Makauniyar Hanya

Chapter 1

by @hindatuauwal


    🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌘



     ✨GABATARWA✨



DAMUWA!



Kai  tsaye zamu iya kiran damuwa da baƙin ciki. Wanda yake addabar zuciyar duk mutumin dayake ɗauke dashi.



Damuwa ko Baƙin ciki kan samune ta ɓangarori uku.



Damuwa ko Baƙin cikin daya sameka yanzu.



Wani yarigada yasameka har yakaima yema rayuwarka illah da ciwo me zafi.



Se wanda kakeda yaƙinin nan GABA zesameka.



Duk irin wannan nau'in damuwan idan yasameka to bakada burin dayawuce samun mafita. 



Sedai dayawan mutane basusan yanda zasu magance damuwoyin suba, sekaga suna ƙarama kansu da kansu damuwa batareda sun saniba saboda rashin sani.



Arayuwan da muke ciki ayanzune zakaga mutum na magance damuwanshi tahanyar saɓon Allah ko jin kiɗe-kiɗe da waƙe-waƙe, ko tahanyar shan kayan maye.



Summan tada abinda ubangiji ya'aiko fiyayyen halitta dashi wato alqur'ani.



Itadai wannan littafi megirma tana wanke zuciya sannan tasan yamata natsuwa da kwanciyar hankali.



Se tafiya nakeyi baku tambayeni tayayane mutane suke ƙarama kansu damuwa tahanyar magance damuwoyinsu da saɓon Allah ba!



Dafari dai kuyi hankali da shaiɗanun cikin mutane. Sune irin mutanenda bazasu taɓa barinka ka aikata alkhairiba matuƙar karataya al'amuranka ainuwar umarni ko shawarinsu sema sujefaka a makauniyar hanya.



    Me'ake nufida MAKAUNIYAR HANYA? Wani hali zaka shiga alokacinda kafarga da shaiɗani/shaiɗaniyar da shawara ko umarninsa yasakaka a makauniyar hanya? Shin mutanen da suke tare dakai zasu cutu suma?



Kash! Kun barni naƙara zarcewa ban baku amsar tambayanku na bayaba.



Domin jin amshoshin tambayoyinku damawasu hanyoyin magance damuwoyinku tahanyar daya dace batareda kun faɗa makauniyar hanya ba seku biyoni cikin wannan labarin mesuna MAKAUNIYAR HANYA!______



    __________________________



🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌘



🌓اءمى الطريق 🌘



♏ HINDATU AUWAL 







AMANAR SADI-SAKHNA 🥰 





BOOK ONE 



    ✨ CHAPTER 1✨



*SAIDI GOVERNMENT GIRLS SOKOTO STATE*



    *B.G.C HOSTEL*



Wani irin shirune ke zagayeda ɗakin. Bakajin sautin komai, dai dai da numfashi ahankali suke fitarwa, baka ganin komai acikin ƙwayannin idanunsu se zallan tsoro da tashin hankalin da yagama cika kowani lungu da saƙo na jikinsu.



"Tass! Tass! Tass.....!"



Ƙarar bindigar dake kuma ɗimau tasu yacika kunnuwansu.



Ƙara lafewa sukayi akan gadajensu, wani irin yanayi daya girmi tashin hankali na kuma cikasu. 



Allah ne kaɗai masanin hankalinda zukatansu ke ciki awannan lokacin se kuma mutuminda yatsinci kanshi acikin garin da masu faɗan aƙidanci kan dinga yawan hatsaniya da kashe kashen rai suna mai uwa da wabi.



Numfashi mai kauri tashaƙa, ƙirjinta na ɗagawa da nauyi mai girma. Zuciyarta ciwo take mata, tana zubda jini kamar dabban da aka tsire da mashi.



Ba tsoro takejiba kamar room mate ɗinta, hankalinta be tashi akan makomar rayuwar taba, tina-ninta be hasko mata abinda zesameta idan masu hatsaniyar suka shigo cikin makarantar suba.



Abu ɗaya takeji Innar ta, haka kawai zuciyarta ke bugawa tana bijiro mata da Innarta bata lafiya, kai in batai ƙaryaba ajikinta takejin kewar Innarta-ta.



Wani irin kewa dabata taɓa jin kalanshiba tsahon shekaru uku data ɗauka amakarantar nan.



Idanunta tarumtse wasu tarin emotions marasa limit na sake danneta. Tarin tinaninnika nasake cunkushe mata ƙwaƙwalwa.



