Chapter 16
by @barista
BIYU A ƊAYA
(Don't judge a book by its cover?
Page 16
Sayyada Barrister
***
YOTA 13
TEAM FIVE INK LEGENDS
Kwarjini da kaifin idanunsa yasa ta sauke idanunta daga na shi, ta sauke numfashi duka a lokaci guda, ta rasa abin cewa, yana nufin ta bashi Alawa kamar yadda ta baiwa yaran...
"Ba za a bani bane?"
Jin sanyayar muryarsa da ya sakar mata a lokacin da bata yi zaton zai yi magana ba yasa ta ɗago kanta ta sake dubansa, jikinta ya yi sanyi ganin Alawar yake so yasa ta saka hannu cikin jakarta ta fiddo ta nuna masa alamun shi kake so? Ya ɗaga mata dukkanin giransa yana nufin eh, ta sauke numfashi a hankali ta ce
"Na sadaka ne"
Sautin muryarta ya ɗarsu cikin zuciyarsa, duk da bai san wacece ita ba, alamu sun nuna tana da nutsuwa, murmushi ya sake yi tare da sassauta muryarsa
"Ban chanchanci a bani sadaka bane?"
"Yara ke karɓa"
"Oh! Sai yau naji wannan batun daman ba a baiwa manya sadaka?"
"A'a ba haka nake nufi ba, waɗanda basu dashi what i mean masu buƙata"
Wani murmushi ya yi wanda bai san ya iya shi ba, har fararen hakwaransa suka bayyana, ya ce
"To ni ma me buƙata ne?"
"Ki bashi kyakkyawar Aunty, mutum kirki ne"
Suka jiyo muryar yaran suna musu magana, ta sauke idanunta daga na shi tare da cewa yaran
"Zan ba shi"
Ta dube shi sosai ta kurawa hannunsa idanu taga hannun hagu ya miƙa mata, ta ɗago tare da nuna hannunsa na dama ta ce
"Da hannun dama, ba na hagu ba"
Sai a lokacin ya an kare ya jinjina kai yana bin yaran da kallo suna shan Alawa, ya miƙa mata hannun dama, cikin nutsuwa ta ajiye masa biscuits da Alawa, ta ɗan yi baya, ta tsaya tare da takure jikinta...
"Kyakkyawar Aunty na gode"
Ta dube shi tare da jinjina kanta alamun ba komai, ta ce da yaran
"Na tafi sai gobe"
"Mun gode kyakkyawar Aunty bye bye"
Suka haɗa baki wajen faɗin hakan. Ta yi taku biyu zuwa uku taji muryar sa kusa da ita
"Kyakkyawar Aunty"
Ya faɗa a hankali, ta juyo taga sakaninsu da yaran akwai rata, kan ta idda mamakin tsaida ta da ya yi ta ji yana sauke mata addu'oi....
"Allah shi karɓa, Allah ya biya miki dukkanin buƙatunki mafi alkhairi, ya yaye miki damuwar da ki ke tare da ita ta koma farin ciki na har abada. Ya ba ki ladan ciyar da marayu da ki ke yi. Na gode da kyauta"
Ya goge mata hadda chak brain nata ya daina aiki, jikinta ya yi sanyi, ta yi farin ciki da wannan addu'oin da ya yi mata, ta manta when last da aka yi mata su....
"Bye"
Ta ji ya faɗa, ya juya zai koma wajen yaran don bai yi tunanin za ta yi magana ba.
"Amin thank you"
Ya juyo ba tare da ya ce komai ba, ta yi sauri ta bar wajen, ya dawo ya zauna kusa da yaren cikin kulawa ya ce
"Ya kamata ku tafi gida"
"Mu marayu ne"
"Na sani amma kuna da wajen kwana ai?"
"Eh a gidan marayu ba"
"Ku tafi"
Ya faɗa da gudu suka bar wajen. Ya kurawa Alawar idanu kamar me nazarin zanen dake jikin, ya jima a zaune sannan ya shigo cikin hotel ɗin.
********************************
Bilqees duk da ƙafarta nayi mata ciwo hakan bai hanata shirya abincin dare wa bakin su ba, kamar yadda suka saba haka su ka yi, an sharya komai bisa tsari. Bilqees ta koma side na Server's ta zauna, ALAJA ta shigo ta zauna tare da cewa
"Sannu Bilqees ya ƙafar ki?"
"Da sauƙi Maa"
"Allah ya ƙara sauƙi"
"Amin"
"Kin dafa abincin gargajiya?"
