MARTANI BY RUKAYYA YUSUF IBRAHIM (A. Y. M Creatives)
Martani Episode 09
MARTANI
A Story of Retribution
Rukayya Yusuf Ibrahim
Arewapen @aymcreatives
GMJ|26|049
Episode 9
Daki ta shige da gudu tana cewa" haka kawai ni da abokina to ina ruwanka".
Ya bita da gudu amma kafin ya isa ta datse kofar.
Yayi ƙwafa yana barin gidan don dama asibiti za shi, ya zo ne yayi mata warning.
Bismillah...
Wasa-wasa A'isha taki daina kula Samir. Shi kuma Ashraf ya kasa ya tsare.
Yanzu ya zamana kullum sai sunyi faɗa, tun suna su kaɗai har su Yaya Rumana sun gane.
Domin wata rana da ya tarfa ta da gudu tayo bangaran su tana kuka zai dake ta.
Yaya Rumana ta same shi tana masa faɗa yayi shiru yana cewa" haba don Allah Yaya kin san me take yi kuwa? Wai a abokanta har da maza kuma nayi mata Magana wai abokinta ne kuma karya take soyayya suke ".
A'isha ta ce" abokina ne, karatu duk muke yi da su bani kaɗai ce kuma".
Murmushi Yaya tayi ta ce" to kai da kace ba ka sonta ina ruwanka ma in ma soyayyar suke?".
Ya zaro ido ya ce" da auran nawa Yaya?".
Murmushi tayi ta ce" shikenan " nan ta yiwa A'isha faɗa ta rakata gidan.
Amma duk da hakan bai sa sun daina ba, domin A'ishatu taki ta daina kula Samir domin ko tayi niyyar rabuwa da shi bata san ta ina zata fara ba.
Shi kuma a ganinsa raina masa hankali take kawai.
Yau ma kamar kullum sun shiga school, ana jiran Malam ya shigo Samir ya ƙaraso inda take yana nuna mata wani lissafi da bai gane ba, ita kuma ta dage tana koya masa.
Sir Kamal ne ya shigo shi da Ashraf domin sanar da dalibai wani taro da wani kamfani za suyi .
Yana shigowa idonsa ya sauka a kanta, cikin ƙanƙanin lokaci ya tsaya gaban su ya na kalolinsu.
A'ishatu ta waro ido tana kallonsa ta kalli Samir ta ce" Samir koma sit din ka ai ka gane ko" .
Bai samu damar yi mata magana ba ya tattara komatsansa ya bar gurin.
Sai a san nan Ashraf ya koma kusa da Kamal kowa na mamakin irin kallon da yakewa A'isha da Samir.
Hatta Sir Kamal sai da ya kalle shi, ya basar har suka gama abinda zasu yi suka fita.
Nabila ta ce" jikina yana bani kin yiwa Malamin nan rashin kunya A'isha. Dan Allah me kikai masa?".
Bata rai tayi ta ce" me kuwa zan masa ? Ni ko magana ban taɓa yi masa a makarantar nan ba".
Barin zancan sukai suka kama hanyar cafeteria don anjima wata laccar ce zasu shiga ta Sir Ashraf.
Samir ne bayan duk sun zauna ya ce" wai me mukayiwa mutumin nan A'isha ko incr kikaiyi masa?".
Cike da tsiwa ta ce" au ni kake tambaya ma , to ban sani ba".
Fatima ta ce" nifa ba wannan ne yake damuna ba, wai ba ku lura yanzu in ya shigo lacca haɗe rai yake ba kuma Allah ni gani nake Samir kamar kai ne kayi masa laifin".
"A'a Fatima me zan masa ni, wallahi ba ruwana".
Summayya ta ce" kuma wai ba ku lura yanzu kullum sai ya zage makarantar nan ko ni kaɗai naga haka?".
"Eh mana yayi ta tsurawa mutane ido kamar me neman wani abu" cewar A'isha tana yatsine fuska.
Ammar ya ce" kuma fa kamar ƴan team din nan ya sa mana ido kun tuna ranar Friday yadda ya kafe Samir da Sadiq da ido.
Anya ba wani abun ke faruwa ba wasu sukai mana shiru".
