Page 7
by @zeeykumurya
*BARA A KUFAI*
*Zeey Kumurya*
7.
BRIGHT PENS 2026
YOTA ID 003
Bismillahir rahmanir rahim
Da sauri Sauri ta kalli abincin da ya baje a ƙafar mutumin da ba ta ko kalli fuskarsa ba cikin faɗuwar gaba, lokaci ɗaya ɗakin ya yi tsit duk aka juyo ana kallon su. Girgiza kai ta shiga yi idanunta akan abincin, ta rasa ma me za ta yi, ga miyar sai turiri take tsoronta ɗaya kar ta ƙona shi.
"Ka yi haƙuri don Allah, hayaƙin nan ne ya rikita ni har ido ya shigar mini na daina gani sosai."
Ta faɗa a ruɗe tana ƙoƙarin saka ƙasan rigarta ta goge masa miyar. Bai ce komai ba ya janye ƙafarsa tare da raɓawa ta kusa da ita zai fita, a hanzarce ta matsa gefe don ba shi hanya, saboda idan ya ce zai wuce a haka dole sai ya gogi jikinka. Ba ta kalli kowa ba duk da tana jin tashin salatin wasu, ƙoƙarin gyara wurin ta yi ta kwashe abin da ya kwasu ta koma ta sake zubo musu wani abincin, sai da ta yi sahu uku saboda suna da yawa, sannan ta kai musu ruwa ta ɗauko tsumma ta goge gurin da ya ɓaci tas, har lokacin ba ta ga wanda suka yi karo ba bare ta san waye, sai da ta sauya kaya ita ma saboda na jikinta duk ya ɓaci.
******* ******
Wani irin gumi ne yake tsatstsafowa daga goshin Juraij, jikinsa ya dinga wata irin tsuma, lokaci ɗaya idonsa ya kaɗa ya yi ja. Ramlah dai tana zaune kamar wadda aka kafa tana kallon shi, har ya miƙe a fusace ya mayar da kayan da ya cire ya ɗauki wayarsa ya yi hanyar fita.
"Wa yake ɗaga maka hankali haka ne? Haka ma da safe fa aka yi? Shikenan ni yanzu ba ni da lokacinka kenan? Da ka dawo gida sai su ɗaga maka hankali, kuma a haka za ka tafi ka bar ni ba za ka taɓa faɗa mini ko mene ne ba, lokacin sallah ya kusa, ba ka ci abinci ba, kai mutum ne da ba ka fita ba tare da ka sake wanka ba, ba ka maimaita kaya idan ka cire a lokacin, amma yau duk ka yi, me yake faruwa ne? Ka sanar da ni ko zan samu nutsuwa don Allah Man."
Ta yi maganar cikin muryar kuka da kissa.
Tsayawa ya yi yana mayar da numfashi na sakanni sannan ya ce. "Abin da ya shafi aikina ne shi ya sa bana faɗa miki."
"Duk da haka ya kamata na san inda za ka je saboda tsaro, ba mu san me anjima za ta haifar ba, a matsayina na matarka ya kamata na san duk inda za ka je ko da ba nisa zaka yi ba, ko da kuwa ya shafi aikinka ne tunda na san ba office za ka koma ba."
"Ba mu da time a yanzu, idan na dawo za mu yi magana."
"Ka tabbata ba wata matsala ko hatsari a wannan fitar?"
"In sha Allah."
Za ta kuma magana wayarsa ta yi ƙara, ya ɗaga tare da karawa a kunne.
"Na gani yanzun nan Sir, gani nan ma na fito zan je gurin."
Ya yi shiru na sakanni sannan ya ce. "Ok tom shikenan, zan zo mu haɗu." Daga haka ya fice daga ɗakin cikin sassarfa.
Ramlah ta raka shi da wani irin kallo.
Har ya ƙarasa inda za su haɗu da su DD videon da ya gani ne kawai yake yi masa gizo a ido, hakan ne yake ƙara rura wutar da take ci a ƙirjinsa, tsabar tunzura ko magana ba ya iya yi, yana jin su Kamal suna tattauna al'amarin amma ko kanzur bai ce ba.
