PAGE 2
by @prettys01
> Tana fita ta ɗauki kayanta ta nufa compound, ko amsa gaisuwar da ake mata na ƴan uwanta masu aiki ba ta yi ba, ta nufa motar da zasu fita, tana zuwa ta shiga, Driver ya shiga sannan ya kunna motar suka fita yana mai jera mata tambayar shin lafiya. Sai dai ba ta ce mai ƙala ba dan ta kasa magana...........✍️
*KADUNA*
_________Kwance take cikin babban duvet, ta dungule waje ɗaya kamar dai mai jin sanyi sosai, duk da kuwa ita kaɗai ce akan gadon amma haka ta naɗe waje ɗaya. Ɗakin babu makusa dan kuwa komai ya dace da zubin ɗakin, komai na ciki pink ne da fari, hatta gadon pink ne, haka komai na room ɗin.
Take wani sauti ya fara amsakuwa a cikin ɗakin cikin sautin waƙar larabci mai sanyi amma yana da ƙara.
A hankali ta zuro fari kuma tsirin hannunta ta cikin duvet ta kai kan wayar dake gefen bed ta ɗauka sannan ta mai da hannun cikin duvet ɗin.
Wasa-wasa sai da ta kuma kwashe minti biyar kafin ta yaye gaba ɗaya duvet ɗin tana miƙa tare da karanto addu'ar tashi daga barci.
Budurwar yarinya ce wacce a ƙalla ba za ta wuci 18yrs ba, Choculate colour ce mai dogon hanci da fararen idanuwa, sai dai bata da ƙiba sam, amma duk da haka tana da body shape kamar coka-cola.
Idanunta ta lumshe sannan ta buɗe, daidai nan suka sauka akan agogon dake jikin bango. 7:15am na safe, ɗan zaro ido ta yi sannan ta miƙa cikin sauri, a tsakiyar bedroom ɗin ta yarda duvet ɗin sannan ta shiga restroom.
Cikin sauri-sauri ta sakar ma kanta shower. 9mnt ta ɗauka sannan ta fito ɗaure da towel.
Dogon gashin kanta sai yararin ruwa yake dan ta jiƙashi sosai, sharp-sharp ta sanya uniform din Islamiyya, dogon wando ruwan toka, farin riga da dogon hijabi har ƙasa.
Tana zura hijab ɗin, ta ɗauki jakkarta sannan ta fita.
Stairs ta sauka cikin sauri saboda lokaci ya ja sosai. Tana sauka a wani haɗaɗɗen parlour mai rai da lafiya, ƙamshin turaren huta kawai ne ke tashi. A natse ta sauke ajiyan zuciya dan tana son turare a rayuwarta.
Babu kowa kamar yadda ta yi tsammani a parlour, Dan haka ta nufa main door ta buɗe ta fice.
Da yake safiya ce, babu wasu ma'aikata a tsakar gidan, amma Driver ya zama ready saboda ita.
Murmushi ta saki har sai da dimple ɗin ta suka lotsa, saboda ganin ƙawarta tsaye jikin motar da shiga irin na ta.
Tana isa suka rungume juna cikin nishaɗi.
"I'm sorry Rukky na tsaida ke ko, wallahi barci ne ya........" da sauri yarinyar dake sanye da niƙaf ta ce.
"Najlah ya isa, ai ke kullum sai kin bada uzurin barci, latti ai munyi kuma kinsan halin Ustaz." ta faɗa dai-dai nan suka shiga motar.
"Hajiya Najlah ina kwana" faɗin Driver yana kunna motar, murmushi ta yi mai tana cuku-cukun ɗaura niƙaf ta ce.
"Baba Mansir na gaishe ka baka amsa ba, Ni kuma na ce bansan gaisuwar." ta faɗa tana ciro mirrow a cikin pocket din jakkarta.
"Wayyo 8:12am shike nan, sunan mu sorry." Faɗin Rukky tana mai da wayarta cikin jakka.
