BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 7

by @prettys01

> "Ta ya zan manta da kai Yayana, kullum da kai nake kwana nake tashi." sai General ya kuma rungumesa yana jin daɗi da farin ciki.............

Kujera suka nufa suka zauna suna sake gaisawa cikin soyayyar juna, jini ɗaya ba ƙarya dan kuwa Abba da General suna kama sosai, sai dai General ya fi manyanta, dan har ya fara farin gashi.

"Gaskiya na yi kewanka sosai, a ƙalla mun kai 4yrs ba mu haɗu ba, ikon Allah." Sai Abba ya sunkuyar da kansa sannan ya ce.

"Hakane Yayana, naga katin bikin su Aneesa, insha Allah har su Marwa za su zo asha shagali da su." sai General ya riƙe hannun ƙanin nasa sannna ya ce.

"Next Friday ne, kuma kaine wakilinsu, na so komai ace da kai aka yi amma yanzu ma lokaci be ƙure ba." Sai Abba ya ce.

"Na gode Yayana, ina ɗan nema wani alfarma Please."

"Tsakanina da kai babu alfarma, me kake so?."

"Ina so ka ban dama na yi ma Amare kayan ɗaki." sai General ya yi murmushi.

"Kayan ɗaki tuni an gama sai dai ka musu ƙyautan wani abu kai." sai ya ɗaga mai kai yana murmushi.

A lokacin wani soja ya kawo lemun ƙwalba da snacks, General ya amsa sannan ya ba Abba yana mai Bismillah.

Tare suka ɗan sha lemun sannan Ganeral ya ce.

"Yau da wuri zan tashi saboda kai, amma yanzu bara na leƙa wajen Ɗalubai, akwai wasan da zasu yi yanzu zan basu mark, ka huta a nan yanzu zan dawo." sai Abba ya miƙe da sauri yana cewa.

"A'a zan bika, nima na zagaya naga masu ɗaukan horon." Sai General ya yi murmushi sannan ya mai alama da su wuce.

"Ameer ku zauna yanzu zamu dawo."

"To Dad." da haka suka fita suna hiran yaushe gamo.

"Har yanzu dai kana nan zaune a tuzuru, ko kunya baka ji, ya kamata ka yi aure har yanzu da ƙuruciyarka." sai Abba ya ja maka ɗinsa sama yana murmushi.

"Yaya na tsufa ai, babu wacce za ta soni a haka."

"Hmmm ba dole sai yarinya ba, ko babbar mace za ka iya nema, ko dai har yanzu yaran nawa halinsu yana nan." Sai ya ɗaga mai, da haka suka fita daga Barack suka shiga ɓangaren makaranta.

"Eh, amma in lokaci ya yi zan yi ko basu so."

"Me ze hana na baka ɗaya daga cikin manyan matan sojoji da suke babban rukuni." Sai ya girgiza kansa yana cewa.

"Yayana ka bar wannan maganar." Sai General ya sanya glass yana ci gaba ta tafiya.

Hira suka ci gaba har zuwa wani ɓangare da aka danada ɗan wasa.

Suna zuwa wajen, aka hau saramai tare da ƙarasa cikin wajen, kujerar da aka tanada zaman sa, ya zauna yana nuna ma Abba kusa da shi, sai ya zauna yana kallon filin wajen wanda aka ƙwaɓa ƙasa da ruwa aka cika waje, sannan aka ɗaura wani gado mai ɗauke da kibiyoyi a jikinsa ta ƙasa, amma tsakanin wannan taɓon da gadon akwai tazara kaɗan.

Abba ya kalla ƴam matan da suke shigowa masu sanye da kaya iri ɗaya, riga fari da ɓakin wando gajere, idanunsa ya kau dar yana latsa wayan hannunsa...........

*NAJLAH* Jikinta har wani tsami yake mata saboda wahala, amma a haka har dambe ta yi da wata soja, saboda an turo sojar da basu horon rana, sai Sojan ta nema raina Najlah saboda yanayin jikinta, ai kuwa Najlah ranta ya ɓaci sai ta ma Sojan rashin kunya, ai take Sojan ta yi kanta tana zaro belt, nan fa Najlah ta shirya faɗa, Sojan na zuwa Najlah ta hau faɗa da ita, tabbas ta sha wiya dan kuwa Sojan akwai ƙarfi sosai, haka ta lallasa Najlah sannan ta kai ƙararta, aka ba Najlah hoto mai tsanani na 2h, haka ta yi babu tsayawa, gaba ɗaya neman wajen kwanciya take, tana so ta kwanta kan gado mai laushi, Mamie ta dinga gasa mata jiki da ruwan zafi, sannan in an gama a rufa mata blanket ta hau Barci.