Sai da suka tsaya suka yi sallar Magriba da ta riske su a hanya sannan suka ci gaba da tafiya. Wata makarantar kwana ta maza da ke baya-bayan gari suka je, tun kafin driver ya gama parking ya buɗe motar ya fita, yana jin DD Sardauna yana ce masa ya bi komai a sannu amma bai ko tsaya ba.
A tsaye cirko-cirko ya samu Principal da wasu teachers da saurin ma'aikatan makarantar cikin tashin hankali, kallo ɗaya ya yi musu ya mayar kan gawarwakin matasan da suke zube cikin jini a bakin hostels, a lokacin su Kamal suka ƙaraso, sai jiniyar motar police ta biyo bayansu. Cikin lokaci ƙanƙani aka fara bincike da duk abin da ya dace, gabaɗaya yaran su 41 an ƙwaƙule musu idanu, ban da surutai babu abin da Principal ɗin yake kamar wani zararre, yana nanata furucin bai san me zai ce wa iyayen yaran nan ba.
Bayan Jami'an tsaro sun gama duk abin da za su yi Juraij ya dubi shugaban police ɗin a kufule ya ce. "Yanzu har aka yi abin nan aka gama amma sai yanzu za ku zo? Mu da muke cikin gari ma mun riga ku zuwa?"
"Motar da za mu taho da ita ne sai da aka je aka ɗauko, an fita da wata, wadda take ajiye kuma ta samu matsala dole sai da muka jira."
Tsabar takaici ji Juraij ya yi kamar ya kikkife shi da mari, mene ne amfanin zuwan nasu to a yanzu? Zai kuma magana DD Sardauna ya dakatar da shi da faɗin. "Me aukuwa ta riga ta afku Juraij, abin da ke gabanmu kawai shi ya kamata mu fi mayar da hankali mu yi a yanzu."
Zuciyarsa kamar ana tashin bamabamai haka ya tsugunna ya zuba wa gawar yaran idanu, ya iyayensu da ahalinsu za su ji? Ya mutanen gari za su ji wannan tashin hankalin? An tura yara ɗaukar ilimi amma a zo a yi musu wannan kisan gillar? Har aka kashe su aka ƙwaƙule musu ido babu wanda ya kawo musu ɗauki? Su waye wannan mutanen da suka zo suka aikata wannan ta'asar? Laifin waye? Nasu jami'an tsaron ƙasa bakiɗaya ko na gwamnati? Su waye suka gaza a cikinsu?
Kamar amsar tambayoyinsa sai ya ga wannan sign ɗin a jikin yara guda biyu da yake gaban gawarsu, wannan alamar da ya fahimci kamar shi kaɗai yake ganin ta, don bai taɓa jin wani ya yi magana a kanta ba, shi ma bai taɓa faɗa wa kowa ba bayan Malam. Wani irin curewa ya ji zuciyarsa ta yi masa a ƙirjinsa, ya ji kamar numfashinsa zai ɗauke. A lokacin ne wakilan sojojin yankin suka zo, ƴan jarida ma suka fara zuwa, amma aka hana su shiga da ɗaukar rahoton komai, har aka kwashe yaran aka gama duk abin da ya dace bin su kawai yake da ido, tunaninsa ya riga ya yi nisa akan kudirinsa, burinsa na ganin ya daƙile ko su waye suke wannan wadaƙar rayukan al'ummar gami da cin karensu babu babbaka.
Suna hanya aka saki labarin mutuwar Sheikh Adnan, kwana ɗaya da wuni sai a lokacin suka so bayyanawa bayan sun gama haɗa ƙaryar da za su sanar wa duniya, tsaki ya ja da ya janyo hankulan duk wanda suke cikin motar, ransa bai kuma ɓaci ba sai ya ga an fitar da sanarwar aika-aikar da aka yi a makarantar da suka je an sanar da cewar yara sha biyu ne, a fusace ya nuna wa DD yana faɗin. "Me ya sa gidan jaridar nan za su sanar da labarin da ba su da sahihancinsa?"