"Wai menene abin damuwa? Picking datti kawai zamu yi."
"Yau fa ya ce dukka zai yi." Rukky ta faɗa kamar ta yi kuka.
Dariya mai ɗan sauri Najlah ta yi tana duban kan titi, a hankali kuma ta kai hannunta ɗaya ta shafo shafaffen cikinta, take ta tuna ko breakfast ba ta yi ba, sai ta lumshe idanunta.
Jin an yi parking yasa ta buɗe idanunta tana duban in da suke, bakin islamiyyar su ce mai suna *Min-Hajjudeenil Islam* .
A hankali ta buɗe ƙofar ta fita, daidai nan Ruky itama ta fito, sallama suka yi ma Driver sannan suka shiga cikin makarantar ta su.
Makarantar babbar ce sosai, ga classes ta ko ina section-section, gefe guda kuma ga mata nan masu irin shigarsu suna tsaye, gefansu maza ne kusan 15 duk suna sanye da white jallabiya da ash ɗin hula.
"Shike nan har an tare latti, wallahi Ustaz ya shiga uku, shi duk ranar dutyn sa sai ya yi halin nasa."
"Uhmmm Ruky kenan, me hali ai baya fasa halinsa." Faɗin Najlah suka isa cikin ƴam matan nan, wanda duk babu yara a ciki saboda ɓangaren hadda ne Ustaz yake shiga.
"Najlah yau ma kin kuma latti kenan." cewan wata dake tsaye riƙe da manyan takaddu a hannu.
Najlah kuwa murmushi ta yi a cikin niƙaf kafin ta dafa yarinyar tana cewa.
"Umaima kinsan Ni da barci ai, wallahi ko Hadda ban yi ba, sai mun shiga aji zan yi haddar Sallama Ustaz." Ta faɗa cikin barkwanci, dariya sukayi sosai dan kuwa kusan mutane da yawa haka suke mai wannan haddar.
"Innalillahi wa'inna ilaiyi raji'un yau duka zai yi." cewan wata tana zaro ido dan ganin Ustaz riƙe da wata doruna mai baki uku.
Ai nan take matan nan suka ruɗe, dama mata ga tsoron duka balle dukkan Ustaz.
Najlah ta kalla Ustaz take tsaye ya fara yi ma maza dukka 6/6 shida-shida, suna wucewa.
Miyau ta haɗiye mai kauri tana matsawa baya, dan a rayuwarta babu abin da ta tsana kamar bulala, dan ta ga picking suke yi shi yasa take zabga latti abin ta.
"Najlah ya da komawa baya ne? Ki matso a fara mana saboda mu shiga a ji da wuri ko ma yi tilawa kafin ya shigo, ga dukkan alamu yau a rikici ya shigo." Rukky ta faɗa tana dariya ganin yarda yau ya haɗe rai sosai.
Ustaz saurayi ne mai kimanin shekaru 26, saurayi mai baiwar hadda da sarrafa Alqur'ani, tun yana shekara 8 ya haddace Alqur'ani, daga nan kuma ya fara bin ruwayoyi iri-iri yana iyawa, ya samu gogewa sosai da har Saudiya sai da yake da silar Alqur'ani. Dogo ne mai cikar kamala ga gemu burin kowace yarinya, shi kaɗai ne malam mai tsauri a ɓangaren Tahfeez, kuma shi ke riƙe da babbar aji. Be yarda da wasa ko raini tsakaninsa da ɗalibai, amma duk da haka yana da farin jini sosai dan kuwa ƴam mata na nuna suna sonsa, sai dai har yanzu babu wacce ta iya samunsa da wannan maganar, a takaice dai yana da zafi dan kuwa ya ci ainiyin sunansa Umar, amma Ustaz ake ce mai.
A hankali muryarsa mai sanyi ya ratsa wajen yana cewa.
