PAGE 1
by @prettys01
______________________Murmushi ne kwance akan fuskar Abba, har ana iya hango fararen haƙoransa a waje, wa'inda suke ajere kuma cikin tsari. Babban mutum ne wanda a ƙalla zai kai 45yrs, sai dai hutu da jikin daɗi sun gama ratsa jikinsa, hakan yasa ba za ka ce yakai 40yrs ba, fari ne shi mai dogon hanci, yana ƙyau masha Allah, a kallon farko za'a za ci Balarabe ne saboda be yi kama da wanda ke kin jin Hausa, dan ya yi kama da larabawa ko shuwa Arab, sannan yana da tsayi sosai da cikar ƙirji, ga haiba da kamala, a taƙaice dai mutum ne mai cikar halitta ta ko ina.
Zaune yake kan kujera yana kallon wani American film mai suka (Prisone Break), yana bibiyan shirin a MBC Max, duk da ya jima da kallonsa Complete amma haka yake zama ya kuma kalla in dai yana free.
"Assalamu alaikum." ya ji muryar ƙaramar ƴarsa, hakan yasa ya amsa yana mai da fararen idanuwansa kan yarinya sannan a hankali kuma cikin sanyi ya ce.
"Wassalamu alaikum, suna ina?." Ya tambaya ganin be ga sauran da ya ce ta kira su.
Yarinya ce budurwar, mai kama da shi sosai, sai dai ita haskenta ya haɗu da ɗan ja-ja.
A ƙasan carpet ta zauna tana cewa.
"Abba gasu nan zuwa." sai ya ɗaga mata kai.
Cikin minti biyu, sai ga wasu ƴam mata biyu sun fito dukkan su cikin p.j-mask kowa da colour ɗin ta, dukka riga ne da wando masu dan girma dan ba su nuna shape.
Suna isowa suka zauna daga gefan ƙanwar ta su, sannan suka haɗa baki wajen gaishe da Abba.
Sai ya kallesu cike da kulawa sannan ya amsa.
Shuru ya yi yana binsu da kallo kafin ya buɗe baki ya kuma cewa.
"Marwa bansan me kike so ki zama ba, dududu you are 21yrs, amma har kika iya tsinka ma Baba Habu mari, wannan wani irin hauka ne." ya kai nan yana ɗan ɗaga murya, duk da faɗa sam baya mai ƙyau.
Babbar cikin su ita ce Marwa, yarinya ce fitinanna mai shegan gadara da nuna isa. Baki ta tura, sannan cikin sangantar ta buɗe baki ta ce.
"Abba wanke mota na sanya shi, shine ya kama ya wanke na Basma, gashi a lokacin fita urgent ya kamani, bansan rai na ya ɓaci ba, shine na shafa kumatunsa, ba marinsa na yi ba." takai nan tana son fara kuka dan har ta fara bubbuga ƙafa sai ka ce ƙaramar yarinya.
"Karki min kuka, ku ba kusan Gaskiya sam, da an fara muku magana sai ku hau kuka, ke kuma Basma me kika yi ma Asabe?." ya faɗa cikin takaicin halayen yaran nasa, sam baya son yana takura musu saboda su ɗin marayu ne, shine uwa da ubansu, ko kaɗan bayan so yaga suna cikin damuwa, gashi suna da mugun taurin kai, har gwamda ƙaramar mai suna Fauza, tafisu daraja mutane sai dai ita tana da ƙyama, ba ta shiga harkan kowa.
"Abba tasan bana son ƙarnin kifi idan ina gida, shine ɗan iskanci ta soya bayan tasan ina falon nan ina kallo" cewan Basma tana haɗe fuska sosai dan ita ba wasa, ba ma ta dariya sai sa'a.
Nunfashi ya ja sannan ya furzar, ga dai su sun girma amma har yanzu suna ca za mai kai.
"Amma ai Fauza ce ta ce ta yi, kinga ba ta da laifi, tunda umarnin ƙanwarki take cikawa" Ya faɗa, again cikin sanyi wanda ya zama halinsa.