"Haka abin yake Juraij."
Tsabar tunzura bai san lokacin da ya ɗaga wa DD Sardauna murya ya ce. "A yaushe aka yi haka." Ba.
Bubbuga kafaɗarsa DD ya yi ya ce. "Take it easy AD Juraij, ba a son ana tayarwa da al'umma hankali ne, idan aka ce yara 41 ne wani ma sai zuciyarsa ta buga musamman tsofaffi, shi ya sa ake faɗar abin da zuciyar kowa za ta iya ɗauka, ba a taɓa fita ɗauko irin wannan rahoton da kai ba ne, that's why hidden ya zama baƙon a wajenka, ka saba komai sai dai ka tura Field officers."
Da wani irin kallo kawai ya bi shi bai ce komai ba, shugaban police da ke sauraren su ya ja siririn tsaki, shi bai so suka riga su zuwa ba, don so ya yi suna zuwa su rage gawar yaran kamar yadda aka ba shi umarni daga sama, saboda ƴan jarida da irinsu Juraij, don su kansu suna sara wa DSS akan kafiya da nacin bin ƙwaƙƙwafin abu da tsananta bincike.
Tare Police ɗin suka tafi da su Principal don ƙwanƙwasar kansu da kyau akan fitar da ainihin adadin yaran da aka kashe ga koma waye, ko da kuwa makusantansu ne. Ragowar yaran school ɗin kuma da ma da ƴan ta'addan suka zo suka zaɓi waɗanda za su yi aikin a kansu kora su suka yi kowa ya yi ta kansa, hakan ya sa su ma ba za su san adadinsu ba, don a zatonsu ma kidnapping ɗinsu za su yi.
Ɓacin ran da Juraij ya koma da shi gida ba ƙaramin tsorata Ramlah ya yi ba, amma a haka ta lallaɓa shi da ƙyar har da hawayenta ya ci abinci kaɗan, bayan ya yi wanka tana jira ya zo su kwanta amma ta ga ya ja waya da system ya nemi gurin zama. Ranta a jagule ta sauko daga kan gadon cikin tafiyar da ta san za ta ruɗa shi ta ƙarasa gabansa ta tsaya, sai da ta gyara wuyan rigar baccin jikinta, sannan ta kashe murya kamar za ta yi kuka ta ce. "Still aiki dai? A daren nan? Ba za ka kwanta ka huta ba?" Ba tare da ya ɗago kansa ya dube ta ba ya ce. "Ki je ki yi baccinki kawai." Yadda ta ji sautin muryarsa ya sa ta kasa musa masa, ta fi kowa sanin idan yana cikin irin wannan yanayin ko magana ba ya son a fiya yi masa. Numfashi ta sauke ta fara ja baya, murya ƙasa-ƙasa ta ce. "Amma ka san ina buƙatar ka ko?" A hankali ya ɗago kai ya kalle ta, sai ya ji tausayin ta ya tsirga masa, amma ba zai iya barin wannan aikin ba, ya riga ya yi bankwana da duk wani abu nasa idan ba dole ba, zai hana idonsa bacci, zai takure kansa, sai ya yi binciken nan, sai ya gano ko su waye, amma ita Ramlah fa? Haƙƙinta da buƙatar lokacinsa da take yi fa?
Taune leɓensa na ƙasa ya yi tare da runtse idonsa.
"Just 1 hour." Ya faɗa kamar mai raɗa.
Murmushi ta sakar masa ta ce. "Bari na kawo maka coffee, na san kana buƙatar shi a yanzu, za kuma ka ji daɗinsa." Kai ya ɗaga mata ba tare da ya buɗe idonsa ba.
Cikin mintuna ƙalilan ta je ta haɗo ta kawo masa ta koma ta kwanta, ya fara sha da kaɗan da kaɗan, bai yi ko minti biyar ba ya ji wani irin bacci na fizgar shi, kansa ya yi masa nauyi, ya so fizgewa amma ya ji abun ƙara gaba yake, hakan ya sa ya miƙe don zuwa toilet ya wanke fuskarsa, amma sai ya ji kamar a kan iska yake saboda layi, a daddafe ya ƙarasa ya kwanta a gefen Ramlah yana sauke numfashi.
