SHI SO DABAN YAKE

Babi na shida

by @dijensy



6



    Yau Jidda bayan tayi sallah subh ko komawa bacci bata yi ba ta tambayesa biro da takarda dawowarsa daga masallaci yayi ɗan jim batare da ya san mai zai yi ba amma bai fahimci inda ta dosa ba mai zatayi da biro da takarda? haka nan ya fita ya duba shagonsa ya ɗakko mata ya kawo mata ta karɓa yana tsaye Jidda ta fara rubuta masa list ɗin abubuwan da take ɓukata sai da ta cika gaba da bayan gajeriyar paper memo note book ɗin ta miƙa masa Hassan ya sa hannu ya karɓa da faraa a fuskarsa ya na kalla ya karanta kayan sabulai ne na wanka da turare da su pad saitin kayan wanka brush da sauran kayan mata na amfanin jiki."Zan sayo miki anjima bacin su ba wani abu da kike da buƙata?"Ya tambaya ta girgiza kai ba tare da ta kallesa ba ya juya jidda tayi murmushin mugunta ta tabbata bai da masaniya kan farashin kayayyakin da ta lissafa masa da ba zai tambayi daɗi ba.Anty Ruƙayya tuni ta fito kichen haɗa abin kari kamar koyaushe ta jera komai a tray ta aiko musu indomie da kwai tayi ta haɗo da toasted bread da kayan shayi da ruwan zafi da ya sha kayan haɗi mai daɗin kamshi sannan daban ta aiko da ruwa a flask Jidda ta miƙe ƙafa ta yi break ɗinta sai da ta gama yayi nasa ya fita da kwanukan Anty Ruƙayya ta hangi Hassan ɗin zai wanke ta sauri ta tashi Amal yau ba makaranta ta turata ta je ta wanke ya bar mata ne don ya ga ta ɗauke soson da omo yarinyar ƙarama sai hankali da wayo ta je ta zuba ruwa a baho ƙarami ta zo ta wanke fita yayi daga nan ya tafi wani shago a unguwar ko zai samu ya rage wasu siyyayyan da yake tunanin za a samu bai sani ba ko tana buƙatar pad ɗin yana zuwa shagon aka ce babu irin pad ɗin brush kawai aka samu shi daman bata tantance ba ya dawo yana tarar da ita ta fito daga wanka yau ma ɗankwali tayi ɗaurin kirji dashi cinyoyinta a waje da saman ƙirjinta ta ɓata fuska tana shafa mai a hankula Hassan yayi sauri yayi ƙasa da kai kan tebirin gefen gadon ya ajje ledar brush ɗin ya sa ƙafa ya fita  ta sauri ta tashi ta saka kaya ledar da ya ajje ta duba ta ga brush ta murmusa "Baka ga komai ba ma tukun"Ta faɗa a ciki ciki.Hassan shago ya shiga ya zamansa yana kiran ogan wajen aikinsa jiya daman ya masa magana ya bashi uzuri tohm mutumin mai fahimta ne ya ce masa ya bashi zuwa gobe koda sukai waya da safen yace masa ya basa sati ɗaya kafin ya dawo aiki ya shiga masa godiya kafin si sallama sai da rana tayi Hassan ya fita supermarket inda yake tunanin zai samu abubuwan da ta rubuta ,towel ya fara gani ya shiga duba sauran  farashin abubuwan da ta rubuta kaf ya lissafa ya ga lokaci ɗaya an tashi 270k sai da ya girgiza toh ko salary nasa bai kai ɗari ba nan hassan ya shiga shawara savings ɗinsa ne yake da kuɗi mai ɗan kauri shima karkaf zai yi idan ya ce zai saya mata daga baya dai ya kaso dubu arbain ya zazzabi wanda yake ganin sun zama dole turare ya sayo mata mai sauƙin kuɗi guda biyu sauran kuwa bai iya siya ba shower gel da su shampo kaɗai sun kai dubu sabain tana shingiɗe sai gashi ya shigo ta miƙe zaune ganinsa da leda ta harari fuskarsa kansa a ƙasa yayi sallama ta amsa a ciki ƙasan maƙoshi.


  Zama yayi ƙasan carpet ɗin yana ɗan ɗagowa daga gefe kusa da ƙafafunta ya ajje ledar ya ɗan sosa gira baya son disappointing nata da kyar ya iya samun kausashin fara magana.


