BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 5

by @prettys01

> "Ok Amanda let's go.... Mamie take care, I Miss you." da kuma rungume Mamie, sannan suka shiga mota, wani jami'in soja ya kunna mota suna barin gidan tare da nufan *Unity Military Academy* dake kusa da Barack na sojoji..........✍️

Tafiyan minti 30 ya kai su *Unity Military Academy*, makarantar horon soja, wannan makarantar ta fi fice a gaba ɗaya Kaduna state, saboda tsanani da kuma horon ta, daga mata har maza, sannan duk wani ɗalibin su sai ya cika wasu matakai yake samun tsallake ko wani irin horon su, suna dabbar tsaro a cikin makarantar, idan ɗalibi ya shiga baya fita sai da babban dalili.

Najlah a class ɗin su ita kadaice take zuwa gida duk bayan sati biyu, ta kwana biyu, dan ganin Mahaifiyarta ta zuwa hadda, da yake tun kafin mahaifinta ya rasu yake kai ta, sai bayan rasuwar su ake kaita gida.

A cikin haraban school aka ajesu, wanda wani net na ƙarfe ne ya rabasu da barrack.

Suna fita suka yi ma sojan godiya sannan suka nufa ɓangaren mata in da suke kwana.

Hostel ɗin kaman wajen kwanan ƴan boarding, gadone masu hawa biyu, a jere har ya cinye wannan wajen, gadaje guda 40 ne cif, sai dai akwai tsari wajen sosai, sannan kowanne gado yana da ƙaramin fankar dake bashi iska.

Najlah da ƙawayenta suka shiga kansu tsaye suna ɗan hira sama-sama, suna shiga suka iske mata kusan agemate ɗin su da yawa, wasu na barci wasu kuma suna hira amma kallo ɗaya za ka musu kasan duk a gajiya suke. Sannan wani doguwar riga ne duk suke sanye da shi, iya gwiwa yar kanti, wanda ya dace da yanayin da ake a yanzu.

Gaisawa ta yi da wasu da suke hira, sannan ta nufa gadonta, wanda ƙasa gadon za ka ja take wani lucker na kaya ke bayyana.

A wajen ta sauya kaya sannan ta haye gadon sama tana ce ma Bin Uthman.

"Yau ki kwana a ƙasa, wallahi zafi nake ji, kuma ma kin ɗana da bananan."

"Ba damuwa ki kwanta, Sir J. Yace gobe akwai fitar 3:30am, dan haka na kwanta, good night." ta faɗa tana ƙwanciya a gadon ƙasa.

Ƙaramin tsaki Najlah ta ja tana kallon Amanda da tuni barci ya ɗauke ta.

Murmushi ta yi dan rayuwar zama soja akwai wahala amma akwai daɗi, suna shan azama fiye da misali, amma duk sun goge sosai, babban burin ta shine zama Soja kamar mahaifinta, tana so ta yi aikin ƙwaƙwarmaya sosai kafin ta mutu, hakan yasa take kuma dagewa, a baya tana son auren Soja saboda ta ƙare rayuwarta a cikin Barack, amma yanzu ba ta so sam, tana so ta samu wani rayuwa a can gafe daban.

Tunawa ta yi da kiran da Ustaz ya yi mata a ɗazu da yamma lokacin barci ya gama cin kanta, ta ji wayar ta yi ringing, sai ta ɗauka ta kai kunni tana sallama cikin kasala da natsuwa.

Wannan sanyayyar muryar nasa ya daketa yana jero mata kirari bayan amsa gaisuwanta.

"Kece ƙƴaƙƴƙƴawan fitilan dake haskaka sararin samaniya, tauraruwa mai annuri da shaƙi, ustaziyya mai zazzaƙan murya, Najlah komai naki daban ne, ina sonki fiye da zato, soyayyarki ta gama ratsa min ɓargon jikina." ya kai nan yana ƙara tausasa harshe, sai dai kafin ya ci gaba da magana, Najlah ta ce.