***** ******
Kansu Ahayan a ƙasa suka nemi guri a tabarmar da aka shimfiɗa suka zauna, Baba ya samo solar mai ƙwayaye uku ya saka, hakan ya sa haske ya wadatu sosai a soron.
A tare suka gaishe da mutanen, suka amsa cikin fara'a, amma ban Sita da ya yi shiru cikin nazari yana ƙare musu kallo.
"Budurwa, wadda ka tabbatar namiji bai taɓa ratsa ta ba, wadda ba za ta wuce shekaru ashirin ba."
Maganganun Yallaɓai suka dawo masa kamar yanzu yake siffanta masa, dukkansu ba za su wuce shekaru ashirin ba a ganinsa, kuma ya san tunda Baba ya kawo masa su ba su taɓa aure ba don ya sanar masa budurwa yake so, a yadda ya yi bincike kuma Baban yana da tsauri, ba ya jin yayansa za su yi tsalle-tsalle.
"Ku ɗago ya gan ku da kyau mana, kun wani ƙunshe kawuna kamar sababbin amaren da."
Baba ya faɗa yana murmushi don ya ƙara burge Sita da iyayensa.
Ahayan ce ta fara ɗaga kai ƙirjinta na wani irin bugu, ta rasa me ya sa ta tsorata haka, jikinta har rawa yake yi. Ummi kuwa ko a jikinta, don ita duk inda ta faɗi sha ne.
Cikin nazari sosai Sita ya ƙare musu kallo, Yallaɓai ya saka shi ayyuka da yawa, amma wannan ya fi nanata masa da gargaɗinsa kar a samu matsala, hakan ya sa yake takatsantsan. Ƙundunbala ya yi ya nuna Zeenat yana sosa kai, saboda ganin ta fi su fes da kyan gani. Kabbara Baba ya saki tare da tafa hannuwa ya ce. "Alhamdulillah! An ajiye ƙwarya a gurbinta, ai dan dai kar na yi maka karanbani ne amma tun lokacin da ka zo mini da batun ita yi maka sha'awa, don ta fi dacewa da kai yadda kake ɗan gayen nan. Ga tarbiyya da ilimi." Ya ƙarashe maganar yana dariya.
Sai a lokacin Ahayan ta ji wani numfashi da ya maƙale mata ya ware, ta sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya. Sallamar su Baba ya yi, zuciyar Zeenat kamar farar takadda ta falfala cikin gida da gudu.
"Umma! Umma! Umma ni ya zaɓa? Da ni za a ɗaura auren"
"Da gaske?" Umma Lantana ta tambaya tana miƙewa a zabure har zanin jikinta na neman faɗuwa.
"Da gaske Umma, wallahi ni ce, da ma kin faɗa."
Rungume ta Umma Lantana ta yi suka dinga tsallen murna, Inno ta taɓe baki, ita da ma Ahayan ce ba ta so a zaɓa, ba ta son ta samu rayuwar farinciki, ba ta son ta tafi ta rasa wadda za ta dinga bautarwa.
Habaici sosai Umma Lantana ta saki a tsakar gida, Umma dai ba ta ce komai ba duk da ta san da ita take, Inno ce kawai ta dinga tankawa.
Tare da Saif Baba suka shigo gidan, ya dire goro da alawa da kuɗi tumi na sadakin Zeenat a tsakar gidan, kusan zaucewa Umma Lantana ta yi da ta ga kuɗin, ta ɗauka ta dinga juya su a ruɗe tana sakin sunbatu.
Su Sita sun shigo wai gaisuwar uwar amarya, nan ma kuɗi masu kauri suka ajiye, hakan ya ƙara fasa wa Umma Lantana kai.
A ɗaki Saif ya samu Inno a rikice ya ce. "Wai waye wannan ɗin? Wanne irin aure ne haka rana tsaka kamar yaƙi? Ina wajensu Musa Baba ya kira ni wai na zo za a ɗaura aure, da mamaki na zo sai na tarar da abin tsoro, don ni wannan al'amarin tsoro ya ba ni ba al'ajabi ba, a ina Baba ya san mutanen nan?"
