Matukar Ina Raye 5
by @mrsisham12
MATUKAR INA RAYE
(As Long as I’m alive)
Writer — MRS ISHAM
*** whataspp.
Page 05
“Zubar da wannan cikin shi ne babban kuskuren da za ki tabka a rayuwarki. In za ki gwada sau dubu, to fa za ki yi rashin nasara sau dubu, kuma za ki sha matuƙar azaba sau dubu. Shi wannan cikin ba zai taɓa fita ba, dole sai ya zo duniya, ko da kuwa hakan na nufin rasa taki rayuwar. Ba ki da ikon hana hakan. Allah ya ƙaddara wannan ɗan tayin sai ya zo duniya, ya yi rayuwa kamar kowa, kuma babu abin da zai canza hakan.”
Cikin hawaye Ummah, da take jin an daure mata baki, ta fisgo magana da ƙyar.
“Amma me yasa? Ba a kaina aka fara zubar da ciki ba, me yasa nawa ya zo da haka? Allah ya san yadda nake shan wahala ni da yayana, shi ya sa nake son kubutar da wannan ɗan tayin, don kada shi ma ya zo ya sha wahala irin yadda muke sha. Hakan zai sa ni cikin ƙunci.”
Murmushi ya yi ya dafa kafaɗarta.
“Na sani, Maimunatu. Amma dole za ki haifi wannan cikin. Allah ya riga ya ƙaddara mai rayuwa ce, kuma rayuwa mai tsayi da ƙalubale tare da tarin nasarori. Kina son sanin wani muhimmin abu kuma? To, kalli can.”
Ya ɗaga yatsarsa yana nuna mata gefen da yaran suke. Nan idon Ummah ya sauka a kan wani kyakkyawan yaro wanda ba zai wuce shekara goma ba a duniya. Yana zaune shi kaɗai cikin ƙunci, ƙafarsa a ɗaure da ƙaca, ya haɗe kai da guiwa, a yayin da sauran yaran ’yan uwansa suke wasa, amma shi yana can zaune cikin kaɗaici da ƙunci.
“Kin gan shi ko? To, abin da ke a jikinki ita ce mahadar rayuwarsa, ita ce garkuwarsa, kuma madubin haskawarsa. Ita ce maganinsa ga duk wata damuwarsa, kuma ita ce za ta warware duk wani kulli na cikin rayuwarsa.
“Haka zalika wannan yaro shi ne mahadin rayuwar abin da ke jikinki. Shi ne garkuwarta, shi ne kariya gare ta. Don haka ke ba ki isa ki raba su ba tun kafin ta zo duniya.
“Kwanciyar hankalinki shi ne ki mayar da hankali wajen ba ta kulawa da raino, wanda sai kin yi haƙuri matuƙa. Ki tuna da wannan, akwai ƙalubale masu yawa da za su tunkaro ta, waɗanda ke ba ki isa ki kare ta daga gare su ba, Maimunatu. Ki zama mai tunawa da hakan a ko da yaushe.”
Dariyar yaran da tsohon suka saka mata, muryoyinsu na fita bibbiyu. Nan ta ji jiri ya ɗibeta.
“Ya Allah…” ta faɗa tana ƙoƙarin faɗowa a kan gadon da take kwance. Da sauri Baba Karami ya riƙota yana mata sannu, shi da Salma da kuma Baffah, domin su ne a ɗakin tare da ita.
Jin muryoyinsu ne ya sa ta buɗe ido ta dube su, tana kuma kare wa ɗakin kallo. Nan ta fahimci a asibiti take, kuma mafarki take yi a ɗazun ɗin, yanzu kuma tana cikin zahiri.
