MATUKAR INA RAYE

Matukar Ina Raye 6

by @mrsisham12


MATUƘAR INA RAYE
(As Long as i’m a Live)

Writer — MRS ISHAM
*** (WhatsApp)



Page 06


Ummah na tsakiyar gida tana alwala ta ga shigowar Waheeda da ruwa ɗauke a kanta. Jikinta kuwa ba a magana. Ba ta kula ta ba, ta ƙarasa alwalarta ta shige ɗaki.

Ko tunanin sauya kaya ba ta yi ba, ta haɗa kwanukan ta wanke su tass, ta jera su cikin kwando. Cikin ikon Allah, omon da ta yi wanke-wanken ya yi saura, da shi ta dauraye uniform ɗinta ta shanya.

Jin gidan shiru da ta yi ta san su Salma sun tafi talla, su Mama Sadiya kuma kowa ta ja yaranta ɗaki.

“Ummah, ina abincina?”

Idar da sallah ta kenan, tana zaune a kan sallaya. Waheeda ta shigo tana tambayar abinci. Ba tare da ta ɗago kai ta kalli inda take ba, ta ce,

“Wuce ki je ki yi wanka. Kazama kawai.”

Tana bubbuga ƙafa ta ɗauki soso da sabulun Camaroon ta je ta yi wanka.

Ɗakinsu da suke kwana ta shiga. Inda Ghana Must Gon kayanta yake ta je ta buɗe, ta fito da wata doguwar rigar shadda mai ruwan maroon ta sanya. Ta kuma saka hula a kanta tana cusa bindin kitsonta da suke fitowa waje ciki.

Ko sallama babu ta faɗo ɗakin.

“Ummanmu, na yi.”

Girgiza kai kawai Ummah ta yi. Ta jawo kwanon abinci daga ƙarƙashin gado ta tura mata gabanta.

Zama ta yi ta buɗe murfin tukunyar da aka rufe kwanon da shi. Washe baki ta yi ganin shinkafa da wake mai da yaji.

Fuska ɗauke da murmushi ta ce,

“Ummanmu, Allah Ya miki albarka. Dama ina ta addu’a Allah Ya sa ba koko ba ne ko miyar kuka.”

Dariya ta so ba Ummah yadda take magana kamar wacce aka ajiye wa dunkulen kaza a gaba.

“Idan kuka ce, an jima ita za a sha ai.”

Sai kuma ta marairaice kamar za ta sa kuka jin an ambato mata sunan miyar kuka.

“Ayya, to ni me zan ci Ummah? Wallahi ni dai ba zan ci miyar kuka ba.”

Tabe baki ta yi tana cire hijabin da ta yi sallah.

“Na rage miki ɗan guntu a tukunya. Yana ƙarƙashin gado. Idan Salma ta dawo da ƙwantain awara sai ki ƙara da shi ki ci.”

A take kuwa murmushinta ya dawo, ta soma cin abincinta.

“Assalamu alaikum! Assalamu alaikum! Ko dai babu kowa a gidan ne?”

Fitowa Mama Sadiya ta yi tana murmushi.

“Haba Sabuwa, wannan irin doka sallama? Ke da za ki shigo ciki kawai.”

“Ke dai bari kawai, aminiyata. Ni da kika gan ni nan sauri nake. A ƙafata nake, zan je taron siyasa. Shi ne na ce bari in tsaya in ba ki kuɗin adashen nan tun kafin in kashe su.”

Jawo hannunta ta yi tana cewa,

“Ahhh, da gaskiyarki. Amma dai mu shige daga ciki. Kin san gidan akwai ’yan tsurku da sa ido.”

Dariya suka sa suna tafawa sannan suka shige ciki.

Buɗe pos ɗinta ta yi ta fito da kuɗi. Ta ƙirga su, naira dubu biyar, ta damƙawa Mama Sadiya. Ita ma ta sake ƙirga su.

“Kuɗin sun cika cif-cif, aminiya. Gaskiya ina jin daɗin adashe da ke. Babu leti, babu komai.”

