PAGE 9
by @prettys01
> "Na shiga ukuna yau." ta faɗa tana kallon yarda Segent George yake huci kamar zaki, da sauri ta mai da hannayenta sama dan kuwa da su take bayani tana wasa da zara-zaran yatsunta kamar wata mayya...........
"Wato duk shi za ki yi ma wannan mugunta ko?."
"General a'a, kawai dai....."
"Shot up, tashi ki bishi zuwa ɗakin ladabtarwa." sai ta miƙe da sauri ta bi bayan Segent George.
Abba ya kalla Yayansa ya ce.
"Yanzu wanna ƴar halittar za su wahalar? Haba Yaya."
"Najlah rashin jinta yafi shekarunta, ina tabbatar maka sai ta yi ƙoƙarin dambe da shi, haka take, duk wanda zai horeta sai ta yi faɗa da shi, ga ta kamar a hure amma sai ƙarfi kaman zakanya." sai Abba ya gyara zama yana jin zuciyarsa na mai zafi.
"Abba ya na ka damu da yawa? Kar dai ita ce taaaa."
"No, kawai dai yarinyar ta burgeni ne."
"Hmmmm shike nan, ko za rakani dubo sojojin da suka je yaƙi, wasu sun mutu wasu suna asibiti, zan dubosu da kaina."
"Muje to." Ya faɗa yana miƙewa tsaye, yasan idan ya zauna dole zai fita neman in da aka kai Najlah, daga nan kuma al'amarin ba zai yi ƙyau ba................
*Al-hussain*
Tsaye yake a garden shi kaɗai yana tunanin Marwa duk da yanzu ya suka gama waya tare, dare sosai dan 11:00pm na dare ya yi, amma yana zaune a wajen saboda yana jiran Merry za su yi magana.
Maganarta ya jiyo, sai ya kalleta, doguwar riga ce jikinta sai gyalen da ga yafa a madadin ɗan ƙwali.
Zama ta yi gefansa sannan ta kallesa a hankali sosai duk da tasan Al-hussain ne, amma dole sai ta tabbar take magana.
"Promise." ta faɗa sai shima ya ce
"Promise." Sai ta lumshe ido, dan dan Al-hassan ne cewa yake. (Wani promise?/ Promise ɗin me?)
"Al-hussain nan da kwana uku ake da buƙatar kuɗi, kuma a wajenka kowa yake da yaƙinin samun kuɗi, sannan FA.1 ya turo saƙo na san ka gani." Sai ya daga mata kai.
"Na gani, gobe za mu haɗu a can, ki kula sosai bansan ko yayane a samu matsala." Sai ta ɗaga mai kai.
"Momy Ina kewarta sosai, ina fatan ta samu hasken wannan aikin namu." Sai ga hawaye sun gangaro mata, sai ga riƙe mata hannu.
"Karki yi kuka, kema kinsan ina kewarta fiye da ke, mu ci gaba mata da addu'a kawai." sai ta share hawayen ta sannan ta ce.
"Shike nan, zan koma ciki, amma ina so na ma magana akan Marwa."
"Ina jinki."
"Uhmmm, a ganinka aurenta da zama cikin mu babu matsala, kar ta zo ta sannan *Promise* ɗin mu, dan komai zai iya faruwa nan gaba." sai ya sauke a jiyan zuciya sannan ya ce.
"Karki damu, zan bi komai a natse kuma wannan Promise ɗin tunda Al-hassan be sani ba babu wani wanda zai iya sani."
"Hakane, good night." Sai ta miƙe sannan ta wuce ciki, ya jima a wajen kafin shima ya miƙe ya shiga ciki.
A bedroom ya iske Al-hassan, yana kallo a tv, da sak P.J mask ɗin jikinsa, zama ya yi gefansa sannan ya ɗaura kansa a cinyar Al-hassan.
"Meke damunka? Ko Marwa ta yi barci ne? Nasan baƙyayin faɗa sosai." Sai Al-hussain ya buɗe baki ya ce.
"I need 3 million naira zuwa gobe, kaji ɗan uwa." Sai Al-hassan ya kallesa da ƙyau sannan ya ce.
"Karka damu, dan kai nake dukka aikin da nake, ina fatan ta hanya mai ƙyau zaka kashe." Sai ya ɗaga mai kai yana cewa.
"Eh, na gode." Sai Al-hassan ya sumbaci kansa sannan a take ya tura mai da kuɗin.