"Kullum sai kunyi latti, to daga yanzu kun dena picking, dukka za dinga muku, nasan za ku yi hankali, ku matso, sannan duk wacce ta bari ita ce ƙarshe dukka 10." ya faɗa yana gyara zaman hularsa wacce ake ce ma taɓa ka ji hadisi.
Ai kafin kice me, mata suka matsawa suna fiddo tafin hannu dan shi ana yake dukka, kowa sai sauri yake karya zama ƙarshe, amma Najlah kuwa tana can baya ta tsira ma tafin hannun ido, tana jin hawaye na cika mata ido.
Kallon yarda yake dukkan ta yi, sai ta yi sauri ta kauda kanta sannan ta gyara zaman jakkarta a baya, tana kallon saura mata biyun da suka rage sannan sai ita, Rukky tuni aka yi mata ta shige aji.
Murmushi ya saki mai sanyi yana kallon Najlah yarda ta tsaya kamar kace tak, ta zura da gudu, ya rasa me Najlah take da shi da yasa baya iya kauda kansa da tunaninta a cikin kansa, yana so yaga tana mai magana, sannan saboda ita yake sanya ƴan ajinsu su ɗaga niƙaf kawai dan yaga fuskarta.
Taku uku ya yi sannan ya kalla matan da ya sallama har sun shiga aji, sai ya mai da idanunsa akan Najlah yana cewa.
"Babu ranar Allah da wannan Baiwar Allah ba za ta yi latti ba, me yasa?." ya kai nan yana haɗiye dariyar da ke shirin kamashi dan kuwa tuni hawaye suka cika mata ido.
"Idan ba za ki yi magana ba, ban hannunki na sallame ki ɗalubai na jira na." ya kuma faɗa yana gyara tsayuwansa, tabbas badan karyayi san kai ba, da ba zai duke ta ba, amma ya zama dole.
Nijlah kuwa, gabanta ne yake ta faɗi, amma haka ta daure, ta aje jakkarta a gefe, sannan ta fizge niƙaf dan ji take zafi na shirin kasheta.
Hannunta ta zuro ta cikin Hijab sannan ta fara to mai addu'ar da duk ya zo bakinta, take kuma hawayen ya shiga gangarowa babu tsayawa.
Miƙa mai ta yi bayan ta durgushe gwiwowinta a ƙasa dan ji take dukka ɗaya zai iya sa ta zuɓe ƙasa.
Numfashi ya yi sannan ya rage tsayin bulalar, a hankali ya kai mata na farko, amma wani irin ihu da Najlah ta saki yatsa ya matsa ɗan baya yana kallonta.
Kuka take kamar ƙaramar yarinya, sannan ta mai da hannun cikin Hijab, ta haɗe kai da gwiwa tana rero kuka cikin wannan muryan na ta mai daɗi..
"Tashi ki wuce aji." Ya faɗa yana yin gaba dan ba zai iya ƙara dukan ta ba kuma be ga alamun tana da shirin bashi hannun ba.
Ko da ya shiga aji, ya nema wajen zamansa ya zauna, sannan ya fara amsar hadda, har ya amsar wa mutane uku Najlah ba ta shigo ba, gaba ɗaya hankalinsa yana kanta, sai da ya fara amsar haddar na huɗu sai ga ta tashigo a jikin duk a sake, tana tafiya sai jan ƙafa take yi.
Kallo ɗaya ya yi mata ya kauda kai, dan kuwa fuskarnan ta ta tayi ja sosai, ga idanunta da suka ƙara ɓula-ɓula, kai kace an kwana ana dukkan ta ne.
Benci na biyu a nan ta zauna kusa da Rukky, barci ne ya cika mata ido, dan haka tana kwantar da kanta sai barci mai daɗi ga ɗauke ta.
Ba ta san tsawan lokacin da ta ɗauka tana barci ba, sai dai jin Ustaz na kiran sunan ta yasa ta farka a firgice.
"Hafsat Abdullahi! Hafsat Abdullahi!!."
"Na.....Na'am." ta faɗa cikin sexy voice da yasa Ustaz Jan dogon hancinsa yana sauke ɓoyayyen ajiyan zuciya.
