CHAPTER [55
Dakinda aka kai Sadauki yashiga,idanunshi kafe akan fuskanshi daye wani irin haske tamkar babu jini ajikinshi,aranshi yakejin baze taɓa zuba ido rayuwan ɗanshi yasal wantaba,ko yayane zetaɓuka,zeyi iya ƙoƙarinshi,idan yakamama har duƙamusu zeyi,shi hakan bakomai bane agareshi matuƙar ɗanshi zeyi farinciki.
*ZAID*
Zaune yake 'a office,fuskanshi ɗaukeda murmushi,yau ɗinnan shikaɗai yasan abinda yakeji,zuciyanshi har ɗagawa takeyi aƙirjinshi,
Wayanshice tai ƙara,murmushin fuskanshi na ƙara faɗada,yaciro wayan,sunan Aunty N dayagani yasanyashi ɗauka,don yasan baze wuce magana akan kayan lefeba,
"Auntyner yakike?"
Yafaɗi muryanshi na bayyanarda ƙaunarta agareshi.
"Kazo yanzunnan!inason ganinka"
"Aun....
Alaman katse wayanda yaji yasanya maganan nashi maƙalewa ama ƙogoronshi,hankali atashe yamiƙe,yaɗauki key ɗinshi yafita,zuciyanshi na ayyanamishi abubbuwa mabanbanta.
Zuciyanshi ce ta tsinke,tsakar gidan babu kuwwa,gidan yayi wani irin shiru,jiyayi ƙafafunshi na lauyewa,suna niman gaza ɗaukanshi,duk da ƙwarinda yake ƙoƙarin bama zuciyanshi.
"Assalamu Alaikum"
Yafaɗi muryanshi can ƙasan maƙoshi,basu amsaba se idanu da suka zubamai.
Zuciyan shine tai wani irin dokawa,ƙirjinshi yabuɗe dawani irin yanayi mezafi,da muryan dayakasa gane ko tashice yace,
"Meke faruwa?ina Maanmu take?"
Yatambaya yana kallon ɗakin,don su gasunan gabaɗaya yagansu,Maanmu ce kawai babu,sekuma Abbu dayake wurin aiki.
"Don Allah kucedani wani abu"
Yafaɗi muryanshi ɗaukeda rauni da karayan zuciya,Aunty Nabila taja numfashi ƙwalla naciko idanunta tace,
"Tana ciki batada lafiya"
"Meyasameta?"
Yasake tambaya yana kallonsu suduka,
"Muna cikin haɗa kaya tayanke jiki tafaɗi,shine muka sami adai daita muka kaita asibiti,doctor Munir yadubata,yace jinintane yahau sosai,tayanda idan batacire damuwan dake rantaba to idan taƙara irin wannan faɗin to zatasamu stroke k...
Betsaya jin ƙarshen abinda zataceba yashige uwaɗɗakan,azaune yasameta akan gado,fuskanta tayi fayau,idanunta sun zurma ciki,jiki amatuƙar sanyaye yazauna agefen gadon idanunshi nakanta.
"Sannu Maanmu,"
Amemakon ta amsashi seta kauda kanta gefe,
Zuciyanshi takarye,murya narawa yace,
"don Allah Maanmu kice dani wani abu"
"Ubanme kakeso incemaka,duk abinda nake gayamaka kana ɗaukane,ko kana saurarone!abinda kaga dama shikakeyi,don haka katashi kaje abinka,gaka ga duniyannan,ta...
"Maanmu don Allah karkimun baki"
Yafaɗi hawaye masu zafi na saukomai,
"Idan banmaka bakiba 'ai baƙin cikinka ze kaini lahira koya naƙasani,"
Jin kalamanta yakeyi kaman wasu abubbuwa masu kaifi da suke yanka ko wani tsoka na jikinshi.yaja numfashin kukanda yakeyi,zuciyanshi na huromai zafi.
Kalamanda suka fito daga bakin Maanmu yasanyashi miƙewa bashiri,agabanta yaduƙa akan guiwoyinshi,kuka yakeyi sosai,muryanshi asarƙe yace,
"Maanmu don Allah karki yafeni,karki barma Mardy ni,nai miki alƙawarin dagayau nabarta,bazan auretaba tunda bakyaso"
Yaƙarke yana rushewa da kuka tareda kife kanshi akan ƙafafunta,murmushi tasaki mecikeda ma'anoni mabanbanta, bayanshi tashiga bubbugawa tana faɗin
"Allah yemaka albarka Autana,yanda kai mun biyayya Allah yabaka waɗanda zasui maka"
Bece komaiba yamiƙe,yadafe kanshi saboda saramai ɗinda yakeyi,idan ba makanta yafayiba to dariya yagasu Aunty Nabila sunayi.