Sai dai ina ba ta samu wannan damar ba, dan yanzu horon ƙasan ruwa za'a yi musu, tsaki ta ɗan ja tana bin ƴan ajinsu cikin wajen, suna shiga suka tsaya a in da suke tsayuwa, Najlah na baya ta zauna dan ta gaji da yawa.

Sama-sama ta jiyo muryan General yana bada umarnin a fara horo, in da wasu mata biyu sojoji suke basu umarni, da numbers suke amfani dan haka aka fito da mata uku kowacce ta tsugunna a bakin wannan wajen, sai da aka tabbatar da sun shirya sannan wata soja ta hura husir, nan take matan nan suka fara jan jiki zuwa cikin wannan taɓon suna mai bin wata igiya, tare da kiyaye kar su miƙe dan akwai kibiyoyi da suke saman su.

Nan fa aka shiga tafa musu ɗan ƙara basu ƙwarin gwiwa, ai kuwa suka ƙara dagewa sosai, kusan minti 5 suka ɗauka kafin suka fito jikin su sai ɗigan taɓo yake, haka aka jinjina musu sannan suka wuce cikin makaranta dan tsaftace jikinsu.

An ɗau lokaci ana haka, kafin aka kira number Najlah, a hankali ta miƙe tsaye tana miƙa tare da nufan wajen.

General ya kalla Abba dake latsa waya yace.

"Abokina da ya rasa ransa wajen ƴaƙin da muka sha faɗa a wancan lokacin da ƴan ta'adda, za ka iya tuna sa?." sai Abba ya ce.

"Sosai ma kuwa, General A.B.D ba."

"Eh Abdullahi, to ga ƙaramar can, mai ɗauke da ɗan ƙwali fari, muna bata horo sosai ga Jarumta kamar dai A.B.D." sai Abba ya ɗaga idanunsa ya kai kan matan ukun da suka fito.

Yana kallon fuskarta take zuciyarsa ta buga da ƙarfi, sai ya rintse ido yana ƙare kallonta, wata ƙyakyƙyawan yarinya ya gani tsaye cikin kayan horo, a kallo ɗaya za gane yarinya ce ƙarama, ga ta fara fat, mai manyan ido da ƙaramin baki, wanda ta tura gaba alamun akwai abin da ba ta so yi ba.

Daga sama ya kuma kallonta yana murmushin da besan na menene ba.

Najlah tsaki ta kuma ja, saboda an kira su kuma me basu umarni ta ɗau excuse ta nufa wajen wani soja tana mai magana.

Ji tayi kaman ana kallonta, hakan yasa ta fara bin mutanen wajen da kallo, har ta kai kan General dake rubutu a paper, a hankali kuma idanunta suka sauka kan wani dake zaune fuskarsa ɗauke da mask.

Idanunsu ne suka sarƙe da juna, sai ta kuma jan tsaki tana ƙara kallon cikin idanunsa da suke kanta.

Ta tsana irin kallon nan, dan ba za ta manta har wani soja ta fasa ma kai ba akan ya kafeta da ido, sai ga wani kuma ya tsura mata ido, baki ta murguɗa mai tana mai hararan sama da ƙasa duk dan yabar kallonta.

Sai dai Abba ya ɗan yi dariya mara sauti yana ƙara kallonta sosai, babu abin da ya fara zuwa mai kai a kanta sai dama suyi magana yaji ya muryanta yake.

'Wannan fa sa'ar Fauza ce, me yasa kake kallonta irin haka?.' zuciyarsa ya tambayesa, sai ya lumshe ido yana kallon yarda ta tsugunna suna shirin shiga wajen.

'Yarinyar ta yi min ne?.' ya faɗa daga ƙasan zuciyarsa.

'Ai baka da yaro da za ka haɗa da ita aure, ta yi maka a matsayin ƴa ko ƙanwa?.' sai ya yi ma kansa dariya sannan ya ce.

