AMARYAR GADO

CHAPTER 9

by @xayyeesherthulhumaerath

AMARYAR GADO

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

AISHA SANI ABDULLAHI

Xayyeesherthul-humaerath

©️2026

 

Jan hankali: Wannan littafi ƙirƙirarriyar riga ce da aka saka wa kowace ƙaddara da ke cikinsa suna. Kada wani labari ko sirri da aka bayyana a cikinsa ya sa a fassara shi da rayuwar wani na gaske. 

 

Gargaɗi: Haƙƙin wallafar littafin na marubuciya ce kaɗai. Ba a yarda a juye shi zuwa wani harshe, ko a canza shi zuwa sautin murya (audio) ba tare da rubutacciyar yarjejeniya ba.

 

 

SHAFI NA TARA

 

Tana tsaye tana kallonsu suka shige daki, Falila ta rufe kofar tana bin Farida da wani irin kallo cikin kaskanci.

 

Gabadaya Farida ji ta yi ta rasa me ke yi mata dadi, kafafuwanta na yi mata dauyi, jan jikinta ta yi ta shige dakinta.

 

Daga dakinta tana juyo sautin badaƙalar da suke aikatawa, musamman muryar Falila, sai wani irin surutai take yi barkatai irin na ’yan bariki.

 

Ko da ta yi kokarin kwanciya ta gagara, domin tamkar kara volume suke na duk wani motsi da sambatun da suke.

 

Farida ta dafe kai gefen gado tana faɗin, “Abun da ban taɓa riska ba, rayuwar da ban san ya ake yinta ba, ni kuma tawa ƙaddarar ta haka ta zo? Haka Sufyan ya lalata rayuwarsa? Ban taɓa zaton hakan ba, Ubangiji shi kaɗai ya san me yake nufi da ni.”

 

Ta karasa maganar tana tashi, toilet ta shiga ta dauro alwala ta fara sallah ko hakan zai sa ta daina jiyo shirmen su.

 

Amma ina, abin ƙara gaba yake, ta gagara samun sukunin yin nafilar ma, duk ta birkice hankalinta ya tashi. Sa hannu ta yi ta fara ƙoƙarin toshe kunnuwanta, can kuma sai dabarar kunna karatun Qur’ani ya zo mata. Ta kunna ta kure volume sannan ta rufe kanta da filo.

 

Ta daɗe a hakan, tana rufe idanunta Sufyan da Falila take hangowa, kafin da ƙyar barci ya yi nasarar sace ta.

 

Karfe biyar na safe ta ji mutsu-mutsun su a falo.

 

Sufyan ya ce, “Kin ga ki zo in maida ki, don in kika kai safiya wasu daga cikin ’yan gidanmu za su iya ganinki?”

 

Falila ta yamutsa fuska, “Haba Sufy, ni fa ka san in ina tare da kai bana son matsawa, na fi so in ta kasance daf da kai. Zan iya hakura da komai indai ina tare da kai.”

 

Sufyan ya ce, “To ai shiyasa nake so mu kiyaye hakan. Kin san unguwar nan kaf danginmu ne, muna kuskure daya za a fahimta. Shiyasa jiyan ma ai sai da dare ya tsala muka samu muka shigo.”

 

Cikin yanayin shagwaba ta rike shi tana, “To daga yau sai yaushe?”

 

Sufyan ya ce, “Kar ki damu, zan kiraki.”

 

Falila ta tashi tana gyara gyalen da ke jikinta ta ce, “Amma ni fa har yanzu baka fadamin wace ce wacce na gani jiya ba.”

 

Sufyan ya ce, “Mu dai tafi yanzu, daga baya zan miki bayani.” Ya karasa maganar yana jan hannunta.

 

Suna fita daga dakin, Farida ta fito falo ta zauna.

 

Shi kuma Sufyan sai da ya maida Falila sannan ya komo gidan. Yana shiga ya tarar da Farida, ganin sa yasa ta tashi ta sha gabansa.

 

Sufyan ya hada rai ya ce, “Ya ke kuma lafiya?”