Yana jin alert ya duba sai ya ga 5M, farin ciki ya kamasa sai ga rungume dan uwansa yana mai godiya.
A take Al-hussain ya tura ma FA.1 4M, tare da gajeran saƙo.
Cikin nishaɗi Al-hussain ya kwanta a gadon Al-hassan, a kusa da juna suka kwanta cike da soyayyar juna.............
*Baseey.*
Ba ita ta samu sakewa ba sai da Harira tabar gidan, take ta ji iska na ratsata, dama yunwa take ji sosai, ta sauka ƙasa ta ɗibo abinci, tare da Marwa suka ci, ita kuma Fauza haushin su take ji.
Sun riga sun bata sallahun a kawo masu aiki mata biyar, a cikin su za su zaɓa, kuma gobe za'a kawo su, shi yasa ba su da wata damuwa.
"Da mun iya girki ai da tare zamu yi ma Abba abinci." Cewan Basma.
"Wallahi kam, sai dai ya daure ya ci wannan." ta faɗa tana taliyar dake gabansu, dariya suka ɗan yi sannan suka sauya hira.
Da misalin 10:30pm Abba ya dawo, yarda kasan yara haka suka koma, suka rungumesa suna mai oyoyo, take ɓakin cikin da ya tawo dashi ya bi iska da soyayyar yaran nasa.
Abubuwan ciya-ciye ya kawo musu nan fa suka hau ci suna raha, sai dai Abba gaba ɗaya hankalinsa baya tare da su.
"Abba meke damunka?."
"Fauza ba komai, kawai gajiya ne, ki ce ma Harira ta haɗa min lemon tea, sai ki kawo min ba zan iya cin abinci yanzu ba." Ya faɗa yana miƙewa tsaye.
"Ya Basma da Ya Marwa sun koreta." Sai suka dalla mata harara.
Cikin mamaki Abba ya kallesu ya ce.
"Me ta yi muku?." Sai Basma ta miƙe tsaye tare da cewa.
"Abba ba ta yi min ba sam, bana sonta, shine na sallame ta."
"Baƙya sonta? Akan wani dalili? Matar da babu ruwanta, information ɗin ta mai ƙyaune kuma tana da sauƙin hali ai." ya faɗa yana jin babu daɗi a cikin ransa.
"Akan wani dalili kasan wa'innan bayanan akan ta? Kamanta ba ka faɗa abu ɗaya da take da shi ba Abba?." ya riga ya harbo jirgin Basma, wato kishin gado ne ya motsa.
Sai ya miƙe tsaye har ya fara tafiya, ya ji Basma ta ce.
"Ranar da ta zo ka ganta Abba?."
"Eh, munyi magana da ita ma." Ya faɗa yana jin tunda ransa na ɓace to na kowa ma ya ɓaci.
"Kenan ka ƙare mata kallo?."
"Uhm tana da ƙyau ba laifi." da haka ya haura sama ya barsu da budaɗɗen baki.
"Kungani ko, aikin banza da wofi kawai." sai ta ja saki ta haura ɓangaren su.
Marwa ta kalla Fauza ta ce.
"Kaman akwai abin da ya ɓata ma Abba rai, shi yasa ya faɗa mata baka."
"Eh naga alama nima, yanzu dai kije wajen Baseey, Ni kuma ko ruwan zafi zan kai ma Abba ya sha Tea."
Take sukai haka, Fauza ta dafa ruwan zafi, sannan ta ɗiba kayan Tea ka nufa bangaren Abba.
A kwance ta samesa a falonsa yana kallon sama, jin sallamar Fauza yasa ya kalleta.
"Abba meke damunka?."
"Ba wani abu bane, kawai na zo sake ganin wani diomand da nake shirin siya ne sai ban samu damar hakan ba." Sai Fauza ta yi murmushi tana cewa.
"Ka nema wani kawai tunda akwai a wasu wajajen Abba." Murmushi ya yi yana riƙe hannunta.
"A'a Autata, Diomand ɗin nan shi nake so, dan haskensa yana kashe ido, gashi duk baya ɗan lokaci darajar sa na ƙaruwa ne, amma karki damu."
"Insha Allah za ka samu, zan tayaka da addu'a nima."
"Allah Ameen, na gode Autata." Sai ta miƙa mai ruwan zafi.
"Sa milk da suger kawai." Ta ɗaga kanta sannan ta zuba yarda ya ce, bashi ta yi sannan ta bar room ɗin.
