PAGE6
by @prettys01
> "Abbeey ina da magana." da sauri Al-hassan ya ƙyafta mai ido, sai ya yi mai murmushi sannan ya taka har kusa da Al-hassan, ya riƙe mai hannu sannan ya kalla Abbeey yana cewa.............
Sai Abbeey ya ɗaga mai kai yana jiran yaji mai zai ce. Al-hassan kuwa ɗan take yatsan Al-hussain ya yi duk dan ya ankare kar ya tona mai asiri, sai dai Al-hussain ko kula shi be yi ba.
"Abbeey, wayarka na ringing." cewan Al-hassan, sai Abbeey ya juya ya ɗauki wayarsa, kafin ya juyo, Al-hassan ya yi sauri ya mai da Al-hussain in da yake tsaye sannan ya sakar mai murmushi.
Al-hussain sam be iya ɓoye-ɓoye ba, in ya so yanzu zai iya faɗa ma Abbeey abin da zai ɓa ta mai rai.
"Ina jinka mana." cewan Abbeey yana kallon Al-hassan. Sai ya yi murmushi yana kuma tausasa murya ya ce.
"Abbeey, ka ga dai Al-hussain yaro ne, be kamata a dinga mai faɗa ba sai addu'a, wallahi tun da ya nuna ba zai iya aiki yanzu ba ka bashi lokaci, Ni kuma na mai alƙawarin duk abin da yake so magana kawai zai yi, ko menene shi kuwa, na tsaya mai akan komai." ya kai nan yana riƙe hannun Al-hussain cikin soyayya da shaƙuwa.
"Mtwwwwssssss ashe kaima ba ka da hankali, da kake mai kallon yaro, shekara nawa ka bashi? Hmmmmmm dukkan ku ne kuke neman addu'a, idan ma an bibiya mutum ɗaya ne ya ban amsoshin tambayata, in kunso ku gyara, na wuce Barack." ya faɗa yana miƙewa tare da bar musu waje.
Da ido suka bi shi har ya fita, sai Al-hassan ya kalla Al-hussain ya ce.
"Fatan babu abin da ya ɓata maka rai?." sai ya ɗaga mai kai yana cewa.
"Zan je gidan su Marwa na ɗauke ta, kar ta yi lattin zuwa school."
"Tom, yaushe za ka haɗamu da ita ne?."
"Hmmmm sai lokacin da ka shirya."
"Shike nan zan sa lokaci domin zuwa ganinta, yanzu dai ba zan Barka ka fita ko abinci baka ci ba." sai Al-hussain ya maƙe kafaɗa.
"Zan ci a school........"
"No, have a sit." ya faɗa yana ma Merry alaman ta kawo mai abinci, ba musu ta kawo mai tana musu murmushi.
Badan Al-hussain ya so ba, haka ya zauna, Al-hassan ya fara bashi abinci a baki, sai da ya tabbatar ya ƙoshi sannan ya gyara mai gashin kansa yana cewa.
"Za ka iya tafiya, ka kula da kanka." ya faɗa yana ɗan rungume shi a jikinsa.
"Koma wake jirana dole na tsaya nima na ciyar da ɗan uwana." cewan Al-hussain yana tashi daga in da yake, sannan ya zaunar da Al-hassan.
Ragowar wanda ya rage shi ya fara bashi, ba musu Al-hassan yake ta amsa yana jin zuciyarsa na mai daɗi.
A haka suka kammala sannan suka yi sallama, Al-hussain ya nufa gidan su Marwa, Al-hassan da Merry suka nufa wajen aiki...............
*NAJLAH*
Ta yi nisa cikin duniyar mafarki, har ta hango kanta a cikin gida tana rayuwar aure da wani Suger Daddy, rayuwar mafarki gwanin daɗi, dan yarda yake nuna mata tsantsan kulawa kamar wata ƴar tsana, hakan yasa tana barci tana murmushi, a dai-dai lokacin da take ƙoƙarin rungume wannan mijin na ta, ta jiyo wani gigitaccen ƙara wanda da shi ake tashin su barci.