"Eh Maa, duk wani abin gargajiya na shirya shi"
"Yawwa good girl, ki ci abinci kada ki zauna da yunwa"
"Ok Maa"
ALAJA sai janta da hira take, suna zaune suka ji shigowar baƙin, nan suka fito ALAJA ta shige ɗaki, su kuma suka kula da dining area. Bilqees ta hango wannan mutumin likita yana zaune, tana ƙoƙarin isowa wajensa sai taga Majada ta je, da mamaki ta tsaya me ya kawo Majada cikin Server's?....
DR Waahab da ƙyar ya biyo abokansa zuwa restaurant, cewa ya yi ayi masa order amma Dr Faisal da Dr Isma'il sun ce a'a ba zayyu ba sai dai ya biyo su tun da abincin dare ne. Yana zaune ya ji an ce
"Yallaɓai"
Ya ɗago ba tare da ya ce komai ba, sai dai arɓa da ya yi da fuskar yarinyar da ta shigo masa ɗaki da safe, ya haɗe fuskarsa..
"Me kake buƙata?"
"Babu"
Shine amsar da ya bata a takaice, ta ɗan basar sannan ta ci gaba da cewa
"Anyway, in kana buƙatar wani abu, I'm here for you"
Ya ɗauke fuskarsa, tabar wajen, Bilqees ta kasa ƙarasa wajen shi tana kallon sa daga nesa har aka shirya masa abinci, ta taimaka a wani ɓangaren bata je ta inda yake ba, sai da ta kammala abin da take yi, sannan ta wuce kitchen ta haɗa masa shayin gargajiya ta kawo a nutse ta ajiye masa tare da cewa
"Yallaɓai bayan wannan akwai abin da kake buƙata"
A hankali ya ɗago jin wannan muryarta, bata bari sun haɗa idanu ba, ta kawar da kanta, ya kalli ƙafarta yaga kamar ta kumbura, saboda yanayin takalmi da ta saka...
"Ina buƙatar fruits"
"Ok"
Ta faɗa ta bar wajen yabi ƙafarta da kallo ganin kamar tana ɗingisawa. Bilqees ta shigo kitchen tana ƙoƙarin haɗa masa fruits, haɗaɗɗen fruit salad tayi masa ta rufe tana ƙoƙarin barin kitchen ɗin Majada ta iso tare da cewa
"Bilqees bani na kai"
Da mamaki ta dube ta ta ce
"Me zan ba ki"
"Abin da ki ka haɗawa wannan baƙon"
"Saboda meye?"
"Ina ruwanki"
Cewar Laraba, ta iso wajen, a nutse Bilqees ta kalli Majada bata ko kula Laraba ba ta ce
"Majada ina yin aiki nane Please kada ki katse ni"
"Ai sai ki ce mu bama aikin mu"
Cewar Jummai, still Bilqees idanunta akan Majada bata kallesu ba, don bata da lokacin hayaniya da kowa, jikin Majada yayi sanyi, ganin kallon da Bilqees ke yi mata na kada ki shiga harkata, ta fito ta barsu a tsaye ta shigo dining area, kai tsaye ta kai masa ta ajiye...
"Na gode"
"Uhm"
Ta faɗa tana shirya masa abinci a plate, taji ya ce
"Ya ƙafarki"
Ta sauke numfashi sai taji sanyi cikin ranta ko ba komai ya tambayi lafiyar ƙafar, amma tunowa da abin da ya yi mata a ranar yasa ta ce
"Da sauƙi"
Ta kammala shirya masa komai, sannan ta bar wajen.
Bilqees ta shigo side na Server's tunani fal cikin ranta na yadda za ayi ta miƙa masa wallet nasa, amma ta rasa gano hanyar ta saka hannu ta sake fitowa da shi ta buɗe ta kurawa photon dake jikin idanu na wani lokaci, ta dinga bin ID card ɗin ɗaya bayan ɗaya tana sake nazarin su, sannan ta maidasu cikin jakarta.
Tana ji har suka kammala cin abinci suka tafi.
Ita ma ta shirya ganin an fara komawa gida. Ta fito ta tadda Alaja ta kammala shirin tafiya, tare suka dawo gida, kasancewar dari yayi har Mamanta ta fara bacci Bilqees ta shigo da sallama da ƙyar Mamanta ta samu ta amsa basar bacci. Sai da ta watsa ruwa sannan ta kwanta.
************************************
Bayan kwanaki biyu, babu yadda Bilqees bata yi ba don ta samu hanyar basa wallet nata amma abin ya gagara, kasancewar baya cin abincin safe sai na dare, ta soma neman room number da yake a hotel ɗin, ta fahimci waiter Isyaku shike yawan kai breakfast hotel yasa ta tunkare shi ta tambaya waye da waye yake kaiwa abinci a hotel, ya bata amsa da sun kai mutum biyar, bata ce komai ba tabar zancen. Washegari da za akai breakfast hotel tabi ta ɗauki room numbers dake jikin food carrier, duka biyar ɗin ta ɗauka.