 

Farida ta ce, “Eh, kila za a iya samun lafiyar daga baya, amma a yanzu dai kam babu.”

 

Kallonta sama da kasa Sufyan ya yi ya kauce zai wuce, ta kara shan gabansa.

 

“Yanzu kai rayuwar da ka daukan wa kanka ta yi maka daidai kenan? Ta dace da kai kenan? Abin da zaka yi wa iyayenmu sakayya da shi kenan? Ga zina, ga shaye-shaye. Wallahi duk da girman kai da ka ke da shi, ban taba tunanin cewa lamarinka ya kai ga hakan ba. Kuma abin mamaki, ko kunyata bare shakkata baka ji? To ka sani wallahi duk abin da ka yi a gidan nan jiya, kamar ka yi su ne a gaban Baba da Abba.”

 

Sufyan ya kalleta yana sakin wani gajeran murmushi ya ce, “Kin gama?”

 

Ga mamakin Farida ganin yadda ko gezau bai ba, bare a kai ga batun nadama, babu a fuskarsa, hakan yasa ta gagara fadin komai.

 

Dariya ya fara yi kafin ya ce, “Kin ga duk wannan abin nan, in kin fasa fada ba cika ’yar halak ba. Wai an fada miki, kema ban san irin rayuwar da kike ba ne? Ai gwanda ni da kike nunawa kowa cewa ke ta Allah ce, ba a san cikakkiyar shedaniya ba ce.”

 

Cikin fushi Farida ta dakatar da shi, “Karka kuskura ka kara danganta ni da shedaniya, kuma ka san karyarka kake cewa ina aikata mummunan aikin da kake yi. Allah raba gatari da saran shuka.”

 

Kara shekewa da dariya ya yi yana, “Allah ko? Musa a baki, Fir’auna a zuci. Jiya da kika gama badakalarki da HOD, na kulaki ko na shiga gonar ki? Bai dameni ba fa. Ki yi rayuwar barikinki, nima in yi tawa, domin daga ni har ke duk mun san mu ba tsarar juna ba ne. Sannan kuma batun fadawa su Abba, ina kara tuna miki da karki fasa.”

 

Ya karasa maganar yana ciro wayarsa.

 

Hoto da bidiyo ya nuna mata wanda ya dauketa ranar ba kaya a jiki, kafin ya ci gaba da fadin, “Wannan kadai shaida ce, zan nuna musu tun kafin ki fadi nawa da baki da cikakkiyar shaida.”

 

Suman tsaye Farida ta yi, kanta ya fara juyawa, cikin ƙarfin hali ta ce, “Allah ne shaida a gareni, ban taɓa aikata zina ba, kuma ba zan taɓa ba da ƙarfin ikonsa. Kuma wannan hoton kai ka san me ka shirya a ranar, don ni ban san komai ba. Don haka na bar ka da Allah, shi zai yi mini sakayya.”

 

Sufyan ya ce, “Auh ko? Ke malama ki fa daina wani nuƙu-nuƙu, kar na ke kallonki daga sama har ƙasa. Fina shekaru ba shi ke nufin kin fini wayo ko dabara ba. Ni fa sai yanzu na fahimci dalilin da ya sa kullum ma ƙara hauhawa kike kamar farashin fulawa. Ashe kema kin san daɗin rayuwar.”

 

Cikin zafin rai Farida ta ɗaga hannu za ta kai masa mari, ya yi saurin riƙewa yana dariyar mugunta.

 

“Ki kula, kar ki fara fa, don yanzu abu kaɗan za ki yi, in je in baza hajarki, dangi ya ɗauka.”

 

Fisge hannunta ta yi ta shige ɗakinta da gudu.

 

Tana zuwa ta faɗa kan gado, hawayen da ta riƙe kar su zuba gaban Sufyan take suka fara ambaliya a fuskarta, kanta na ƙara sara mata.