Ba ta da nauyin barci dan haka da sauri ta toshe kunnuwanta tana ƙoƙarin buɗe idanunta, sai ta yi addu'an tashi daga barci ( alhamdulillahil lazi ahyana, ba'a dama amatana, wa'ilaiyin nushur.......)
A natse ta miƙe daga barcin tana kallon agogon ɗakin, 3:00am uku na dare, ji ta yi kaman ta fasa ihu, amma ba yarda ta iya haka ta sauka ganin dukkansu kowa tana ta sauri ana sauya kaya dan Sir J ba shi da sauƙi.
Ɓaƙaƙen kaya suka sanya, riga sa dogon wando, sai musulmai su ɗaura wani gyalle wanda da shi da babu duk ɗaya.
Cikin sauri ta nufa hanyar waje in da mata ke ta fita, gaba ɗaya suka fito kowa da barci a cikin kanta.
Wani dogon arnen mutum dake tsaye cikin kayan sport wears green, ya hura musu husir, alaman su zama ready sannan ya hura wanda za su fara gudu.
Yana hura na gudun, matan suka fara gudu, nan take ya sakar musu karnuna guda 7 a bayan su masu matsiyacin gudu, idan har ba kai gudun da za ka riga karnukan nan ba akwai horo dake biyo ba.
Ai kafin ka ce me, barci ya gudu a cikin kan Najlah, gudu kawai suke yi a cikin wani uban fili da ko ƙarshen sa ba sa iya gani, dan ma akwai hasken lantarkin dake wajen.
Yarda kasan suna gudu da iska haka matan nan suke, dan sun horo ta wannan ɓangaren, a ƴan gaba-gaba Najlah take, sai gumi take yi, gashi ta gaji amma haka take calla ƙafarta dake cikin sneakers ba.
Cikin ikon Allah suka isa in da aka umarce su, a cikinsu mata uku ne kawai karnukan nan suka wuce, hakan yasa Sir J. ya manna musu wani sign a goshi, daga nan aka shiga horon dare, sai 5:00am aka tashe su, jiki duk ya yi tsami, suna koma wa room kowacce sai barci, Najlah kuwa haka ta daure har sai da aka kira sallan asuba ta yi sannan ta kwanta jikinta ko ina yana mata ciwo.
Haka rayuwar su take a cikin wannan school ɗin, cikin dare horon gudu da faɗa, Safe (Morning routine) tashi da wuri sosai (misalin 6am) za su yi drill (tsayuwa, tafiya kamar soja) wanda suke ɗaukan lokaci wajen yi.
Daga nan sai Breakfast 9:30-10:00am. Ɗaga nan Kuma z su yi wanka tare da shiga ajin karatu, suna Subjects kamar - English, Maths and Government. Haka ta ɓangaren karatun Malam suma shahararrun mugaye ne masu zaman kansu, mistake kaɗan za ka sha punishment mai yawa.
Manyan horon da suka fi yi da rana sune, Marching (tafiyar soja), Push-up da running, Discipline sosai (ba wasa).
Sai yamma a kuma cin Abinci, sai a je bangaren hutawa in da za su hutane kawai su sha iska da wasanni.
Sai dai duk abin da ake yi lokacin sallah na yi ake barin musulmai suje su yi, haka rayuwar suke take tafiya kullum.
_Washegari_ Najlah ce tsaye cikin cikakkiyar uniform ɗinta, farar shirt mai ɗauke da tambarin *Unity Military Academy*, sannna ta sanya farin wando mai ajiyu da yawa, takalmanta suka ƙara haska shigarta dan suna white ne ƙal, beret ɗinta kuma ya zauna daidai, sai P-cap data sanya shima white.
Haka suke wannan shigar amma kafin a gama horo sai kayan nan sun koma ruwan ƙasa, gashi duk weekend suke wanki, ita in ta gudu gida sai a wanke mata.
Lumshe idanunta ta yi tana kallon ƙawayenta da suma suka kammala shiryawa.
"Najlah fine gurl, yanayin jikin ki na burgeni sosai."
