BUDURWAR ABBAN MU

chapter 13

by @prettys01

PAGE 1️⃣3⃣.


> “Wa ya ga Mamansu Basma." Ya faɗa yana hasaso wanan ranar, da haka ya shiga mota Driver ya kunna suna barin unguwar..............



Najlah na shiga parlour ta zauna gefan Mamie tana cewa.

”Mamie ya kika ga saurayin na wa?.” 

“Uhmmm ba laifi amma gaskiya ba yaro bane, ya miki girma da yawa, zan so ki aura wanda zai......” da sauri Najlah ta miƙe tsaye tana katse Mamie.

“Mamie, shi nake so, shi zan aura idan har zan yi aure, kuma rayuwa da mutuwa duk na Allah ne, sai na aura saurayi ya mutu da wuri, Ni shi nake so." 

“Ai ba abin ta da jijiyoyin wiya bane, Yayasu ma sun yi magana da General akan haka, kuma sun amince.” sai Najlah ta yi murmushi.

“Hmmmm hakan yafi dai, bara na je na sauya kaya." Da haka ta haura sama.


“Yarinyar nan bata san menene kunya ba sam? Dan General ya yi magana ta fahimta ne da mu ne, ga kuma yarda ya zo girma da arziki, amma da karnuna zan sake mai, ko kunya ba ya ji ko uwar me Najlah za ta mai oho.” 

”Adam, namu mu tayata da addu'a kawai, kasan Najlah akwai kunnin ƙashi, idan ta ɓoƙe yarda kasan bushashshen icen da ya ƙarye. Ta shi mu koma Barack.” Yayansu ya miƙe tsaye.

“To Mamie a kwana lafiya, sai mun haɗu wajen bikin.”

“To shike nan Adam, da wuri zani saboda akwai aiki, ɗa zu ma mukayi waya da Mardiyya (Matar Yaya).” 

“Shike nan, bye." Suka yi sallama tare da wucewa, ita kuma ta gyara zamanta a parlour.


Tasan kusan kowa na familyn general, Dan kuwa abotan dake tsakanin mijinta da shi ba kaɗan bane, wanda har ita da matarsa suka kulla ƙawance mai tsafta, ta yi mamaki wai da suka ce Abba shike bin General, ba ta taɓa ganinsa ba sai yau, kuma ba ƙyarya suna kama da General, gashi yana da natsuwa da kamala, koma menene ta bari gobe idan ta je bikin za su tattauna da Mardiyya.........



*********
Da farin ciki ya isa gida, bayan Driver ya yi parking a parking lot, sanan ya ɗauki jakkan ya fita direct ya nufa ciki, har lokacin dai mata sai kai da komo ake kai kace rana ne.


Jin an kira sunan sa yasa ya juya yana kallon Fauza da ta nufo sa da gudu, tana zuwa ta rungumesa tana cewa.

“Sannu da dawowa, Dad tun ɗazu Dad (General) ke nemanka, sai na ce mai ka tafi wajen walimar shine ya ce za ku haɗe a can, fatan ka ganshi?." 

”Eh Autata, kinga walimar ma nan." Sai ya nuna mata jakkar nan, murmushi ta yi tana mai raɗa.

“Abbana zan iya ganin menene a ciki.” kai ya girgiza yana ci gaba da tafiya.

“A'a ba za ki gani ba.” sai ta juya ta nufa wajen ƙawarta.



Abba yana shiga ciki, ya cire babban rigarsa sannan ya fiddo wayarsa, yana ɗan latsawa, be ɗau lokaci ya buɗe wannan jakkar, abubuwan cine masu, fried chicken rice ɗin da ya tabbatar shine Baby ta yi da hannunta, ya zauna ya hau ci yana lumshe ido.

Fried chicken rice ne wanda ya ji spices ya koma yellow, ga mai ya fito a ciki, sannan green and red pepper an musu yankan round, albasa kuma aka yanka cube shafe, da slize, sai abinci ya ba da wani style na daban, sannan da mix-meat da aka mai dahuwar ciki amma launinsa ya fita brown, sai ƙamshi yake sosai.

Lumshe ido ya kuma yi, da sauri kuma ya kira number Najlah, bugu uku ta ɗauka.

“Babayna ka isa gida lafiya?." 

“Alhamdullah, ina nan ina satin wannan hadaɗen fried chicken rice ɗin, wallahi ya yi daɗi, dole na biya tukwicinsa.” 

“Hmmmm bayan wanda ka ba me gadi ya ban, na ga saƙo kuma na gode." Sai ya yi murmushi yana tuna wani babban leda da ya bada a miƙa mata.