Baffah, da likita ya sanar masa dalilin zubar jinin da ta yi, tare da tabbatar masa cewa cikin yana nan lafiya ƙalau, nan ya shiga surfa mata bala’i tare da cewa,
“Haba Maimuna, kin ba ni kunya. A ce duk yadda nake ƙaunarki da fifita ki, shi ne za ki yi ƙoƙarin zubar da jinina? Ashe dama akwai ƙiyayyata a ranki ban sani ba? To ko su Sadiya da ƙiri-ƙiri suke nuna min bakin hali, ai ba su yi abin da ke kika aikata ba, tunda duk suma suna da ciki, amma ba su yi yunƙurin zubarwa ba.”
A nan ne Ummah ta san suma suna da ciki.
Haka ya ƙarasa faɗarsa. Ita kuwa ba ta ce da shi ci kanka ba. Haka ta gama kwanakin da aka kwantar da ita har aka sallame ta.
Bayan ta koma gida, abin da ya faru cikin mafarkinta ya tsaya mata a rai sosai. Amma da ta tuna cewa mafarki ai ba gaskiya ba ne, sai ta cire al’amarin a ranta cak, ta fuskanci zahiriyar rayuwa.
Mama Jamila ce ta fara haihuwa, aka sa wa yarinya suna Rabi. Bayan wata uku kuma Ummah ta haifi yarta mace, yarinyar da babu abin da ta baro na Ummah, har ma za a iya cewa ta fita, domin kyakkyawa ce ta bugawa a jarida kamar ba ’yar mutum ba.
Ba za ka taɓa ganin ta da Baba Karami da Salma ka ce ’yan uwanta ba, saboda su duk kamannin Baffah suka kwaso.
Ranar suna, Ummah da kanta ta zaɓa mata suna, aka sanya mata Waheeda.
Haka Mama Sadiya ita ma ta haifi mace, aka rada mata suna Ikilima.
Tun Waheeda ta fara girma ta soma gwada musu nata kuruciyar yadda ya zo, domin ba ƙaramar rigimammiyar yarinya ba ce. Ga neman tsokana da dukan yaran mutane, har ’yan uwanta su Ikilima ba ta ƙyale ba, duk da kan su ɗaya. Amma ba ta raga musu mugunta iri-iri ba wanda ba ta musu, har ’yan makarantar su ba ta bari ba. Ga ta da rashin kunya da tsiwa tun ba ta wuce shekara takwas ba.
Tun Ummah na mata duka idan ta yi abu, har ta koma yi mata addu’a, domin lamarin Waheeda kullum cikin ƙara girma yake. Ga shi Ado, kaf cikin ƙannensa, ya fi ji da ita. Ko ta yi abu idan ana dukanta, shi ke tare mata. Hakan ya sa ba ta tsoronsa, kuma ta fi sakewa da shi fiye da Baba Karami da suke ciki ɗaya, domin duk duniya, idan a mutane ne, babu wanda take tsoro irinsa. Ko Ummah ba ta tsoranta kamar yadda take tsoron Baba Karami. Baffah kam ta mayar da shi tamkar Kakanta Mallumjo.
A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, inda Mama Jamila ta kuma haihu, ta haifi yara maza ’yan biyu, Habibu da Musa.
Baba Karami ya buɗe shago da taimakon Kakansu Mallumjo. Ya ba shi kuɗi ya buɗe shagon kayan sanyi da kuma caji, domin tun da ya gama University bai samu aiki ba, haka yake ta buga-buga. Ganin haka ne ya sa Mallumjo ya buɗe masa shago. A lokacin kuma Ado na ajin ƙarshe a University, shi ma da zarar ya gama za a buɗe masa nasa shagon.
Rayuwa ta sauya, inda a hankali Baffah ya soma samun ƙarayar arziki. Ya zama babu abin da yake da shi da ya wuce wannan gidan da suke ciki. Duk ya sayar da kadarorinsa ya biya bashi, sannan kuma an yi amfani da sauran kuɗin wajen tafiyar da gida. Sosai suka shiga matsin rayuwa, inda aka cire su Waheeda a makarantar kuɗi suka koma ta gwamnati. A lokacin su Salma sun gama secondary.