"Bin Uthaman zageni kinji, ai ƴar Luu haka an fi ƙyau." sai suka kwashe da dariya.
"Two ɗays kin manta kina kirana da Ƴar Luu, sai yanzu ko....wallahi bana so." ta kai nan yana tura baki.
"Beasty leave Najlah, mu yi gaba an fara fareti." sai Amanda ta juya ta fara tafiya, hakan yasa suka bi bayanta suna tafiya.
Suna isa tsakiyar filin wajen, sai ɓangaren Barack suka sanya National Anthem a wani abu mai ƙara.
Take su Najlah suka ƙame a in da suke kamar wasu gumaka, ba wanda ya kuma motsi a wajen, ba su kaɗai ba hatta wa'inda suke filin horo duk sun ƙame.
Numfashi dubban jama'a ne kawai ke fita a natse, amma babu wanda ya motsa, a irin wanna yanayin ko wani abu ya cijeka ba ka da ikon motsi saboda tsabar darajar da suke ba ƙasar su Nigeria 🇳🇬.
Suna tsaye har aka gama sannan kowa ya motsa ya ci gaba da abin da yake yi.
Najlah ta zo daidai wajen hawa stairs kawai ta buga somasol ajere guda uku, sai ga ta kan stairs ɗin.
Ɗan ihu aka mata ana tafa mata, sai ta yi murmushi tana cewa.
"Na tashi da ƙarfi, da waye za su mu kokawa kafin General ya so?." ta yi tambayar tana kallon ƴan uwanta mata, sai dai babu wacce ta yi gigin yarda.
"Najlah ai babu mai iya kokawa dake."
"Hmmm Amanda to ke ki shigo, just for joke, tunda ba shugana a nan." Sai Amanda ta kalleta da kyau sannan ta ce.
"Okay." da haka ta shigo cikin filin, su kuma suka basu waje ana musu tafi.
Najlah ta cire p-cap ɗin ta, take gashin kanta ya bayyana wanda aka yi mai kitso biyar manya, an naɗe su waje guda.
Salon faɗa ta shiga, in da ta gyara tsayuwa tana yi ma Amanda alaman ta fara kawo farmaki...............
*Abba*
________Nunfashi ya sauke a natse, sannan ya yi horn a bakin wani babban gida, take aka buɗe mai gefe sannan ya kusa kan motarsa ciki yana jin be ƙyauta ba, dan rabon da ya zo family house ɗin su ya manta.
Motoci huɗu ne a parking space, a nan ya faka sannan ya fita daga motan yana ƙare ma gidan kallo.
Tabbas ya samu sauye-sauye da dama, a hankali ya shafa gashin kansa sannan ya mai da hularsa ya fara tafiya a natse.
Direct main door ya nufa wanda wannan babban falon da ya haɗa sassa na cikin gidan.
Hannu yasa ya tura yana mai sallama.
Cak ya tsaya yana kallon matar da ke tsaye cikin wani blue less Mai ƙyau.
Tray ɗin dake hannunta ta saki tana zaro ido tare da cewa.
"A.....Ab.....Abba!?." sai ya yi mata murmushi yana jin kewan kowa na cikin gidan.
Ai da sauri ta nufa ƙofar da ta fara gani ta shiga tana shelan, Abban Abuja ya zo.
Take manya da yara suka fara fitowa da sauri dan ganin shin da gaske shine wai.
Ilai yana tsaye a in da yake, suka rufa mai ana ta mai oyoyo cikin so da ƙauna.
Ji yayi farin ciki ya cika sa sosai, ai kuwa ya dinga rungume ƴan uwansa yana.
Sun ɗau lokaci kafin suka bashi waje suka zauna aka fara gaisawa, da hirar yaushe gamo.
"Babban Yaya yana ina? Ina so na yi mai surprise." ya faɗa yana kallon matar Yayansa.
Kafin ta buɗe baki yaransa biyu mata da suka fara tasawa suka ce.
"Yana Barack." Sai ya yi murmushi yana cewa.
"Ku bar abincin nan sai na dawo, zan je na ganshi." ya faɗa yana miƙewa tsaye.