"Ustaz kalaman soyayyar sun burgeni sai dai kai kanka baka min ba, ba wai baka da ƙyau ba ko wani abu, sai dan bazan iya auren ka ba, nasan kasan ina karatun soja, kuma yarda nasan familyka mutanene masu mai da mace Matar gida, daga gida sai neman addini, to Ni kuma Soja nake son zama, rayuwar mu sam ba zai yi daidai ba, sannan ba ɓoye-ɓoye da ace kai suger Dady ne, wallahi zan amince, zan aureka, duk kuma wanda ya ce zai ta da jijiyoyin wiya akan haka zan yi maganinsa............. a mutumce ka ya ƙuri da ni, Allah ya ba ka macce ta gari." ta kai nan tana son katse wayar sai dai jin maganar sa cikin wani irin yanayi yasa ta tsaya tana saurarensa.

"Yanzu baƙya sona kenan?."

"A'a, ta ya zance bana sonka! Kaifa Malami nane kuma ɗan uwana a addini, ina sonka amma ba soyayyar aure ba, sai an jima." da haka ta kashe kiran tana blockimg ɗinsa....

Barci ne mai daɗin gaske ya ɗauke ta tare da tunanin irin training ɗin da za su sha zuwa gobe ko tace nan da ɗan awanni......................

*Abba.*

Ko da ya dawo gida, a parkour ya zauna yana jiran dawowar Marwa da Basma, Fauza kawai ya samu ta dawo daga school, cikin fara'a ta amsa mai gaisuwar har suna ƴar tsokana, hakan yasa fahimci basu sanar da ita komai ba.

Su biyu suke zaune a parlour buna kallo, sai dai shi Abba hankalinsa na kan yaransa, yasan Marwa tana tare da Al-hussain, be san dalili ba yaron sam be yi ba, ace tun safe har yamma suna tare da Marwa, shi zai kawota gida daga school, sannan su zauna suna hira har magrib, daga nan ya wuce, to insha Allah daga isha'i suke fara waya har cikin dare, gaba ɗaya yaron be da sa'a, ko da ya tambaya Marwa sai ta ce mai.

"Ɗan uwansa ke juya musu dukiyar su." da haka be kuma sake maganar yaron ba, ya dai bari yaga iya gudun ruwansu ne kawai.

Jin an buɗo ƙofa an shigo yasa, ya mai idanunsa kan ƙofar, Basma ce ta shigo hannunta riƙe da farin rigar likitanci, tana haɗa ido da Abba, ta haɗe rai tana turo baki sama.

Leɓanta kawai ya motsa alamun gaishe shi take yi, sai ya amsa yana ce mata.

"Basma ina kika tsaya sai yanzu?." ya faɗa cike da kulawa.

Kamar ba za ta amsa ba sai ta ce.

"Asibiti muka je. Fauza tashi ki koma ɗaki." ta faɗa tana ƙare haɗa fuska, kamar Hajiya Karima da kanta, dan wani lokacin ita take komawa sak.

"Kallo nake yi, a ɗakin mu babu channel ɗin nan." cewan Fauza.

"Na ce ki tashi ki koma ɗakin mu, dan kuwa wannan parlourn yana gab da a kawo mai shi, dan kuwa Abba aure yake nema."

Cikin mamamki Fauza ta kalla Basma sannan ta mai da idanunta kan Abba.

"Abba da gaske aure za ka yi?." ta tambaya kamar mai jin tsoron abin da zai ce da ita.

"Yanzu ba aure nake nema ba, amma idan ina da rabon yi zanyi, komai Allah ke tsarawa." ya faɗa yana tuna abin da Miss Ayo ta ce mai da aka tashi wajen aiki. 'Sir ya kamata ko baka da ra'ayin auren, ka dinga nuna musu za ka iya yi, kawai su zama ready, ko da da wasa kake musu, idan yau ka faɗa be yi musu tasiri ba, washe gari zai yi musu, ya kamata suna jin shakkar ka.'

Besan dalili ba sai kwai ya ji yayi na'am da wanan maganar.

"Mene!? Abba aure kuma? Akan wani dalili?" cewan Fauza cikin tashin hankali.

"Fauza aure dai wanda kika sani, amma ba yanzu ba sai nan gaba zan......." da sauri ya mai da idanunsa kan Basma, wani tukunyar ƙasa da aka yi mai ado da furannin ɗaki, shi da buka a ƙasa ya tarwatse.

