MATAR GIDA PAGE 22
MATAR GIDA 022
SHUUKRAN/22
P22
Bayan tafiyar Ɗalha da Muhsin kamar yadda Ammi ta faɗa sun fita gaisuwa da Amirah tun misalin sha ɗaya na safe basu suka dawo gida ba sai bayan sallar azahar,daga gidan barka sun wuce shoprite yadda Ammi ta yiwa Amirah siyayyar sutura ready made masu yawa masu kyau da tsada,bayan komawarsu gida ne Amirah na zaune cikin ɗakinta a can bangarensu da Ɗalha wayarta ta yi ƙara alamar shigar kira jakarta ta hannu dake daure kan gado ta dauko ta ciro wayar ganin Kabir ne ke kira yasa ta ɗaga wayar ba tare da ɓata lokaci ba ta amsar kiran daga ɗaya bangaren Kabir ya ce '' yanzu na zo gida aunty ke faɗa min mijinki ya zo jiya kin wuce'' murmushi Amirah ta yi kafin ta ce ''mallam aiy sai ka bari mu gaisa ko,daga amsa waya sai jero zance'' Kabir ya ce ''Allah sarki yayata ta kaina ki yi hakuri,ina uni ya gida ya yara?" Amirah ta ce ''to ko kai fa,kowa yana lafiya ya ka ke ya kasuwa?" Kabir ya ce ''alhamdulillah,wai ina yaran ne suntafi makaranta ne?" shiru Amirah na wasu ƴan sakanni kafin ta ce ''ina Kano har yanzu'' cike da mamaki Kabir ya ce ''kano a ina? ba ki tafi Kaduna ba?" Amirah ta ce ''eh ina gidan Ammi amma shi ya wuce tun da safe" shiru Kabir ya yi kafin ya ce ''me kuma ya faru?" Amirah ta ɗan yi murmushi kafin ta ce ''babu komai fa Ammi ce ta ce na zauna bayan kwana biyu sai na koma'' Kabir ya ce ''ok in babu damuwa zan iya zuwa akwai maganar da nake son mu yi ne'' Amirah ta ce ''babu matsala za ka iya zuwa'' Kabir ya ce ''to bayan sallar la'asar zan zo'' Amirah ta ce ''sai ka zo'' daga haka suka yi sallama
Misalin ƙarfe biyar Amirah ce zaune parlourn baƙi tare da Kabir,ƴar aikin Ammi ce ta shigo parlour hannunta riƙe da tire da ta daura ruwa da lemo tare da kofi,a gaban Kabir ta dire tiren kafin ta fita daga parlour Amirah ta na kallon hoton da Kabir ke nuna mata cikin wayarsa sai murmushi take ita kaɗai can ta miƙo masa wayar ta ce ''a ina kuka haɗu?" Kabir ya ce ''facebook''Amirah ta ce ''ikon Allah ai kam ta wayeni ƙanwar mijin Rumaisa ce, ƙawata dake aure a Kaduna ita da mijinta duk ƴan Adamawa ne a can suke,kasuwanci ya kaisa Kaduna ya zama kaman ɗan garin'' Kabir ya ce ''haka ta faɗa min'',har sannan fuskar Amirah dauke da murmushi ta ce ''amma kamar tana karatu ban sani ba jami'a ce ko diploma'' Kabir ya ce ''diploma ce, yanzu take shekarar karshe'' Amirah ta ce ''masha Allah ya yi kyau,Yasmin yarinyar akwai hankali ba laifi ga nitsuwa''shi dai Kabir ya yi shiru ya bar Amirah nata faman zuba can dai ya ce ''tsawon watanni biyu kenan haduwarmu,har yau taƙi yarda na je gidansu,so nake da naje na kai kuɗin sa rana gaba ɗaya amma taƙi ita kawai makaranta,makaranta, na ce mata ba yanzu za'a yi auren ba sai ta gama karatu amma taƙi yarda'' shiru Amirah ta yi tana nazarin maganar da Kabir ya yi kafin ta ce ''yaushe zata gama? Kabir ya ce semister ɗaya ya rage mata'' Amirah ta ce ''to mallam ka yi hakuri mana ta kare semister kamar yanzu ne aiy'' murya can ƙasa Kabir ya ce ''haka ne'' haka dai suka kasance Kabir bai bar gidan ba saida aka fara kiran sallar magrib kafin ya yiwa Ammi da Amirah sallama
Aisha ce zaune cikin ɗakin ta tisa Unaisa gaba tana bata wasu magunguna jiƙo haɗin wankin mara,sai wani ɓata fuska Unaisa ke yi ita dai Aisha bata ko kalle fuskar Unaisa ba bayan Unaisa ta gama shan wannan Aisha ta dauki wani maganin da aka dama da nono da zuma da miƙawa Unaisa ta ce ''maza shanye'' ganin babu alamar wasa a fuskar Aisha yasa Unaisa ƙarbar kofin ta kai baki ta shanye,wata kwanon silver mai murfi Aisah ta dauko ta dire shi gaban Unaisa tare da buɗe kwanon ta ce ''bismillah ki cinye duka zan je na haɗo maki ruwan'' kazar hausa ce cikin kwanon da aka dafa ta da magungunan gaba ɗaya kazar ta canza kala ta yi baƙi kirin haka Unaisa ta rinƙa ci ba da son ranta ba,tana cikin cin kazar ne Ɗalha ya kirata,ta rinƙa kallon wayar kamar baza ta amsa kiran ba,tun jiya take