ZAREN KADDARA

CHAPTER [56

by @hindatuauwal

*ABBY*

Tsaye yake ajikin motanshi,yana waigewaige,ta'inda zega yaro ya'aikeshi yemai sallamada mai gidan,

Mahmud yagani zeshiga gidan,don da alamama daga masallaci yake,don ba'ajimaba da idarda sallahn 'isha'i.

Dasauri yaƙarisa gareshi tareda miƙamai hannu sukai musa biha da murmushi akan fuskanshi yace

"Yagida ya iyali"

"Lafiya kalau"

"Sunana Muhammad mahaifin Sadauki"

"Allah sarki"

Fadin Mahmud yana murmushi,

"Alh.dama nazone naroƙi alfarma daga gareka!duk da nasan mumasu laifine sedai sadauki yanason yarinyannan wallahi yanzu haka yana gadon asibiti,besan halinda yake cikiba"

Yaɗan tsagaita yanason danne raunin dayake tasomai,nantake tausayin Muhammad yakama Mahmud sedai bayida yanda zeyi bakin alƙalami yarigada yabushe.

"Iname baka haƙuri Alh.kuma abinda yafaru abaya yarigada yawuce,mun daɗe da gogeshi daga zuciyoyinmu,haka Allah yaƙaddara,itakanta yarinyan bataƙishi saboda wannan abun bane sedon akwai wanda takeso ɗan uwan tanema don yanzu hakama bikinsu saura kwanaki 10"

"Shikenan Alh.nagode,se'anjima"

Muhammad yafaɗi guiwa asage.

Da haka sukai sallama,Mahmud yashige gida,Muhammad kuma yakoma asibiti,

Mahmud na shiga palonshi yaga Ummah Khadija azaune tanajiranshi,zama yayi akan kujera tausayin Muhammad nasake nashemai zuciya,

"Wai Abban Adam inakatsayane inata jiranka kazo muci abinci"

Sedayafara ɗaukan juice ɗin data ajiye 'a glass cup sannan yace,

"Nazo shigowane nahaɗuda mahaifin sadauki"

Nantake yabata labarin yanda sukayi,Ummah tai shiru tanajinjina irin wannan soyayya da Sadauki yakema Mardy.

Wayantace tai ringing,sunan Ramlat zane 'a screen ɗin wayan,Ummah taɗauki kiran fuskanta cikeda murmushi, gaisawa sukayi,Ramlat tai mata andawo gida lafiya,

"Lafiya ƙalau"

Ummah ta amsa,

Dagacan ɓangaren Ramlat tace

"kayan damukai magana dake ɗazune aka kawo bayan fitanki,gobe idan Abbanta zedawo daga wurin aiki zan bashi seya kawomiki"

Cikin jin daɗin karamcin da ɗiyar yayartata tai mata tace,

"tom nagode,Allah yemiki albarka"

"Bakomai Ummah don Allah agaidasu Mardy"

Tafaɗi da murmushi acikin muryanta,

"Insha Allah zasuji agaida mai gidan nawa"

Dahaka wayattaƙare,Ummah ta'ajiye wayan tana cewa,

"Kaga kayanefa muke hira takecemun tayi ordern kayan gyaran jiki daga Abudabi,shine nace dazan samu dana siyama ƴan biyuna,shine tace inbari idan ankawo natan seta bani tunda ita bayanzu zatai amfanida shiba,shinepha yanzu takirani"

Taƙarke tana murmushi da alama abinda Ramlat tai mata yemata daɗi sosai,shima Mahmud murmushin yayi,aranshi yanacewa mata seku.

*ASMA'U*

Kwance take akan gado,wayanta na hannunta tana dannawa,wayattace tai ƙara sunan yaya yabayyana 'a screen ɗin,

jitayi zuciyanta tayi tsalle,ta tattaro tadawo wuya,daƙyar ta'iya saita kanta taɗau wayan zuciyanta na dokawa kaman Adam ɗinne agabanta,zata'iya cewa ayanzu bawanda takejin nauyinshi aduniya samada Adam,tun rananda yace yanasonta bata ƙara yadda sunyi ido 4ba,k...

"Kifito ina bakin gate"

Muryanshi me taushi da daɗi takatsemai tinani,kafin kuma tace komai yakatse wayan,

Jiki ba ƙwari tamiƙe taɗauki hijjab buttermilk tasanya,flat shoe tazira,fuskannan nata tsaph agyare se wani irin glowing takeyi saboda gyaran da sukesha awurin Ummah bana wasabane.