Fatimah ta ce" Allah ni Samir nake zargi domin ko ranar da muka makara naga ya daka ma tsawa".
Samir ya ce" Allah ni babu abinda nayi masa , in kuma laifin nayi to ban san nayi ba".
Za su sake magana Juwaira ta ce" ga shi can dan halak shi da Sir Kamal".
Shiru sukayi domin yanzu suna fara tsarguwa da wannan sabon salon nasa.
Haka wasu ma dake gefe suke tattauna domin kowa ya fahimci kusan kullum sai yazo yayi shawagi a gurin ya koma office.
Kamal ne ya dubi Ashraf ya ce" dazu wai me yaran nan sukai ma naga ka nufe su a fusace?".
Murmushi yayi ya ce" namijin ne yayi min laifi, shine na ganshi a class din . Amma zan kama shi".
Murmushi Sir Kamal yayi ya ce" ai nayi tunanin ƴar budurwar ce , amma tunda shi ne kuje can ku ƙarata".
Ashraf ya ce" kasan budurwa ne ?".
"A'a ban santa ba, kwanan nan na fara ganinta ma . Amma fa gaskiya bazan boye ma yarinyar ta shiga raina. Jira nake na samun babbar kawarta mara surutu tayi min jagora ".
Kafin Ashraf ya yi magana suka ji ihun ƴan makarantar.
Nan take suka kai maganan su zuwa gurin, kare ne ya a shigo yana bin su duk inda sukayi shine suke ihun.
Hangota yayi cikin waddanda suke gudun .
Sir Kamal ya ce"me yasa suke gudu ai dole ya bisu " .
A'isha tayi tun-tuɓe karan yayo kanta , cikin ta shin hankali ta ƙwalla kara ta fadi a sume.
Sir Kamal kawai bude ido yayi ya hango Ashraf da karan a hannunsa ya buga shi da ƙasa ya kuma daga shi ya buga da ƙasa yana hucci har sai da kan karan ya fashe ya yarda shi a mace.
Ya dubi A'isha yadda ta fadi ya tsaya yana kallonta yama rasa me zaiyi.
Sir Kamal ne yazo da ruwa ya ce" ga ruwa watsa mata firgita tayi ".
Nabila da Summayya ne suka tallafo ta aka shafa mata ruwan , nan da nan ta fara numfashi sama-sama me haɗe da kuka tana koƙarin miƙewa ta gudu.
Riketa suke amma koƙarin kwacewa take musamman da ta hango karan a kusa da ita yana zubar da jini.
Miƙewa yayi ya kalli su Nabila ya ce " ku cikata" suka kalle shi da mamaki.
Summayya ta ce" bata cikin hayacina Sir ta firgita sosai ne daman ko ganin kare bata son yi ita".
Bai bi ta kanta ba ya mayar kansa ga A'isha da ta damke idonta tana fusge-fusge ya ce" A'isha!! " Da dan ƙarfi yana kallonta.
Ta buɗe idonta a hankali akansa tana cewa" don Allah ka ya hakuri bazan ƙara ba".
Sa hannunsa yayi a baki alamar tayi shiru ya nuna mata karan ya ce" ki nutsu ya mutu, ki ta shi daga nan zaki bata kayanki ". Yayi maganar yana miƙewa .
A hankali ta ta shi tana duban gurin tana ajiyar zuciya.
Kowa na mamakin yadda akai ma Sir Ashraf ya iya daukar karan ya kaishi har lahira.
Sir Ashraf ya kalli Kamal ya ce" muje ko" ya bar gurin zuciyarsa na bugawa har lokacin, domin ya shiga tashin hankaline lokacin da idonsa ya gano masa faduwarta.
Bin bayan su tayi da kallo ta dubi Nabila ta ce" ya akai karan ya mutu ne?".
Summayya tayi saurin cewa" Sir Ashraf din da kullum ki ka tsana shine ya ceceki yarinya. Ba kiga yadda ya dinga buga shi da ƙasa ba har ya mutu".
Shiru A'isha tayi domin jikinta duk ya mutu.
Zuciyarta kawai ce mata take " Sir Ashraf fa? To me yasa ya kashe karan ? Saboda ni".
Nabila ce ta dafata tana cewa" zo muje class".