 

“Kenan akwai masu yi mini kallon mazinaciya? Na yi kama da mazinaciya? Ta yaya? Ni Farida? Zina, zina fa! Ya Allah, me yasa tun da na zo duniya nake fuskantar ƙalubale kala-kala? Me nake aikatawa? Laifin me na yi? Komai ni, komai ni? Ban san yaushe zan fara jin daɗin rayuwa kamar kowa ba. Rabbie, na tuba, ka yafe mini, ka gafarta mini, ka haneni aikata sabonka, kar ka ba wa zuciyata damar aikata maka abin da bai dace ba.” Ta ƙarasa maganar tana sakin kuka mai tsuma zuciya.

 

Shi kuwa Sufyan ko a jikinsa, ɗaki ya shiga ya ƙarasa shiryawa. Ya fito zai fita daga gidan kenan ya tarar da mai gyara ya kawo wa Farida motarta, don HOD ya ba shi number ɗinta ya kirata. Kafin ta fito, Sufyan har ya tafi.

 

Karɓar key ɗin ta yi ta masa godiya, ta koma ciki. Wanka ta shiga, ta fito daga wankan kenan ta jiyo sallamar Inno. Hijabi kawai ta zura ta fita falo.

 

Inno na ganinta ta fara rattaba salati, “Me ya faru haka? Idanuwanki suka yi jajur, gasu sun fito radau kamar mujiya! Kar ki ce mini kuka, Safiyanu ya sanya mini ke, Faridatu.”

 

Farida ta yi murmushin ƙarfin hali ta ce, “Aa, zauna mana, Inno.”

 

Ta faɗa tana riƙe hannun Inno da nufin ta zauna.

 

Inno ta zauna tana, “Yoo, ke! Waye ta zama? Ina ganin husuma a kwaryar idanuwanki, Faridatu.”

 

Farida ta ce, “Ba wani abu fa, ina wanka ne sabulu ya shigan mini cikin ido.”

 

Inno ta yi doguwar ajiyar zuciya, “Ko da na ji mana, har hankalina ya kwanta. Ai na san Safuyanu ba ya yin wanga aika-aikar. Ina yake ne?”

 

Farida ta ce, “Ai yanzu ya tafi makaranta.”

 

“Masha Allah, in dai kuna zaune lafiya? Kwana biyu ban samu zuwa ba, nace yau bari na yi asubanci in duba ku.” Cewar Inno.

 

Farida ta amsa da, “Lafiya lau, Inno.”

 

Inno ta taɓe baki, “To ya batun tsaftar dai? In dai ana yi ana goga alimun ɗin? Kin san fa rashin tsaftar nan tsaf zai iya hanaku samun albarkar aure. Don so nake nan da wata tara cif ki sambado muna ’yan tayi biyu masu kama da ke.”

 

Inno na faɗin hakan, gaban Farida ya yi mummunan faɗuwa. A idanunta ta fara hango yara sun yi kama da ita, cikin zuciyarta ta fara ayyanawa, “Allah ya kare, ai ko zan haihu ma ba dai da Sufyan ba, bare kuma bana fatan in haifi yaran da za su yi kama da ni, su fuskanci wulakanci da tozarcin da nake kan fuskantar…”

 

Inno ce ta taɓa ta, ta katse mata zancen zucin tana, “Faridatu, ya ne? Ko ma har an samu rabon ne dai ba labari? “

 

Inno ta ƙara taɓe baki tana kallon Farida, “Da ana cewa ba a so ba, ashe na munafunci ne, tunda har an makalewa miji an samu rabo. To ai shikenan, yanzu zan je in shaida wa iyayenku a fara tanadi, don ni zan zo zaman wanka.”

 

Farida ta buɗe baki, “Aa fa, Inno, babu komai. Don Allah kar ki faɗa wa kowa.”

 

Inno ta ce, “Babu wani nan, yi min shiru. Kin ga bari in tafi in shaida musu an samu abin rabo ne, kila ma rabon ’ya mace ne ya kashe Ahmad.”

 

Inno ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin tashi, daidai lokacin Sufyan ya shigo ɗakin.

 

Tana ganinsa ta fara washe baki, “Sufuyanu, ashe kuma…”