Sanda ta fito palon babu kuwwa hakan yabata daman fita,ajikin motanshi taganshi atsaye,yayi kyau sosai cikin wata brown ɗin yadi mara nauyi,

anyimai kwalliya da manyan bottle,sajennan nashi takwanta luph afuskanshi,kanshi babu hula,hakan yabama gashin kanshi dayasha gyara daman ɗaukan ido tasigan jan hankalin duk wanda yagani,

Ƙamshin tiraren ziyad natashi daga jikinshi kaman anyi ɓarin companyn ajikinshi.

"Barkanki da fitowa Baby"

Yafaɗi yana sakin wani ƙayataccen murmushi daya ƙara fitoda ainihin kyawunshi,cikeda jin kunya taduƙar dakanta tace,

"Yaya gani"

"Nima baby gani"

Yafaɗi muryanshi anarke,ta wutsiyan ido takalleshi zuciyanta na ayyana mata abubbuwa mabanbanta daƙyar ta iya buɗe baki tace,

"Yaya muje gida"

"No taɗi nazo"

"Taɗi!"

Asma'u tamaimaita kalman dariya natasomata amma setasa hannunta ta toshe bakinta,

Adam yagyara tsayuwanshi yana cewa,

"yes taɗi nazo"

Wannan karon afili Asma'u tasaki dariyanta,yanda yake furta kalman kaɗai dariya yake bata,

shikam ye tsaye yana kallonta,kallo sosai,tayanda har yamanta komai, yakejin tamkar shida itane kawai aciki da wajen duniyannan.

sedatai mai isanta sannan taɗago kai takalleshi setaga shima ita yake kallo,hakan yasanyata sadda kanta ƙasa tana gyaran muryanda yasanya Adam dawowa hayyacinshi.

Befurta ko kalma ɗayaba se buɗemata motan dayayi,cikeda rashin fahimta takalleshi,amma kallonda yemata yasanyata ɗauke idanunta bashiri.

Batun yanzuba idanun Adam lahani sukemata,balle kuma ayanzu datake ganin wasu abubbuwa cikeda idanun nashi.

batada zaɓin dayafi tashiga motan,tana shiga yamaida ƙofan yarufe,tukun shima yashiga,ya kunna motan sukabar gidan,suna tafe waƙar namenj metaken namatsu na playing acikin motan.

Kunya yahana Asma'u kyakkyawan motsi,dai dai da numfashi ahankali takeyi don duk lokacinda yafurta kalman namatsu ɗinnan jitakeyi kaman tai fuffuke tabita tagan dake gefenta tafice.

Jitayi motan ta tsaya tabuɗe idanunta dake lumshe tun ɗazu 'a gate ɗin gidan meruwan fari anyimai ratsin golden awasu wuraren,megadin nagama buɗewa yadanna hancin motan acikin gidan.

Asma'u tabuɗe idanu tana kallon gidan,Adam ye packing suka fito,se alokacin taƙara ganin tsaruwan gidan,

madai daicin gidane mai ɗaukeda plate biyu,se bene,se ayanzu tagane ko wani gidane,ɗaya daga cikin gidajenshine dayakan siya,

Gyaranda gidan yasha yasanyata kasa gane gidan,haraban gidan take kallo tanajin wani irin yanayi nayawo akanta,yanayine damacenda taziyarci gidan aurenta kaɗai zata fahimta.

"Muje ciki ko!"

Muryan Adam yafaɗi adai dai saitin kunninta nadama,kasa magana tayi se kanta data gyaɗamai,atare suka shiga plate ɗin farko,dawani madai daicin palo tafara karo,farin shafenda akaimai yahaske ginin,

Idanuntane suka ciko da ƙwalla,tasani wannan fentin badon kowwa yayiba sedon ita,saboda favorite colour ɗin tane,tasha faɗin inzatai aure zata roƙi mijinta yemata farin fenti.iyayenta sui mata fararen kayan furniture's.

"Nagode"

Tafurta cikin muryan kuka hawaye na silalomata,yabuɗe baki daniyyan magana wayanshi tai ƙara tun daga ringingtone ɗin yagane ummahce,yanda behaɗa ƙaunansu da komaiba hakanyasa akomai nashi nasu daban yake.