Da ido ya bita, yanzu yake har wajen danginsa ya dawo amma babu wacce ta iya tambayar ya suke, amma can kowa su yake tambaya.
"Zumuncin nan dole ya sauya." Ya faɗa yana tuna abin da ya tsaya mai a rai.
Tun bayan barinsu Barack suka nufa asibitin 4 to 4, inda aka kai jami'an da suka samu rauni, anan ya ga tashin hankali mara misaltuwa, dan kuwa yawancin sojojin sun rasa wani sashi na jikinsu.
Idan hankalinsa ya yi dubu to ya gama tashi, haka ya yi na maza da shi aka dinga basu kulawa, wa'inda suka mutu kuma, suka dubasu, a lokacin sai da kuka ya ƙwace mai, dan kuwa ya ruɗe da ganin yarda mutane suka koma, wasu a bokiti aka zuba namansu, take Abba ya ɗauke huta, ba shi ya farka ba sai da yamma, gashi a Abuja sai kiransa ake yi akan meeting da za su yi a washegari.
Haka badan ya so ba ya biyo Flight dan ba zai iya driving ba, ya so sake ganin Najlah sai dai Allah be yi ba, gashi ko numberta be amsa ba, shine duk ya shiga tashin hankali.
Bayan ya gama shan Tea ɗin ya tashi ya shiga bedroom, wanka ya yi sannan ya fito ya kwanta, da yake akwai stress akan sa yana ƙwanciya barci ya yi gaba da shi................
*Najlah*
Ko da suka shiga wannan ɗakin sai ta tirje ta ƙi ƙarasawa ciki, sai da George ya yi da gaske tukun ta shiga ciki, sai ya umarci da ta tsugunna a ƙasa.
Kallonsa ta yi yarda yake magana a fusace, sai hakan ya sa ta yi murmushi sannan ta gyara tsayuwanta tana cewa.
"Uhmmm Segent George, kasan cewa gaba ɗaya rukunin mu kallon gaɓo muke maka, har ce min aka yi kai ikon da ke hannunka ne kawai ƙarfin ka amma sam ba ka da jarumta, kuma sai na duba al'amarin na ga hakane, baka dambe da mu sai horanmu, shin me yasa baka faɗa da mu.....ko kana tsoron za ka sha wiyane?." Ta kai nan tana jin daɗin yarda tarkon ta ya kamashi, haka dama sojoji suke, suna da zuciya sosai, kuma ba'a ce da su matsorata, dan daga lokacin suke sauya maka.
"What?......Ni suke ma kallon rago?." ya faɗa a fusace.
"Sosai ma kuwa, amma da wata rana za ka kwada dambe da ƴar rukunin mu, idan ka lillisa yarinya to za mu kiyaye ka, ko Ni fa bana jin tsoronka dan gani nake kaman da macce nake tsaye." sai ta matsa baya tana ƙoƙarin shiga wani rami, wanda yake da mugun tsawo, tanan mutum zai shiga sai Segent George ya toshe wajen, sannan ya fita ya yi tafiya mai tsayi zuwa cikin daji, anan wajen fita yake, idan mutum ya shiga haka zai rarrafa har can wajen, sannan ka fito kasha iska sai ka koma, shine horo na farko a wajen Segent George.
"Dakata." Ta ji ya faɗa, sai ta yi murmushi sannan ta juyo tana cewa.
"Kar ka ce za ka yi faɗa da Ni dan za ka sha kunya." Sai ya nunata da yatsa sannan ya ce.
"Get ready." Yana faɗin haka ya fita waje.
Najlah kuwa ta hau dariya dan kuwa an zo wajen da take so, kan table ta kalla sai ta hangi plate an rufe da leda, da sauri ta isa wajen ta buɗe, sai yanzu ta tuna ko breakfast Sir J. be bari ta yi ba.
Nan ta ga lafiyayyen Doya da ƙwai, ai kuwa ba ta damu da dattin da hannunta ya yi ba, ta fara cin doyar nan kaman an aikota.
Pure water ta gani ta ko fasa tana sha ta na ci, a haka ya shigo ya sameta, sai ya yi mata murmushi yana cewa.
"Ki ci da ƙyau, dan kuwa kafin ki sake cin abinci da bakinki sai kin kwana biyu, ina jiranki a waje, babu mai hanani goge raini da rukuninku yau, dama General nake shakka to ya bar Barack." da haka ya juya ya fita a fusace.