"Abba yanzu wucewa za ki yi, bayan ga Dining can an cika maka." cewan matar ƙaninsa da ta kawo mai abinci kala-kala.
"Karku damu anan zan kwana, Bara naje." ai take duk farin ciki ya rufa su sosai.
"Ina yarana fatan suna lafiya?." sai ya kuma kallon matar Yayansa ya ce.
"Suna Lafiya, suma suna nan zuwa next week insha Allah." da haka ya ja yara biyu maza suka fita tare.
Ji yake a yau ya cika wani babban gurbin da ya manta, ya kwana biyu yana tunanin zuwa amma Allah be yi ba, sai yau Allah ya bashi ikon zuwa, ya so dukkansu zu zo, sai suka nuna ba za su ba, be ja maganar ya barsu saboda ba su jima da jituwa ba, duk da har lokacin Marwa ba wani sakewa da shi ba.
Mota ya shiga shi da Mazan nan sannan suka nufa Barack in da yayansa ke aiki, baban General ne, kuma Soja ne mai riƙon gaskiya.
Yana driving yana ma yaran tambaya akan makaranta, sai suke bashi amsa suna yi suna dariya.
A bakin get ɗin Barack ɗin suka faka, sai ya kalla babban yaron wanda a ƙalla zai kai 15yrs, ya mai alama da ido.
Sai yaron ya kiran number mahaifinsu, bugu biyu aka ɗaura, sai dai kafin yaron ya yi magana wata murya mai zafi ta dake su.
"Ina aiki? Koma menene ku jira na dawo gida." sai yaron ya yi sauri ya ce.
"Dad muna get ɗin Barack, wani tsoron abokinka ya zo dubaka." Sai aka kuma magana cikin mamaki.
"Aboki......okay, yanzu zan turo a shigo da ku." da haka ya katse kiran.
Sai Abba ya ɗauki facemask ya sanya sannan ya ɗau farin glass ya sa akan fararen idanunsa masu sheƙi.
"Wow Abba ba lallai ya gane ka ba a lokaci guda." cewan ƙaramin yana mai dariya.
"Hmmm Yayana ne fa, kunsa shi ko mara gaskiya ne yana saurin ganewa balle Ni ƙaninsa."
Kafin su kuma magana sai ga wasu sojoji biyu sun buɗe get ɗin sunyi musu alama da su fito.
Tare suka fita suka bi bayan sojojin nan.
Abba ji ya yi ya tsinci kansa cikin nishaɗi kawai, sai ya buɗe yana bin sojojin wlumshe ido sannan ya ajen da ido, ganin wasu na training, wasu na wasan dambe.
Babban office suka nufa in da a can General A.A ya ke wato Adam Adam.
Suna isa bakin ƙofar, sojojin suka wuce, sannan wasu sojojin dake wajen suka buɗe mai kofa suna mai alama da ya shiga.
A natse ya tura ƙofar yana mai sallama a natse.
Babban office ne wanda yake da kujeru, takaddu, da wasu abubuwa amma komai a tsaftace yake.
Wani babban mutum ne zaune yana latsa system, sai ya ɗaga idanunsa kan yaran nasa da wani da ya zo a matsayin abokinsa.
Wani ƙawataccen murmushi ya saki yana cewa.
"Mubarak hmmm it's reel?." Ya tambaya yana miƙewa daga inda yake.
Da sauri Abba ya ƙarasa gabansa yana sauke mask ɗin tare da rungume yayansa cikin so da kulawa, a tare suka riƙe juna suna jin wani farin ciki na kamasu.
"Yayana nine."
"Me yasa Mubarak!? Why ka manta da Ni na tsawon lokaci." sai ya girgiza kansa yana raba jikinsu .
"Ta ya zan manta da kai Yayana, kullum da kai nake kwana nake tashi." sai General ya kuma rungumesa yana jin daɗi da farin ciki.............✍️ END.
*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:
📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*
#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️🔥
★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story
by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*SHIDORIA WRITER'S TEAM📚✍️*
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.