Nan da suka ga idan suka ci gaba da zama a haka, to fa komai zai gagare su. Duk da a haka ma Baba Karami shi yake kawo kayan cefane, amma duk ranar da bai samu ba, haka duk suke zama da yunwa har sai idan Mallumjo ya turo musu da kayan abinci.
Wannan dalilin ya sa Mama Sadiya ta fara daurawa Zuwaira talla. Ummah kuwa, ba don ranta na so ba, ita ma ta soma daurawa Salma talla. Idan sun yi abin tallan ne suke samun abin da za su ci a ciki.
Mama Jamila kuwa, wata yarinya ta yi haya tana mata talla tana biyanta.
Da wannan suka samu suke rufawa kansu asiri su ci, har ma shi Baffah ya ci. To tun da ya ga haka, ya kashe zuciyarsa ya daina neman aiki. Ya dogara da abin da suke yi da kuma kuɗin da Baba Karami ke ba su. Ya koma ba ya yin wani aiki da ya wuce zaman majalisa.
Ita kuma Waheeda, wannan tallan da su Salma suke fita ne yake burgeta. Ta yi ta yi Ummah ta soma daura mata, amma ta ƙi. Daga ƙarshe ma, suna gama primary, Ummah ta cireta a makarantar gwamnati ta sanya ta a makarantar kuɗi saboda suna samun rufin asiri da kuɗin tallan.
Ganin haka ya sa su Mama Jamila ma suka mayar da ‘ya’yansu zuwa makarantar kuɗi, inda suka haɗu da Waheedatu.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Allah Ya ba Mallumjo ikon haɗa auren Baba Karami da Labiba.
Labiba ta kasance ’yar maƙwabciyar Mallumjo ce. Tana zaune ne da kishiyoyin mahaifiyarta. Ganin irin wahala da azabar da take sha saboda rashin uwarta a gidan ya sa Mallumjo ya ji tausayinta, saboda tana da hankali da nutsuwa. Wannan dalilin ya sa ya nema wa Baba Karami aurenta.
Ba tare da gardama ko nuna baya so ba, Baba Karami ya amince da auren nasu saboda yana matuƙar son Kakansu Mallumjo.
“Ummah…” Baba Karami ya katse mata tunanin da take yi ta hanyar kiran sunanta.
Zama ya yi a gefenta yana riƙo hannunta. Ita kuwa ta zuba masa ido, ba tare da ta amsa kiran da ya mata ba.
“Ummah, na san ba ni kaɗai al’amarin Waheedatu yake damuwa ba, ke ma yana damunki, kawai ba kya nunawa ne. Iya ƙoƙarinmu muna yi a kan yaran nan da wannan gida, amma ita ta fita daban, rashin ji uwa jaririyar shaidanu.”
Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta furta,
“Kai ma da bakinka ka faɗa, Babana. Ta fita daban. Waheeda ba kamar sauran ’yan uwanta ba ce. Yarinta ce kawai yake dawainiya da ita, amma daga zarar ta balaga ina sa ran za ta nutsu, in sha Allah.”
Murmushi ne ya subuce masa ba tare da ya shirya ba.
“Nima ina fatan hakan. Ko aure za ki mata idan ta girma ɗin, eh Ummah?” ya faɗa ta sigar zolaya.
“Ah ah, Babana. Ina da burin ta yi karatu sosai ta zama likita. Shi ya sa na mayar da ita makarantar kuɗi. Ina son Waheeda ta zama wani abu a rayuwa, kuma ina ji a jikina ɗin za ta zama.”
Murmushi ya kuma yi yana kallon fuskar mahaifiyarsu, yana hango tsananin ƙaunar Waheeda a cikin idanunta da yadda take da buri sosai a kanta na ganin ta zama wata mace abar kwatance a rayuwa. Shi ma yana fatan hakan saboda ita ce ƙarama a cikinsu.
“Allah Ya amsa hakan, Ummah. Bari in samu in tafi. Ina so in tsaya a hanya in siyawa Labiba magani.”
Ya faɗa yana miƙewa.
Cikin kulawa ta furta,
“Ka gaishe min da ita da jiki.”