'Wallahi a komai ma, kawai ta yi min ko da a matsayin mata.' kalmar mata ya daki cikin kansa hakan yasa ya lumshe ido yana tuna cewa shi ba yaro bane, kuma tunda yake be taɓa tunanin zai iya auren small girl ba, ya fi ba da cikin manyan mata, yawanci zaurawa ma tunda wa'innan suna da hankali.

Zuciyarsa ce ta kuma bugawa a lokacin da Najlah ta fara fitowa daga cikin taɓon, jikinta sai ɗigan yake, haka gefan fuskarta ya ɓaci sosai, ga shi ta haɗe fuska ga bakin nan a gaba.

Murmushi kawai ya yi yana kallon yarda ake tafa mata amma ko a jikinta.

"Ga gani ko, jaruma ce ƴar tawa." Sai Abba ya jinjina kai yana tambayar abin da ya tsaya mai a cikin kansa.

"Gaskiya na ga alama, ya sunan ta ne?."

"Najlah, amma ainiyi Hafsat." sai ya maimaita sunan nata akan leɓansa *Najlah*.

Idanunsu ne suka ƙara sarkewa dana juna, ai kuwa Najlah ta kai hannunta sai tin wiyarta, sai ta sa yatsarta ta ɗaura a saitin wuya tana gogawa alamun za ta yanka shi, sai ya nuna kansa, ta ko ɗaga mai tare juyawa ta fara tafiya.

Ba shiri ya kauda kansa yana janyo addu'ar da ta zo bakinsa, dan kuwa a yarda ta juya, ta fara tafiya haka mazaunanta suka hau rawa sosai.

Ze iya cewa tunanin haka be taɓa kamashi ba akan wata mace sai yau, daga haka ya rasa sukuninsa, yana dai zaune ne kawai, har General ya gama suka bar bangaren be kuma ganin Najlah ba, ba haka ya so ba amma babu yarda ya iya, daga nan gida suka nufa, in da ya je ya iske wani tarba mai rai da lafiya.

Sai a lokacin ya ga yaran Yayansa da za'a aurar mata uku, Aneesa, Munirah da Suhaila, wanda lokaci ɗaya Allah ya kawo musu mazajen aure, sai aka sanya lokaci.

Gaisawa suka yi da ƴam matan sosai sannan suka wuce ɓangaren su.

"Yaushe ne na yara na auren?." cewan Y.aya yana cin abinci.

"Bansan dalili ba ko maganar aure ba su zo, har ƙwanda Marwa tana da sauri sai dai yaron be kwanta min ba sam."

"A'a karka shiga harkan yaranka sam, idan yana da hali mai ƙyau ai shike nan tunda ba kai za ka zauna da shi ba."

"Uhm haka ne, to ita Basma ai babu mai iya soyayya da ita, tsaurinta ya yi yawa, gashi ba ta iya magana a tausashe ba, to wani Namiji ne zai ɗau rashin biyayya...sai Fauza ita yarinya ce, tukun dai." sai Yaya ya ɗaga mai kai yana cewa.

"Allah ya musu zaɓi na alheri, amma kafin a kai ga su, kaifa, yaushe za ka cika ma Hajiya Mama burinta, ya kamata ka yi aure."

Take fuskar Najlah ta hasko mai, amma a haɗe fuskar take, zai so yaga murmushin ta.

"Yaya, misali idan na nema auran yarinya za'a bani kuwa?." sai Yaya ya aje spoon ɗin hannusa ya kallesa.

"Uhmmm amma kai me za ka yi da yarinya tsakani da Allah, mace riƙarƙa kake so saboda halin yaranka, amma ace ka aura sa'ar Marwa ai ba magana." sai Abba ya ce.

"Na sani, amma za'a iya bani kuwa?."

"In dai yarinyar na so me zai hana, ba tsufa ka yi ba, dan ma kayi auren wuri ne, amma har yanzu da kai saurayi ne." Sai suka yi dariya suna sauya hira.

Haka Abba ya zo kwanciya barci ya ƙi zuwa sai tunanin Najlah tana mai alamun za ta yanka shi, shi kaɗai ya dinga yi, ya manta shaf da ya ɗauki hotonta, da ko kalla ya yi zai ji sanyi da yanayin da yake ciki, abu kaman wasa barci ya mai sallama, haka ya dinga juyi yana murmushi.

