CHAPTER [57
Dagudu Adam yaƙariso inda suke,betsaya tinanin komaiba yasureta dagajikin Omar dake durƙushe yariƙe Asma'u yana kuka,
Adam nashirin tada mota Omar yashigo idanunshi sunkaɗa sunyi jajir hawaye nacigabada bin kuncinshi.
Zuciyan Adam takarye yasan maza na kuka sedai bai taɓa ganin babban mutum kamanshi yana kukaba,baki yabuɗe daniyyan yinmai magana sekuma ye shiru don bayanzu bane lokacinda yadace.
Suna shiga asibitin aka amsheta,sukuma akadakatar dasu awaje,
ajikin ɗakin Adam yatsaya,shikam Omar yakasa samun matsaya sekaiwa yake yana komowa kuma har yanzu idanunshi zuban hawaye suke,
ga numfashin shi dayaketa faman sarƙewa,ganin yana niman sumemishi yasa Adam ƙarisawa inda yake ayanayin dayake baya buƙatan ace dashi komai abinda yakeji kaɗai ya isheshi.
Adam yazaunar dashi,yakalleshi cikin idanu yace.
"Ja numfashi!kaja numfashi"
Omar yabuɗe ƙofofin hancinshi,yashiga jan numfashi kaman yanda Adam yace yayi,jiyayi hu-hunshi yabuɗe,zuciyanshi tashiga amsawa aƙirjinshi,
Adam yazauna akusada shi yana riƙoshi jikinshi,kaman haka yakejira,sekawai yaruƙun ƙumeshi yana ƙara fashewa da matsanancin kuka.
Adam ye shiru,yana saurarenshi,tausayin mutumin dake gabanshi na kamamai zuciya.
"Yaya ina take,tana ina?"
Yaji muryan mardy na tambaya,sedaya fara raba jikinshi dana Omar,sannan yamiƙe yariƙo mardy da duk taruɗe,
ummah na tsaye itama tana kallonshi,duk da bata tambayeshiba yasan lafiyan Asma'u takesonji,dayike tun suna hanyan asibiti shida Asma'u.
Anas daya kawosu yajuya daniyyan tafiya,idanunshi suka sauka Omar dake zaune,hankali atashe yaƙariso inda yake,mamakin yanda akayi Omar yazo asibiti na sarƙafemai zuciya.
Shidai a'iya saninshi yasan abakin gate yabarshi,yashiga wurin ummah khadija yakaimata saƙonda Ramlat tabashi,
yanacikin gidan sanda ummah takira Adam tana tambayanshi suna ina,nan take yasanarmata suna hanyan zuwa asibiti,ganin yanda hankalinta yatashi yasanyashi karɓan mata driving ɗin,don ayanayin datake ciki idan har tai tuƙi tokomai ze'iya faruwa.
"Husnah!Yer Anas husnah nagani"
Yatsinci muryan Omar nafaɗi asanda yaƙarisa gabanshi.
"Wata husnah"?
Anas yatambaya kanshi na kullewa,
"yer....
Fitowan doctor daga ɗakin yasanya maganan nashi katsewa,atare suka nufeshi,doctor yakallesu atsanake,suduka expression iri ɗayane akan fuskokinsu,
"Meke damunta,meya sameta,wani condition take ciki?"
Atare suka watsomai maban bantan tambayoyin suna kafeshi da idanunsu.
Doctor ye murmushi yana jin-jina ƙaunan dake tsakaninsu,yanayin fuskokinsu kaɗai ya isa yanunamaka soyayyan dasukema juna megirmace,
"Kunga ku kwantarda hankalinku bawani abubane yasameta da alama tashiga shock ne shiyasa tasuma,
amma yanzu munbata taimakon dayakamata,har tasamu bacci,insha Allah tana tashi shikenan"
Atare suka sauke numfashi,Adam yace,
"zamu iya shiga muganta?"
"Eyy amma pls banda hayaniya"
Atare sukace,
"insha Allah bawanda zeyi magana"
Doctor ye murmushi yana kauda jikinshi daga bakin ƙofan yanda zasu samu daman shiga.
Akwance take,idanunta alumshe,kaman yanda yafaɗi bacci takeyi,sekuwwa yanimi wuri yatsaya,banda mardy data zauna abakin gadon tana kamo hannun Asma'u,
suduka idanunsu nakanta,basuko ƙiftawa,kaman ancemusu insun ɗauke idanunsu akanta ɓacewa zatayi.
BAYAN AWANNI 'UKU.
"Abba,Abbana!Abba....."
Tafaɗi daƙarfi tana yunƙurawa tazauna,idanunta abuɗe,dahanzari Omar da Mahmud suka ƙarisa wurinta,kowanne yariƙe hannunta ɗaya yana cewa.
"Sannu"
Kallonsu tayi,sekuma tafashe da kuka tana ƙanƙame hannayensu dake cikinnata.
"Husnah"
Omar yafaɗi muryanshi narawa,hawaye nabin fuskanshi,kallonshi tayi hawayenta naƙara gudu,
Itakanta tarasa yanayin datake ciki,tarasa metakeji azuciyanta,hatta abinda take gani kasa aminta tayi,sekawai tarungumeshi tana sake fashewa da kuka.
Suduka tsayawa sukayi suna kallonta,zuwa yanzu zuciyoyinsu sun basu amsan tamba yoyinsu,tambayo yinda suketama kansu akan meye matsayin Asma'u awurin waɗannan.
