Chapter 25(drama)🤣
by @smauta
Hasken sanyin safiya ya karade ko ina kaka na zaune akan gadon ta na jinya an jingina mata pillow dede na bata ruwa,kawu labaran ne yashigo dauke da tray na tea da bread,yaya ya jikin kike jinshi yanzu, labaran naji sauki banajin komai Allah ya sakama ku da alheri shikuma wannan yaro da yaketa dawainiya damu Allah ya biya shi da gidan aljanna gaba daya dakin ya dauka da amin,dede ta kalli manar dake gefe tana sunkuyar dakanta kasa........
Kawu labaran yayi tari to nidai akwai abinda nakeso mu tattauna daku kafin lokacin tafiyar nan taku tayi,abu na daya yaya dede bataiman adalci kiri kiri ta zige Alhaji bazaaje dani ba kasar waje to wallahi ki sani yadda kike da hakki kanta haka nike dashi,kaka tasan halin kanenta sarai tace labaran muyi aiki da hankalin da Allah ya bamu kafin ayi damu muyi da kanmu ga iyalan ka saika tsallake su kabar su,duk inda muke labaran nuna tare dakai, jinjina kanshi yayi Allah ya kara maki lafiya Amin............
To game da wannan yarinyar da khalilu ninaga abinda nagani wannan yaron khalil mutumin kirki ne ya ceci rayuwar ki yaya ya dauki dawainiyar mu to s gaskiya ninaga ya dace a bashi auren manar, dede ta kalle shi shekeke kawu mi kake nufi?Aure nikeso in daura masu ranar juma'a indai khalil ya yarda,shuru dakin yayi sai sautin na'urorin kaka,manar tayi tsalle ta mike a'a kawu dan Allah karka aura mani shi banison shi kaka baban halim ne fa🥺
Kaka tace halim kawarki?eh kaka,kawu labaran ya fusata meyasa bazaki aure shi ba kinfi son muyita zama dake dama tana wuce maki to baki isa ba nine de mai badaku aure nagama magana ta muddin Alhaji ya yarda juma'a iwar haka kin zama matar shi,kin manta ke marainiya ce wannan itace damar ki aure kuma rufin asirin ki ne bari kiji in gayamaki.......
A hankali kaka tace labaran ka rage murya asibiti muke kabari aji daga bakinta,hawaye manar tashiga gogewa kaka wallahi yanaman kallon diya ne ba soyayya ba tausayi ne kawai karku tilasta mashi dan Allah,dede ta rungume manar ba wanda zai maki dole yarinya ta,kawu labaran ya kara hayaka kece kike daure mata gindi tayi wasa da damar ta ko saurayin kirki bakida shi,idan kika bari wannan ya tafi zakici gidanku...........
Kofar dakin aka budo yaji duk maganar da sukayi fuskar sa ta canza,kawu labaran naji abinda kuke tattaunawa,washe baki yayi to Alhamdulillahi ka yarda,manar ya kalla idanunta sun cika da kwalla tana girgiza masa kai kadan ya juya ya kalli kawu,kawu nagode da wannan tayin darajar da kayi mani amma aure anayin shi a bisa amincewar juna manar ba kaya bace da za'a dauketa a saida lokacin da ake so mutum ce mai ƴanci kuma tanada zaɓi............
Kufa yan Abuja haka kuke wannan figigiyar yarinyar har wani Æ´anci tasani nine babanta,da kaushin murya khalil ya kalli kawu labaran yace nine wanda zai tsaya mata koda duniya zata juyaman baya nima kuma koda zan rasa abinda nakeso duk duniya bazan zuba ido naga an takurawa manar ba,kusa da manar ya matsa muje dr na neman mu a hankali dede ta saketa suka fita zuwa office din Dr.........
Sir hajia na samun sauki sosai ya kamata a fara processing visa zuwa Germany nan da 1 week,na fahimta dr ka fara paperwork nizan dauki nauyin komai,manar a ranta take kiyasta wai wane irin kudi gareshi wannan,ya juya kallon manar yayi kanta na kasa,ina ganin mama da kaka zasu tafi sai jude ya bisu koda zasu bukaci wani abu.............
Nikuma fa?mezakije kiyi? lokacin komawar ki school ya kusa so bazaki bisu ba amma shut up nagama magana magana 😂 murmushi ya sakar mata tana nan zaune ta rasa ina zata saka kanta taji dadi kiri kiri jinyar kakarta ace bazaa tafi da ita ba,nifa bazan koma wata school ba wallahi su kaka zanbi kallon ta yayi to ranki ya dade adawo lafiya,a waje suka tarar da kawu labaran nan waje shi kadai yana magana da kansa yarinya kinma kanki amma nasoki da yaron nan 🤣🤣🤣🤣🤣KAWU KAKI SADUDA DAI🤣🤣🤣
Office din visa germany dake nan cikin abuja dakin cike da mutane Khalil na rike da files Dede na gefen sa tana tasbihi manar kuma na zaune ta cika saura kadan ta fashe ta tabbatar bada ita za'a tafin ba,maaikacin wurin ne ya fito da visa mutum ukku oga Flight dinku juma'a mai zuwa 2pm na rana,ansa yayi to Alhamdulillahi nagode dede tace Allah ya kaimu lfy ya dawo damu lfy cikin ranta...........