“Babu godiya tsakanina da ke, Ni dai dan Allah mukai aure ki dinga min irin wanna shinkafar kullum, wayyo daɗi." Ya faɗa yana kai wani loma bakinsa.

Dariya ta dan yi.

“To shike nan, kaman kasan ina son chocolate expecally C.C.” 

“To asha lafiya, nikam bayan wannan sai wanne kika dafa? Na fara ci kar tumbina ya cika.” 

“Snaks ne Mamie ta yi, amma saura duk Ni na yi maka, kuma kai kaɗai za ka cinye dan kuwa na girka komai ne cike da soyayya."

“Dole ɗanɗanon ya rikitani, ina zuwa kaman ana knocking." 

“Ok ka bar wayan a haka, Maybe Yarana ne suka shigo, ka ga sai na fara jin muryansu, kafin na gansu gobe." 

“An gama ranki shi daɗe." Da haka ya aje wayar, sannan ya nufa ƙofa ya buɗe.


Be yi tsammanin ganinsu ba, shi yasa be katse kiran ba, sai kuma gasu su ukun.


Hanya ya basu suka shigo, sai ya zauna a in da yake yana fatan kar Baby ta yi magana.

Suna zama Marwa ta ce.

“Abba ko neman mu baka yi, ka kawo mu gidan nan ka sharemu, haba Abba. Kuma ɗazu sai nemanka nake yi amma baka nan.”

“Da kun zo ai da kun sameni, ɗazu ne na fita, to yanzu me kuke so?.” 

“Munzo gaishe da kai ne." Cewan Fauza tana ƙoƙarin ɗaukan wayar Abba.


Da sauri ya ɗauke yana cewa.

“Ina naki wayan?." 

“Uhmmm duba abu zanyi kawai.”

“A'a. Baseey ba magana ne?.” sai ta ɗago idanunta ta kallesa, yasan duk baƙin cikinta saboda sun zo Kaduna ne.

“Maganar ne banjin yi, yunwa nake ji dama, Fauza miƙo min roban nan.” ba musu Fauza ta miƙa mata.

Abba ya kauda kai, baya so ya hanasu ci karsu fahimci komai, gashi cike da soyayya aka girka mai komai.

“Bara na ɗau plantain chips ni.” cewan Marwa tana ɗauka.

Nan take suka hau ci suna ɗan hira tsakanin su, take Najlah ta katse kiran, Abba yana ganin haka yasan ta ji haushi, sai ya lumshe ido yana duba abu a cikin wayar, yana gama latsawa ya aje yana mai shiga toilet.


Hannu ya wanke ya fito, sai ya ga wayarsa a hannun Baseey, ta riƙe tana kallon screen ɗin sannan tana kallonsa.


Kauda kai ya yi yana mai fatan ta aje mai waya, dan kuwa akwai matsala idan ta buɗe, yasan bincike za ta yi.

Basma idanunta kan Abba har ya zauna, sai ta gyara zama sannan ta fara magana cikin tuhuma kamar wata alƙaliya................






****************

Kallonsu ya yi sannan ya ja tsaki, a irin yanayin nan ne yake banbance su, dan kuwa Al-hassan ya natsu ne yana kallon ƙasa, shi kuma Al-hussain sai cika yake yana ɓatsewa.

“Na sake faɗa, ba za ka yi aure yanzu ba, saboda ba ka gama hankali ba, dama Al-hassan ne be da matsala, kai kuwa ko aikin yi baka yi, dame za ka ciyar da matan?." Kafin Al-hussain ya yi magana Al-hassan ya ce.

“Abbeey Ni zan ciyar da su, ba ma shi kaɗai ba, Ni zan ɗauki nauyin komai da ya shafi bikin, yanzu haka ma na riga na gama haɗa mai akwati."

“Al-hassan ya isa!, Akan me kake mai duk wannan? Shi ba namiji bane kamar kai? Me yasa ba zai nema da gumin sa ba." Abbeey ya faɗa cikin ɓacin rai.

“Namiji ne kamar Ni, sai dai duk abin da ƙanina yake so, shi nake gani a dai-dai, Ni nasan cewa akwai ranar da tabbas zai fara zuwa wajen aiki da kansa.....” da sauri Al-hussain ya katse sa da cewa.

“Ba zan yi aiki ba, na ce ba zan yi komai ba, wai dole ne sai ka fita na nema."

“A'a, kana da Ni ka ji."

“Dalla kumin shuru, gaba ɗaya ba ku da hankali, mtwwssss aikin banza, kai ka zauna a gidan ka yi ta kwanciya, kai kuma ka kashe kanka da wahala, na rasa gane muku wallahi."