"Wai soyayya na faɗa?." ya faɗa akan leɓansa, ganin babu mai bashi amsa yasa ya ɗauki pillow ya rungume yana ƙara ganin Najlah na mai gizo, hakan yasa ya ƙudurta gobe zai koma Barack ko dan ya ganta.

Ba shi barci ya ɗauke sa ba sai gab da lokacin Sallah, ai kam barci ya yi gaba da shi cike da muradin sake ganin Najlah.................

*Marwa* Zaune take kan sopa tana waya da Al-hussain, wanda tun safe suke tare har yamma, sannan tun ɗazu suka fara waya da shi, a natse cikin wannan muryan nasa dake sa ta ƙara narkewa a cikin soyayyarsa ya ce da ita.

"Gobe ki wuce school, a can zamu haɗu, Al-hassan zai zo ku gaisa." Sai ta yi murmushi.

"Gaskiya na ji daɗi sosai, kullum na ce ka nuna min hotonsa sai ka nuna min naka, ko naka wanda aka yi double jikinka, finally dai zan gansa." Tana ji ya ɗan yi dariya sannan ya ce.

"Hmmmm ki tabbar kin dawo ruwa dan za ki iya suma saboda mamamki."

"Haba dai, ba yau na fara ganin identical twins ba, balleku kallo ɗaya zan gane ku, kaine fa masoyina." sai ya yi murmushi.

Da haka suka sauya hira, har sai da barci ya ci ƙarfin Marwa sannan ta mai sallama tana shiga bedroom Dan ƙwanciya.

Gado uku ne kowa da nasa, Fauza tuni ta yi barci akan takaddu, sai Basma dake latsa system akan na ta gadon.

Marwa ta kwanta tana addu'ar barci tare da kallon Basma tana ɗaukan wayarta dake ringing.

"Baki ga kirana bane? Ko barci kika yi?." cewan na cikin wayar dake handfree.

"Na gani kawai ban ɗauka bane." Basma ta faɗa cikin ko in kula.

"Kamar ya kina gani? Wato 7 missed called duk kina gani?."

"Eh." Sai ta ji ya yi ƙwafa yana cewa.

"Basma hulakanci babu ƙyau, dan na ce ina sonki ba shine zai sa na ɗauki komai daga gareki ba......"

"Ɗan dakata Malam, karka ɗaga min murya dan ba zan ɗauka ba mtwwssss."

"Ni kike ma tsaki?."

"An yi maka ɗin, na ji duka mtwwssss." ta kuma jan dogon tsaki.

Marwa ta girgiza kai tana gyara kwanciya, dan ta gaji da magana akan abu ɗaya, haka Basma take, ba ta yarda saurayi ya ɗaga mata murya, gashi ba tasan menene biyayyan soyayya ba, ba ta kiran saurayi kuma in an kirata sai ta gamada take ɗauka, sannan kai tsaye za ta faɗa kawai ba ta son magana ne, daga nan su yi faɗa ta yi blocking number mutum, shike nan sun rabu sai ta kuma wani, gaba ɗaya samari ba su wuce sati ɗaya da ita saboda halinta.

"Ke wai dan kin samu ana sonki ma shine za ki hulakantani." Ya faɗa cikin masifa, ai da wani irin zafin nama Basma ta aje system ɗin tana ɗaukan wayar take da cewa.

"Kan bala'i......lallamai Shamsu ashe baka da hankali, wato Ni kake so ma, irin na rasa samari ɗin nan....wallahi dan rage ma kaina lokaci yasa nake waya da kai, ka kalla kansa a mudubi za ka fahimci haka, mtwwssss......."

"Allah na gode ma da ka nuna min Basma ba matar aure ba ce, Allah na gode maka, banza kawai, ki ƙarata da kanki" Ya faɗa tare da kashe kiran gaba ɗaya.

Wani abu ta ji ya tokare mata zuciya, sai ta cillar da wayan tana tashi daga kan gadon, idan ranta ya yi dubu to ya ɓaci, har wani tiriri take yi na masifa.