____
Ashraf tunda suka je office Sir Kamal ya fara masa tambayoyi akan A'isha ko ya santa ne .
Shi dai ko uffan baice masa ba, karshe ma cewa yayi kansa ciwo yake din yayi hakuri yayi masa shiru.
___
A'isha tana komawa gida zazzaɓi ya rufeta domin ta firgita sosai.
Yaya Rumana ce ta shigo ganin ko ta dawo don bata leko ta ce musu ta dawo ba.
A falo ta tarar da ita ta kudundune sai karkarwa take.
Cikin sauri ta fita kiran Ashraf a waya , suka dawo ita da Zeenah suka taimaka gurin cire mata hijabin jikinta.
Ko da yazo cewa yayi su tafi zai mata allura zazzaɓi ne ba wani abun ba.
Tana jin ya ce allura ta miƙe da karfin hali tana cewa" na warke ma fa, ina samun bacci zan ware".
Zeenah tayi murmushi ta ce" to zo muje kiyi wanka sai ki kwanta".
Ta kama hannunta suka shige dakinta ta haɗa mata ruwa mai ɗan dumi ta rakata har toilet din san nan ta fito.
Yaya Rumana ta ce" Allah Sarki daga gani bata son allura, ta shiga wankan?".
"Eh ta shiga" Zeenah ta bata amsa a garje ce.
Kallonsu yayi ya ce " yanzu za a kira magrib kuje kawai , zan mata allura zata ji sauki in nayi mata allura".
Suka fita suna cewa " to Allah ya ƙara lafiya".
A'ishatu kuwa ko da ta fito, dakyar ta zura kayan bacci riga da wando ta kwanta sai bacci.
Bayan sallar Ishaqi ya dawo gidan rike da yogurt da kaza sai kuma magunguna da allurar da zayi mata.
Ya jima a falon ganin bata fito ba yasa yayi ta maza ya tura kofar dakin.
Sa-sanyan kamshin ɗakin ya daki hancisa ya lumshe idonsa ya sauke su akan A'isha da take bacci tsakani ga Allah.
Murmushi yayi da ya tuna maganarta dazu" don Allah kayi hakuri baza ƙara ba". Ya fita ya dauki yogurt din da ya shigo da shi ya kawo mata mata da kazar ya ja mata kofar.
____
Kwananta biyu ta murmure bayan ta sha allura da dole ya tsaya yayi mata.
Daga nan rikincin su ya dora daga inda ya tsaya akan batun kula Samir.
Ga kuma Sir Kamal da yasa mu Juwaira ya ce tayi masa hanyar samun number A'isha.
Bata bawa Sir Kamal fuska ba , don acewarta ko single take bai yi mata ba kwata-kwata ba.
Babu yadda Juwaira bata yi mata ba amma ta ce" ita fa tana da Samir".
Juwaira ba tayi kasa a gwiwa ba taje ta fadawa Sir Kamal.
Suna office su uku ya shigo kamar an jeho shi yana tsaki.
Malam Abba ya dube shi ya ce" Kamal lafiya kuwa?".
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Allah wata yarinya nake so , amma sam taki bani hadin kai wai dan class din su take so" .
Ashraf ya juyo ya ce" kai dadina da kai shirme ai yanzu sai ka hakura ko".
"Haba Ashraf bazan iya ba , ina matuƙar son A'isha kuma dole ne wannan yaron ya rabu da ita".
Cikin mamaki ya ce" wacece A'isha?" .
Kamal ya ce" wannan wacca na faɗa ma din, wacca ka kashe karan nan da zai cijeta".
Mikewa yayi da sauri yana fadin ka ce" ta ce dan ajinsu kuma take so?".
Girgiza kai yayi ya ce" eh haka ƙawarta ta ce min".
Wayoyinsa ya dauka ya fice ya dubi Kamal ya ce " zo muje ka raka ni".
Sir Kamal da sauran Malaman suka bishi da ido amma babu wanda ya ce uffan.
Sir Kamal ya biyo shi jiki a sabule yana cewa" ina zan raka ka?".
Ya juyo ya ce "gurin ita yarinyar ".
Kafin Kamal ya ce wani abun Ashraf ya hango su , tana kusa da Samir suna hira.
Kamal ya ce" wan can yaron take so wai".
