"
Tafaɗi cikin farincikin daya nuna har akan fuskanta.
"Duk abinda yasamu"
Tashi tayi tazubamai farfesun,sannan ta tai makamai yaɗauraye bakinshi.
"Ke kikira Ummu kice mata adawo da yarin yannan"
Ye maganan asanda yagama haɗiye farfesun dake bakinshi.
Kai tagirgiza tana bashi amsada,
"No!bazan iyaba"
Murmushi yayi yana ƙara nutsadda idanunshi akan fuskanta,datai jaa,kaman jini yataru.
Fuskanta yakanyi hakanne aduk sanda wani abu yabata kunya,kamar dai haka.
Sosai yake murmushi yana kallon fuskanta don yanason wannan side ɗinnata.
"Shikenan bani wayata nakirata"
"Please kar kai haka"
Tafaɗi tana langaɓadda kanta gefe,
"Niba zan'iya jurewaba,gaba ɗaya gidannan babu daɗi da batanan"
"Ba...
"Karma ki wahaladda bakinki"
Kallonshi tayi,acikin ƙwayannin idanunshi taga matsayan zancenshi,don haka setaja bakinta tai shiru.
*MAHMUD*
"Yakake,yagida,ya iyali duka"
"Lafiya ƙalau"
Mahmud yafaɗi asanda yake sakin hannun Alh.Mujahid dayazo wurinshi.
Alh.Mujahid yasunkuyar dakanshi,yafara magana cikin sanyin jiki,dayake nunida koma menene zefito daga bakinshi bamai daɗibane,abune dashi kanshi bayada yanda zeyi.
"Dafaridai iname baka haƙuri akan abinda zefito daga bakina,dannasan baze maka daɗiba,sedai aganina hukuncin dana yanke shine yafi,
Maganan aurennan dai na haƙura,badon komaiba sedon matata,
Kowani aure anayin shine saboda abubbuwa guda uku,
Ƙaunan juna,tausayi da kuma kwanciyan hankali,
Allah yasani inason Asma'u,ina ƙaunarta sedai nasan idan harna aureta matata bazata taɓa barinta tasamu kwanciyan hankaliba.
Kaga innai haka aina cutar da'ita,don haka nina haƙura,kuma duk abinda nakawo nabar mata,ubangiji yemata zaɓin alkhairi"
"Shikenan Alh.babu komai nagode"
Mahmud yafaɗi guiwa asage,hakanan sukai sallama zukata duk babu daɗi.
Kai tsaye palon Ummah Khadija yanufa,azaune yasamesu suduka,harda Adam suna buga game da Nadr,
Ganin yanayin daya shigo yasanyasu fahimtan ba lafiya ba.
Babu wanda ya'iya cewa komai,aƴan kwanakinnan ba abinda zasuce ga Allah se godiya,daga wannan se wannan,ƙaddarorinsu se ruftomusu sukeyi,batareda sunyi shiriba,kuma basada halin gujemusu,dolene su rungumesu koda da hannu ɗayane.
"Gashi"
Ummah tace,tana miƙama mahmud glass cup ɗin da taɗibo mai ruwa mai sanyi,
Karɓa yayi ba musu,tunda yaɗora bakinshi akan cup ɗin besaukeba sedaya shanyeshi tass!!!
Numfashi menauyi yasauke,wacce tafi kamada ajiyan zuciya,
Maganan dake kan harshenshi yake taunawa,Allah yagani ba abinda yafi tsana samada yaga ɗayansu acikin damuwa,musamman damuwan da bayada halin yin musu maganinshi,
Sedai yazasuyi da ƙaddara,duk abinda yake samunsu jarabawane daga ubangijinsu,
Sun amsa tareda godiya agareshi,kuma suna fatan cinye duk waɗannan jarabawoyin,domin akowace jarabawa akwai alkhairi me tarin yawa.
"Asma'u"
"Na'am Abba"
Ta'amsa tana tattaro hankalinta gaba ɗaya tamiƙamai.