"Banza......Ni ce banza Shamsu, ka shiga uku, wallahi sai ka yi nadama, kan bala'i." Ta faɗa tana fita ta zauna akan kujera.

Yarda ta zauna a haka gari ya waye dan yarda take ji ko barci ba za ta iya ba saboda tsabar ɓacin rai.

Idanunta sun kaɗan sunyi ja, amma ba hawaye, kalma ɗaya take tunawa, *Banza*

Wanka ta yi tare da sallar asuba, sannan ta shirya cikin wani doguwar riga na atamfa, tashin su Fauza ta yi tana ƙarasa shiryawa.

Cikin barci Fauza ta kalleta sannan ta ce.

"Ina zuwa ne kike shiri ko 7am be yi ba?."

"Police station." Ta faɗa tana ɗaukan jakkarta sannan ta nufa hanyar fita.

"Basma." sai ta tsaya cak tana sannan ta juyo ta kalla Marwa dake shirin shiga toilet.

"Please ki ci wani abun kafin ki fita." sai ta ɗaga mata kai sannan ya fita.

"Ya Marwa me za ta je yi a police station?."

"Hmmm kinsan Basma, maybe rigima ta yi da wani za ta sa a kamashi." Sai Fauza ta girgiza kai tana jin babu daɗi, haka Basma take abu kaɗan za ta kai ka staion, da yake D.P.O ɗin yana sonta, kuma kaman yaron Abba ne, shi yasa take zuwa ya yi ma duk wanda ya so rashin mutumci.

Basma na sauka ta nufa Kitchen dan jin motsi a ciki, kofar ta buɗe tana kallon sabuwar mai aikin nasu, babbar macece wacce ba za ta wuce 32yrs ba, baƙa ce amma a tana da jiki sosai, ga wani hips Masha Allah, take wani abu ya tsaya mata a wuya, duk da kuwa doguwar riga ce jikin Matar.

Matar jin an shigo ta yi sauri ta jiyo tana gyara zaman gyalenta tare gaishe da Basma cikin ladabi kamar yarda aka ce ta dinga musu.

Basma kuwa ƙare mata kallo take yi, tana ƙyau sosai, ga manyan Breast wand zai ɗauki hankali, ita jiya sam ba ta lura da yanayin matar ba.

Hannu Basma ta sa ta ɗauki glass cup sannan ta sake shi ya faɗi kasa.

"Idan na dawo zamu yi magana muddin kina son aiki a gidan nan dole ki bi kowani dokana."

"Insha Allah zan bi komai." Cewan matar cikin biyayya.

"Kwashe wannan." Ta faɗa tana ɗan ja baya.

Ai cikin sauri matar ta miƙe jikinta har rawa yake kar-kar, ta ɗauko faka da tsintsiya, ta hau kwashewa, ko ina na jikinta sai rawa yake yi.

Basma ta ja tsaki sannan ta fita, dan akwai aikin dake gaban tane da zama za ta yi ta kora ma matar warning, yanzu da Abba ne ya shiga cikin ɗin fa?, da shi ne take ta ma rawar jiki haka fa?.

Sai Basma ta girgiza kai tana shiga mota tare da cewa.

"Inaaaaa.......wallahi da sake." Da haka ta figa mota sai station.

Da yake safiya ce ba yawaitan motoci, hakan yasa ta dinga sharara gudu, a ƙofan station din ta tsaya *Central Command Station* sannan ta fito daga motar ta shiga ciki.

Akwai jami'ai sosai, suka dinga gaisheta dan sun san wacece, direct office ɗin D.P.O ta nufa, wanda sukai waya akan ya shigo da wuri.

Tana shiga ta iske sa, zaune yana duba wasu files, yana ganinta ya miƙe da sauri, jikinsa ya fara rawa yana mata murmushi, shi har ga Allah yake son Basma, Amma ta kasa bashi dama, kuma kullum cikin faranta mata.

Babban mutum ne dan yana da mata da yara biyu, amma Allah ya ɗaura mai soyayyar Basma sosai.

"Ina kwana Divisional Police Officer D.P.O." sai ya yi murmushi yana cewa.

"Lafiya lau Basma, ai da kin turo min information na yaron har gida za ku kawo miki shi." Sai ta sauke ajiyan zuciya ta ce.