“Abbeey ka ya ƙuri dan Allah."

“Hmmmm na ji, ku shirya gobe zamu Kaduna, babban abokina General A.A zai aurar da yaransa mata, sai ku shirya."

“Gaskiya ba zan samu zuwa ba Ni." Abbeey be kallesu ba amma yasan wa ya faɗa haka, sai ya lumshe ido ya buɗe, kafin ya yi magana Al-hassan ya riga sa.

“Shike nan ƙanina, Abbeey Sai mu tafi tare kawai." Wani kallo Abbeey ya musu yana cewa.

“Ku ɓace min daga gani." Da sauri Al-hassan ya miƙe yana ɗaga Al-hussain da ya kafe waje ɗaya.

“Tashi mu je." 

“Babu inda zan je sai ka ya tabbatar min da zai nemo min auren Marwa." 

“Ni na ce ina son ka yi abu, ai baka yi, sai kai na yi maka wanda kake so, to baka isa ba wallahi.” da haka Abbeey tashi ya bar musu wajen.


Al-hussain kaman zai fashe haka ya koma, ya kafe waje ɗaya da ido.

“Ka bar komai a waje na, zan mai magana kuma zai sa lokaci, kawai kaima ka dinga ƙoƙarin bin umarninsa.”

“Ba wani nan, kawai dai Abbeey baya sona ai na sani, kai kaɗai yake so, baya ƙyauna ta saboda ina son Momy fiye da shi, hmmmmm.” 

“Magana cikin fushi be da fa'ida sam, ka je ka huta, kuma ka sa a ranka za mu bi sa Kaduna, insha Allahu komai zai yi daidai.” sai Al-hussain ya miƙe sannan ya fita a zafafe.

Al-hassan ya dafe kansa yana lumshe ido yana mai cewa.

“Momy komai dake faruwa kece sila, Allah ya so ma daga Ni har su Al-hussain babu wanda ya biye miki, balle ki kaimu ga duhu mara ƙare wa, kai alhamdulillah, Allah mun gode maka." Da haka ya bi bayan Al-hussain ɗin...............



***********


“Tunda muke da kai bamu taɓa ganin kasa password a waya ba, sai yau, hakan ya sa na ji ina zargin akwai abinda kake ɓoye mana Abba." Sai Abba ya kalla Basma wacce take kallonsa cike da zargi.

Already ya shirya ma tambayar su dan haka ya ce.

“Ban taɓa sawa ba sai yau, kuma hakan yana da nasaba da shagalin nan da na zo, at anytime ɓarayi suna iya sace waya, shi yasa na sanya idan mun koma gida zan cire.”

“Ai kana zuwa irin bukukuwa haka, me yasa su ba ka sawa?." Marwa ya kalla sannan ya ba ta amsa.

“Saboda ban taɓa kawo za ka sake min waya ba, last biki da mukayi aka sake ma abokina waya, shi yasa na sanya password, before a iya cire key ɗin za'a yi sauri a gane location na wayar.” 

“Hakane wallahi." Cewan Fauza tana murmushi da kuma yarda, Marwa ma ta yarda sai dai Basma sam ba ta gamsu ba.

“Ok, menene password ɗin zan duba abu?." Gabansa sane ya faɗi dan kuwa sunan Najlah ya sanya.

“Kawo na cire." 

“A'a faɗa min kawai." Ta kuma faɗa tana kafesa da idanuwa.


A take wayar ta sa ta hau ringing, cikin sautin da ya sanya ma Najlah kawai, waƙar soyayya amma na Arabic, kauda kansa ya yi yana basarwa amma baya fatan Basma ta ɗauki wayar, dan kuwa da kalman da Najlah za ta fara shine *Babynahhhhhh*.

“ Wanene 01IMH?." Ta faɗa dan ba ta gane ma'anar sa ba.

“Au Muhammad ne ban wayar." Ya yi sauri ya amsa wayar yana rejecting call ɗin.

Sai a yanzu yake gode ma Allah da ya sanya ma Najlah *01IMH* wannan sunan soyayya ne wanda aka sarrafa shi da ma'ana mai ƙyau.

“Sai da safe." Cewan Basma tana miƙewa, da haka Marwa da Fauza suma suka mai sallama sannan suka fita.


Tashi ya yi ya rufe ƙofar sannan ya kira Najlah, sai dai kira uku ba ta ɗauka ba, a na huɗu ta ɗauka, cikin salon burgewa Abba ya ce.

“ONLY ONO IN MY HEART (01IMH), ya kike abin so na?” sai ya ji ta fara kukan shaƙwaɓa tana magana cikin in'inna da taɓara tana cewa..............🙈✍️
END