Da sassarfa yayi gurin kamar zai yi gudu , kawai sai ganinsa sukai a gabansu.
Samir ya mike ganin irin kallon da Ashraf ke masa .
Danƙo wiyansa Ashraf yayi ya zaunar da shi , shima ya zauna ya ce" me nene hadin ka da wannan yarinyar?" Yana nuna masa Nabila.
Samir ya ce" Sir Class mate ce kawai " ya dawo da hannunsa kan Fatima ya ce" ita kuma wannan fa?" .
"Sir ita ma haka".
Hannunsa ya juya ya ce" wannan da wannan fa?". Ya nuna masa Summayya da Juwaira .
"Dukansu Sir abokan karatu na ne".
Ashraf ya kalli A'isha da ta sunkuyar da kanta ya na kallon Samir ya ce" har wannan ma Abokiyar karatunka ce?".
Samir yayi saurin daga kansa ya ce" eh ".
Sir Kamal ya kalli Samir " da gaske kake wannan ba budurwaka ba ce ?".
Samir ya ce" eh sir ".
Juwaira ta ce" kai! budurwarsa ce fa".
Nabila ta ce" Sir wai me ya faru ne , me Samir ko A'isha suka yi?".
Ashraf da idonsa yayi ja ya ce" da gaske soyayya kuke da wannan yaron A'isha".
Ta dago a hankali ta girgiza kanta ba tare da ta iya cewa komai ba .
Ya mike tsaye yana daka mata tsawa " magana zaki yi min ba girgiza kai ba".
Nabila ta ce" don Allah Sir kayi hakuri in wani abun aka ce ma A'isha tayi, ita ba ta soyayya ma don da auranta aka ".
Ba Ashraf ba hatta ƙawayanta sai da suka kalli Nabila cike da mamakin furicinta.
Ashraf wata boyayyar ajiyar zuciya yayi don ko ba komai yanzu hankalinsa ya dan kwanta.
Kamal ya ce" aure kuma?".
A'isha ta dakawa Nabila harara ta ce" sir don Allah in laifi nayi kuyi hakuri kar mutane su dauka wani abun ne".
Ashraf ne ya kalli yadda aka fara taruwa ya ce" ki same ni a office yanzu" yaja hannun Kamal su ka bar gurin.
Suna barin gurin ta kalli Nabila cike da takaici ta ce" me kika yi haka don Allah?".
Samir ya ce" da gaske kina da aure ko kawai faɗa Nabila tayi?".
_______
Dubansa tayi kafin ta ce " ka tambayeta mana, tunda waƙa a bakin mai ita ai tafi dadi".
Nabila tayi saurin cewa" in banyi hakan ba ya kike so nayi. Kin san me zai yi miki ne A'isha?".
Ajiyar zuciya ta saki ta kalli Juwaira ta ce" duk ke ce kika haɗa wannan masifar, da na ce bana son Sir Kamal ina ruwanki da cewa muna soyayya da Samir?".
Summayya ta ce" ba ta da wani da lafi Malama, karya tayi ba soyayyar kuke ba".
Samir ne ya ce" maganar gaskiya mu ba soyayya muke ba, kawai mun tafi da ku a fahimtar ku ne, kuma daga yau Ni ba ruwana da lamarinki A'isha.
Saboda ni iyayyana ba masu karfi ba ne, kije karbi soyayyar Sir Kamal kunfi da cewa, don a yadda na ga ransu ya baci nan musamman Sir Ashraf sai ka ce shine ma yake son naki , gaba daya duk ya hakikance".
"Tab! Ai sir Ashraf ba zai taba son A'isha ba wallahi duk matan makarantar nan, kawai dai yana yi ne saboda abokinsa" cewar Summayya.
Zama A'isha tayi ta dafa kanta ta ce" yanzu Samir akan wannan maganar zaka fara wannan dogon sentence din nan?"
"Haba A'isha wannan fa maganar gaskiya ce, ni ba kowan kowa ba naja da masu iko".
Shiru tayi tasa hannu bibbiyu ya tallafa kumatinta, Nabila ta dubeta ta ce"ya ce kije office din sa ki same shi fa ".
