chapter 14
by @prettys01
PAGE 1️⃣4⃣
> “ONLY ONO IN MY HEART (01IMH), ya kike abin so na?” sai ya ji ta fara kukan shaƙwaɓa tana magana cikin in'inna da taɓara tana cewa.............
“Sai.... da......na...nace maka..... da soyayya.............na...na.yi maka girkin shine......ka bari Yarana suka cinye ko?." Sai ta fara shashsheƙa, ji ya yi hankalinsa ya tashi, da sauri da ce.
“I'm sorry Baby, kinsa Yara ne, shi yasa na barsu, haba Mamansu." Sai ta yi ɗan dariya, wanda Abba ya ji sa har cikin zuciyarsa.
“Uhmmm ka dinga ce min *Ummeen Basma* na fi son sunana." Sai ya yi dariya.
“To Ummeen Basma, a yi haƙuri, kinsan halinsu ai." Take ta ɗan kaurara murya da sigar wasa ta ce.
“Na manta, haka suke ai, shike nan Allah ya musu albarka.”
“Ameen Ammeen Basma."
“Wallahi sunan akwai daɗi.”
“Kuma ita ce hukumar gida na ba.”
“Zama ta dena ne wallahi, tsaf zan sai ta musu zama kafin mu aurar da su."
“Tom Ammeen Basma Allah ya ja kwana, zan iya ganin ƙyakyƙyawan fuskar ki kuwa?."
“Why not Babynahhhhhh, Kira VD ɗin."
“Thanks Dear.” da haka ya mai da V.d suka dasa wayarsu cike da soyayya.
Ba su suka rabu ba sai 2:13am na dare, suka yi sallama da juna suna kwanciya da tunanin juna...........
Ɓangare Basma kuwa, gaba ɗaya ta ji ta sake tsarguwa da lamarin Abba, sai dai ta shanye komai ne dan ba gida suke ba, ko da ta shiga ɗakin da suka sauka, kwanciya ta yi dan barci take ji sosai, Fauza kuwa tuni tabar bangaren nan, sai Marwa da ɗauki wayan Al-hussain.
Yau dai wayar babu armashi sam, dan kuwa Al-hussain rai a ɓace yake, kuma duk yarda suka yi da Abbeey ya faɗa mata.
“Kamar yarda Al-hassan ya ce, ka dinga mai biyayya, My Love ƙasan yau da gobe akwai banbanci, yanzu baka ganin nan gaba Al-hassan zai sauya maka, ya dena ɗaukan dukka ɗawainiyanka, ya kamata kaina ka dogara da kanka."
“Hmmmmm har abada Al-hassan ba zai sauya min ba, wai ma dole mutum sai ya fita zai nema? Ni bazan yi ba, ina so ayi mana aure, mu rayu tare a gida, in kika tafi aiki, kafin ki dawo zan miki komai, na yi girki da na gyara gado." Sai ta danne dariyarta dan kuwa bil-haƙƙi da gaske Al-hussain ke yi.
“Idan hakan ta kasance ka zama matar Ni kuma mijin.”
“Eh ba komai hakan ya min.”
“Shike nan, yanzu dai ka bi Abbeey ɗin gobe, sai ma na tura maka location na inda nake, sai mu haɗu.” sai ya yi shuru sannan ya ce.
“Danke zan zo, amma badan shi ba.”
“Na ji to, yanzu dai ka saki ranka ko na katse kiran nan.” take ya yi ƙoƙarin sai ta yanayinsa, sannan suka ci gaba da waya.
Sam ba sa gajiya da juna, kullum cikin hira suke, kuma suna manne da juna, sune ake kira da jini da hanta.
*Washegari*
Tabbas gidan biki ya cika, ƴan uwa da abokan arziki sun cika ko wani lungu da saƙo na gidan, ga kuma bataliyan sojoji da suka cika bangare guda.
An dawo ɗaurin aure, shi yasa cikin gidan ba matsaka tsinke, maza masu babban riga sai hotuna akesha, a cikin angwaye ɗaya soja ne, hakan yasa wasu sojoji suke taka mai baya duk in da zai shi.
Wow gida ba magana, mata duk suna sanye da wata golden atamba, dark blue sai fari da baƙi da aka yi ƙwalliyar atamfar, kusan kowa shine a jikinta, wasu kuma Less masu tsaɗa.
Amare uku ne suka fito a jere, take hankalin kowa ya koma kansu, inda suke sanye da less iri ɗaya, burin kowacce amarya, amma nasu mai tsaɗan ne sosai, farin Less da golding style a jiki, an yi musu ɗinki iri ɗaya dogayen ruguna sai gyale da takalmin golden.