"Wallahi Mom ɗin mu ba ta da Kishiya, babu wata macce da za shigo gidan nan ta rayu wallahi babu ita." ta faɗa tana yarda wasu ƙwalaɓe a ƙasa, aikuwa ɗaya ya yanke ta.

A ɗan ruɗe Abba ya yi kanta ta ɗaga mai hannu, sannan ta kalla jinin dake ɗiga daga hannunta zuwa ƙasa ta ce.

"Idan har da gaske auren za ka yi, to duniyar zamu bar maka, kamar yarda jinin nawa ke zuba haka zan yanke jikina, wallahi Abba ba zan jura ganin wata maccen da sunanan Kishiyar Mom ba.........zan iya kashe koma wacece." sai ta fashe da kuka tana yarda rigar hannunta.

Cikin sauri Abba ya nufeta sannan ya riƙe hannun da jinin ke ɗiƙa, ya danna yatsansa a wajen yana girgiza mata kai.

"Kune rayuwata, ba zan jura ganin kuna cikin damuwa ba a kai na, maganar aure ne daga yanzu na rufe sa har abada." ya kai nan yana jin soyayyar yaran nasa na ƙaruwa a cikin zuciyarsa.

"Dan Allah karka sake maganar wata maccen, ji nake zuciyata na ci da wuta."

"Insha Allah, Baseeyna share hawayen kinji." sai ta rungumesa tana goge hawayen na ta.

Da yake tsakanin Uba da ɗa sai Allah, kan kace me suka shirya, da kansa yayi ma hannun dressing, sannan ya basu abinci a baki, dan sun yi sabuwar mai aiki.

Ba laifi ta iya aminci sosai, so suke suga takun na ta Ƙafin su amince.

Abinci suke ci cikin nishaɗi da walwala kamar ba su ba, Abba ya zage yana basu abinci da musu hirar ban dariya, amma cikin zuciyarsa kuwa yana nan da wannan maganar ta ƙarin aure ko ta tsiya ko ta arziƙi.

Akwai masalci a cikin gidan wanda yake da ƙofa biyu, ɗaya na cikin gidan, ɗaya kuma yana waje gidan, me gadi ke kiran sallah, 6:30pm ya kira sallah, dan haka Abba ya nufa bedroom ɗin sa, Alwala ya yi sannan ya fito yana sanya lins ɗin hannun riga.

Yana fitowa tsakiyar Parlourn, sai ga Marwa ta shigo, tafiya take cike da nishaɗi, sai blushing take yi, sai dai suna haɗa ido da Abba ta haɗe rai sosai, ta buɗe baki ta ce.

"Sannu da gida Abba." sai ya yi murmushi ya ce.

"Lafiya lau, Al-hussain ɗin ya wuce kenan?." Sai ta ɗaga mai kai sannan ta haura sama, shi kuma ya girgiza kai sannan ya fita.

Marwa na shiga part ɗin su, ta aje handbag ɗinta kan sopa tana kallon Basma take kallo a tv.

"Abba tin yaushe ya dawo?."

"Nima a gida na same sa." sai ta taɓe baki sannan ta zauna tana cewa.

"Sai na ga hankalinsa a kwance, ba dai kun mai magana ba!?." ta faɗa cikin tuhuma.

Basma kuwa sai ta mai da hankalinta kan Marwa.

"Karki damu mun shirya, sannan ya yi nadaman abin da ya yi, ke kinsan na fiki ɗaukan komai da zafi, amma tunda na bar zancen kema ki bari kawai......kalla hannuna duk saboda haka na ji ma kaina ciwo." ta kai nan tana nuna mata hannunta.

Da sauri Marwa ta isa kusa da ita tana kallon hannun da yasha bandage.

"Why Basma!?."

"Hmmm saboda ya tabbata ba wasa nake ba, never mind, tashi ki watsa ruwa ki huta." Sai Marwa ta ɗaga mata kai tana cewa.

"Amma karki sake, bana so wannan ai be dace ba, da waccan matar muka samu sai mu yankata zai fi ai."

Sai Basma ta yi murmushi tana mai da hankalinta kan tv, ita kuma Marwa ta shiga babban bedroom ɗin su..............

