BUDURWAR ABBAN MU

PAGE

by @prettys01

> Mene!......kardai kina goyan bayan Abba? Inaaaaaaa, ko dai baki jin abin da ya ce ne : muryanta akwai daɗi kuma tana da ƙyau, HABA!." ta kai nan tana ji dama Harira na gidan a yanzu, babu abin da zai hana ta yi mata mugun duka, tunda har hankalin Abba ya kai kanta, sannan ta sanya a cire mata harshe ta yadda ko magana ba za ta sake yi ba. Marwa ta janyota kusa da ita sannan ta buɗe baki cikin wani irin yanayi ta ce...........

"Ki natsu mana, kema kinsan zance ne, babu wata shegiya da za ta iya rayuwa da Abban mu, dan haka ki kwantar da hankalinki.........."

"Me yasa kike bin komai a hankali? Idan bama nuna mai huta-huta akan al'amarin ba zai iya samun dama ya fara kula mata, narantse miki da Allah da a ce a yanzu zan ga Harira sai na sa an kulleta." Ta kai nan tana ji har lokacin ƙirjinta yana mata zafi.

"Duk yarda kike ji ina jinsa ko ka fiye da naki, sai dai ina dannewa saboda in muka hau ba mai iya saukar da wani, yanzu dai ki kwantar da hankalin Please." Ta kai nan da sigar roƙo da rarrashi.

"Na ji, amma ki sani ba zan kuma yi ma Abba magana ba. Hmmmm." Sai ta shiga bedroom sannan ta buƙo ƙofa da ƙarfi.

Marwa ta zauna kan kujera tana ciwon bakinta, tasan zuwa gobe komai zai wuce, amma tabbas kalmar da Abba ya faɗa ya huda mata zuciya *Tana da ƙyau ba laifi, ga muryanta akwai sanyi.*

A fili ta yi tsaki tana kwanciya a kujeran tare da cewa.

"Wasa ne ma tunanin wata maccen a cikin gidan, dan har abada Mom ba ta da Kishiya.".........

***********

Bayan sunyi parking, Ya Adam ya Kuma ɗaukar Najlah zuwa ciki, a parlour ya sauketa, sai ya bi bayan Yayansu zuwa wajen Mamie.

Me aikin Mamie ce ta kawo ma Naljah youghout wanda ta umarta, sai ta fara sha, murmushi saki tana mai da idanunta kan Mamie dake saukowa daga stairs cikin tashin hankali.

A ruɗe ta iso gabanta ta rungume Najlah tana jin hawaye na zubo mata tana cewa.

"Me ya sameki?."

"Outch ciwona." Ta faɗa a taɓare fiye da kullum, dama wani lokacin taɓarar baya tashi sai tana kusa da Mamie.

Da sauri Mamie ta ɗaga ta tana cewa.

"Sorry, sannu kinji."

"To, ya kike Mamie?." ta faɗa tana shafa fuskarta.

"Lafiya nake, amma me ya sameki ne? Kalla ciwuka a jikinki? Innalillah....tun ba yanzu ba nake rabaki da son zama Soja amma kafiyarki tana da yawa."

"Uhmmm Mamie, karki damu, faɗa na yi da wani."

"Zamu wuce Mamie, hankalinki yana wajen ƴarki fitinanniya." Cewan Adam suna saukowa daga stairs.

"Ki ja ma Yarinyar nan kunne, ba ta jin magana, faɗa ta yi da wani soja." Mamie ta zaro ido tana ɗauka hannu akai ta ce.

"Shine ya kusa kashe min ita? Ku kuna ina haka ta faru?."

"Ki dena ɗaga hankalinki dan kuwa abokin faɗarta yana kwance cikin mawiyacin hali, ƴarki ta kusa kashe mutum yau, shi yasa aka ba ta suspension."

"Yayansu bangane ba? Wannan ce ta yi dambe da soja?." Ta tambaya tana ƙare ma Najlah kallo.

Adam da ya afka ma abinci ya miƙe yana ci ya ba Mamie wayarsa, amsa ta yi tana kallon video yarda ke kokawa da ƙaton namiji.