Yana shiga ɗakinshi yakwanta akan gadonshi,hawaye nabin fuskanshi,jinshi yakeyi kaman bashiba,jiyakeyi duniyan namai wani iri,cikin ƴan wasu mintoci komai yacanja daga yanda yasanyashi,ji yakeyi kaman wani yemai musayan rayuwa batareda saninshiba,bayajin zuciyanshi aƙirjinshi se wani garwashin wuta dayake ƙonashi tako'ina.
Hawayenshine suka ƙara gudu akan fuskanshi,sakamakon muryanta dayaji acikin kanshi.
"Ina sonka Omri,banida burin dayafi narayu dakai,idanna sameka nagama samun duk wani abu danake nema arayuwannan,saboda kaine komai nawa,idan babu kai to babu Mardy."
"Ya rabby!"
Yafaɗi yana sake rushewa da kuka,ko alabarai betaɓajin yanayi me ɗacin wannanba,atarihin rayuwanshima gabaɗaya betaba ganin ƙwalla acikin idanun wani namiji dayasan kanshiba,yaɗauka ƙarfin zuciyan maza baya barinsu susami raunin dazasu zubda ƙwalla.
To amma shi ayanzu yana kuka,ƙirjinshi kaman zebuɗe zuciyanshi tafaɗo kuwwa yaga halinda take ciki.
Unin ranan gabaɗaya aɗaki yayishi,ba'abinda ketadashi se sallah,yanaganin kiran wayan Mardy amma yakasa ɗauka,abincin da aka kawomai ma ko arziƙin kallo besamuba balle yakaishi bakinshi.
Bayan sallahn magrib Abbu yadawo,sedaya tsinkayi dai dai lokacinda Abbu yagama kimtsawa sannan yanufi ɗakin,zuciyanshi naƙara narkewa da ciwon gaske.
Ye sallama Abbu ya'amsa daga cikin dakin,yafi mintina biyar atsaye bekomotsaba saboda yanda jikinshi yake rawa ahankali,hatta ƙafanshi daya ɗaga rawa yakeyi,yashiga kanshi aƙasa,yazauna aƙasan kujeranda Abbu yake zaune,baki yabuɗe yanajin zuciyanshi kaman zata fito tabakinshi,hakan yasa muryanshi fitowa babu 'amo balle sauti.
"Abbu don Allah kayahaƙuri kayafemun"
"Mekayi?"
Abbu yatambaya yana kallon fuskan Zaid daya sauya kala,duk da bayada haske amma fuskantashi tasauya launi da fasali,
"Maanmu taroƙeni akan narabuda mardy kuma nayarda"
Yafaɗi kwalla naciko idanunshi da harsun kumbura.
"Meyasa kai haka,idan kasan tun farko bazaka iya jure kowani irin ƙalubaleba meyasa kabari aka kai wannan matakin"
Zuwa wannan lokacin Zaid yakasa danne kukanshi,sedai bame sautiba,wani irin silent crying yakeyi me ciwo kuma cikin kukan yabuɗe bakinshi muryanshi ta fito.
"Abbu nasan ban isa inhana Maanmu rasuwaba,amma bazanso tamutu tana fushi daniba,inaso ko zamu rabu yazamana tatafi tabarni ko intafi inbarta taname sanyamin albarkanta,
Kuma Abbu duk ƴan uwana bameson aurena da Mardy,idan mukai aure ahaka inada tabbacin bazamui farincikiba balle musamu natsuwa bama iya wannanba,
Abbu mardy tanada wani saurayin,wanda yake matuƙar sonta don yanzu haka yana gadon asibiti ciwon zuciya yakamashi,nasami labarine awurin abokina dayake aiki 'a companynsa.
Abbu bawai nafaɗi haka bane saboda inaso nakaucema maganan aurenta kona nuna Sadauki yafini sonta,
a'a sedai inada cikakken yaƙini akan illanda soyayyanta yemai nibai munba,kuma inada tabbacin farincikin dazata samu agidanshi bazata samu agidanaba,
kuma masu lallura irinna Sadauki basu cika tsawon rai aduniyaba idan inada rabon auren Mardy anan gaba zan aureta amma ayanzu na sadaukarda ita agareshi."
Baba Lecturer ye shiru yana kallonshi,duk abinda yafaɗi yasan gaskiyane.
"Shikenan Allah yasa haka shiyafi alkhairi,yahaɗa kuwwa da rabonshi,kai kuma ubangiji yemaka albarka,yabaka ladan biyayya."
"Ameen"
Ya'amsa cikin kukanda yakasa dainawa.
Masu karatu kuya hakuri mutsaya anan semun hadu a chapter 56
Dafatan dai labarin yakayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui min comment,kununa min reaction dinku,kui min sharing a group group naku.
Taku Hindatu Auwal
Se anjima....
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
®By Hindatu Auwal
*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*
*ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN*
FACE BOOK PAGE:@Hindatu Auwal Hausa Novels
AREWA PEN:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
_____________________________________