“In sha Allah.”
Ya bar ɗakin. Yadda ya barta haka ya fito ya tarar da ita gwafe. Sai ya yi ganin yadda idonta ya yi ja tsabar kuka da wahala.
“Ba kin ce ba ki jin magana ba? Zan yi maganin fitsarancinki.”
Yana gama faɗin haka ya fice a gidan.
Ya Ado ya dagata yana karkade mata rigarta. Cikin sanyin murya ya furta,
“Je ki ba wa Ummah haƙuri, ki ce ba za ki sake ba.”
Simi-simi ta wuce ɗakin Ummah. Ganin ta shigo mata ɗaki tana raƙube-raƙube a jikin bango ne ya sa ta ce,
“Lafiya kam?”
Murya a sanyaye ta ce,
“Ummah, don girman Allah ki yi haƙuri, ba zan ƙara ba.”
Fuska a tsume Ummah ta ce,
“Na ji. Zo ki zauna a nan.”
Zama ta yi kusa da ita tana jiran ta ji me za ta ce.
Sai da ta karance ta na wasu daƙiƙu, kana ta soma faɗin,
“Waheeda, kina so in mutu ne?”
A firgice ta ɗago ta kalleta. Ummah ta gyada kai sannan ta ci gaba da faɗin,
“Eh mana. Kin ga idan na mutu sai hankalinku duk ya haɗu ya kwanta. Da wanne kike so in ji? Da rayuwar wannan gida da nake zaman haƙuri, ko kuma da maganar da kike jawo min a waje? Idan jinina ya hau na faɗi na mutu, na san daga sannan za ki yi hankali.”
A tsorace take kallon Ummah, wanda ita kanta Ummah sai da ta fahimci maganganunta sun yi tasiri a ranta.
“Ba zan ƙara ba fa, Ummah. Ki daina faɗar haka. Ni ba zan iya rayuwa a duniyar nan ba idan babu ke.”
Murmushi ta yi ta jawo ta jikinta ta rungume, tana shafa bayanta ta ce,
“Allah kaɗai Ya san gawan fari, Waheedatu. Shi ya sa nake so ki samu ingantacciyar rayuwa, yadda ko ba na raye ba ba za a wulakanta ku ba, ke da Salamatu, tunda ku ne mata. Kin ga rayuwar gidan nan dai yadda take. Wannan dalilin ya sa nake fatan ki zama abar kwatance yadda kowa zai dinga alfahari da ke a rayuwar nan. Amma sam kin ɗauko hanyar da ba za ta bulle miki ba. Na rasa a ina ne kika koyi rashin ji.”
Ɗagowa ta yi ta dubi fuskarta sannan ta ce,
“Ummah, na miki alkawari ba zan ƙara ba. Zan zama good girl.”
Duk da ta san alkawarin Waheeda kamar alkawarin ’yan siyasa ne kafin su ci zaɓe, bayan an ci zaɓen kuma su watsar, sai kawai ta yi murmushi tare da faɗin,
“To Allah Ya sa, da na fi kowa farin ciki. Yanzu ki tashi ki je ki haɗa kayan wanke-wanke ki dauraye su. Idan omon ya yi saura sai ki wanke kayan makarantarki.”
Miƙewa ta yi tana cewa,
“Ummah, duk da omon naira hamsin ɗin za a yi wannan?”
“Je ki fara. Idan bai isa ba sai a kuma siyo wata ta hamsin ɗin.”
Lokacin da ta fito ta samu har Salma ta gama suyan awara ta shiga wanka. Ya Ado kuma ya tafi. Su Rabi ne da su Mama Jamila a cikin gidan, domin Zuwaira ma an gama mata suyan kayan tallanta, tana ciki tana kwalliya.
Babu wanda ta kula a cikinsu. Ta sunkuya ta soma tattare kwanukan da za ta wanke. Sai da ta gama haɗa kwanukan tsaf, za ta wanke, ta je diban ruwa a drum ta ga wayam babu ruwa. Ko hijabi ba ta tsaya sawa ba, ta sunkuci bokiti ta fita.