Cikin sauri Basma ta miƙe da sauri tana girgiza kai tare da cewa.
"Abba.....Abba yanzu akan wannan ne kake mana faɗa, me yasa Abba? Dan bamu da mahaifiya ko." Sai ta share hawaye da suka zubo mata sannan ta ci gaba da cewa.
"Ba zan sake ba, na gode." Da haka ta nufi stairs da sauri har da gudu-gudu.
Dafe kansa ya yi, yanzu a haka gani suke ya musu faɗa, bayan cikin tausasawa ya yi maganar, yana mugun ji da su fiye da komai nasa, ba shi da fata sai ganin sun dauwama cikin farin ciki.
"Ku je ku kwanta." ya faɗa yana latsa remote ɗin tv ya kashe.
Tashi suka yi, babu wacce ta mai yarda suka saba idan za su nufan ɗaki dan barci, sukan rungumesa harda yi masa peck a kumatu sannan su rabu, sai dai yau ko kalla mai daɗi be samu a wajen su ba, haka suka wuce suka barshi jikinsa duk ya yi sanyi.
Ya tsana a dinga ɓa ta musu rai, yasan abu ɗaya zai yi ya ɗan sassautar da fushin Basma, shine koron Asabe daga aiki.
Har ranshi be ji daɗin abin da Basma ta yi ma dattijiwar matar ba, amma ba yarda ya iya farin cikinsu shine ƙwanciyar hankalinsa.
Ya jima a zaune cikin damuwa sannan ya tashi ya haura sama, part ɗin sa ya shiga, ko watsa ruwa ma ba zai iya ba saboda yarda yake ji, gani yake idan har ɗayarsu ta yi kuka to ya ci amanar mahaifiyarsu ce, dan amana ta bar mai su.
Haka dai ya kwanta duk damuwa ya ishe shi, tunaninsa ɗaya Allah yasa Basma ta iya yin barci, kar ta yi ta kuka dan yasan hakinta, tana da mugun zafin rai, da sanya abu a cikin rai, ga naci, gaba ɗaya dai halin mahaifiyarta gareta, dama kuma da ita take kama.
*****
Zaune suke gaba ɗayansu a ƙaramin parlournsu, hira suke yi cikin nishaɗi da walwala kamar ba sune suka shigo part ɗin su suna cikin damuwa ba.
"Ai in ba haka muka yi ma Abba ba, ba zai kore su ba, ƙwanda mu zubda hawaye, dan hakan na ɗaga mai hankali." Cewan Basma sai Fauza ta ce.
"Amma yanzu idan aka koreta wa kuke so a kawo? Kusan matar nan tana da tsafta irin yarda nake so, kuma tana iya ƙoƙarin ta, a ƙalla shekara 10 muna tare da ita, tana kula da mu, be dace a koreta ba sam." Ta kai nan tana jin babu daɗi.
"Wallahi sai ta bar mana gida, hakuri kawai nake da ita, dokokina kowanne sai ta rushe min, haƙuri yakai ƙarshe akanta, ko a jiyan na ce karta kuskura ta ba Iro mai wanki abinci, saboda ya min laifi, amma munafukar matan nan sai da ta bashi." Ta kai nan tana jin ranta na ƙara yi mata zafi.
"Basma calm down, Baby Fauza don't worry, in dai mai tsafta kike so zamu sanya Abba ya samo miki." faɗin Babbar su wato Marwa. Da haka suka sauya hirar kowacce ta ci gaba da abin da take yi tun farko.
******* Marwa ita ce babba mai shekara 21yrs, sai Basma 20yrs ba wani ta zara tsakanin su , sai ita auta Fauza, mai 17yrs, su uku kaɗai Allah ya ba Alhaji Mubarak, dama bashi da fata sai na Allah ya bashi yara mata uku, ya raine su har zuwa auren su, ya zama shima ya shiga sahun wa'inda aka musu bushara da gidan Aljanna akan rainon yara mata. Hakan yasa da Allah ya bashi matan ya ke mugun ƙaunarsu fiye da misali.