"Zo ki ban hadda." Ya faɗa yana nuna mata wajen zaman be bada hadda.
Babu musu ta miƙe jikinta a mace, ta isa wajen ta zauna, sai dai kafin ya buɗe baki ta fashe da kuka tana rufe fuskarta.
Ba Ustaz kaɗai ba har ƴan ajin duk kallonta suke yi, duk da kuwa sunsan halin Najlah, ita ba ta ɗauki kuka a wani abu ba sam, duk da girmanta.
"Subuhanallah, me ya faru?." cewan Ustaz yana jin tasirin sautin kukan na ta.
Najlah kuwa, numfashi ta ja sannan ta tsaida kukan tana cewa.
"Yunwa nake ji.........banci abinci ba.....ina jin yunwa." Ta kai nan tana shirin sake fashewa da sabon kuka.
Ai kan kace me ƴan aji suka hau dariya duk da kuwa Ustaz ne a cikin ajikin.
"Kuna hauka ne za ku yi mata dariya, duk ku fita ku yi neeldown." Ya faɗa yana so su bashi waje dan su gana da Najlah sosai.
Fitan suka yi sannan ya mai da hankalinsa kan Najlah ya rage murya sosai.
"Me yasa baki yi breakfast ba?."
"Na yi latti ne." ta faɗa tana kallonsa sosai.
"Muga hannun dana dukka?." Ba musu ta nuna mai tafin hannun da tuni ya washe da radaɗi.
"Kiyaƙuri kinji, banso na dukeki ba, yanzu me kike so ki ci?." Yarda yayi maganar yasa Najlah yin ɗan murmushi sannan ta ce.
"Yanzu Mamie za ta aiko min da shi."
"Sannu autar Mamie." Sai ta ɗaga mai kai tana tura ƙaramin bakinta gaba.
"Dan Allah ki rage saurin kuka, duk ƴan ajin nan sun rainaki, kuma gashi kin girma sosai, ko aurar da ke muka yi za ki zauna." ya faɗa dan so yake ta kuma magana. murmushi kawai ta saki sannan ta ce.
"Ustaz zan iya tafiya wajen zamana?." sai ya ɗaga mata kai.
Yarasa me yasa bata iya tsawaita hira da shi, sai dai yaji daɗin hirar yau.
Wajenta ta koma ta zauna, sannan ya umarci ƴan ajin da su shigo, kowa sai ƙus-ƙus suke yi, dan kuwa sun gama fahimtar Ustaz ya faɗa soyayyar Najlah shaƙwaɓa.
Fita ya yi daga ajin dan kuwa ba zai iya ci gaba da kallon Najlah a haka ba, duk ta koma abin tausayi kamar marainiya.
Yana fita kuwa, ƴan aji aka buɗe chapter.
"Najlah Shaƙwaɓa, kinyi wuff da zuciyar Ustaz fa.........." da sauri wata ta ƙwace maganar Umaima.
"Ba kuga da ya kalla fuskarta sai ya sauke ɓoyayyen ajiyan zuciya ba." take suka ƙwashe da dariya.
A dai-dai nan Driver ya yi mata waya akan ya iso cikin makarantar, kuma malamin su ya amsa zai kawo mata, godiya ta mai sosai, sannan ta kalla ƙofa in da Ustaz ya leƙo yana kiran sunan ta.
Dukka ƴan aji suka yi shuru dan ganinsa, a natse ta miƙe ta isa gabansa ta amsa basket ɗin tana cewa .
"Na gode." ta amsa tana juyawa.
"Please ki ci da yawa." sai ta tsaya cak, a hankali ta kuma juyawa ta kallesa, tana so ta ƙure iskanci ƴan ajin sai ta buɗe baki ta fara magana cikin shaƙwaɓa wanda haka Allah ya yi ta .
"Ustaz uhmmm ina son ruwa mai sanyi dan Allah." ta faɗa yanda duk za su iya ji.