Famfon gidan wata mata da ke gaba da gidansu kaɗan ta je, nan ta samu layi.
Kutsawa cikin layin ta yi ta dire bokitinta tana haɗe rai. Duk kallonta suka yi.
Wacce take kan dibawa ce ta ce,
“Ikon Allah, Waheeda! Ke da kika zo a ƙarshe, shi ne za ki turo robarki nan? Kin san fa an riga ki.”
“Antyn Safara’u, magana ta gaskiya ba zan iya bin layi ba. Sauri nake, zan je in soma wanke kwanuka.”
Ta faɗa tana kuma matsar da bokitin gaba.
Wacce aka kira da Antyn Safara’u ta ce,
“To ai ba haka ake yi ba. Alfarma za ki nema, idan an baki to.”
Tana turo baki ta furta,
“Yooo, ai bokiti ɗaya nake so, ba randa ko drum zan cika ba.”
“Sai ki jira ki diba ai, fitsararriya kawai.”
Cewar wata budurwa tana watsa mata harara.
Buɗan bakin Waheeda sai cewa ta yi,
“Kin san wacece fitsararriya ai.”
A hassale budurwar ta cakumo gaban rigarta tana…
“Ke, ɗan ubanki me kike nufi?”
Cikin rashin tsoro, duk da ganin yarinyar ta girme mata nesa ba kusa ba, ita ma ta cakumo rigarta tana cewa,
“Ba dai nawa uban ba, sai dai ubanki mai zama a ƙofar gida yana busa sigari.”
Wani mari ta ɗauke ta da shi kafin Waheeda ta dawo hayyacinta. Yarinyar ta kuma falla mata wani.
“Ni sa’ar ki ce da za ki zagi ubana. Wallahi yau sai na cire miki rashin kunyar da kike ji da ita.”
Waheeda da ta ji zafin marin har cikin ranta ne ta samu hannun yarinyar ta gantsara mata uban cizo, wanda ya sa sai da ta saketa saboda azaba.
Ganin haka ya sa Waheeda ta rungumeta tana kai mata naushi ta ko’ina. Haka suka kai ƙasa suna dambatuwa.
Babu yadda mutanen wajen ba su yi ba, amma sun kasa raba su. Ga filin wajen yashi ne fara, duk sun yi futu-futu da jikinsu. Da ƙyar wani babban mutum ya banbare Waheeda daga jikinta.
Mutumin ne ya dube ta ya ce,
“Haba Halima, ke kuwa me zai haɗa ki dambe da ƙanwar bayanki? Idan rashin kunya ta miki, ai wajen iyayenta za ki je ki kai ƙara. Amma wannan ai jawa kanki raini ne, a ga kina dambe da sa’ar ƙanwarki.”
Halima, da hawaye ya cika mata idanu, ta ce,
“Zagi na fa ta yi saboda na mare ta, shi ne ta cije ni. Duba fa ka gani, har jini wajen yake yi. Shegiyar yarinya, mayya!”
Ko digon hawaye babu a idonta. Ta dubeta da kyau, ta riƙe ƙugu tana jijjiga jiki kamar wata katuwar budurwa.
“Ni dai ba mayya ba ce, sai dai uwarki, Uwani dallaliya, ita ce mayya. Kuma wallahi ban barki ba sai na rama marin da kika yi min, muguwa, azzaluma, algunguma!”
Riƙe haɓa Anty Safara’u ta yi tana kallon Waheeda. Mutumin kansa ya gagara magana da ya fahimci yarinyar ba kunya ce ta wadace ta ba.
Hakan ya sa ya ce wa Halima ta tafi gida kawai.
Gudun kada ta kuma yin faɗa da sauran yaran wajen ya sa suka cika mata bokitinta, aka ɗaura mata. Ta nufi gidansu jikinta futu-futu, kamar wacce aka kwato daga bakin kura.