Matarsa Hajiya Karima, macece mai zafin kishi da rashin sanin darajar maƙasƙanci, haka take tun kafin haɗuwarta da Alhaji, cikin ikon na Ubangiji kuma suka haɗu har suka yi aure.
Hajiya Karima, sai da ta raba Alhaji da gaba ɗaya danginsa duk da suna da wadata dangin nasa, amma ita rayuwarta su rayuwa ita da ƴaƴanta kaɗai.
Alhaji kuwa da yake mutum ne mai sanyi, gashi yana son Hajiya Karima, sai ya zamana duk mai ta ce haka yake yi, ko da baya so baya nuna mata.
Ko bayan da Allah ya basu zuri'a, lamarin be sauya ba ta ɓangaren danginsa, dan babu wanda yake zuwa wajensa, shima haka baya zuwa wajen kowa.
Mahaifiyar Alhaji da kanta ta nema ma Alhaji wata yarinyar dangin dan ya aura, sai dai Hajiya Karima daga jin wannan zancen, ta je har family house na Alhaji, ta ci mutuncin su, har da mahaifiyarsa, ba ta tsaya a nan ba, a wannan ranar suka bar Kaduna da zama gaba ɗaya, shi kuma Alhaji Mubarak ya biye mata suka bar kaduna.
Al'amarin da yasa Mahaifiyar Alhaji ta yi mugun fashi da shi har ga dangin nasa, da kuma wannan fushin ta bar duniya.
Hajiya Karima ko a jikinta, sai ci gaba da zuba mulki ta yi a cikin gidan, haka ta kuma raina yaranta mata su uku, tana da burika sosai akan yaranta, sai dai mutuwa mai yankan ƙauna ta rabasu, ba ciwo haka kawai Hajiya Karima ta faɗi, daga zuwa asibiti sai gawa.
Misalta tashin hankalin da Alhaji da yaranta suka shiga baya faɗuwa, al'amarin da ya kusa taɓa mai hankali, sai cikin ikon Allah ya dawo dai-dai.
Daga wannan lokacin kuma ya ƙara jin soyayyar marayun yaransa fiye da komai, duk da wasu halayen da suke da shi baya so, amma baya iya tsawatar musu.
A yanzu da rasuwar Hajiya Karima an rufa shekara 8yrs, masu aiki suke kula masa da yaran nasa, ya so a lokacin ya mai da su Kaduna amma yaran da yake halin Hajiya Karima suka biyo, suka ce ba za su ba.
Be yi mu su musu, ya bar zancen, amma lokaci zuwa lokaci yakan kaisu gida dan suga dangi, saboda babu mai zuwa wajensu, kuma Alhaji Mubarak be damu da hakan ba.
Babu yarda ba'a yi da Alhaji daya ƙara aure ba, amma Marwa ta daka tsalle ta ce "Babu uban da zai yi ma mahaifiyarta kishiya". Wannan shine kalmar dake faɗa, shi kuma ya zauna akai dan beson ɓacin ran yaransa.
A haka suke rayuwa abinsu cike da farin ciki, domin komai da suke so suke samu, komai wahalar sa.
Marwa ta shiga high school yanzu in da take karatun masa communication, Basma Kuma ta fara zuwa karatun midwife free, sai ƙaramar su wacce take S.S3 a school.
****
Washegari ya maka Sunday, babu wanda ke fita a gidan duk suna gida, hakan ya sa sai 11am suke tashi.
Abba ne ya fito parlour cikin wani farin jallabiya mai sheƙi da haske. A hankali yake takawa har ya sauko gaba ɗaya, sannan ya zauna a kan kujera mafi kusa.