DR Waahab kwana biyu da yake breakfast a hotel yake jin hakan ya yi masa, baya son hayaniya, yanzun ma yana cin abinci ne OG ya yi kiransa a waya ya ɗauka
"Morning Sir"
"Dr Abdulwahab how was your morning"
"Alhamdulillah so good Sir"
"That's great, ka sanar anjima za mu yi meeting"
"Ok Sir"
"Aha by 2:00pm"
"Ba damuwa zan sanar"
OG ya katse wayar, Dr Waahab ya kammala breakfast 11:00am ya yi ya leƙo ta window yaga yaran suna nan kamar kullum, ya fito zuwa inda suke, sanye yake cikin shiga ta shadda ruwan biro yayi kyau sai ƙamshi yake tashi, ya iso ya tadda kyakkyawar Aunty na zaune, ya ɗan tsaya daga nesa yana kallonsu, tana yi musu magana kamar nasiha take yi, ya iso kusa dasu tare da yin sallama, ta amsa yaran ma suka amsa ya zauna ya kalleta yaga abin gabanta kawai take yi, ya sauke numfashi ta kammala raba musu Alawa bata bashi ba ya kura mata idanu, sai ta miƙa masa ya karɓa tare da cewa
"Allah ya karɓa kyakkyawar Aunty"
"Amin"
Yaran suna murna suna nuna masa, yana so ya yi musu siyayya amma rashin wallet nasa ne ya kawo masa cikas, yana mamakin a ina ya yada shi...
"Da fatan ba za ka cutar da yaran ba?"
Ya ɗan jinjina da jikin bango ya saki murmushi kaɗan a lokaci guda ya kuma cewa
"Me yasa zan cutar dasu?"
"Ni ma ban sani ba"
"Nayi kama da me cutarwa ne?"
"Ai basu da kama"
"Yadda kike jin tausayinsu haka ni ma"
"A'a ba zai zama ɗaya ba"
"Me zai hana?"
"Kowa da yadda zuciyarsa take"
Ya kurawa fararen ƙafafunta idanu ganin yana kallonsu yasa ta gyara ta rufe, ya ɗan basar be san me yasa yake son sanin ta ba, yana so yaga fuskar da take bayan wannan niqabin....
"Na tafi"
Ta mik'e da sauri zata bar wajen ya ce
"Kyakkyawar Aunty"
"Angel"
Ya ɗan ware idanunsa yana kallon, da mamaki ya furta
"Ango! Is that your name?"
"Yeah"
Ta faɗa tayi gaba. Ya sauke ajiyar zuciya ya dawo cikin hotel ɗin yana maimaita sunanta. Ya tadda Dr Faisal a ƙofar ɗakinsa suka shigo tare ya zauna yana ɗan miƙa..
"Ka fita shan iska ne?"
Dr Faisal ya tambaye shi. Dr Waahab ya bashi amsa da
"Eh, akwai meeting anjima by 2:00 pm in ji OG"
"Ka sanar ne?"
"Tun da akwai platform ai zan sanar yanzu"
"Yawwa don kada wasu su fice"
"Yeah"
Dr Faisal ya tafi, Dr Waahab ya ɗan kwanta tare da lumshe idanunsa kyakkyawar Aunty ke yi masa yawo a kai, zuciyar sa na zayyana mata siffarta, ya hau online ya sanar da meeting da za ayi, yana shirin sauƙa
Wayarsa tayi ringing yana dubawa yaga Ashfat ce ya ɗauka tayi sallama ya amsa tare da cewa
"Ya mutan gidan?"
"Suna nan lafiya Ya Waahab, ya aiki?"
"Sai godiya"
"Ka ci abinci?"
Ya yi shiru sai ka ce wani yaro take tambayar ya ci abinci, to haka zai zauna, amma ya ce
"Eh"
"Kada ka zauna da yunwa za tayi maka illah"
Ya ɗan yi murmushi yana likita take faɗa masa illar yunwa, ai sai dai shi ya sanar da ita.
"To in sha Allahu"
"Take care"
Faɗa a hankali ya ce
"Thanks"
Ta katse wayar, ya sauke numfashi, bacci ya ɗauke sa a yadda ya kwantan. Sai a zahar ya tashi ya watsa ruwa ya yi sallah, lokacin meeting na yi ya fito suka shiga hall dake cikin hotel ɗin...