"Ina zan sani? Mu dai namu ido, tunda ƴarsa ce."
"Duk da haka Inno ya kamata mu yi wani abu akai, gaskiya kar mu bari a tafi da yarinyar nan, na fara yi masa magana ya gwasale ni wai ya san angon farin sani."
Tsaki Inno ta ja ta ce. "To ba sai ka rabu da shi ba, ina ruwanka? Bana son wannan shishshigin naka fa Saif, ka kiyaye ni wallahi."
"Amma..."
"Fice ka ba ni guri dalla, bana son shirme da iskanci."
Ta katse shi a harzuƙe.
Zuciyarsa babu daɗi ya bar ɗakin yana ta saƙe-saƙe, ga shi sai kiran Abba Adam yake wayarsa ba ta shiga, ya san shi kaɗai ne zai iya hana Baba ya hanu, shi su Sitan ne kwata-kwata ba su yi masa ba, bayan haka ma bai taɓa ganin irin wannan azazzalallen auran ba.
Duk yadda ya so ya ƙara fahimtar da Baba amma ya ƙi sauraren shi, duk da haka bai karaya ba ya dage kai da fata ba za a tafi da Zeenat ita kaɗai ba, sai an haɗa da ƴan rakiya kamar kowacce amarya, a nan Baba bai bula masa ƙasa a ido ba ya amince. Umma da Inno ya wakilta amma Umma Lantana ta buga ƙasa ta ce. "Wallahi ba zai yiwu ba, zan kirawo masu kai mini ƴata amma ban da ƴan gidan nan, abu na baƙinciki na san me za a ƙunshe a je a barbaɗa mata a gidan? Tunda ga hassada nan muraran an bayyana ta."
Wasu Aminanta guda biyu a unguwar ta aika suka zo, suna ta mamaki da wannan lamarin suka kama Zeenat don tafiya kai ta, sai a lokacin jikin Umma Lantana ya yi sanyi ta saka kuka, da ƙyar aka ɓanɓare Zeenat daga jikinta. Har da Umma aka tafi saboda yadda Saif ya nace, Inno dai ƙin zuwa ta yi. Da ma mota biyu su Sita suka zo da ita, sai suka shiga ɗaya su Umma ɗaya, Saif da Ummi suka bi bayansu a napep.
Tun da Baba ya zo wa Sita da batun ƴan rakiyar amarya ya kira Yallaɓai ya sanar masa, a take ya tura masa address ɗin wani gida ya ce su je can, idan mutane sun tafi sai ya kai masa ita guest house ɗin.
An kai Zeenat lafiya madaidaicin gidanta na bogi, wanda ganin shi ya wanke mata zuciya, kukan da take na rabuwa da Ummanta tuni ta neme shi ta rasa, don gida ne mai kyau har da bene, ga kayan furnitures masu kyau a ko'ina. Bayan ƙawayen Umma Lantana sun gama yi mata huɗubar da za su yi mata suka juyo suka bar ta ita kaɗai ƙwal, zuciyarta cike da saƙe-saƙen burika da irin rayuwar da za ta shimfiɗa ta jin daɗi a gidan aurenta.
***** ******
Tamkar yaɗuwar wutar da ke cin yayi haka mutuwar Sheikh Adnan da kisan yara ƴan makaranta ta baza ƙasar da kewaye cikin ƙanƙanin lokaci, ko'ina sai zancen ake tare da alhini, wakilan gwamnati sun yi magana da yi wa al'umma ta'aziyya na rashin babban Malamin da aka yi, tare da alwashin gano waɗanda suka kashe ɗaliban da alƙawarin hukunta su.
***** ******
Zaune suke a katafaran parlour su bakwai sun yi shiru suna mayar da numfashi, duk da sanyin AC da ke parlourn amma gabaɗayansu gumi suke yi, tsakiyar dare ne, hakan ya sa gurin ya ƙara yin tsit.