 "Na sayo miki wasu kayakin amma ban samu na siyo miki wasu ba ,Jidda sunyi kuɗi dayawa aljihu na ba nauyi.Kinga idan nace zan saka kuɗi na duka na sayo tohm tarewar mu a gidan da nake mana gini zai yi nisa don zuwa nan da bai fi wata biyu ba nake son na kammala komai mu koma nan ɗin nasan a takure kike idan na saka savings ɗina na siya miki kayakin tohm daga nan har wata uku zamu iya kaiwa bamu tare ba  koma huɗu ya kika gani ?"Ta wani kallesa tana jawo ledar da ya siyayyar ta ciro kayan ciki ta ajje su kan gadon tana turo baki "Tohm sai na shafa wani man idan wannan ya ƙare?Haka zan ta zama ba zan wanke kai na ba ? Wannan turaren ma ni bansa ka siyon ba da barinsa kayi".Ta faɗa tana turɓune fiska "Kiyi hakuri sai a canja ki faɗi wani mai sauƙin kuɗin amma baki ce min komai ba gameda maganar ginin ai ni zaɓi na baki idan kin ce ayi amfani da wancen kuɗi sai na siyo maki".Ya furta a tausashe.


 "Duka nawa kuɗin item ɗin ya kama?"Ta tambaya tana kafesa da ido ya sunkuyi da kai "Ɗari biyu da sabain kuɗin savings ɗina kuwa ɗari uku da hamsin ne ,abinda ya rage a gidan kwayayen fitila ne da irinsu kan fanfo sai penti ina so kuma idan an samu rara na siya  maki fanka ta tsaye wasu abubuwan da zaki buƙata".



   Shiru Jidda tayi don ta raina kuɗin toh ko siya mata abubuwan yayi tana da sauran abubuwan buƙata kuma ta gaji da zaman cikin ɗaki ɗinnan "Ka barshi".Ta faɗa ya ɗan ɗago da mamakin amsarta "Nagode da fahimta".Ita dai bata sake cewa komai ba yace "Wanne zan canjo maki turaren?"


   "Kawai ka barshi".Ta faɗa tana tattare kayan da ya siyo ta tashi ta buɗe sif ɗin tana saka towel ɗin a ciki ya ɗago yana ɗan kallon ta daga tsayen da take ya saurin ɗauke ido ganin ta rufe sif ɗin.

 



>>>>>>>>>>>



   

   Ƙarfe sha ɗaya da ƙwata agogon bangon ya nuna Jidda tayi juyi a kan gadon tana juyar da kanta ɓangaren hagu kafin ta buɗe idanunta ,hasken rana da ya shigo take kalla yadda ya haske kan gadon ya tabbatar mata rana ta fito ta miƙe da kyar tana miƙa haɗi da kallon angogon ta kalli lokaci tayi guntun tsaki tana sauke idanunta kan ɗakin da ko ina tsaf ta san Hassan ɗin ne ya gyare shi yau sati uku da aurensu amma ko tsintsiya bata taɓa ɗagawa ba ,har kullum Hassan ke shara ya wanke toilet ya tsaftace ko ina ba abinda ya canja gameda tsanar auren da jidda take tun safe zata zauna ɗaki sai dai Anty Ruƙayya ta aiko mata abinci ta cinye zaman ɗakin ya fara gundurarta daga cin abinci sai bacci.Tashi tayi tsaye tana miƙe tsahonta ta leƙa window tana hango shanyar kayanta da Hassan yayi mata ta taɓe baki tana wucewa banɗaki duk kayanta da ta cire zai ɗauka ya wanke hakan ba komai ne a wajensa ba shekaranjiya ma tana kallo ya haɗa da nasa da na su Usman uniform ɗin makarantarsu ya wanke ya goge.Bayan ta gama uzurinta ta fito tana buɗe kwanukan abin karin safe da ya bar mata wani abun flour ne da bata taɓa gani ba ta dai ji ƙamshi har cikin hancinta shi ba fanke ba shi ba buns ba ta ɗanɗana tana taunawa taji kamar da ƙwai aka kwaɓa flask ɗan ƙarami ta buɗe ta zuba kunun gyaɗa ne lafiyayye  tasa a gaba  ta shanyesa Jidda abin daɗin flour biyu ta rage shima anjima zata cinye kafin na rana yazo Hassan tuntuni ya koma aiki  tana tsaka da wannan tunanin aka ƙwanƙwasa ƙofar waje tana jin muryar Amal ta amsa tana fita ta buɗe Yaseer ne ne ba sanin ƙanin Jidda tayi ba ta dubesa”Nan Ya Jidda take?"Ya tambaya Amal ta girgiza masa kai "waye?"Ta ji muryar Anty Ruƙayya a bayanta har zai juya ta kirasa ya kama sunan Ya Jidda a baki ta yi murmushi tace masa "Nan ne ka shigo"Amal ta matsa masa ya  shigo ciki  Anty Ruƙayya ce ta yi mata sallama a ƙofar ɗakin ta tashi tana buɗe ƙofar da kyau ta zage labilen ɗakin da murmushi a fuskarta tace mata "Kin yi baƙo yana parlour".