Tananan azaune batareda tamotsaba har aka kira sallahn athuba. Zuwa wannan lokacin gari yayi tsit,sanyin athuba yaratsa, kiraye-kirayen sallah kawai kakeji.



Daƙyar taiya raba jikinta da gadon datake, da nauyi mai girma ta ɗaga ƙafafunta.



Kamar kowace ɗaliba haka ta daure taɗauro alwallah tazo tai sallah. 



Bayan ta idar da sallahn ta koma kan gadonta tasake kwanciya kunnu wanta na jiyo mata sautin muryikansu dake bada labari akan halinda suka tsinci kansu adaren jiya.



"A.Tafidah....Tafidah...are you hearing me?"



Muryar Umaima dake tsaye akan Maryam kefaɗi, hannunta na shafa gefen kumatunta don tabbatarda Maryam ɗin najinta.



Lumsassun idanunta tabuɗe, yanayin datake ciki na fitowa ƙarara acikinsu. hakan yasa Umaima cewa



"Meke damunki? Bakida lafiya ne?"



Jiki asaɓule tasauke hannun Umaima dake kan fuskarta, yanayin data kwana dashi adaren jiya nasake cikamata zuciya.



Head girl ne ta shigo bakinta ɗaukeda sallama,suduka suka amsa amma banda Maryam dake zaune zuciyarta na wani irin dokawa aƙirjinta.



Gaban gadon Maryam taƙariso tana cewa:



"Kitaso muje principle nakira"



Batace komai ba tasauko daga kan gadon, slippers ɗinta dake bakin gado tasanya tanabin bayan head girl.



Suna shiga Office ɗin idanunta suka sauka akan fuskar Hamma Ummar.



Kamar shima jira yakeyi yaganta se kawai yamiƙe, tana kallonshi yamiƙama principle hannu sukai musabiha, kunnuwanta na jiyo mata kalaman dasuka sanya zuciyarta tarwatsewa aƙirjinta.



"Allah yaƙara haƙuri yajiƙan wanda suka rigamu"



"Waye ya mutu?!..."



Ƙwaƙwal wanta taje fomata tambayar, zuciyarta nason dakatar da abinda hakan ke nufi, tinanin tarasa wani daga cikin ahalinta kaɗai nasanya numfashin ta barazanar ɗaukewa.



Bazata iyaba!....bazata iya ɗaukar nauyin rashin wani daga cikin ahalin taba. Tashiryama komai na rayuwa amma banda nauyin rashin wani w.....



Hannunta da Hamma Ummar yakama yasanya tina-ninta katsewa. Idanunta tadago takalleshi, tasan Hamma Ummar, tasan kowaye shi,don yanayinshi ayanzu na bayyanar matada balafiyaba.



Bakinta tabuɗe daƙyar ta lalubo muryanta daƙyar tafurta



"Hamma meke faruwa?"



"Bakomai"



Ya'amsata dasauri muryanshi na bayyanar da akasin abinda yafaɗa.



Kafin tasake cewa komai yaja hannunta dake cikin nashi, mashin ɗinshi da yazo dashi suka hau.



Addu'a sosai takeyi acikin zuciyarta, Ubangiji yasa komai bai faruba, komai yakasance yananan ayanda tabarshi.



Ahaka suka karisa ƙofar gidansu datake cikeda maza da mata, masu alwallah nayi, waɗanda suke tsaye suna magana sunayi.



"Ubangiji kasa komai bai faruba"



Wata ƴar ƙaramar murya daga cikin kanta tafaɗi, zuciyarta na matsewa da wani irin tashin hankali mara misaltuwa, jikinta ye sanyi ƙalau, daƙyar taiya ɗaga ƙafafunta dasukai mata nauyi kamar wacce akaima dabai bayi da sarƙa.



Cikin gidan ta shiga, tundaga zaure takejin hayaninyan mutane kaman wanda ake taron biki ko suna.



Da Goggo tafara cin karo aƙaramin zaure tana tsaye tana ƙirga kuɗaɗe, batabi takan taba tanufi ɗakin Innarta.



Gawa tagani ashimfiɗe atsakiyar ɗakin, anrigada angama shiryata cikin farin likafani.



Kanta ne yasara, zuciyarta tai wani irin tsalle kamar zata faso allon ƙirjinta tafito, jikinta yasoma ɓari numfashinta na maƙalewa aƙirjinta.........



  Afuwan masu karatu anan zan dasa aya. Nasan bakuji daɗiba amma kuya hakuri muhaɗu a chapter 2.



Taku  AMANAR SADI-SAKHNA 🥰