A hankali macen cikinsu ta sauke numfashi, ta miƙe ta ɗauki ƙaton jug ɗin da ke kan Centre table ta tsiyaya musu tataccen ruwan ƴaƴan itatuwa a glass cup, sai da ta miƙa wa kowa sannan ta zauna ta fara shan nata, lumshe idonta ta yi tana jin yadda sanyin lemon yake ratsa maƙoshinta, gami da kore mata ƙarnin jinin da suka gama sha a ɗazu.
Bayan duk sun dawo cikin nutsuwarsu Janwuya ya dube su a tsanake ya ce. "Dole akwai masu yi mana zagon ƙasa, ko a cikin yaranmu na gidan nan ko kuma a cikin yaran gari!" Jinjina kai suka yi, wani guntun tsoho mai siffar ban tsoro ya ce. "Na daɗe da fuskantar haka, kamar yadda na fahimci wanda ya ƙi bayyana goɗiyar da Ƙanzula take ta magana a kanta akwai shirin da yake ƙullawa a ɓoye, ko na ganin ya zama shugaba ba tare da mun farga ba, ko kuma na son kawar da mu ya kasance shi kaɗai ne Shugaban wannan tafiyar." Kallon-kallon suka shiga yi cikin gamsuwa, murmushi macen ta yi ta ce. "Ina nan ina aiki akan wannan kamar yadda na faɗa muku, soon zan zo da bayanin komai, don haka a bar wannan maganar, mu yi ta abin da yake gabanmu, wato batun ƙananun ƙwarin da aka gano suna son tsokano tsuliyar dodo, masu son dole sai sun shiga gonarmu."
"Wannan ma ba abin damuwa ba ne, domin kuwa ba abin da suka isa su yi mana, kawar da su a doran ƙasa ya fi kashe sauro cikin bacci sauƙi a gurinmu."
"Duk da haka ya kamata mu ƙara ƙure gudun linzamin dokin da muke kai, domin ɗan-hakin da aka raina yana iya tsole ido watarana."
"Babu wannan ranar, domin kuwa duk satar ɓera bai isa ya shigo daji neman abinci ya tunkari kejin Zaki ba." Cewar Tsohon nan.
Murmushi Janwuya ya yi ya ce. "Wannan haka yake, kafin ma ya ƙarasa ga kejin ƙananun namun daji za su yi fata-fata da namansa, su cinye shi tas ko ɗigon jininsa ba za a gani ba." Dariya suka saki a tare da haɗe glass cups ɗin hannunsa guri guda suka ɗan bubbuga, ban da mutum ɗaya da yake bin su da wani irin kallo.
"Kwana biyu ƙwaro duk ka yi sanyi, me yake faruwa ne?" Janwuya ya jefa masa tambayar yana tsare shi da ido.
Ƙara tamke fuska ya yi ya ce. "Na karya wani sharaɗi ne na ƙungiya ko kuma akwai abin da ake yi da na fasa?" Girgiza kai Janwuya ya yi.
"To ba komai, duk abin da kuke faɗa ina sauraron ku ai."
Wani kallon macen ta yi masa ta ce. "Ƙwaro mai babban aiki, ɗan ƙaramin sauro mai kayar da gwiwa, ka manta shi tamkar wahainiya yake? Yau ka gan shi fari gobe baƙi, yanayin nasa ne kawai ya juyo a haka." Dariya suka saki gabaɗaya suna ci gaba da yi masa kirari, duk da haka bai ko murmusa ba, sai ma runtse idanunsa da ya yi.
Sun daɗe suna tattaunawa da raba ayyukan da Ƙanzula ta ba su a yau a tsakaninsu, a ƙarshe suka karrama wanda ya jagoranci aikin samo idanun matasa 41 kamar yadda yake a tsarinsu duk wanda ya yi wani aiki sai an karrama shi da tarin dukiya a kuma ɗaga darajarsa zuwa mataki na gaba, matakan da wanda ya cika adadin da Ƙanzula ta ambata shi zai zama shugaba lamba ɗaya a ƙungiyar.
*#Zeey Kumurya*
*****