PAGE 4
by @prettys01
"Marwa kike ko? Hmmmm auren Al-hussain zai iya zama babbar masifa a rayuwarki saboda *PROMISE* ." sai ta kunna motar tana nufan get ɗin fita daga makarantar.............✍️
Direct wani babban Companyn haɗa duk wani abubuwa da ake gini da su ta nufa, hatta cement suna bugawa, Company yayi suna sosai, *A.M.A NIGERIA LIMITED* , hatta gidaje suna siyarwa, haka kuma suna da hotels duk masu ɗauke da wannan sunan a manyan unguwanni.
Tana sauka a mota ta fita tana sanya chewing gum a bakin.
Merry, a ƙalla ba za ta wuce 23yrs ba, ba ta da wani tsayi sosai, sannan tana da duhun fata, sai da akwai da ta ƙyau masha Allah.
Ɓangaren manager ta nufa kai tsaye, tana shiga duk wanda ya ganta sai ya gaisheta da girmamawa, da kai kawai take amsawa, har ta isa babban office.
Ba ta tsaya knocking ba ta tura tashiga, tana shiga idanunta suka sauka akan Al-hassan dake zaune kan kujera yana operating system.
> Ni marubuciya sai da na ɗan tsorata, dan ganin sak Al-hussain zaune kan kujera, basu da banbanci ta komai, hatta shigar dake jikin wancan shine a jikin wannan, farin riga mai dogon hannu, da Black jeans, sannan ɓakin gashin kansu sunyi cum iri ɗaya, hatta murmushin su iri ɗaya ne sak........ya Allah, wannan kamar ta yi mugun ɓaci jama'a.
"Al-hassan Barka da wannan lokacin." ta faɗa tana zama kan wani kujera.
"Yauwa Merry, ya Al-hussain ɗin? Fatan yana lafiya." ya faɗa da irin muryan wancan ɗin.
"Uhmmm ai kai a rayuwar duniyar nan ba ka da wanda kake tambaya fiye da shi, ko Ni baka ban kulawa haka, sannan zan iya cewa ko 10mnt ba ka yi da kiran sa ba .......ya girma fa ba yaro bane." ta faɗa tana haɗe girar sama da ƙasa.
Murmushi Al-hassan ya yi sannan ya ce.
"Au ashe abin da kika ce ma Al-hassan kenan idan bana nan, to Hussain ne." ya faɗa yana ƙura mata.
Ɗan zaro ido ta yi tana ƙare mai kallo, harga Allah ba ta iya banbance su sam, dan komai nasu iri ɗaya ne, da dai Hassan yana da wani tabo a gefan kumatunsa na hagu, sai dai bayan wani lokaci Al-hussain ma yaje ya yi tabon ya zama babu mai gane su, gashi kansu a haɗe idan in suka so, suna iya sauya wa kansu suna.
Gaba ɗaya kanta na kullewa akansu, sai dai take ta tuna reaction ɗin da Al-hussain ya yi a school, wanda Al-hassan baya da wannan yanayin na soyayya, kuma da Al-hussain kawai take da matsala saboda *PROMISE* .
"Hmmm Al-hassan kai ne anan, wancan ɗan soyayyar yana can wajen Marwa." sai Al-hussan ya yi murmushi yana cewa.
"Ɗan soyayya ne kam, yanzu dai tashi ki hau aiki, na tura miki zanen wannan gidan ki duba tare da lissafin kayan aiki."
"Ok, kace Chairman ya motsa." Ta faɗa tana miƙewa sannan ta fita daga office.
Murmushi ya yi sannan ya ci gaba da aikinsa amma rabin hankalinsa yana kan Al-hussain, duk da basu jima da yin waya ba amma yana son ya kuma jin muryansa............
*KADUNA* Ko bayan da ta shiga cikin Parlour nan, ba ta iske kowa ba, sai ta aje jakkarta kan kujera sannan ta nufa ɓangaren Mamie, tafiya take tana ɗan yi waƙe-waƙe dan Najlah gwamace wajen waƙoƙin soyayya.
Handle ɗin ƙofar ta buɗe sannan ta shiga bakinta ɗauke da sallama.
Wata babbar mace ce zaune daga saman sopa tana riƙe da waya tana latsawa, kai daga gani kasan ta dace da zaman parlour, fara ce ƙal matar, gata mai jiki Masha Allah.