"Okh, Auwal zo." Ya faɗa yana kiran ɗalubi ɗaya daga mazan ajin, ita kuma ta nufa wajenta ta zauna.
Ba ta ce komai ba ta ɗauki abinci ta hau ci bayan ta musu Bismillah, Babu wanda ya kulata.
Tana cikin ci Auwal ya kawo mata ruwa, ta amsa tana mai murmushi.
Abinci kaɗan ta ci sannan ta rufe kular tana duban wacce ke sit ɗin gaba tana cewa.
"Fatima Muhammad Sani, sannu, nace sannu, wai dan Ustaz na tausasamin zai ya zama saurayi na? Hmmmm har da ke Zee, kina wani cewa saboda Ni yake sa a ɗaga niƙaf.........kun raina min wayau fa.......kut hmm" ta faɗa tana ɗan cijan leɓe.
Rukky murmushi ta yi sannan ta ce.
"Cikin ki ya ɗauka dole bakinki ya buɗe."
"Uhmmm, Rukky ki yi shuru, wallahi dai-dai nake da kowa a cikin ajin nan, nasan kunsan Ni, bana ɗaukan robish........"
"Najlah shaƙwaɓa, wannan maganar ba abin ta da jijiyoyin wiya bane, in ma soyayyar ne ai ba wani abu bane, dan kuwa Ustaz ya kai a so shi, malami mai Capacity." cewan wata daga baya, nan fa aka ɗan yi dariya.
"Aunty Murja barni da su, Ni kunsan wani abu ma......wallahi wallahi bana son auren saurayi, na fison Namiji ya ɗan manyata haka, wallahi sun fi iya love." Cewan Najlah tana juyo ido. Nan ma dariya suka kuma sawa dan kuwa in dai ana maganar saurayi, Najlah ce kawai mai ce wa ta fison ta aura mijin wata.
"Ke banda abinki, ai ki aura saurayi shine daɗin aure, me mata kuwa sai yarda aka yi dashi........." da sauri Najlah ta katse Aunty Murja.
"Hmmm Aunty Murja, ni fa banso wallahi na fison na yi aure naje in da zamu dinga show da matar mijina, na taso gidan mu ba wani armashi kuma ace na yi aure na zauna Ni kaɗai.........ke Ni bama zan yarda a kaini wani gida ba, a haɗe mana, kai hmmm a lokacin akwai abu." ta kai nan har ta lumshe ido.
"Ah lallai Najlah baki da hankali, ba kisan kishi ba ko? To wallahi wata akan mijinta har kisa za ta iya yi."
"Allah ya haɗani da irinta Meenal, ai gida haka yafi suger, ance muku zama ina kallon finafinan soyayya da rikici duk a banza ne? Hmmmm, ba zaku gane auren Suger Dady akwai daɗi ba, ba su da damuwa sam, ga iya ririta sosai, kuma duk wani abu da zanyi, sai dai ya ce yarintane, wallahi auren su akwai............" da sauri ta haɗiye sauran maganar ganin Ustaz ya shigo.
Idanunta ne suka sarƙe da na shi, sai ta janye tana mai da hankalinta kan Alqur'ani da ta buɗe amma surutu ya hanata ta yi karatun.
Da ita ya fara ci gaba da amsar haddan, bayan ta fito ta zauna ta fara rero mai shafi ukun farko na Suratul An'am. Daga Ustaz har ɗaluban ajin wani natsuwa ne ke sauakar ma kowa, dan kuwa Najlah akwai baiwar ƙira'a.
Cike mamaki ta ga takai haddar nan babu mistake, tana gamawa ya yi mata sign sannan ta koma ta zauna, farin ciki ne ya kamata dan kuwa ayar da take karantawa ne idan za ta yi barci, shi ke sa ta yi saurin rike abu.
*Wa bil-haƙƙi an zalnahu wa bil-haƙƙi na zal.* Sau 16 kafin ka kwanta barci, yana ƙara kaifin brain.