Tana kaɗa kai ta ce,

“Aka ce miki ni wasa ce? Ni kam aminiyata, yau gidan naku shiru haka. Ko dai mutanen naki ba sa nan ne?”

Yatsina fuska ta yi ta ce,

“Wallahi suna nan. Kowacce munafukar tana ciki, ita da yayanta. So nake ma in fita in haɗo sauran kuɗin adashe na, sai ga ki kin shigo.”

“Cabb! Kishiya ko masifa. Ni ina ganin ƙoƙarinki ma. Kin san wallahi da ni ce, ba zan zauna da kishiya ko kwara ɗaya ba, balle har biyu. Tuni zan fitar da su. Ke, ni fa mijina, shi da sake aure sai dai a lahira. Wallahi na gama da shi.”

“To ai gwara ke sau dubu, Sabuwa. Mijinki yana da shi, yana muku komai. Kin ga kuwa sai yadda kika yi da shi. Wannan mai ma na sama ya ci balle ya ba na ƙasa. Kina gani a gidan nan, mu muke yin komai. Har ma shi mu muke ciyar da shi. To me zan tsaya bata lokacina wajen mallake shi? Uban me zai min? Na fi jin daɗi ina zaune da yayana muna neman kuɗinmu. Ba boka, ba malami. Idan kishiyoyi kuma suka min, in ci kutumar ubansu ba daga ƙafa.”

Dariya Sabuwa ta saka tana dafa ta.

“Gaskiya kam. Kar ki daga musu ƙafa kam. Duk wacce ta ce za ta yi da ke, ta hau cikin ’yar banza, ki turmusheta.”

Mama Sadiya ta ce,

“Yooo, tun yaushe. Bari in ɗau hijabina mu fita tare.”

“Ah ah, ba ruwana. Kar mijinki ya ce daga zuwana har za ki fita.”

“Ke dallah, share shi. Mu je kawai.”

Fitowa suka yi. A ƙofar gida suka tarar da Baffah zaune shi da abokansa. Ya ga fitowarsu, ko inda yake ba ta kalla ba, balle ya sa ran za ta tambaye shi izinin fita.

Wani abokin Baffah mai suna Baba Rabe ne ya jijjina kai cikin mamaki ya ce,

“Yanzu Baffah, lalacewarka har ya kai matarka ta wuce ta gabanka a kan idonka ta tafi anguwa ba tare da ta tambaye ka ba?”

“To ai wannan kaɗan ka gani, Rabe. Dukkansu biyu haka suke. Sun gama raina shi. Ita uwar su Salamatu ce kawai take da hankali. Matuƙar za ta fita, sai da yardarsa. Amma ka ga Jamila da Sadiya, yadda ka san zaman kansu suke yi.”

Cewar Malam Audu.

Siririyar iska Baffah ya fesar tare da faɗin,

“Inda sabo ya kamata a ce na saba zuwa yanzu. Matan nan biyu sun fi ƙarfina yanzu, yadda ka san ba ni ne mijinsu ba.”

Murmushi Malam Zakiru ya yi. Tun da suka fara maganar, bai ce musu komai ba sai yanzu da Baffah ya yi magana.

“To ai idan za a bi na barawo, a bi na mai kaya. Kai ne nan ka bata gidanka tun farko, Baffah. Kar ka manta fa, waɗannan matan su suke ciyar da kansu kuma suke ciyar da kai. Babu abin da kake yi a gidan. Sun koma mazan kai, kai kuma ka koma matar gida. Da a ce ba ka kashe zuciyarka ba, kana kawo musu ɗan cefane, ko ba yawa, to tabbas ba za su bokare haka ba.”

Ko da suka gama sauraron Malam Zakiru, Malam Audu ya ja tsaki.

“Ashsha! Ashsha! Haba Malam Zakiru, sai ka ce ba ka sani ba. Mata nawa ne suke ciyar da kansu da mijinsu, har ma da iyalan mijinsu, kuma suke girmama mazajensu? Su na nan birjik a ko’ina. Don kawai ya samu karayar arziki ba shi yake nufin shi kenan ba ya da sauran daraja a idanunsu. Su dai kawai sakarkarun mata ne.”