A hankali ta kalla Auta wacce ta shigo ta tsira mata ido, sai ta yi mata alama da hannu da nuna mata cinyarta.
Ai kuwa da sauri Najlah ta isa wajen tana zama kan cinyar Mamie tare da fara magana cikin yanayinta.
"Uhm kiyakuri Mamie, bansan na yi latti ne shi yasa na tafi makaranta banyi breakfast ba." ta faɗa tana kwantar da kanta jikin Mamie.
A natse Mamie ta buɗe baki tare da cewa.
"Na dena amsar wannan uzurin ki sauya wata.....Dan Allah ji beki! Kullum ƙarewa kike kamar ana ɗibanki ana miya, bakison cin abinci, ga kinan kaman fallen Littafi, a haka wai kina aikin ƙarfi hmmmm." ta kai nan tana ɗan girgiza sirirn hannun Najlah.
Baki ta tura gaba tana ƙare shigewa jikin Mamie sannan ta ce.
"Ina ci fa yanzu.....jiya da yamma indomie ɗaya na cinye, haka abincin da kika samun kusan rabi na ci, kinsan ba'a son muna cin abinci masu nauyi ko da yawa."
"Hmmmm na ji amma ban yarda ba....." sai maganar na ta ya katse sakamakon buɗe handle ɗin da aka yi tare da sallama.
Take Mamie ta faɗa ɗa murmushi ganin manyan yaranta biyu sun shigo cikin uniform ɗin sojoji.
Najlah kuwa kallo ɗaya ta yi musu ta lumshe idanunta tana ƙare matse Mamie a jikinta.
"Mamie Ina wuni fatan kina lafiya?." suka haɗa baki wajen faɗa.
"Lafiya lau Mazan fama, ya Barack?."
"Alhamdullah." Cewan babban ciki.
Maza biyu ne wanda kusan tsayin su ɗaya, sai dai kana kallonsu kasan mai duhun fatan shine babba, saboda ya fi cikar fuska da cikar haiba, duk a murɗe suke sosai.
"Ke kuma uban me kike yi a jikinta haka? Sai kin karya mana ita?." Cewan ƙaramin cikin tsokana.
"Allah na tuba, wannan ai ba za ita karya Mamie ba, yarinya kamar sandar rage, a fige take kamar kazan Mayu......" take ya haɗe maganarsa ganin Mamie ta haɗe fuska.
"Yayansu ka fita a idona wallahi, kaima Adam haka, duk saboda bakin ku ne yarinyar nan ta ƙi ƙiba, to sai ku sa ta a gaba ku yi ta mata habaici, gashi daga zuwanku kunsa ta fara kuka.......ku tashi ku koma in da kuka fito shine kawai." ta kai maganar tana ɗan kashe musu ido ɗaya alamar wasa take musu.
"Mamie ashe da kazar Mayu nake kama?." Ta faɗa tana shirin fashewa da kuka.
"Barsu ai, yanzu za su tafi karki damu kafin anjima kema ki wuce." Sai Najlah ta ɗaga mata kai sannan ta buɗe idanunta da suka yi ja tana cewa.
"Ya Adam ka ɗauko ma Mamie towel za ga goyani barci nake ji." ta faɗa tana ɗan hamma.
"Auta ko cikina zan iya mai da ke ai, Yayansu ɗauko min a cikin drawer." cewan Mamie duk cikin wasa.
"Ke ai baki da hankali sam, dalla tashi ki shirya, kinyi ɓako, wannan shine saurayi na 7 da na kawo miki, karki kuskura ki yi rejecting din sa, yaron akwai hankali da natsuwa." Cewan Yayansu cikin haɗe fuska, wanda shine zai sa Najlah ta fahimci ba da wasa yake ba.
"Kudai kuna da matsala, wai dole sai ta yi aure ne yanzu, 18yrs fa, amma kun isheta da maganar aure, ga ku geme-geme da ku baku da budurwa bare mata."
"Mamie kinga mu Maza ne, muna lasting, amma kinga wannan yarinyar duk abushe take, idan muka barta nan gaba ko ganuwa ba za ta yi ba." cewan Adam cikin tsokana.
Daƙuwa Mamie ta yi mai tana cewa.