"Asma'u ko wani bawa da ƙaddaranshi,kuma duk abinda ubangiji yajarabcemu dashi yasan zamu iya ɗau kane,
Don haka inaso kiyahaƙuri akan duk abinda zakiji daga gareni,sannan ki godema Allah bisa jarabawoyinshi agareki"
Yanumfasa tareda kallonta don yaga reaction ɗinta.ganin kanta asunkuye hakankalinta akanshi yasanyashi cigabada cewa,
"Fitan danayi yanzu Alh.Mujahid ne yazo,yasanar dani yafasa aurenki"
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un"
Ummah tafaɗi hankali atashe,
Adam ye shiru yana rasa mezece,
Asma'u tabuɗe baki daƙyar,muryanta tafito asanyaye,
"Shikenan Abba Allah yasa haka shiyafi alkhairi agaremu"
Tana kaiwa nan tamiƙe,tafiya takeyi kaman zata wuce ƙafafunta,ko ganin gabanta batayi sosai saboda ruwan ƙwallan daya cikasu,tana shiga ɗakin ta faɗa kan gado ta fasheda kuka me sauti koda wasa bata taɓa zaton zataji wani'abu a zuciyanta saboda Alh.Mujahid ba,
atinaninta zuciyanta tagama kokama kowanne da namiji tunda ta rasa Kabir,kuma tun ranar da matarshi ta bar gidan nan ta ƙudurema ranta bazata aureshi ba,
ta ɗauka ta gama da wannan babin ashe ba haka bane,wani irin abune yake kai kawo a zuciyanta dayake barazanan tarwatsa zuciyannata gabaɗaya.
*ADAM*
Asma'u na miƙewa yabita da kallo zuciyanshi na matsewa a ƙirjinshi,idanunshi ya lumshe a gajiye,ya gaji da ganin yanda rayuwa take wasan kura dasu,
Zuwa yanzu yakamata ace yayi wani abu ko zuciyoyinsu zasu samu sauƙi,dan dama ko Alh.Mujahid baice ya fasa aurenta ba shi ba zai bari asma'u ta aureshi ba,bazai taɓa bari rayuwarta tashiga wani hali ba,
tasha wahala sosai a rayuwarta,ta haɗu da ƙaddarori kala kala,zuwa yanzu yakamata ta samu natsuwa,idanunshi da sukayi jajur kaman wutan murhu ya buɗe yana bin bayan asma'u,
yayi tsaye a bakin ƙofan sakamakon sheshsheƙan kukan ta da yaji,kaman bazai motsaba sai kuma ya murɗa ƙofan baya,ya shiga a hankali,a zaune ya ganta itace dai take kuka.
Kallonshi tayi batayi aune basai ji yayi wani irin kuka mai ƙarfi ya taho mata zuciyanta na karyewa,kuka takeyi me sauti,jikinta har yana kyarma,takowa yayi a hankali ya zauna a gefenta,hannunshi yakai kan fuskanta yana share mata hawayen,
hannunta tasa ta ture hannunshi tana girgiza kai baice komai ba sai kallonta dayakeyi,jawota yayi jikinshi,ya mannata a ƙirjinshi.
yanayin da suke ciki bai hanashi jin wani abu ba saidai baibi ta kanshiba balle har yabada ma'ana dan ba yanzu bane lokacin daya dace.
Bayanta yake bubbugawa ahankali,sedata numfasa sannan tajanye jikinta daga nashi tana maida kanta 'a pillow ɗin dake kusada ita,idanunta alumshe tana sakin ajiyan zuciya,ga kanta dayake ciwo ahankali.
Kanshi yaranƙwafo saitin fuskanta daye jajir na kuka da damuwan datake ciki,yanajin ɗumin numfashinta dayake fita ahankali,kasancewan shi mutum me karanta da fahimtan halinda mutane suke ciki yasanyashi cewa
"Nakamuda soyayyanki acikin yanayin da muke ciki ayanzu,zamui farinciki da abinda muke dashi,bansaniba ko zan samu soyayyanki tawannan fanin,amma ina fatan zaki buɗe dukkannin zuciyanki alokacinda muke tare.
Babu buƙatan takura zuciyanki wajen ganin kin maidani matsayin da baki taɓa hangowa ko acikin mafarkinkiba,
Ki kalleni amatsayin abokinki kaɗai yawadatar,komai zebiyo baya tattatareda lokutan dazamu kasance atare,"
Shiru kawai tayi tana kallonshi, ganin haka yasanyashi miƙewa yafita,don baze takurataba,with time zasu zama kaman ko wasu masoya.
Masu karatu kuya hakuri mutsaya anan semun hadu a chapter 54
Dafatan dai labarin yakayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui min comment,kununa min reaction dinku,kui min sharing a group group naku.
Taku Hindatu Auwal
Se anjima......
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
®By Hindatu Auwal
*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*
ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN
FACE BOOK PAGE:@Hindatu Auwal Hausa Novels
WhatsApp:
AREWA PEN:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
____________________________________