Take aka rufa ma Amare, mata suka hau buɗa, maza kuma aka hau hotuna, sojoji kuwa aka ƙame ƙam.
Hoto aka sha sosai, in da kowani ango aka mai da matarsa, sannan aka yi gaba ɗaya.
Abba ne kai ya ɗau huta dan kuwa Yaya ya sakar mai abubuwa da yawa, sai da aka dinga kiransa tukun ya samu ya zo aka yi hoto da shi.
Fauza dake tsaye cikin ango an yi mata riga da skirt, ya kira.
“Ki yi sauri ki kira min sauran, su fito a yi hotunan da su." Ya raɗa mata a kunne.
Da sauri ta nufi cikin gidan, ba ta ɗau lokaci ba sai ga ta fito, kusa da Abba ta tsaya ana musu hoton.
Marwa ma angon ne jikinta, doguwar riga aka yi mata mai ƙwala, Basma kuma riga da skirt, wanda Matar Yaya ce ta yi musu, da safan nan ta basu, kuma ikon Allah sai ya yi musu daidai.
Tun da ta yi wanka ta sanya na ta amma Basma ta ƙi sawa, sai da suka yi ɗan rigima tsakaninsu shine ta sanya, sai gashi atamfar ya fi ɗaukan ta saboda duhun fatarta.
Abba farin ciki yake sosai, balle da ya sanya yaransa a gaba aka yi musu hutuna, sai ya ji yana fatan Allah ya nuna mai ranar da zai aurar da su haka.
Abba ne a tsakiya, yasha Men Less sky blue sai ƙyalli take, gefansa na dama Marwa ta tsaya kusa da shi sosai, ɓangaren hagu kuma Basma ce ta tsaya tana gyara vail ɗin ta, Fauza ta tsaya gaban Abba, haka suka sha hoto, sannan Amare ma suka shiga aka yi da su.
Ana gama hoton ya nema Basma ya rasa dan tuni ta koma ciki, dama kansa ya yi zafi, ya yi waje ya a ci gaba da ƙarɓan ɓaƙin General.
Misalin ƙarfe 3:00pm, Abba da General suka miƙa daga rumfar da suke, suka fita dan taro motar sojoji biyun da suka nufosu.
Suna isowa, Ya Adam da ke sanya da ƙananun kaya ya fita daga mazaunin Driver, ya zagayo ya buɗe ma General Umar Hakimi, wanda suke ma inkiya da Barkono.
Saramai ya yi, shi kuma Abbeey ya fito cikin farin shadda mai ƙyau, yana fitowa ya yi murmushi, a lokacin Dad da Abba suka iso.
Sai Dad ya rungume abokinsa yana mai Barka da zuwa.
Abba kuwa ya suka yi musabiha.
A tare suka kalla saurayin da yake gaishe su cike da natsuwa da girmamawa.
Suka amsa tare suna mai murmushi.
“Al-hussain ko? Baka gane Ni ba?." Cewan Abba yana ƙare mai kallo, sai Al-hassan ya girgiza kai.
“Baba ba nine Al-hussain ba yana cikin mota." Sai Abba ya ce.
“Ikon Allah."
“Mubarak a ina kasan yaran Barkono?."
“Yana zuwa zance wajen Marwa ne." Kafin Abbeey ya yi magana, suka ji sak muryan Al-hassan ya dake su ana gaishe su.
Duk suna kalla Al-hussain dake tsaye da irin shigar Al-hussan.
Abba da yau ya fara ganinsu ya zaro ido yana ƙare musu kallo.
“Laaa Abbana ina wuni." Cewan Al-hussain da ya ga Abba har da tsugunnawa ƙasa, Abbeey ya kauda kansa, Al-hassan kuma ya yi murmushi.
“Alhamdullah, ashe dai ɗan gida ne, tashi ɗan albarka." Sai Al-hussain ya miƙe yana cewa.
“Abba Marwa tana ina?."
“Yarona ai ka bari ku shiga daga ciki, Muje Barkono." Da haka suka fara tafiya cikin natsuwa.
Al-hussain ne ya sanya mask, saboda in za su fita tare haka suke yi kodan su kauce ma idon mutane.
A wani ɓangare aka sauke su, cikin tarban mutumci, Abba sai a yanzu ya ji Al-hussain ya kwanta mai, dan kuwa Barkono mutumin kirkine sosai.