Bilqees kasancewar baƙin nasu basa cin abinci rana yasa ta samu hutawa sosai, sai bayan la'asar ta shiga kitchen, aiki tayi sosai ta shirya musu abinci na gargajiya saboda ta fahimci yawancin su suna so, sauran aikin kuma ta barwa su Laraba da Jummai suke ta yi sun saka sauran ma'aikatan a gaba suna cewa suyi wannan su bar wancen har suka kammala.
8:00 pm yana yi Dr Waahab suka shigo cikin restaurant ɗin, sun samu tarɓa kamar kodayaushe, sai dai yau duk abin da yake buƙata yaga an jera masa already ya sauke numfashi shayi ya zuba yana kurɓa, sannan ya ci abinci sama sama, yana kallon sauran mutanen su sai hira suke suna nishaɗi, sai 9:00 pm suka tafi. Bilqees suka dawo gida.
*********************************
Bilqees babu yadda ba tayi ba ta haɗu da wannan mutumin likita amma abu ya gagara, ta yanke shawarar zuwa hotel ɗin da kanta a wannan safiyar ta miƙa masa wallet nasa, sai da ta tabbatar sun kammala tarɓan baƙin sun wadata su da duk abin da suke buƙata, waɗanda basu zo ba kuma an shirya musu nasu za a kai musu, waiter Isyaku da sauran ƴan rakiyar sa suna fita da breakfast tabi bayansu, suka shiga ciki ita ma ta shiga tana bin su a baya ba tare da sun sani ba, ganin bangaren da suka kai abincin yasa ta dakata har sai da suka kammala suka tafi sannan ta soma bin ɗakin tana nocking da an fito sai taga ba likitan bane, sai ta yi gaba a haka ta iso ɗaki na huɗu tayi nocking jim kaɗan aka buɗe ya leƙo ganin ma'aikaciyar RESTAURANT ɗin ne yasa ya ɗan haɗe fuska, bai bata damar shigowa ba, ya tsaya a bakin ƙofar yana sauraron ta...
"Barka da safiya"
Ta faɗa zuciyarta na bugawa, tsoro ya mamaye ta ga kwarjini da ya sake cika ta dashi..
"Yawwa sannu"
Ya faɗa a hankali ta ce
"Daman ranar da naji ciwo ne, kuma ka duba ƙafata, har ....
"Kin ga dakata, wannan maganar ta wuce, kuma na yi miki kashedin kada ki sake zuwa inda nake, to me yasa za ki kawo kan ki masaukina"
Daram ƙirjinta ya buga, me yake nufi da wannan maganar? Jikinta yayi sanyi, hankalinta ya tashi....
"Don haka ki yi tafiyarki kada ki sake zuwar min masauƙi"
Sabar ɓacin rai kamar ta sunduma ihu, wannan ai cin mutunci ne, shi bai saurari da me ya kawota ba kawai ya yanke mata hukuncin kawo kanta tayi, cikin ɗacin rai ta ce
"Ka bani mamaki, me yasa za ka fassara zuwana da kawo kaina gare ka? Kasanni ne? Babu wata alaƙa da ta taɓa shiga sakaninmu amma kake jifata da wannan abin"
Ransa ya sake ɓaci, me yasa ne ma'aikatan Alaja restaurant basu da kunya, haka wata ta kawo kanta gare shi babu kunya babu tsoron Allah, shine ita ma wannan tazo ta gwada sa'arta...
"Me ya kawo ki? Ina cin abinci ne sakanina daku, kuma an kawo min, sannan gaki a tsaye babu ko kofi a hannunki balantana plate"
"Shi kenan na gode, laifi na ne amma daga yau ba zan sake zuwa inda ka ke ba"
Ta fiddo da wallet nasa ta miƙa masa tare da cewa
"Ga abin da ya kawo ni"
Jikinsa yayi mugun sanyi, ya ɗan runtse idanunsa ya buɗe yana bin wallet dake hannunta da kallo tabbas nasa ne, a ina ta samu, a hankali ya karɓa, yana jujjuyawa..
"Daga yau ka fara jin uzurin mutum kamin ka yake masa hukunci, amma tabbas ka ɓata min rai"
Ya rasa abin da zai ce, har ta juya cikin ɓacin rai zata bar gurin, sai kuma ta tsaya tare da juyowa ta iso kusa da shi tare da cewa
"Don't judge a book by its cover, Dr Abdulwahab Waseem KIRAWA"
Ta juya ta yi tafiyarta ta bar shi nan tsaye ka ƙame kamar an shuka shi.....
Ayi hakuri da typing errors.
Comments and share fisabilillah