Najlah kuwa ba ta san yanayi ba, sai da ta gama yaɗe ƙwan ta cinye, doyan kuwa wasu ta ci wasu gatsa ɗai-ɗai ta musu, sannan ta shanye sauran ruwan, miƙa ta yi sannan ta nufa waje in da take jiyo hayaniya sosai.
Tana fita ta tsaya cak dan ganin sojoji manya sun zagaye gefe ɗaya sannan ga ƴan rukuninsu suma a gefe ɗaya.
Dama wajen dan dambe aka tanada, dan kuwa an yi gyaran wajen da wasu abubuwa masu laushi kaman katifa, Segent George yana tsaye a wajen yana magana cikin ɗaga murya.
"Zan yi faɗa da wacce ƴar alhakin, babu ceto, babu agaji, na ku ido ne, na tsawon minti 20, a mutu ko a yi rai." ya kai nan yana ma Najlah alamun da ta shigo.
Take mutane suka hau surutu dan ganin yarinyar da zai yi faɗa da ita, dan kuwa Segent George mutum ne mai tsayi da faɗi, ga jikinsa duk a murɗe.
Najlah kuwa hankalinta kwance ta nufa Ya Adam dake tsaye cikin tashin hankali.
"Uban me ya haɗa ku da wannan mugun?." ya faɗa yana ɗan janta gefe.
"Laifi na yi sai na faɗa mai maganganu marasa daɗi, karka damu na riga na shirya mai..........idan kuma na suma dan Allah ka kaini wajen Mamie ta yi min jinya, karku kai ni asibiti, in Kuma na mutu.........ka ce ma Mamie Ina sonta......" Ta kai ƙarshen maganar cikin sanyi da shaƙwaɓa.
Sai Ya Adam ya rungumeta yana jin soyayyar fitinanniyar ƙanwar ta sa.
"Ba zan iya hana faɗar nan ba, amma karki manta ke Jaruma ce." sai ya raba jikinsu sannan ya sara mata, duk dan karta karaya, take ta yi murmushi sannan ta juya ta fara sauka cikin wajen dan yana ƙasa ne, masu kallo kuma suna sama.
Tana fara tafiya aka hau mata tafi, wasu dama duk ta ishesu da fitina, gani suke yau dole a yi maganin Najlah a filin wajen nan, gashi duk manyan cikin Barack ɗin sun fita.
Bin Uthman hawaye kawai ta share tana jin zuciyarta na yi mata zafi, tasan yau kashin Najlah ya bushe a wajen Segent George.
Najlah ba shiga wajen ta ƙare ma Segent George kallo, ita sai a yanzu ta ga ashe yana da ƙwanji, baki ta taɓe, sannan ta yi shirin faɗa.
Ai kuwa a fusace Segent George ya yi kanta kaman ya ga sa'an sa, yana zuwa ya ɗaga Najlah cak, ya nuna ma Allah sannan ya sake ta faɗi ƙasa, kafin ta tantance me ya yi ta yi ya kuma cakumanta ya ƙara bugata a ƙasa.
Take ta ɗauke huta na tsawon minti biyu, wasu sun za ci ta suna ne ma, sai ga shi ta motsa da ƙyar, a hankali kuma ta ja jikinta ta zauna tana ƙare ma mai kallo, ganin duka biyu ya yi mata ta fara leƙa lahira.
Bakinta ta taɓa in da ta ji ya fashe har jini ya fito, sai ta goge tana miƙewa tsaye.
Ita haka faɗarta yake, duk yarda take son dambe, idan aka zo ƙwabzawa, ba ta kare kanta a dukkan farko, a wanan lokacin take gama karantar yanayin abokin damben na ta, ta riga ta gane salon damben na sa, shi yasa ta bari ya jibgeta.
Dama idan dambe za ka yi ka fara samun sakewa da ɗan kokawan, kafin ka fara nuna naka basiraka, ta riga tasan cewa yanzu gani yake saura kaɗan ya gama da ita, amma ita sai an jibgeta take samun ƙarin karfi.
Kamar ɗazu ta tsaya cak tana jiransa, ai kuwa ya yi kanta da gudu yana sureta zuwa sama, sai dai a yanzu yana ɗagata Najlah yi sauri ta miƙe tsaye akan kafaɗara, sannan ta sakar mai wani wawan naushi akan farantin kansa, take ya yi ƴar ƙara yana dafe wajen.