kiransa bai ɗaga ba bai kuma kirata ba sai yanzu wayar tana daf da tsinkewa ta amsa shiru ta yi bata ce komai ba daga ɗaya bangaren Ɗalha ya yi mata sallama bata amsa ba saida ya yi sallama sau huɗu a na biyar ne ta amsa kamar jira yake ta amsa nan ya shiga bata hakuri inda ya ce ''Allah ya huce zuciyar gimbiya nayi busy ne sosai,jiya ina office Abba ya kira ni ya faɗa min Amirah ta dawo gida to shi ne na je dauko ta yanzu haka ina kan hanyar dawowa Kaduna ki yi hakuri Unaisa kaina ne ya yi zafi yanzu haka ni kaɗai zan koma gida Ammi ta ce Amirah ta zauna a can'' daga haka ya yi shiru itama Unaisa shiru ta yi tana nazarin maganganunsa kamar baza ta ce komai ba can ta ce ''saboda ta dawo ka ƙi amsa kirana? kawai dan za ka je dauko ta anya ina da daraja a wajen ka?" Ɗalha ya shiga girgiza kai kaman yana gabanta ya ce ''no ba haka bane ba ki ji me na ce ba kai na ne ya yi zafi,yanzu haka fa mun tsaya shan mai ne na kiraki ɗan Allah ki daina wannan tunanin gimbiyata'' cike da ɓacin rai Unaisa ta ce ''kamar yaya na daina tunani waya kawai aka yi maka amma ka biyo hanya a jiyan ka tafi wajen matarka daman kana so ta har haka?" zuwa yanzu Ɗalha bai san abinda zai cewa Unaisa ba kawai ya yi shiru yana jin yadda take masa rashin mutunci cikin waya,Aisha yayar Unaisa ta shigo ɗakin bayan ta gama haɗawa Unaisa ruwan wanka ta ji yadda Unaisa na rashin tarbiyya a waya, da wani irin sauri ta karɓi wayar ta kashe ko ba'a faɗa mata ba ta san da Ɗalha take waya tsabar ɓacin rai Aisha bata san sanda ta wanke Unaisa da maruka har uku ba cike da ɓacin rai ta fara magana inda take faɗin ''kin san abinda ki ke kuwa hala kin fara hauka ne bamu sani ba? wanda za'a daura maki aure dashi nan kwanaki takwas ki ke yiwa tijara haka? kina cikin hankalinki kowa'' Mama tare da ƴan uwanta suka shigo ɗakin Anty Lantana autar su Mama ce ta yi magana ta ce ''me ke faruwa Aisha?"nan Aisha ta faɗa masu abinda ta sani cewar ta shigo ta ji Unaisa na zagin Ɗalha ta daura da ''kuma fa ba yau ta fara wannan halin ba tun da aka sa masu rana ta rinƙa yiwa bawan Allah rashin mutunci da wane da tuni ya ce ya fasa''
Mama da su Anty Lantana sun nime waje cikin ɗakin sun zauna kafin suka fara yiwa Unaisa faɗa kan abinda take bai dace ba,daga haka sun daura da nasiha,tun ɗazu wayar Muhsin ke faman ringing Ɗalha ya mayar da dubansa ga Muhsin ya ga barcin sa yake hankali kwance hakan yasa Ɗalha sa wayar a silent suna daf da shiga garin Kaduna ne wayar Ɗalha ya yi ƙara alamar shigar kira ganin lamba ce babu suna ya sa Ɗalha amsa wayar tare da sata a sipeka muryar Hafsah ya ji kamar tana kuka lokaci guda hankalin Ɗalha ya tashi hakan yasa ya fara magana cikin rawar murya ya ce ''lafiya Hafsah me ke faruwa?" cikin muryar kuka Hafsah ta ce Fauziyya ce'' tsabar firgita saida kanbon mota ta kusa kubcewa a hannu Ɗalha ba tare da nitsuwa a jikinsa ba ya ce ''me ya same ta?" Hafsah ta ce ''ina kitchen ta biyo ni ban san sanda ta dauki gorar haypo ta kai baki ba kafin na ankare ta sha hypo'' cike da firgice da kiɗima cikin ɗaga murya Ɗalha ya ce ''what'' Hafsah ta cigaba da kuka cikin kuka ta ce ''tun ɗazu nake kiran layin Baban Muneebah amma bai ɗaga wayata ba'' a hankali Ɗalha ya sauko daga kan kwalta ya yi parking mota a gefin titi lokaci guda jikinsa ya yi sanyi sosai murya can ƙasa ya ce ''ina ku ke yanzu?" Hafsah ta ce ''asibiti likitoci suna duba ta'' a sanyaye Ɗalha ya ce ''oky tura min sunan asibitin'' daga haka ya kashe waya Muhsin ya kafe Ɗalha da ido yanayin da yaga Ɗalha a ciki ya sa hankalinsa tashi bayan Ɗalha ya ajiye waya Muhsin ya ce ''me ke faruwa mutuwa aka yi?" murya can ƙasa Ɗalha ya ce ''Fauziyya ce ta sha hypo'' gyara zama Muhsin ya yi ya kafe Ɗalha da ido tsabar mamaki can ya ce ''ina suke yanzu Ɗalha ya ce ''asibiti'' shiru Muhsin ya yi kafin ya ce ''ok zan karasa tuƙin wane asibiti ne'' Ɗalha ya miƙo masa wayarsa ya ce ''ka duba zaka ga sunan asibitin''
SHUUKRAN