"Karka damu nan nake so a kawo shi, daga nan ka batar da shi na sati ɗaya, bayan ya ci wiya sai a dawo da shi, ina so yasan saboda zagina da ya yi shine aka mai haka."

"Shike nan Basma, yanzu ki ban address ɗin sa ki koma gida, zuwa anjima sai ki dawo, ai ko wani irin sharri za mu laƙa na mai." Sai ya ta mai murmushi.

Latsa wayarta ta yi sannan ta ce.

"Sai na dawo ɗin." Sai ya kalla wayarsa da saƙo biyu suka shigo, ɗaya information akan yaron na biyu kuma alert ɗin 50k.

Take ya hau mata godiya sannan ya rakata har bakin mota, ta shiga ta bar wajen, tana jin daɗi a ranta.

"Shamsu sorry for yourself." Ta faɗa tana kunna waƙar larabci a cikin motar sannan ta nufa school........

*Marwa*

A natse ta aje wayar dake hannunta zuwa kan jikinta, ta kalla filin makarantar na su, in da mutane ke fa zirga-zirga, murmushi ta yi dan yanzu ta yi waya da Al-hussain ya ce ta zauna a wajen, kuma ta tabbatar tana riƙe da ruwa, hakan yasa ta yi murmushi tana jin ta ƙosa su iso.

Tana daga zaune motar Al-hussain ta shigo school ɗin, sannan direct wajenta ya nufo, sai ta gyara zama tana zuba ma motar ido, bakinta ɗauke da murmushi.

Parking aka yi, sannan aka ɗauki minti biyu kafin aka buɗe ɓangaren Driver.

"Baby Love ki kulle idanunki." Ta ji Al-hussain ya fada, sai ta rufe tana cewa.

"Na kulle."

A hankali Al-hussain ya fara fitowa daga mazauninsa, sanye yake da manyan kaya, Men Less coffee brown ya ji aiki sai walwal yake, ga wani arnen hula dake kansa, yana fitowa ya kulle motar sannan ɗaya ɓangaren shima aka buɗe, sai irin takalmin dake ƙafar Al-hussain ya fara fitowa.

Kafin gaba ɗaya gangan jikinsa ya bayyana, shigarsu dai sak iri ɗaya, murmushi ne kwance akan fuskokinsu, sai Al-hussan ya zagayo kusa Al-hussain, hatta tsayuwar ma iri ɗaya suka yi.

Mutane ne masu wucewa suka fara tsayawa ganin ƴan biyu masu masifaffen kama, kowa mamaki ya ƙamshi saboda irin makar ta yi yawa, take aka fara musu hotuna sannan wasu suka hau kiran friends ɗin su su zo suga abu.

"Buɗe." Ta ji an fada, a hankali ta buɗe idanunta tana ganin mutane sun zagayesu, sai a hankali ta fara kallon ƙafafunsu da takalmin su iri ɗaya, a hankali ta fara binsu da ido, har zuwa fuskokin su, wani ɗan zabura ta yi tana rufe ido tare da ƙara buɗe wa, sai dai yarda suke tsaye sun zura mata ido suna murmushi iri ɗaya sak, a razane ta miƙe tsaye tana shirin gasgata abin da idanunta suke gani, dan kuwa Al-hussain ɗin ta ta ga ya koma guda biyu, Rufaida bottle water ta buɗe sannan ta wanke fuskarta, sai ta kallesu da ƙyau, tana jin kaman ta isa gabansu amma ƙafarta ta yi mata nauyi.

A lokacin ɗaya suka buɗe baki tare da yin magana iri ɗaya kuma cikin sauke nunfashi ɗaya, al'amarin da ya ƙara burge gaba ɗaya mutanen wajan.

"Ki ƙara so, sannan ki cinka abokin rayuwarki." kanta ta dafe dan jin muryansa ma iri ɗaya sak.

"Ya Allah, wai da gaske abin da nake gani haka ne." sai suka ɗaga mata kai.

Zufan dake fuskarta ta goge da gefen gyalanta sannan a hankali kaman mai jin tsoron wani abu.

A gabansu ta tsaya tana kallon fuskokin su, tare da jikinsu, alama koda guda take nema dan gane masoyinta sai dai ta kasa ganewa.

"Kace wani abu?." ta faɗa tana kallon na gefan damanta.