"Assalamu Alaikum"
Sallaman su mubeen yakaraɗe ɗakin,muryoyinsu ba amo suka amsasu,ƙarisa shigowa sukayi,
Adam yajefi mubeen dawani irin kallo,dasauri yarausaya kai tareda haɗe hannayenshi alaman ban haƙuri,
Saboda lokacinda Adam yasanar mishi suna asibiti Asma'u ba lafiya,yagayamai kada suzo,amma yakasa haƙuri,salin 'alin yaso yafito tunda ayanzu ya'iya driving amma mubeena tace seta bishi,bayada yanda zeyi hakanan yakwasosu suka taho.
"Abba"
Asma'u tafaɗi tana ɗago idanunta takalli fuskan Omar daye sharkaph da hawaye,lallausan murmushi tasaki,sabbin ƙwalla suka ciko idanunta,tasa hannu tashiga sharemai hawayen fuskanshi,haɗida girgizamai kai alaman yadaina kuka.batasan lokacinda Nadr yaƙariso bakin gadonba,se muryanshi dataji yanacewa.
"Aunty kidaina kuka"
Atare suka kalleshi,tukun Omar yalalubo muryanshi daga inda yaɓuya yace,
"Wayeshi"
"Ƴan biyun Noury"
Tafaɗi tana kama hannun Nadr tasaka acikin na Omar,kallon yaron yayi naɗan wani lokaci,tukun yazame jikinshi daga kan gadon yahaɗe Nadr da Nadra yarungume aƙirjinshi,hawaye nacigabada bin kuncinshi.
Mardyce tai ƙarfin halin tambayan Asma'u,
"Wayeshi?"
"Mahaifina"
Ta'amsashi hawayen farinciki naƙara silalomata,adai dai kuma lokacin Omar yamiƙe,takalleshi tace.
"Abba ga ummah ta,ga Abba na,dukanan family ɗinane"
Baki yabuɗe zeyi magana doctor yashigo,seye shiru,doctor yatsaya agaban Asma'u yana cewa.
"Ashekinfarka,ya jikinnaki"
"Da sauƙi"
Ta'amsashi tana ƙoƙarin tsaida hawayenta,
"Ba'inda yake miki ciwo"
"Eyy"
Tabashi amsa tana ƙoƙarin ɗora murmushi afuskanta,nantake yabasu takaddan sallama,tareda ƴan wasu magunguna.
*NO 2 MALAM ISMAIL ROAD,FULANI LOCAL GOVERNMENT*
Zaune suke 'a falon Baba Alhaji,ba abinda kakeji se sheshsheƙan kukan wasu,wasu na addu'a,wasu naƙara jinjina ƙoƙari da riƙon amanan Mahmud tareda nagartacciyan matanshi data tayashi riƙon marayu,don ba'abinda Asma'u taɓoye musu agameda labarin yanda suka riƙesu,
Bayyana irin farincikin da suke ciki baze misaltuba sedai kawai 'ai shiru,
adaren su Mahmud sukaso tafiya amma su daddy suka hanasu tafiya,adole suka haƙura,sashi guda aka basu,iyalan gidan nadabai bayedasu.
Adaren Asma'u kasa bacci tayi,data rufe idanunta hotunan abubbuwanda suka faru take gani suna gilma mata tacikin ƙwayannin idanunta,har yanzu wani sashi na zuciyanta yakasa gazgata abinda yafaru,
wai yau itace acikin ƴan uwanta,dazata kirada danginta,ga nagartaccen mahaifinta data ɗauka tarasashi tattareda zaren kaddaran data sauya akalan rayuwanta,
murmushi tasaki,tukun tafara dariya kaman wacce tazauce,can kuma seta miƙe tai sujjada tashiga godiya ga ubangiji hawaye nabin fuskanta,
Ganin takasa bacci yasanyata miƙewa ta fito daga ɓangarenda akabasu,tai tsaye 'a compound ɗin gidan tana kallon kyau da tsaruwa na gidan,sakamakon akwai hasken glops na solar dana taurari.
Hannu taga ana ɗagomata daga garden ɗin da ke gaban plate ɗinsu,
tundaga inda take tahango fuskan Omar dake murmushi,yana sanye cikin wata brown ɗin jallabiya,itama ta-ta fuskan nawashewa da murmushi ta-taka zuwa garden ɗin.
"Meyafaru?"
Omar yatambaya asanda Asma'u kezama akujeranda ke hannun damanshi.
"Bakomai kawai nakasa baccine"
"Gani nakeyi kaman bada gaskeba,kaman mafarki nakeyi,akoda yaushe zan'iya farkawa inga bada gaske bane,inga rayuwata tanan ayanda take,ƙuncin danake ciki yakuma bai-bayeni....
"No!Abba dagaskene,duk abinda yafaru azahiri yafaru,muɗinne muka sake haɗuwa,kuma bazamu sake rabuwaba insha Allah."
Asma'u tafaɗi tana ƙoƙarin ƙwarara Omar,tawani fannin kuma zuciyanta take tabbatar mawa dagaskene abinda yafaru a'unin yau,don ba'iya Omar ne keganin komai amatsayin imagination ko mafarkiba.
Masu karatu kuya hakuri mutsaya anan semun hadu a chapter 58
Dafatan dai labarin yakayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui min comment,kununa min reaction dinku,kui min sharing a group group naku.
Taku Hindatu Auwal
Se anjima.......
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
®By Hindatu Auwal
*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*
*ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN*
FACE BOOK PAGE:@Hindatu Auwal Hausa Novels
AREWA PEN:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
_____________________________________