Jikinsa a sanyaye yake, saboda abin da zai aikata, yasan idan ba hakan ya yi ba, to Yaransa fushi za su yi da shi, shi yasa tunda suka fito sallar asuba ya sallama, Baba Habu bayan ya bashi kuɗi masu kauri, sai dai hawayen da Baba habu ya fara yana roƙan kar a koreshi yasa zuciyarsa tsinkewa, yana da rauni sosai, amma haka ya danne ya ce
"Babu abin da ka yi, kawai dai naga lokaci barin ka aiki ya yi ne." abin da ya faɗa kenan yana wucewa, sai ya ji duk babu daɗi.
Yanzu babban matsala shine yarda zai kori Asabe a gidan nan, matar akwai ta da hakuri sosai, ita kaɗai ce a masu aiki ta jima saboda tana da kau da kanta, haka take haƙuri da halin yaran nasa.
Iskar ya furzar daga bakinsa sannan cikin dauriya ya buɗe baki ya cewa.
"Asabe! Asabe!! Asabe!!!."
"Na'am Alhaji." Ya jiyo ta amsa daga Kitchen.
A hankali ya mai da idanunsa sai tin ƙofar kitchen.
A sukwane ta fito hannunta riƙe da ludayi.
Babbar mace ce sosai, wanda zasu yi sa'a da Abba, duk da wahala yasa girmanta fitowa sosai. Tsugunnawa ta yi daga can nesa da shi tana cewa.
"Alhaji gani, ko wani abu kake so a dafa maka?." ta faɗa cike da tsantsar ladabi.
A hankali ya kuma sauke nunfashi sannan ya kalleta a natse.
"Ki shirya kayanki, zan sa a mai dake garin ku."
A ɗan ruɗe ta ce.
"Alhaji Lafiya? Meke faruwa ne?."
"No karki damu, lafiya lau."
"A'a Alhaji, ko dai Buhari ya rasu ne? Dan jikinsa babu daɗi, dama duk na ƙosa ƙarshen wata ya yi aban albashi na tura su kai shi asibiti........Alhaji ya rasu ko?" Ta faɗa cikin wani irin rauni da yasa Abba rintse ido, take wani abu ya faɗo mai, sai ya yi gyaran murya yana cewa.
"Kibar kuka ba wanda ya rasu, naga shekaru sun fara ja miki, kina buƙatar hutu, shi yasa na ce zan baki hutu, ki koma gida gaba ɗaya, zan baki jari da duk wani abu da kike so, sannan lokaci zuwa lokaci in kina so sai ki dinga leƙomu." ya kai nan yana fatan ta gamsu.
Murmushi ta yi sannan ta share hawayen ta tana cewa.
"Alhaji, wallahi ko daga yanzu har zuwa ƙarshen rayuwata zan zauna na yi muku aiki, Alhaji ka min halancin da bazan iya mantawa da shi ba, dan haka ka barni wallahi zan iya, amma idan akwai abinda nake yi kuskure sai ku faɗa min zan gyara." Ta faɗa tana gyara zamanta a kan carpect.
"Babu ko ɗaya, ki shirya kawai." yana kai wa nan ya miƙe ya fara tafiya.
"Alhaji, Nagode Nagode sosai, Allah ya saka maka da alheri." Ta faɗa tana jin babu daɗi har cikin ranta.
Be amsa ba ya haura sama, sai ta miƙe ta koma Kitchen, murmushi ta yi sannan ta kashe gas ta fita, wani ɗan ɗaki dake gefan Kitchen ɗin ta shiga, wanda anan take rayuwa.
Ita ta sani cewa wata rana dole sai ƴam matan gidan nan sun koreta, sam yaran ba su da mutumci, tana matuƙar kai zuciyarta nesa akansu, sai dai kullum cikin addu'a take musu.
Hawaye suka gangaro mata a lokacin da ta kammala haɗa kayanta, tasan da wannan aikin ta dogara, duk da ya ce zai mata komai amma tana son aikin na ta.
Tashi ta yi ta sanya hijab ruwan goro sannan ta ɗauki Ghana-most-go, ta fita Parlour.
Sai ta aje a gefen kujera mai ɗaya sannan ta haura stairs.