"Yau gani ga ɗan uwana a gaban Marwa." Ya faɗa yana murmushi, sai ta mai da idanunta kan ɗaya.

"Kaima ka ce wani abu."

"Yau gani ga ɗan uwan a gaban Marwa." sai ta rikice dan maganar ma iri ɗaya sak.

Take ta tuna abin da ya ce mata ɗazu.

'Kar mu zo ki kasa gane ni.' a lokacin dariya ta yi tana cewa.

'Duk yarda kamar ku ta ɓace, ina zuwa kusa da kai zuciyarta za ta ban alama.' sai suka yi dariya gaba ɗaya.

Sai dai gashi tana gabansu amma ta kasa gane waye saurayinta da suka ɗau sama da shekara suna tare.

Ajiyan zuciya ta sauke sannan ta kalla cikin idanunsu, sai dai babu wani sauyi duk iri ɗaya ne.

"Kina ɓata lokaci kuma kinsan ɗayan mu na zuwa wajen aiki." Cewan na gefan haƙu, take Zuciyarta ta raya mata shine Al-hussain, sai ta yi murmushi lokaci guda kuma ta rungumesa tana cewa.

"Na kamaka." take zuciya biyu suka daka tsalle lokaci guda, sai ya yi sauri ya ja baya yana cewa.

"Buduwarka ta faɗi Al-hussain." sai ta kalla ɗaya, dariya ya yi sannan ya riƙe hannunta yana janyota kusa da shi.

"Baby Love You fail why?." sai ta tureshi tana cewa.

"Kaine ko kai?." Ta nuna su dukka, sai wanda ta fara runguma ya nuna ɗayan ya ce.

"Shine masoyinki." Al-hussain kuma ya ɗaga kai yana sake mata murmushi.

Kan tane ya kulle, tabbas Al-hussan ta fara runguma, saboda yanayin da ta ji baƙone a wajenta, tunda sau da dama tana rungume Al-hussain sai dai ba ta taɓa jin yarda ta ji ba.

A hankali ta ɗaga idanunta ta kalla Al-hassan, sai ta ga kaman murmushin yana haɗe da wani haske-haske, kaman kuma cikin idanunsa ƙwantaccen farin ruwan madara ne. Sai ta ja dogon numfashi sannan ta isa kusa da Al-hussain.

"Baby Allah ya yi halitta, wallahi na kasa gane ku, kamar ta yi yawa." Sai ya ja dogon hancinta sannan ya ce.

"Ai kam tun yanzu ya kamata ki gane mu, dan ke matar Al-hussain ce." Sai suka taka a tare suka zauna a in da ta tashi.

Al-hussain ne ya sallama kowa na wajen sannan ya gyara zamansa a tsakiya Al-hassan da Marwa.

Hannunsa na cikin na ta ya ce.

"Yau dai ga ki ga ɗan uwana." ya faɗa yana ɗago hannun Al-hassan ya haɗa dana Marwa.

Take wani haske ya gittasu sannan suka ji wani sanyi ya ratsa hannun nasu.

"Ku biyun nan kune mutane masu muhimmanci a rayuwata, dan haka yarda ɗayan ku zai soni dole ya so ɗayan ma." ya faɗa yana raba hannunsu, take wannan sanyi ya ɓace sai dan ɗumin hannun Al-hussain dake hannunta. A hankali ta ɗaga idanunta ta kalla Al-hassan, sai idanunsu suka sarƙe da na juna, wannan haske ya ƙara gilma musu, sai suka kauda kai kowa ya mai da hankalinasa ga Al-hussain dake ta koro musu jawabai akan soyayyar juna...............✍️

> Littafin nan babu ƙarya Fan's, Chakwakiyar dake ciki akwai mamaki sosai, sannan kuwa Dramer labarin ya kusa fara ɗaukan saitin.

> Finally dai Abba ya yi gamo 🤭

> Marwa an ruɗe da ganin twins Lokaci guda, amma anya babu wata ayar tambaya da zai biyo baya🤷✍️

> Tsakanin Marwa da Basma wacece ta fi bala'i ne.....Baseey ba sauƙi 🤭🤭🤭

> Mu dai haɗu da ku a kashi na gaba da yardan ALLAH 🥰

*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:

📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*

#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.