"To wasa ya wuce, Najlah je ki shirya ki zo ki ga yaron, ina fatan ku daidaita da shi." sai Najlah ta miƙe daga jikin Mamie sannan ta ce.
"To amma wallahi idan yaro ne bazan yarda ba." ta faɗa tana tura baki sannan ta nufa ƙofa ta fice.
Murmushi suka yi sannan Mamie ta ce su je ƙasa su ci abinci, za ta leƙo idan saurayin ya wuce, da haka suka sauka zuwa ƙasa, suka beje a tsakiyar parlourn suka hau cin abinci tare da wani abokin aikin na su.
Kusan 15mnt suka ɗauka kafin suka fara jin ƙara akan stairs, sai duk suka mai da hankalinsu a kan wacce ke tafiyar, da sauri Yayansu ya ɗan zaro ido yana haɗe girman sama da ƙasa.
Ko uniform ba ta cire ba, hasalima yarda take haka ta sauko, tana tafiya tana turo wannan bakin nata, a natse ta iso cikin Parlour sannan ta nema waje ta zauna tana gaishe da saurayin dake zaune sai zabga mata murmushi yake yi.
Haɗe fuska ta yi sosai tana ƙarema saurayin dake zaune kallo.
Saurayi ne wanda ba zai wuci 25yrs ba, yarinya duk yana bayyane a fuskarsa, gashi ko ɗan gemun nan babu, sai dogon hanci kaman pensil.
Numfashi ta ja sannan ta mai da hankalinta akansa da yake magana cikin natsuwa amma muryansa babbar ce sosai, kai kace ana dukan durom.
"Sunana Sulaiman, nasan sun isar miki da saƙon, gaskiya Adam ta yi min, ina sonta......." da sauri maganar na sa ya tsake, jin wani irin tsawa da Najlah ta yi mai.
Shi abin dariya ya bashi, sai ya saki murmushi yana kallon yarda da miƙe tsaye sai faman huci take yi.
"Ni kuma baka min ba! Bana sonka......Bana sonka......dan haka ta kama kanka, Yaya sau nawa nake ce muku ku bari da kaina zan kawo muku zaɓina......wannan be min ba." ta kai nan tana kallon cikin idon Yaya dake kallonta cikin ɓacin rai.
"Ke wai waye sa'an ki? Faɗa min menene aibin Sulaiman?." cewan Adam a hassale.
"Saboda yaro ne! Na ce muku babban mutum nake so haba dan Allah." daga haka ta juya ta fara tafiya.
"Ni kuma nace yamin, dan haka zai dinga zuwa zance lokaci zuwa lokaci." ɗan zaro ido ta yi sannan ta juya ta kalla Yaya.
Tabbas Najlah kala biyu ce, akwai ta da shaƙwaɓa sosai, sai dai tana masifa da mugun taurin kai, duk kuma halin Babansu ne wanda ya rasu tun shekarun baya a wajen wani yaƙi da ƴan ta'adda.
A natse ta ci gaba da tafiya har zuwa kusa da Sulaiman dake zaune, zama ta yi gefansa sannan a buɗe baki ta ce.
"Ka ce da su baka shirya mutuwa ba, dan wallahi aurena mutuwa ce a gareka, ba kashe ka zan yi ba, zan dai gana maka azaba ne iri-iri, dan kuwa fatar jikinka zan dinga ɗayewa, uhmmm ka dai yi tunani, Ya Adam, babu mai aura min wanda bana so a cikin ku, dan Allah ku kama kanku." takai nan tana wani mugun murmushi.
Da haka ta bar musu parlourn gaba ɗaya, ba ta kuma fitowa ba sai da ta tabbatar da sun bar gidan, sanan ta saki jikinta ta ci gaba da abubuwan da suke gabanta.
Kamar yadda ta yi tsammani Mamie ba ta ce mata komai ba akan saurayin, sai ita ma ta basar, wajen 5:00pm na yamma, Rukky ta zo suka yi assignment tare, sai gab da magrib ta wuce gida bayan sunyi sallama dan kuwa anjima kaɗan za ta wuce makaranta.
Ba ta samun ishanshen barci sai weekend, Shi yasa ba ta wasa da kowani dama idan ta samu.
Tana sallar isha'i ta kwanta barci mai daɗi ya ɗauke ta, sai dai ba ta jima ba aka fara tashin ta, ko da farka ta ga Mamie tsaye a kanta, sai ta yi murmushi sannan ta miƙe tana rungume Mamie ɗin.