Sosai wannan magana ta Malam Audu ta tsaya wa Malam Zakiru a wuya. Sam bai ji daɗi ba. Ɗaukan carbinsa ya yi ya miƙe tsaye tare da faɗin,

“Ni dai zan faɗa maka gaskiya. Idan za ka nemi sana’a, ka nema domin dawo da martabarka a cikin gidanka ku huta lafiya.”

Ko daƙiƙa ɗaya bai ƙara ba ya yi gaba abin sa.

“Meyasa nake ji kamar Malam Zakiru baƙin ciki yake maka ne? Yoo, idan ba baƙin ciki ba me za a kira wannan? Haushi yake ji, shi matansa ba sa yi masa komai, shi ya sa.”

Cewar Baba Rabe.

Washe baki Baffah ya yi ya ce,

“Ahhh, to idan fitsari banza ne, kaza ma ta yi mana.”

Karfe uku na yamma, Ummah ta sa Waheeda ta shirya cikin uniform ɗin makarantar allo da suke zuwa.

Ɗaukan allonta ta yi tana cewa,

“Ummanmu, sai na dawo.”

“To, ’yar albarka, a dawo lafiya. Ki leka ɗakinku ki ce wa su Ikilima maza su tashi ku wuce Islamiyya.”

“To.”

Kawai ta faɗa tana nufar ɗakin. A kwance ta same su suna barci. Ganin za su bata mata lokaci ne ya sa ko tashin su ba ta yi ba, ta fita tana cewa,

“Oho dai, na tafi. Idan sun tashi daga asararren barci sai su je.”

Inda su Baffah suke zaune ta je ta ja burki ta tsaya.

“Baffah, zan tafi Islamiyya. Ka ba ni murtala in siya alewar madara.”

“Ina sauran ’yan uwanki?”

Baffah ya tambaye ta yana zaro murtalan a aljihun babban rigarsa.

Sai da ta karɓi kuɗin kafin ta ce,

“Su na barci.”

Ta wuce.

Ba su suka tashi a makaranta ba sai shida saura aka taso su. Suna tafiya, ita da kawarta Safara’u, suna tsokanar wannan suna tsokanar wancan har suka iso.

Waheeda ta shiga gidansu, ita ma Safara’u ta wuce nasu gidan.

Salma, dake zaune tana hira ita da Zuwaira, ce ta ga shigowarta.

“Yawwa, dama ke nake jira. Zo ki ga abin da na kawo miki.”

Da sauri ta iso don ganin mene ne.

Buɗe jakarta ta yi ta fito da wani abin hannu mai kyau kamar warwaro ta miƙa mata.

Cike da farin ciki ta karɓa tana sanyawa a hannunta.

“Kai, Yaya Salma, ya yi kyau sosai. Yaya Zuwaira ki gani fa, har wani kyalli-kyalli yake yi kamar an sa burbudin diamond a ciki.”

Dariya Salma da Zuwaira suka saka.

Zuwaira ta ce,

“Ke dai, autar Ummah, akwai shiririta.”

“Bari in je in nuna wa Ummanmu.”

Ta faɗa tana barin gurin.

Bayan an yi sallar Magariba, sun ci tuwon dare, inda Waheeda kuma ta ci sauran shinkafa da wake na dazun tare da awara.

Aka soma fitar da kayan suyan doya da awarar dare. Dama haka suke yi, da safe a fitar da koko da ƙosai a siyar, da rana kuma a yi awara, da dare kuma a yi doya da fulawa da kuma awara.

Salma tana zaune tana suyan doya sai ga saurayinta, Amadu.

Tana ganinsa ta saki murmushi, shi ma haka. Yana zama a dakalin gurin ya ce,

“’Yan matana, ba magana ne?”

Ya faɗa yana zuba mata ido.

Shiru ta yi kamar ba da ita yake magana ba, ta ci gaba da suyanta.

Zuwaira, da take nata gurin suyan, ta ce,

“Ai fushi muke yi da kai. Dazun sau biyu tana kiranka, ba ka ɗaga ba. Ba dole ta ƙi kulaka ba.”