Sai ta kuma yin sauri ta buga somasol ta sauko ƙasa, sai ta falla da gudu, tana zuwa ta taka jikin wajen take ta juyo tana daka tsallake, sai ta sakar mai wani mari a fuskarsa.
Ai ba shiri ya durgushe dan ganin taurari ya yi, kafin ya kuma ankara ta kai mai wani duka na uku a fuskarsa, sai ya kai hannunsa dan ya kare kansa, nan take ta buge hannun sannan ta daki bakinsa, haƙoransa biyu suka fito.
Sai ta tsaya tana ɗan rangaji, dama haka take in ta fara kai farmaki ba ta tsayawa.
A fusace Segent George ya nufeta, ai kuwa Allah ya bashi sa'a ya mata duka ɗaya ta zube a wajen, ya tsugunna yana haɗe hannu zai nausheta, sai ta yi sauri ta tokaresa.
Nan fa suka fara cin uban juna, suka yi jini da majina amma babu wanda ya haƙura, Najlah faɗa take da zuciya ɗaya tana son fanshe duk abin da ya yi mata.
Shi kuma yana son kar ya faɗi mutane su mai dariya, hakan yasa ya dage.
Da yake ƙaramin jiki gareta ba ta jin nauyinsa, haka ta fara wanashi a cikin filin, har sai da ta tabbar ya gaji, take da mai wani duka a baya wanda yasa ya faɗi ƙasa, ai kuwa ba ta tsaya ba ta hau kansa ta fara kai mai yaƙushin da saboda shi ta tara farce masu tsayi.
Ta cijesa a kai, sannan ta ko ji mai ciwuka masu yawa a jiki, burinta ya cika in da ta fasa mai kai, nan kuwa ta sake sa tana ji ana faɗa lokacin dambe ya cika.
Ta daka tsalle duk da jikinta ciwo suke mata, ai take wani soja ya sakar musu waƙar sojoji a wata M.P.
Najlah ta buɗe baki ta fara bin waƙar nan kaman ana yaƙi ta na ɗan tsalle waje guda tare da ɗaya hannu ɗaya, yarda gaba ɗaya sojojin suka yi.
"SOJA!!! YEH, SOJA!!! YEH, SOJA!!! YEH, HORAH!!! YEH, HORAH!!! YEH." Waƙar sai ya ƙara mata nishaɗi, ai kuwa ta koma kan Segent George ta sumbaci kansa, ina da yake ta juyi yana neman ɗauki.
Jikinta ita ma akwai raunuka sosai, amma haka ta gama tsalle-tsalle da sunan rawa, take ta zube a sume saboda jirin da ya ɗauke ta.
Nan fa aka washe su sai ɓangaren masu kula da lafiya na cikin Barack ɗin, in da aka basu kulawan agaji.
Kowa sai maganar Najlah yake yi dan kuwa ta ƙara tabbatar musu da cewa jinin Soja shike yawo a jikinta, sannan a yau ta shata dogon layin dake tsakanin ta da masu son rigima da ita, har Sir J. ya ga faɗan, sai ya ƙara jinjina ma ƙarfin Najlah da kuma wayan da take da shi.
Kwance take tana sauke ajiyan zuciya a natse, ta farka amma an yi mata alluran barci, sai dai jinin ta yana da ƙarfi, dan kuwa tana barcin tana magana.
Yayyinta biyu suke zaune gefanta suna kallonta cikin tausaya ma halin da take ciki, dan kuwa ta samu rauni sosai, dan wani ciwon ma an yi mata ɗin ki.
"Yarinyar nan ba ta jin magana wallahi, dan Allah ji yarda ta koma." cewan Yayansu cikin ɓacin rai.
"Hmmm ko da kana nan ba za ka hana faɗar nan ba, dan yarda Segent George ya ɗau zafi da ita."
"Adam ai gashi nan ya ja ma kansa, dan wallahi babu mai sake bashi girman nan." Sai suka yi sauri suka kalla Najlah dake magana tana barci.
"Na manta ban ƙwaƙule mai idon ba...ku bari na cire.....ku...ku barniiiii." Sai ta yi shiru tana ci gaba da barci.
Yaransu ya girgiza kai yana tashi ya fita, Adam kuwa ya dunguran mata kai yana cewa.
"Masifaffiya kawai."