Zuciyan Asma'u tai tsalle aƙirjinta,lokaci guda taname buɗe bakinta cikin sigan dayake bayyana nashiga uku,manyan idanunta sukayo waje cikeda nadama,gabaɗaya tamanta Ummah batasanda fitowantaba seyanzu.

Batajin abinda Ummahn takecewa sedai yanda Adam yayida fuska yasanyata fahimtan Ummahn faɗa takeyi,hakan yasata ƙara ruɗewa danasanin biyo Adam na lulluɓeta kaman ƙaton bargo.

"Insha Allah Ummah yanzu zamu dawo"

Taji muryansa yafaɗi,batajira yasauke wayanba tai gaba abinta,tanajin kaman tarufe ido taganta agida,koda Adam yazo amota yasameta,tai tsiri tsiri da ido kaman wacce taima sarki ƙarya.

Dariya tabashi amma seya dake don yasan dariyanshi ze'iya sa Asma'u kuka,sekawai yema motan key,megadi yabuɗe musu gate suka fice.

Haka suka biyo hanya jigum jigum babu mecema ɗan uwansa komai,ita Asma'u kunyan haɗuwada Ummah yahanata magana,tayi danasanin biyoshi datayi yafi cikin kwando daga ƙarkema seta koma tinanin yanda akayi tayarda tabiyo Adam.

Shikam dariyan yanayinta yahanashi magana,yanda fuskanta yayi ayanzu baƙaramin nishaɗi yabashiba,ahaka suka'iso gida,Adam ye packing,Asma'u tai zaune kaman andasata fuskanta nabayyanarda yanayin datake ciki afili.

For the first time da Adam yadanne dariyanshi yace.

"Mujeko?"

Kallonshi tayi tai rau-rau da idanunta ƙwalla na cikosu,

"Meyafaru kuma"?

Yatambaya cikeda kulawa,

Asma'u taja hanci,hawaye nasaukar mata tace,

"Idan ummah ta tambayeni mezan cemata"

"Cewa zakiyi kinje ganin gidanki"

Asma'u tazaro idanu waje tana kallon fuskan Adam daye magana hankalinshi kwance,sekuma tashiga girgiza kanta hawaye na ƙara gudu akan fuskanta duk yanda Adam yaso danne dariyanshi kasawa yayi,sekawai yakife kanshi asitiyarin motan yabuɗe haƙwaranshi talatin yanamata dariya.

Wani irin takaicine yacikata,daman meneman kukane akajefeshi dakashin awaki,'ai sekawai jinta yayi tabuɗe baki tanamai kuka.hakanan yahaɗiye dariyan yajuya gareta yashiga lallashi daƙyar yasamu tahaƙura shima dasharaɗin batare zasu shiga gidanba.

Yana kallonta tafita amotan tashiga takawa ahankali,kaman megudun ƙasa tabuɗe ta afka ciki,sedata ƙarisa bakin gate ɗin sannan talurada mutumin dake tsaye awurin,

yajuya baya dawaya kare akunninshi wanda yake nunida waya yakeyi cikin wata murya ma'abociyan taushi da sanyi,

kaman butun butumi haka Asma'u tai tsaye tana saurarenshi,babu uhm bare uhm-uhm,gabaɗaya ranta yafita daga gangan jikinta yaje wani wurin yaɓuya.

Batasan yanda akayiba sejitayi yabangajeta,taɗaga ƙwayannin idanunta tasauke akan mutumin dake gabanta,

kallonshi takeyi sosai,idanunta kaman zasu faɗo ƙasa,zuciyanta tamatse aƙarƙashin haƙarƙarinta,dawani irin yanayi da tunda tazo duniya bata taɓa tsintan kanta acikiba.

Baki takeso tabuɗe amma takasa sema kanta daya sara yana haurawa wani duniya dabatasan ko inabane.

Hankali atashe Omar yashiga girgizata,akiɗime yashiga kiran sunanta,

"Husnah!Husnah!Husnah!!!..."

Masu karatu kuya hakuri mutsaya anan semun hadu a chapter 57

Dafatan dai labarin yakayatar daku,kudai kui min comment,kununamin reaction dinku,kui min sharing a group group naku.

Taku Hindatu Auwal

Se anjima..........

*ZAREN KADDARA*

*حبلاالقدر

®By Hindatu Auwal

*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*

*ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN*

FACE BOOK PAGE:@Hindatu Auwal Hausa Novels

WhatsApp

AREWA PEN:Hindatu Auwal

PHONE NUMBER:***

_____________________________________