Bayani ya musu kan dalilin da ya sa bai samu ɗaga wayarta dazun ba.

Haƙuri ta yi, suka fara hira tana suya, suna zance.

Ana haka Waheeda ta fito ta same su. Ta tsaya a kansu tana tafa hannu.

Duk ido suka zuba mata.

“Lalalala! Yaya Salma, amma me Baba Karami ya gama faɗa miki yau da safe a kan wannan Amadu ɗin? Bai ce kar ki sake kula shi ba? To aradu, ki sa a ranki kamar Baba Karami ne ya gan ku a nan, domin sai na faɗa masa.”

Ta faɗa tana hararan Amadu da ya yi sakare yana kallonta.

A tausashe Salma ta ce,

“Haba kanwata, don Allah kar ki yi haka. Ni ce fa, ni da dazun na siya miki abin hannu mai kyalli-kyalli.”

“Oho dai sai na faɗa. Ni ba a cin amana da ni, abin hannun ma da na bogi ne.”

Zuwaira da ta tunzura ta ce, “Ke dai wallahi Waheeda akwai butulu. In kin fasa faɗa masa.”

Murmushin mugunta ta yi ta dubi Salma.

“Da na yi niyyar ba zan faɗa ba, amma wallahi Yaya Zuwaira ta ja miki.”

Tana faɗin haka ta juya da niyyar shiga gida. Da sauri Amadu ya sha gabanta yana cewa,

“Haba yar autar Ummah, kin san ni da ke ai ba ma haka. Yanzu bari in ba ki na siyan kifin Malam Garba, wannan mai ɗan karen daɗin nan.”

Murmushi ta yi, dama abin da take jira kenan, cin hanci. Ba yau ta saba musu haka ba. Duk lokacin da suka tsinci kansu suna hira sai ta bayyana ta ce za ta faɗawa Baba Karami. Daga Amadu ya ba ta kuɗi, shikenan an rufe bakinta.

Dari biyar ya fito da shi ya ba ta. Tana murmushi ta karɓa ta bar su a gurin.

“Ka yi wa Allah ka daina ba yarinyar nan kuɗi haka.” Salma ta faɗa rai a ɗan bace, domin ba ta son abin da Waheeda take mata. Har ta rasa yadda za ta yi da ita.

“Baby, bana son ta ja miki matsala ne a gurin yayanku. Kin san halinta sarai, ba sai na tsaya faɗa miki ba.”

Shiru ta yi, ba ta sake magana ba.

Kofar gidan su Safara’u ta je ta same su suna wasa da yaran maƙota.

“Ke Safara’u, zo ki ji.”

Barin wajen wasan ta yi ta zo gurinta tana cewa,

“Mene ne? Ko za ki yi wasan ne ke ma a ƙara layi?”

Dallah ta watsa mata harara.

“Mtssw! Dalla ni, wa ya gaya miki abin da ya kawo ni kenan? Zuwa na yi ki raka ni gurin Garba mai kifi.”

Zaro ido ta yi.

“Me za ki yi a gurin, ke da ba kuɗi ne da ke ba?”

Fari ta yi da idanunta, kana ta zaro mata dari biyar ɗin da Amadu ya ba ta.

Da mamaki Safara’u ta ce,

“Ke, wa ya ba ki kuɗin nan har naira dari biyar?”

“Amadu, saurayin Yaya Salma.”

Dariya ta yi tana cewa,

“Yau akwai cin daɗi. Har yawuna ya soma tsinkewa. Mu je, mu je.”

Ko da suka sayi kifin a gurin, kofar gidan suka dawo suka zauna gaba kaɗan da su Salma suna cin kifinsu suna hira.

Safara’u ce ta ce,

“Waheeda, kin ga fa gidan nan har an kusa kammala shi. Abunka da masu kuɗi, katoton gida haka daga farawa har an kusa kammalawa.”

Kallon tafkeken gidan da aka kusa kammalawa ta yi. Gida ne da ke kallon gidan su. Gida mai girma ba na wasa ba, ya haɗu iya haɗuwa, kamar ginin ƙasashen waje. Daga yanayin zubinsa ma ka san ba gidan ƙananan mutane ba ne. An gama komai, an zuba fitilun wuta ta ko’ina a jikinsa, waɗanda suka haskaka layin. Fentin waje ne kawai ya rage a yi.