A bakin ƙofar su ta tsaya sannan ta fara knocking kamar tana shafa jikin Jariri, dan haka suka ce a dinga musu.
Cikin sa'a ta jiyo muryan Marwa. tana tsaye aka buɗe ƙofar, ai da sauri ta tsugunna tana gaishe da Marwa cike da kulawa.
Marwa dake tsaye jikin kofa ta kalla Asabe da kyau sannan ta ce.
"Fatan dai kin zo mana sallama ne?" Da sauri Asabe ta ɗaga mata kai.
"Shigo to." Da haka ta matsa mata, sai Asabe ta miƙe a hankali sannan ta shiga ciki.
Taku huɗu ta yi sannan ta tsugunna daga gefe tana gaishe da Fauza.
Fauza waya take latsawa, sai ta kalla Asabe sannan ta amsa cikin sakin fuska.
Marwa zama ta yi kan sopa sannan ta ɗaga murya tana cewa.
"Baseey, Baseey come out, kin yi baƙuwa." Takai nan tana mai da hankalinta ga Tv gaba ɗaya.
Riga da dogon wando ne jikin Basma, ta fito tana ɗan magagin barci, ga dukkan alamu ba ta jima da tashi ba. Tana isowa cikin Parlourn nasu ta ci karo da Asabe tsugunne kamar marainiya, take ta saki murmushi tana zama kan hannun kujera sannan ta ce.
"What's going on?."
"Sallama ta zo yi mana." cewan Fauza.
"Aunty Basma, zan tafi dan Allah ku yafe min idan na cutar da ku, Alhaji ya ce......" Cikin sauri ta ɗaga mata hannu sannan ta ce.
"Ok na gane, tashi ki tafi, Allah ya tsare." Tana faɗin haka ta miƙe tare da komawa ciki.
Jiki a sanyaye ta miƙe ta fita, tana aiyana halinsu ba zai sauya ba.
Tana fita ta ɗauki kayanta ta nufa compound, ko amsa gaisuwar da ake mata na ƴan uwanta masu aiki ba ta yi ba, ta nufa motar da zasu fita, tana zuwa ta shiga, Driver ya shiga sannan ya kunna motar suka fita yana mai jera mata tambayar shin lafiya. Sai dai ba ta ce mai ƙala ba dan ta kasa magana...........✍️ END. *PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:
📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*
#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️🔥 ```🔥 TALLAH! TALLAH!! TALLAN MUSAMMAN!!! 🔥 ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU 📢 Jama'a ku fito ku ji labari! Shin kun san Hajiya Safiyya Baiwar Allah? 🤔 Idan ba ku sani ba, to ku matso kusa ku saurara sosai! Ina ƴanmata? Ina matan aure? Wannan damar taku ce! 💃 ✨ Hajiya Safiyya Baiwar Allah ta kawo muku: ✔️ Kayayyaki na zamani ✔️ Masu inganci sosai ✔️ Kuma a farashi mai sauƙi 🛍️ Kayayyakin da ake da su sun haɗa da: Jakkunkuna masu kyau, launi-launi, iri-iri Zanukan gado masu kayatarwa, domin ƙara wa ɗakinku armashi 🛏️ Hijabai masu kyau da ɗaukar hankali 👗 Kayan kitchen masu ƙyau da araha 🍽️ 💥 Duk abin da kike buƙata don gyaran gida da ƙara ƙyalli yana nan a wuri guda! ⚠️ Kada ki bari wannan dama ta wuce ki! 📞 Tuntuɓi yanzu: *** 📍 Location: Unguwar Sunusi, Kaduna 💬 Ko da kuɗinki kaɗan ne, sai kin samu abin da zai burge ki!```
📢 SANARWA TA MUSAMMAN!
*Duk mai son a tallata masa hajarsa cikin tsari mai kyau da jan hankali, ya tuntubi:* 💼 ~PRETTY SK~ 📞 *** ✨ Muna yi maka tallan da zai jawo hankalin kwastomomi cikin sauƙi!🥰
★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story
by ```PRETTY SK ✍️```
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.