Ko bayan da General ya dawo ya samu wannan labarin, sai ya rasa me ze yi, har video ya gani dan wasu sun ɗauƙa, ɓangaren da aka kwantar da su ya je, ya iske Segent George cikin mawiyacin hali. General ya dafe kansa sannan ya nufa in da Najlah take.
Zaune ya isketa amma har lokacin drib yana shiganta, tana ganinsa ta yi fuskar tausayi tana marairaice mai.
A zaunen ta sara mai tana cewa.
"General, Segent George ya kusa kasheni, ban mai komai ba ya ce dambe za mu yi shine kawai......" sai ta haɗiye maganar tana kallon cikin wayar da wani soja dake bayan General ke nuna mata.
Miyau ta haɗiye sannan ta kallesa za ta yi magana ya ce.
"An baki suspension na sati ɗaya, bayan kin dawo kuma za ki fuskanci abin da zai biyo baya." Da haka ya yi hanyar fita, sai ya tsaya cak yana jin abin da take cewa.
"Na gode Sir, dama ina son ganin Mamie, so nake ta ganni da wa'innan raunin saboda tasan mace mai kamar maza ta haifa." Sai General ya yi murmushi sannan ya fice.
Drib ɗin ta fizge ta matse wajan, sannan ta sauka a gadon a hankali, takawa ta yi kusa da wani mudubi ta kalla kanta, ba ƙarya ta sauya sosai, dan ciwuka gasunan ta ko ina, sai ta ja tsaki sannan ta shiga tattara abubuwanta dan a daren nan take so a mai da ita gida.
Nurse ɗin da tashigo ta hau Najlah da masifa akan me yasa ta cire drib ɗin hannunta, sai Najlah ta yi mata wani irin kallo tana ɗaukan ƙaramin wuƙan dake gefen lemu ta ce.
"Yishshshsh, yanzu ki sallame Ni Ko kuma kafin safe ke za ki kwanta anan, dan kuwa maƙogaronki zan..........." Da sauri Nurse din ta ce.
"Kin warke ai, ina zuwa." Da haka ta fice a ruɗe.
Najlah ta zauna tana jiran masu tafiya da ita, kusan 10mnt aka ɗauka, sai ga Yayansu da Adam, suka haɗa komai na ta suka fita da shi, sannan suka ce ta taka, sai ta maƙe kafaɗa tana cewa.
"Ya Adam ka ɗauke Ni ba zan iya tafiya ba." Ta faɗa tana tura baki.
Sai Yayansu ya ja tsaki sannan ya fita, Adam kuma ya harareta.
"Bansan iskanci, ba yanzu kike tafiya ba anan?."
"Ƙafar ta riƙe ne ai." Sai ya dunguran mata kai sannan ya ɗauke ta cak.
"Yarda kika san na ɗauki jinjira." Sai ta ji murmushi tana cewa.
"Ai ita ce, jinjiran Mamie." A mota ya sanyata sannan suka bar Barack ɗin...............
*******************
Ɓangaren Basma kuwa, tana shiga bedroom ta yi jifa da wayarta, take ta faɗi ta fashe, sannan ta tsaya tana huci, a lokacin Najlah ta shigo, sai ta yi sauri ta dafa kafaɗa Basma, hannu ta sa ta cire na Marwa tana cewa.
"Muryanta akwai sanyi......haka ya ce fa."
"Come down, Abba yana cikin damuwa ne kika mai wannan tambar, shi yasa ya faɗa miki haka." Sai Basma ta juyo ta kallata ido cikin ido.
"Mene!......kardai kina goyan bayan Abba? Inaaaaaaa, ko dai baki jin abin da ya ce ne : muryanta akwai daɗi kuma tana da ƙyau, HABA!." ta kai nan tana ji dama Harira na gidan a yanzu, babu abin da zai hana ta yi mata mugun duka, tunda har hankalin Abba ya kai kanta, sannan ta sanya a cire mata harshe ta yadda ko magana ba za ta sake yi ba. Marwa ta janyota kusa da ita sannan ta buɗe baki cikin wani irin yanayi ta ce..............✍️ END.
> Na yarda Basma ta haukace jama'a, wai nikam za ta iya zaman aure ma kuwa 😳? Kishinta ya yi yawa, tun akan Uba balle a zo na ta, hmmmm tab akwai aiki.
> Najlah na ce sannu fa 🤭. Kaima Abba sannu 🥰. *PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:
📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*
#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️
★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story
by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.