“Kin tuna lokacin da gidan yake kango, muna shiga mu yi ta wasan boji-boji? Amma ki ga har an gama. Ko ma su waye masu wannan kuɗin, suna da mahaukacin arziki.”

Amadu da ke jin hirarsu ne ya ce,

“Gidan ’yan uwan sabon Gwamna Ablbasheer Mai Dawah kuke magana. Su ne za su dawo nan.”

Zuwaira cike da mamaki ta ce,

“Wai da gaske shi Gwamna ne zai dawo nan, ko kuma su waye a cikin danginsa?”

Murmushi ya yi.

“Wa ya faɗa miki Gwamna ne? Ana miki maganar Almustapha Mai Dawah Family, wanda kaf garin nan babu wanda zai nuna musu iko da dukiya.”

Zaro ido Salma da Zuwaira suka yi jin maganar Amadu, domin sun san yadda ake ta faɗin kuɗin wannan family da kuma yadda suke da faɗa a ji a Gombe. Abin da ya kashe su da mamaki shi ne, wai su ne za su dawo anguwarsu da zama.

Salma ce ta furta,

“To amma ai ba an ce a New GRA suke ba? Me yasa za su dawo nan anguwan, kuma me yasa za su bar can unguwarsu ta masu kuɗi?”

“Allah kaɗai ya san dalilinsu. Mu dai ai daɗinmu za mu yi makotaka da Almustapha Mai Dawah. Anguwar nan za ta samu ci gaba sosai, ina tabbatar muku.”

Safara’u da Waheeda dai suna saurarensu ne kawai, ba wai don sun fahimci su waye Mai Dawah Family ba. Tun da yau suka fara jin sunan, abu ɗaya kawai suka fahimta daga hirarsu shi ne, masu kuɗi ne sosai kuma suna da dangantaka da sabon governor su.

Su Salma ba su shiga gida ba sai wajen ƙarfe tara da rabi na dare. A lokacin har su Waheeda sun kwanta abin su. Da suka dawo, Salma ta shiga ɗakin Ummah da cinikin ranar.

“Ummanmu, ba ki kwanta ba?”

Tana zaune riƙe da wani littafi tana karantawa ta ce,

“Ban yi barci ba. Ke dama nake jira ku shigo. Ba zan iya barci ba sai na tabbatar kun shigo lafiya, Salma.”

Murmushi ta yi tana zama, tare da fito da kuɗin cinikin ranar daga jakarta ta zuba a kan gado.

“Ummah, yau Alhamdulillah komai ya ƙare. Kuɗin sun fito cif-cif.”

Ummah ta ƙirga kuɗin ta ga naira dubu huɗu da ɗari uku.

“Masha Allah. Allah Ya ƙara kasuwa mai albarka. Allah Ya muku albarka. Yanzu ki je ki kwanta, kin ga dare ya yi, kowa ma ya kwanta.”

“To Ummah.”

Ta faɗa tana fita daga ɗakin.

Ummah ta adana kuɗin a ƙarƙashin filonta, sannan ta kwanta tana yin addu’ar barci.

“Zuuu, har kin kwanta?”

Salma ta faɗa tana shiga ɗakinsu, inda ta tarar da Ikilima, Rabi da Waheeda suna kwance a kan ɗaya daga cikin katifun, yayin da Zuwaira kuma take kwance ita kaɗai a kan ɗayan.

“Barcin ma ya ƙi zuwa. Yau na gaji, shi ya sa nake so in yi barci da wuri.”

Salma ta rage kayan jikinta, sannan ta ɗaura zani a ƙirji ta kwanta.

“Ni kuma bana jin barci. Ina so in yi waya da Amadu, amma wayar ba ta da caji.”

Ta faɗa tana sake kunna wayar, amma tana kunnawa take mutuwa saboda cajinta ya yi ƙasa sosai.

Zuwaira ta ce,

“To ni dai na kwanta. Asuba ta gari.”