Ɓangaren na daban aka kai Al-hussain da Al-hussain, suna aka cika musu gaba da kayan more rayuwa, Al-hussain ne ya ga kiran PA.1, dan haka ya fita dan suyi magana a natse, fita ya yi daga gidan gaba ɗaya.
Al-hassan kuma ya gyara zama yana latsa wayarsa.
Ya ɗan jima a haka kafin yaji an yi sallama, ya amsa yana cewa a shigo, Buɗe labule ta yi ta shigo .
Idanunta ne suka sauka kan masoyinta, sai ta zaro ido tana mai kallon mamaki, tasan sunyi waya akan idan ya isa wajen bikin nasu za ta tura ma nata location ɗin, daga nan kuma ba su sake waya ba, sai yanzu sa Abba ya kirata ya ce ta shiga part ɗin akwai ɓaƙo dake jiranta, da ta shigo rai a haɗe amma ganinsa yasa ta nufesu da gudu.
Al-hassan kuwa ganinta sai ya sa ɗauke huta na lokaci, tunda daga ranar da ya fara ganinta ta shiga addan rayuwarsa, tunaninta da mafarkinta ya yi sau ba adadi, sai kuma yau ga ta gabansa, cikin shigar da ya ƙara mata ƙyau.
Kafin ya buɗe bakinsa da ya yi mai nauyi, ya ji ta faɗo mai jiki tana rungumesa.
Take wannan yanayin ya sake haskawa a gagan ruhinsu, kalaman dake bakinta suka ƙame jin sanyi a jikin Al-hassan. Gashi ta faɗa mai jiki sosai, a hankali ta kalla fuskarsa ta ce.
“Innalillah Al-hassan ko?.” cike da mamakin ganesu ya ɗaya mata kai.
Sai ta yi ƙoƙarin miƙewa, da sauri ta tsaya dan kuwa dankuninta ya kama mai riga, zai ta lumshe ido tana jin wannan sanyi na ratsa mata jiki.
Jikinsa shima ya mutu, amma haka ya yi jarumta, ya sanya hannunsa ya cire ɗankunnin gaba ɗaya.
Da sauri ta miƙe tana matsawa baya.
“Dan Allah kaya ƙuri."
“Ba komai." Ya faɗa yana miƙewa tsaye, a hankali ya tako kusa da ita sannan ya miƙa mata ɗankunnin, sai ta juya kanta, alaman ya sanya mata.
Ba musu ya ƙara taku ɗaya suka kusa haɗewa, ya sanya mata yana mai jiyo sautin numfashinta, wanda ita ma tana jiyo nashi.
Yana gama sama mata ya ja baya dan kuwa sai yanzu ya tuna wacece Marwa a gareshi, maccen da Al-hussain yake mata mugun so ne.
A natse ya koma ya zauna yana cewa.
“Yanzu zai shigo, amma ya kika gane bashi bane wannan." Sai ta sauke ajiyan zuciya tana cewa.
“Bansan me yasa ba jikika yana da sanyi, nakan ji sanyin har cikin jikina." Ta faɗa tana juyawa dan kuwa Al-hussain ne ya shigo.
Yana ganinta tsaye ya faɗa ɗa murmushi yana sauke mask ɗin sa.
Kusa da ita ya isa yana riƙe mata hannu.
“Wow Kinyi ƙyau My love.”
“Na gode, kaina haka Baby." Sai ya yi murmushi, A hankali kuma suka taka har kan wani kujera yana cewa.
“Ina fatan da kika shigo baki aita komai ba, dan na ga photocopy na yana wajen." Ba ita kaɗai ba hatta Al-hussain dake mamakin abin da Marwa ta ce, dan shima haka yaje ji, sai ya yi dariya.
“Babu abin da ya faru, da dai baka shigo da wuri ba da kuwa.....” da sauri ya rufe mata baki da hannunsa .
“Karki sa zuciyata ta buga.” sai ta ɗaga mai gira.
Da haka suka fara shan soyayyarsu, sai dai rabin hankalinta yana kan Al-hassan, shi kuwa jin sun ishesa da soye-soye ya miƙe tsaye.
“Ina zuwa Tweeny?.”
“Albasa zan nemo na kawo muku?." Cikin rashin fahimta Al-hussain ya ce.
“Albasa kuma na mene?."
Sai Al-hussan ya juyi ya kallesu ya ce.
“To ai naga kuna ta soyewa ne kar kuyi ƙauri shi yasa zan nemo albasa, hakan zai sa man ya jima a huta yana soyuwa." Dariya suka yi dukkansu sannan ya fice, su kuma suka ci gaba da soyewa...............✍️
END.