"Ki tashi ki koma makaranta, zan kira wayar Yayanku gobe muyi waya." Sai Najlah ta ɗaga mata kai.
Ba musu ta tashi ta shiga toilet, bayan ta fito ta ɗauki wani ƙaramin jakkan baya ta goya sannan ta kashe wayarta tana miƙa ma Mamie.
"Ga wayata ki dinga kunnawa somethings, Dan sai nan da two weeks zan dawo" sai Mamie ta ɗaga mata kai tana jin kewar ƴar ta ta.
Hannunsu cikin na juna suka fito Compound ɗin gidan, wanda hasken fitilune ta ko ina saboda dare.
"Ki kula da kanki, sannan ki rage wannan narkewan da kike yi." Sai Najlah ta ɗan yi dariya, daidai nan suka isa kusa da wata mota dake tsakiyar gidan.
Wasu mata biyu suka fito daga sit ɗin baya, suna sanye da farin t-shirt da gajeren wando shima fari ƙal, sai ɗaya ta ɗaura p-cap akanta.
Gaishe da Mamie suka yi cikin natsuwa ta amsa tana musu murmushi.
Hijab ɗin jikinta ta cire tana ba Mamie, take shigar dake jikinta ya bayyana, sai irin na matan nan, harda white shoe, sai ta ƙara ƙyau, du kuwa da ita ce siririyan ciki sauran su fita cika.
Wani ɗan ƙwali ta ɗan ɗaura a kanta tana cewa.
"Bin Uthman, faɗa ma Mamie ya nake komawa a school, gani take bana iya komai." ta faɗa tana kallon ƙawayen nata.
"Mamie, gaf ajin mu Najlah ta fi kowace macce hazaƙa, duk da itace siririya a cikin mu, amma tana aikin da yafi na matsayin mu, da kinsan irin horon da muke sha da baki ce haka ba, tun asuba muke tashi mu fara training, har cikin Barack muke shiga, muna shan wahala sosai." wacce ta yi maganar ta kai nan tana ɗan dafe goshinta. Sai Najlah ta ce.
"Kawai Duka ne bana so, amma ko wani punishment zan iya jura na tsawon awanni."
"Najlah muje yanzu pass 10."
"Ok Amanda let's go.... Mamie take care, I Miss you." da kuma rungume Mamie, sannan suka shiga mota, wani jami'in soja ya kunna mota suna barin gidan tare da nufan *Unity Military Academy* dake kusa da Barack na sojoji..........✍️ END.
*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:
📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*
#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️🔥 ```🔥 TALLAH! TALLAH!! TALLAN MUSAMMAN!!! 🔥 ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU 📢 Jama'a ku fito ku ji labari! Shin kun san Hajiya Safiyya Baiwar Allah? 🤔 Idan ba ku sani ba, to ku matso kusa ku saurara sosai! Ina ƴanmata? Ina matan aure? Wannan damar taku ce! 💃 ✨ Hajiya Safiyya Baiwar Allah ta kawo muku: ✔️ Kayayyaki na zamani ✔️ Masu inganci sosai ✔️ Kuma a farashi mai sauƙi 🛍️ Kayayyakin da ake da su sun haɗa da: Jakkunkuna masu kyau, launi-launi, iri-iri Zanukan gado masu kayatarwa, domin ƙara wa ɗakinku armashi 🛏️ Hijabai masu kyau da ɗaukar hankali 👗 Kayan kitchen masu ƙyau da araha 🍽️ 💥 Duk abin da kike buƙata don gyaran gida da ƙara ƙyalli yana nan a wuri guda! ⚠️ Kada ki bari wannan dama ta wuce ki! 📞 Tuntuɓi yanzu: *** 📍 Location: Unguwar Sunusi, Kaduna 💬 Ko da kuɗinki kaɗan ne, sai kin samu abin da zai burge ki!```
📢 SANARWA TA MUSAMMAN!
*Duk mai son a tallata masa hajarsa cikin tsari mai kyau da jan hankali, ya tuntubi:* 💼 ~PRETTY SK~ 📞 *** ✨ Muna yi maka tallan da zai jawo hankalin kwastomomi cikin sauƙi!🥰
★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story
by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.