A fusace ta dago kanta tana duban Nabila ta ce" bazanje ba! Na ce bazanje ba kizo ki kai ni".
Juwaira ta ce" a'a fa dole kije domin baza ki ja mana jarfa ba muna zaman-zamanmu".
" Wallahi bazanje ba , daman ai duk abinda ya faru ke kika ƙula munafuka kawai".
Ammar ya ce" a'a Aisha mahaukaciyar ina ce ne? Malamin ki ne fa. Dole fa kije kiran nan da yayi miki, kuma Juwaira gaskiya ta faɗa tunda duk nan soyayya muka san kuna yi da shi Samir din.
Don haka ki ta shi sayunki a likafa kije ki same su, domin soyayyar Sir Kamal sai tafi miki ma akan ta waninsa ".
Bai rufe baki ba ta mike tana cewa" in kun isa kuja ni kuka kai ni, kuma bani nake hauka ba sai dai in ku.
Wai me yake damunku ne , soyayya ana yinta ne dole, rayuwata ce don haka bana son abokinsa kuma bana kaunarsa don haka banga dalilin zuwa na gurinsu ba, in kuna ganin kun isa kuja ni ta karfin tsiya " ta yi hanyar barin gurin foo!! Kamar zai ta tashi sama.
Sadiq da Fatima suka tare mata hanya suna cewa" Allah A'isha akan ki ja mana matsala gwara muyi miki kama-kama mu kaki".
Cike da kosawa da murmushin kun raina min hankali ta ce" ku dauke ni to , don Allah ku gwada".
Sumayya ce ta yi kanta zata sunkuceta da yake babu dalibai a gurin sosai wasu duk sun shiga lacca yasa cikin ƙarfin hali ta maketa ta fadi a gurin.
Samir ya ce" kunga kuzo muje mu fadawa Sir Ashraf, shikenan kunga sai mu fita can ta karata , ita ta ɗaukowa kanta matsala".
Nabila ta ce" a'a baza ayi haka ba zata je don Allah kuyi hakuri ".
"Don Allah karku hakura , ka ji masifa ? Daman wai da irin mutanan da nake zaune kenan. Marasa lissafi? Akan wannan dalilin zaku kai ni gurinsa ko tilasta min . To bari kuji duk ɗan da acikinku baije ya faɗa masa cewa na ki zuwa ba shi ba dan halak ba ne" tayi gaba abunta.
Nabila na ƙwalla mata kira amma inaaa....tayi gaba domin zuciyarta har wani tafarfasa take , tsabar ƙuna.
Summayya da Samir ne sukai gaba su Ammar suna binsu a baya domin zuwa office din su sa Ashraf.
Nabila ta ce" wai ku menene haka ne, yanzu ku sai kuje ku fadawa Sir Ashraf taƙi zuwa?".
Juwaira ta kyalleta ta ce" mu ai ba tsoranta muke ji kamar ke ba, in ke zaki tsaya taja miki matsala fine, amma mu dole sai mun nuna mata ƴaƴan Sunnah ne gaba da baya".
Binsu tayi tana cewa" muje inji abinda zaku faɗa, gaskiyar A'isha da ta ce bata son haka kuke ba, ai wallahi zaman tare yafi karfin haka.
Saboda san zuciya irin naku, gwara ku ƙara jefata a matsala ko?".
Samir ne ya ce" ai duk mutumin da yake da confidence irin na A'isha yana da Uwa a gindin murhu ne. Mu kuma bamu da kowa sai Allah dole ne mu fitar da kan mu".
Shigar su office din ce ta sa Nabila ta yi shiru ba don ranta yaso ba.
Sallama sukai Ashraf da Jamil da Kamal da suka tisa shi da tambayoyi duk suka dago suna kallonsu.
Samir ya yi ƙarfin halin cewa" daman munzo akan A'isha ne, ta ce bazata zo kiran da kai mata ba.
To mu sam ba ruwanmu, kuma ni wallahi ba soyayya nake da ita ba.
To don karta ja mana masifa shi yasa muka zo mu wanke kanmu".
Sumayya ta ɗora da cewa" kuma Sir ta ce indai mu ƴan halak ne muzu mu faɗa muku, daman ita ba tsoron kowa take ba, don Allah mu ba ruwan mu".