Suratul Israel Ustaz ya fara karantawa cikin wannan muryan nasa mai ratsa zuƙata, idan akwai abu guda dake burge Najlah da Ustaz, shine iya karatun Alqur'ani, bayan wannan sam baya burgeta, ta fison namiji babba wanda ya girmeta sosai.
Tafseer ya musu sosai, dan yana da ƙyau ga kowani ɗalibin Hadda, da yasan ma'anar abin da yake karantawa.
Ba su suka tashi ba sai 2:30pm, dama sati da Lahadi ne kawai suke Hadda.
Mota suka shiga ita da Rukky suna ɗan hirar karatu, suna shiga Driver ya ɗau hanya.
"Me yasa baƙya kula Ustaz ne? Kinsa baya kula kowacce mace sam, amma ke yana son kuna magana, zan iya rantse kina ji yana kiranki da aka tashi amma ko kallonsa kin kasa yi.....menene matsalarki wai?." Rukky takai karshen maganar cikin jin haushin Najlah.
Murmushi Najlah ta yi sannan ta ce.
"Ƙawata bana son ɓata ma kaina lokaci, bana son shi sam, badan komai ba sai dan ya min yaro sosai." ta faɗa hankalinta a kwance tana latsa wayarta, baki buɗe Rukky ta yi tana jinjina kai.
"Hmmm Najlah kinfi ƙarfi na wallahi, ke dai ba'a gane alƙibilanki, ai na bashi number ki kuma zai kira ki."
"Na ji amma wallahi bana son shi, dududu ba zai wuci 27yrs ba, amma nafison mai +40yrs."
"Allah ka ganar Najlah." ta faɗa a yin da take shirin fita daga motar, da sauri Najlah ta riƙe mata hannu tana marairaice fuska sannan ta ce.
"An jima ki leƙo musha hira, sannan muyi aikin Ustaz, in ya so sai mu raba hukunce-hukuncen, da kowa ya gama nashi sai mu kwashe na juna, ba lallai ya gane ba." Ta kai maganar cikin salon muryarta mai sanyi da shaƙwaɓa, duk da haka ta ke ko in ce Mamie ta sangantata.
"Malama ba hula ne a kai na ba, ki dena kashe min wannan idanun naki masu kama da wacce ta bugu, in da sarari zan shigo." Cewan Rukky tana ma Najlah dariya ganin ta ɗaure fuska.
Ƙofar ta rufe musu, sannan Driver ya ƙarasa gidan dake gaban wanda Rukky ta shiga sannan ya danna horn..........
****************
Gyalen kanta ta gyara zamansa sannan ta fiddo wayarta tana ɗan dubawa, tsaki ta kuma ja tana kallon wayar Abba dake kan showglass na Parlournsa. Be jima da ya tashi ya shiga ɗauƙo mata key ɗin mota ba, amma kira na uku kenan dake shigowa.
A natse ta miƙe ta fara takawa zuwa wajen, daidai tana ɗaukan wayar, Abba ya fito daga bedroom.
Sai ta kalla sunan dake kai sannan ta kallesa, take ɗan annurin dake fuskarta ya ɗauke, ta kalla Abba da ƙyau tana cewa.
"Wacece Miss Ayo?" sai Abba ya yi murmushi yana jin soyayyar babbar ƴar tasa.
"Marwa sabuwar mataimakiya ta ce." ya faɗa yana miƙa mata key ɗin daya ɗauko.
Har ta miƙa mai wayar wani kiran ya kuma shigowa daga Miss Ayo ɗin.
Cikin sauri Marwa ta yi pecking duk da kuwa ta yi latti sosai zuwa school.
Cikin salo da karya murya wata murya ta daki kunnuwansu daga cikin wayar, duk da kuwa kana ji kasan ba bahaushiya ba ce.
"Good morning Alhaji, dan Allah in baka wuce ba, ka biyo ta gidana ka ɗauke Ni sai mu tafi meeting ɗin tare, motata ya lalace........." ai cikin masifa da tsiwa Marwa ta ce.