*Al-hussain*

Kwance yake yana barci a natse, kai daga ganin yarda yake sauke ajiyan zuciya zai tabbatar maka da hankalinsa a kwance yake sosai, ga wani iska na A.C plus turarukan ɗaki masu samar da natsuwa.

Yana da haske daidai, gashi cikakken namiji mai cikar haiba.

A hankali ya fara motsi, sannan ya buɗe idanunsa, hannusa ya kai kan tarin gashin bakinsa ya shafa yana miƙe, ya ziro fararen ƙafafunsa zuwa kan wani takalmi dake gefan gadon a ƙasa.

Sawa ya yi sannan ya miƙa ya shiga toilet, kusan 20mnt ya ɗauka yana gasa jikinsa sannan ya fito ɗaure da towel.

Wow na ce wow, tsayayyen namiji mai jini a jika ne, yana da suma mai yawa, baƙi mai laushi, haka yake ta ɗigar da ruwa, ga ƙirjinsa dake bayyane kai sai dai ace masha Allah kawai.

A natse ya isa gaban mirrow sannan ya fara shafa lotion a natse, yana cikin yi aka buɗo ƙofa aka shigo.

Murmushi kawai ya yi dan yasan waye ya shigo.

Be juya ba har sai da ya ji an dafa mai kafaɗa, sai ya daga idanunsa ya kalla wanda ke bayansa ta cikin mirrow.

Halittan Allah kenan, wato yarda kasan poster ne, ɗaya da riga ɗaya babu, haka suke tsaye, tsayi, kama, launin ido, yanayin gashin su, harda murmushin da suke sakar ma juna sak iri ɗaya ne.

"Allahumma inni kama ahsantu-kalƙi, fããhasin kulƙi." cewan Al-hassan.

> (Addu'ar kallon mudubi ne, yana da kyau duk lokacin da muka kalla mudubi mu yi ma Allah godiya, domin halittar Mutum babbar halitta ne......kar na ja ku 🥰🤦)

"Menene banbancin mu? Komai namu iri ɗaya, hatta murya, sai dai akwai abu biyu da muke da banbanci." Cewan Al-hussain yana juyawa ya fuskanci Al-hassan.

Sai Al-hassan ya zaunar da Al-hussain a kan kujera ya fara taje mai gashi yana cewa.

"Na farko zuciya, zuciyar mu ba iri ɗaya bane, na biyu kuma sha'awa.....haka Allah ya yi Ni bana jin feeling ɗin da kake ji, hasalima mata basa gabana." Ya kai nan ya ɗauko wani riga da wando wanda sak shine a jikinsa.

Murmushi Al-hussain ya yi sannan ya ce.

"Hmmm karka bari na riga aure, dama ka shirya tare zamuyi aure kuma nan da ɗan lokaci kaɗan."

"A'a Al-hussain ban shirya aure ba yanzu, kai dai Allah ya bada sa'a." sai Al-hussan ya haɗe fuska yana kallon cikin idon Al-hassan dake ɗaura mai belt.

"Ƙanina Ina sonka fiye da komai na rayuwata, dan Allah ka dinga kula min da kanka." ya faɗa cikin wani irin rauni.

"Nima ina so ka sosai, ka rage tausayin da yawa, I'm not a child." sai suka yi murmushi a tare.

Ya Allah, Ya Allah, yarda kasan mutum na magana da kansa a mirrow haka suke, sun tsaya suna kallon juna, ga komai na su iri ɗaya, hatta agogon da suka sa iri ɗaya ne.

Black trousers ne da back shoes, sannan da shuɗin riga mai dogon hannu, kai shigar dai masha Allah kawai.

Hannunsu cikin na juna suka tafiya a natse, haka suke taka stairs ɗaya bayan ɗaya, har suka iso tsakiyar babbar parlournsu wanda yake kama da ga falon wani sarki ko shugaban ƙasa.

Dan kuwa wasu arnayen kujeru ne suka shaƙe parlourn, ta ko ina sai walwal kawai, hatta fankokin da suke parlourn huta suke yi gwanin burgewa.

Ma'aikata mata huɗu da suke parlourn suka bisu da ido kawai suna yaba wannan halitta ta Ubangiji.