  Ba yabo ba fallasa jidda ta giɗa kai ta bi ta a baya tana zuwa parlour ta waro ido da mamaki haɗi da buɗe baki tana murmushi  "Yaseer nawa kaine daman?"Ta faɗo kujerar tana rungume shi yana kallonta a kunyace duk ta bashi kunya Amal sai kallonsu take tazo shigewa ɗaki Jidda ta dafa masa kafaɗa "Ina Umma? Ina Anty Baby mai yasa Abdallah bai biyoka ba”.


 Murya ƙasa ƙasa ya kalleta  "Umma bata san na zo ba Anty baby ta kwatanta mani gidan daga wajen ball nake".Jidda ta ɗaga gira "Allah da gaske ? "


 Tashi tayi suka fito waje ta kirasa ɗakinsu ko a jikinta ta sa ya zauna kan gadon tana tsaye sai jera masa tambayoyi take "Wayata fa? Tana wajen wa yanzu?"


 "Umma"Ya amsa mata Yaseer ya tambaya yaushe zata zo gida ta ɗan ɓata rai "Na kusa zuwa ,zan baka wasiƙa ka kaiwa Anty kaji kar ka min wasa da ita dan Allah".


Abin daɗin flour ta bashi ta leƙa waje ta ga giftawar Amal ta kirata yarinyar ta tsaya a bakin ƙofa "Je ki tambayi Ummanki idan da ragowar kunu a zubawa Yaseer” Ta faɗa Amal ta jinjina kai ta tafi ta kai saƙo wajen babarta Anty tayi murmushi "Sai dai na haɗa masa shayi wallahi kice ya ƙare na bawa Shafiha ragowa ɗazu".Amal ta dawo da shayi da Anty ta haɗa ta sa ta kawo mata a wani ƙaramin tea flask Jidda ta karɓa "Toh jeki"Ta faɗa tana sauke labilen ta shigo ta bashi hira tayi ta jansa dashi sai da ta ga ya  damu da ya tafi  ta rabu da shi ya tafi kar a gano ya  saci hanya wasiƙar da ta rubutawa Anty Baby ta sa masa a aljihu ta rakasa har waje tana kallon layin unguwar tasu wata kwata ta hanga da ta ke tsakanin layin ta yamutsa fuska ta komo ciki ta rufo ƙofar tana dawowa ɗaki duk ranta a daƙule Baba ya kawota akurkin gidannan kamar prison kaico da rashin wayon da tayi.Ta ke faɗa a ranta da bata biyewa Malika ba da ba haka ba Allah ya isa tsakaninta da ita.Jidda take ta saƙe saƙe a rai ,wanka ta shiga ta fito ta shirya hatta kayan sawar nata sun isheta ta gaji da ganinsu tunda ba yawa ne dasu ba.Tana ƙule a ɗaki tana jiyo yaran na harkokinsu a tsakar gida da rana bayan zuhr suka kawo mata abincin rana ta karɓe tana musu canji da kwanukan safe ba abinda ya dameta Amal ta kai bakin rariya ta kaɗa omo ta wanke.


  Hassan da yake wajen aiki tun huɗu hankalinsa ya yo gida baisan me yasa ba amma yanayin sa ya canja ba kamar da ba da lokacin ma yake ganin saurinsa Jidda tana ransa duk motsin da zai sai ya tuna ta da rigimarta ɗaɗinsa ɗaya bata sake ta da masa da maganar saki ba amma har yanzu bai san a wani matsayi zaman nasu yake ba.Ƙarfe biyar ya fito daga wajen aiki yana tahowa gida a hanya ya tsaya ya  saya mata kankana da abarba kulli biyu ya yo ya taho dashi tun a soro da ya iske Usman ya bashi ya kaiwa Ummansa ya shigo ɗakinsu ya yi sallama yana tarar da ita kamar koyaushe kansa a ƙasa sau ɗaya ya kalleta ya sunkuyi da kai fuskarsa da fara a yayi mata sallama….





Arewapen