"Ɗan dakata Malama, wacece ke? Uban me wa ya baki umarnin kiran Abban mu? Lallai ashe baki da hankali......."
"MARWA!." faɗin Abba a ɗan tsawace dan kuwa Miss Ayo babbar macece.
Wayar Marwa ta saki ya faɗi akan carpet sannan cikin rawar murya kamar mai shirin fashewa da kuka ta ce.
"A......Ab....Abba tsawa kake min akan wata......Abba yanzu amanar Mom kake ci dama....." Sai hawaye shar kaman an buɗe panpo.
Shafa suman kansa ya yi sannan ya ce.
"No Marwa. Ba haka bane, aiki kawai muke tare amma......." Sai ta ɗaga mai hannu tana cewa.
"Ya isa." Da haka ta aje mai key ɗin ta juya ta fita da guda tana share hawaye.
Abba kuwa kasa ƙwaƙwƙwaran motsi ya yi, a hankali kuma ya zauna a kujera mafi kusa da shi, yana zama ya lumshe idanunsa, ya rasa meke damun su Marwa, in dai akan kishi ne, babu ikon mace ta kirasa to sai ya yi da gaske suke haƙura, har ga Allah yana son ya yi aure tun a baya amma saboda tsoron abin da zai faru yake fasawa.
Ba zai manta lokacin da ya nema wata Bazawara ba Amina, besan yarda aka yi ba har dai Marwa ta sani, a ranar suka nufa gidan su Amina, suka ci mutumci kowa na gidan, sannan ta ma Amina kashe sosai ko ya ce jan kunne dan kuwa harda sojoji biyu ta je, shi kansa ya ga abu dan sai da suka dena mai magana na fiye da wata ɗaya, sai da ƙyar suka haƙura akan ba zai sake kula kowacce irin macce ba, shi kuma ya amince.
Wai dogon numfashi ya kuma ja, sannan a hankali ya miƙe yana mai bin hanyar fita ɗan duba halin da Marwa take, duk da yasan zuwa yanzu ta faɗa ma Basma, dan Fauza ta wuce school tun ɗazu....................✍️ END.
> Ba wasa wannan alƙalamin mai zafi na ɗauka.
*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:
📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥* ```🔥 TALLAH! TALLAH!! TALLAN MUSAMMAN!!! 🔥 ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU 📢 Jama'a ku fito ku ji labari! Shin kun san Hajiya Safiyya Baiwar Allah? 🤔 Idan ba ku sani ba, to ku matso kusa ku saurara sosai! Ina ƴanmata? Ina matan aure? Wannan damar taku ce! 💃 ✨ Hajiya Safiyya Baiwar Allah ta kawo muku: ✔️ Kayayyaki na zamani ✔️ Masu inganci sosai ✔️ Kuma a farashi mai sauƙi 🛍️ Kayayyakin da ake da su sun haɗa da: Jakkunkuna masu kyau, launi-launi, iri-iri Zanukan gado masu kayatarwa, domin ƙara wa ɗakinku armashi 🛏️ Hijabai masu kyau da ɗaukar hankali 👗 Kayan kitchen masu ƙyau da araha 🍽️ 💥 Duk abin da kike buƙata don gyaran gida da ƙara ƙyalli yana nan a wuri guda! ⚠️ Kada ki bari wannan dama ta wuce ki! 📞 Tuntuɓi yanzu: *** 📍 Location: Unguwar Sunusi, Kaduna 💬 Ko da kuɗinki kaɗan ne, sai kin samu abin da zai burge ki!```
📢 SANARWA TA MUSAMMAN!
*Duk mai son a tallata masa hajarsa cikin tsari mai kyau da jan hankali, ya tuntubi:* 💼 ~PRETTY SK~ 📞 *** ✨ Muna yi maka tallan da zai jawo hankalin kwastomomi cikin sauƙi!🥰
★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story
by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.