"Tweens ɗin Abbeey masu kama ɗaya, yau dai sai na cinka waye mutumina wato Al-hussain." sai suka yi murmushi suna kallon tilon ƙanwar ta su Merry.

Merry dake tsaye gabansu, tana bin su da kallo tana so ta gane waye Al-hussain sai dai ta kasa ganewa, sai ta kai hannunta ta danna dai-dai saitin zuciyar wanda ke gefan dama, sai dai ya ƙara mata murmushi, sai ta mai da mai sannan ta yi irin yarda ta yi ma ɗayan ta latsa mai zuciya.

Sai ya yi sauri ya dafe wajen yana cewa.

"Auch Marwa na kwance a wanje." sai suka yi dariya dukkansu tana cewa.

"Dan love."

"Na ji ɗin, ga Abbeey." Ya faɗa yana mai da idanunsa kan wani ɗan babban mutum da ya iso parlourn cikin kayan sojoji.

A natse ya iso in da suke sannan ya kallesu yana mai yaba ƙudira ta ubangiji.

"Al-hussain biyo NI zan yi magana da kai." ya faɗa yana zama a kan kujera.

Kafin Al-hussain ya motsa, sai Al-hussan ya yi gaba, sannan ya tsugunna gaban Abbeey yana tsugunnar da kansa ƙasa, dama ya saba haka, idan dai Abbeey zai yi Al-hussain faɗa, to Al-hassan ne ke zama, dan Abbeey ɗin ma baya gane su.

Take Abbeey ya haɗe fuskar sannan ya kallesa cikin takaici ya ce.

"Kai me yasa baka da hankali ne........ace kai baka san ka nema kuɗi ba sai hutu, ko kunya baka ji, ace Maryam da take ƙanwarka tana fita aiki, amma kana zaune waje guda, baka da abin yi, shin wannan rayuwa ka zaɓar ma kanka?." Ya kai nan yana jin haushin halin Al-hussain ɗin.

"Abbeey Insha Allah zan gyara........"

"Kullum haka kake faɗa, ka dubi ɗan uwanka mana, ka yi koyi da shi." sai Al-hussan ya kuma cewa.

"Insha Allah Abbeey."

"Tashi ka bani waje." a natse ya miƙe tsaye har zai fara tafiya sai Al-hassan dake tsaye daga gefe ya buɗe baki ya ce.

"Abbeey ina da magana." da sauri Al-hassan ya ƙyafta mai ido, sai ya yi mai murmushi sannan ya taka har kusa da Al-hassan, ya riƙe mai hannu sannan ya kalla Abbeey yana cewa.............✍️ END.

```🔥 TALLAH! TALLAH!! TALLAN MUSAMMAN!!! 🔥 ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU 📢 Jama'a ku fito ku ji labari! Shin kun san Hajiya Safiyya Baiwar Allah? 🤔 Idan ba ku sani ba, to ku matso kusa ku saurara sosai! Ina ƴanmata? Ina matan aure? Wannan damar taku ce! 💃 ✨ Hajiya Safiyya Baiwar Allah ta kawo muku: ✔️ Kayayyaki na zamani ✔️ Masu inganci sosai ✔️ Kuma a farashi mai sauƙi 🛍️ Kayayyakin da ake da su sun haɗa da: Jakkunkuna masu kyau, launi-launi, iri-iri Zanukan gado masu kayatarwa, domin ƙara wa ɗakinku armashi 🛏️ Hijabai masu kyau da ɗaukar hankali 👗 Kayan kitchen masu ƙyau da araha 🍽️ 💥 Duk abin da kike buƙata don gyaran gida da ƙara ƙyalli yana nan a wuri guda! ⚠️ Kada ki bari wannan dama ta wuce ki! 📞 Tuntuɓi yanzu: *** 📍 Location: Unguwar Sunusi, Kaduna 💬 Ko da kuɗinki kaɗan ne, sai kin samu abin da zai burge ki!```

📢 SANARWA TA MUSAMMAN!

*Duk mai son a tallata masa hajarsa cikin tsari mai kyau da jan hankali, ya tuntubi:* 💼 ~PRETTY SK~ 📞 *** ✨ Muna yi maka tallan da zai jawo hankalin kwastomomi cikin sauƙi!🥰

*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:

📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*

#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️🔥

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.