Nabila ta ce" amma anyi mutanan kawai , don kawai ku kare kan ku,shi ne ko kazo kuna mata sharri. Ai inda wanda baya tsoron kowa bai wuce ke ba Summayya.
Yanzu kuma anyi walƙiya A'isha zata san irin zaman da zata yi da ku".
Ta juya ta kalli Sir Kamal ta ce" kai kuma Sir wallahi abunda kuka baku kyauta ba.
Ita soyayya ba dole ba ce don ta ce kawai bata son ka sai ka dauko mata Sir Ashraf yazo kamar zai dake ta.
A'isha ba ta da laifin don ta ce baza tazo ba, domin ba akan ilimin da tazo nema ba ne kuke nemanta akan son zuciyarku ne". Ta juya ta bar gurin idonta yayi ja.
Ashraf ne ya mike da mamaki akan fuskarsa yana cewa" Kamal kaga abinda ka jawo mana ko . Kamar wannan yarinya tazo tana faɗa mana magana, bari naje naga uban da ya tsaya mata ". Ya bita foo!! Kamar ya tashi sama shima .
Sir Jamil da Kamal suka biyo shi, suna yi masa magana, inda su Samir suka maro musu baya.
Nabila tana fita wani class ta shiga inda tasan Aisha ba zata wuce nan ba.
Kuma dai dai shigar ta Ashraf ya hangota .
Bata san sun biyota ba tana shiga taji kukan Aisha ta nufi inda take tana cewa " A'ishatu kiyi hakuri don Allah, na fahimci abunda sukai miki kuma na rama miki , ki daina kuka Please ".
"Ni ki ƙyalle ni, ba hadda ke ba, wai ni suke cewa mahaukaciya, ba gara abunda Sir Ashraf yayi min ba ma . Daman wai haka ake zaman abotar yake? In dai masifa ta shafi daya kowa sai ya goce ba ruwansa?".
Nabila ta ɗagota da ƙarfi ta na cewa" kinga ki nutsu mana, sunje sun fadawa Sir Ashraf da su Sir Kamal ba za ki zo ba.
King muje don Allah kar ace baki da kunya don abinda Summayya ma ta ce kenan wai ba kya tsoron kowa , amma na fadawa su Sir din gaskiy".
"Ke! Ke! " Muryar Sir Ashraf ta karade hall din sakamako babu mutane da yawa yasa har amsawa hall din yayi.
Nabila ce ta dago tana dubansa tana riƙe da A'isha da kuka duk yayi mata caɓa-caba.
Ya kalli Nabila ya ce" waye sa'anki a cikin mu da zaki zo ki fadi magana son ranki?".
Su Summayya da sauran team din ,su ka zuba musu ido Juwaira harda murmushin mugunta.
Yayinda Sir Kamal ke cewa " Dr. Live her please ba girman mu ba ne".
Nabila cikin tsoro ta fara cewa" ni kuyi hakuri don Allah, banyi haka don nuna rashin kunya ba ko wani abun ba".
Juyawa yayi ga A'isha da take ta tafka musu harara ya ce" ke kuma daman ance bakya tsoron kowa ko ? Har na kira ki amma ki ki zuwa".
Cike da tsiwa ta ce" munafukan sunje sun fada ma kenan" .
Ta juya tana kallon su Samir ta ce" ga shi a gabansa na nace bazanje ba kusa ya ka she ni, na ce kusa ya kashe ni".
Sir Kamal ne ya ce" ke daman da gaske baki da kunya wai ? A gaban mu kike wannan ɗaga muryar?".
Cikin ido ta kalle shi tayi murmushi kana ta ce " au kai ma bani da kunyar zaka ce . Me nene laifina don na kare kaina? Don kawai ka ce kana sona na ce bana yi ina da wanda nake so sai ya zama laifi, har ka ɗako min mutum kamar zai dake ni. Rayuwata ce fa ba takarda handout din ku ba.
Ina da ƴanci na nayi abinda nake so da rayuwata , kuma duk cikinku ba abinda ya shafeku ba ne, to Allah indai abunda nayi rashin kunya ne banyi nadamar yinsa ba , kuma a shirye nake na sake wan..".
Saukan mari hagu da dama ne ya katse mata maganarta.