"Da wannan gardin take dambe?." ta faɗa tana buɗe baki.

"Uhmm da shi na yi, daga yanzu sai ki dena ɗauka ta raguwa, zan je na kwanta, Mamie Ina son suspension ko dan zuwa na ganki." Ta kai nan tana miƙe wa ta haura sama.

"Ya Salam, wai Najlah ce wannan?."

"Fitar ƴarki ya fi haka ma, dan haka ki dena mata kallon raguwa, mace ce mai kamar maza, Mamie mun wuce dare na yi." Sai ta ba Adam wayarsa, sannan ta rungumesu tare da musu addu'a, da haka ta rakasu har bakin get, su ka wuce, sai ta gaisa da sojojin biyun da suke mata gadi sannan ta shiga ciki.

Ba ta tsaya a ko ina ba sai ɗakin Najlah, ai kuwa ta isketa cikin duvet ta naɗe sannan ta dunƙule a ciki, sai Mamie ta girgiza kai sannan ta rage mata A.C ta fita daga ɗakin.

Najlah jiki ya yi tsami, barci ya ɗauke ta mai daɗi, ballema an samu yarda ake so, ga A.C ga babban gado.

Kiran sallar farko ta farka, ta tashi a natse, har dai lokacin jikinta be dawo daidai ba, amma ta da sauƙi, bayi ta shiga, ta sakar ma kanta ruwa na tsawon lokaci, tana gasa jikinta, sannan ta yi alwala, bayan ta fito ta sanya wasu riga da wando masu laushi, sannan ta yi sallah, ta jima aka dadduma tana roƙan Allah. "Allah ka bani Miji ɗan Suger Daddy kaman Aboki." ta shafa addu'ar sannan ta koma ta kwanta, take wani barcin ya kuma ɗaukarta.

Sai misalin 10:23am ta farka, ta yi miƙa tana jin daɗin yau ta yi barci har ya isheta, sai ta sauka ta yi brush.

Parlour ta nufa, a nan ta iske Mamie tana zaune, sai ta isa kusa da ita ta zauna tana gaisheta.

"Lafiya lau, ai na shigo sau ba adadi amma ba ki tashi ba, ya jikin na ki?."

"Alhamdullah, ina jin yunwa Mamie." ta faɗa tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.

"Gasu can a Dining ai."

"Uhmmm ni ke za ki bani a baki." Ta faɗa da sigar shaƙwaɓa.

Mamie ta yi murmushi sannan ta rike mata hannu, Dining area suka ƙara sa, sannan Mamie ta yi feeding sosai, da suka gama suka dawo parlour, Mamie ta fara mata tsifa tana cewa.

"Kanki sam baya samun kula, dan ma baya zuciya da duk ya zube."

"Hmmmm dan bana so ne da tuni an mun ƙwal-ƙwal, dan wani jami'i a wajen haka ya dinga ma mata ƙwaryan molo, nikam na ƙi yarda, shine suke ce dole sai irin kitson nan."

"Allah na tuba in aka miki aski ai ba za ki yi ƙyau ba sam, yanzu tunda sati za ki yi, zan wanke miki gashin, ki sha iska da shi a haka kafin za ki wuce na miki irin wannan."

"Yauwa Mamie na, na yi kewanki sosai."

"Nima haka Najlahtah." Da haka suka saura hira, suna yi suna dariya cikin son kasancewa da junan su..........

*Abba.* Bayan ya dawo sallar asuba sai ya zauna a babban parlour, ya kunna tv yana kallon labarai, sai dai hankalinsa baya kan tvn yana tare da Najlah, yarda take magana tana zaro ido hakan na mai tasiri a cikin kansa sosai, wayarsa ya ciro ya kira number General, duk da kuwa lokacin 7:12am, bugu uku ya ɗauka.

Sai suka gaisa, sannan General ya ce.

"Jiya nasan ka gaji shi yasa ban kira ba, na kira drivernka ya ce ka iso lafiya, to ya jikin?."

"Alhamdulillah Yaya, ya mutanen gidan?."

"Suna lafiya yanzu muka yi waya da su, dan a Barack na kwana." sai Abba ya sosa kai yana tunanin ta ina zai fara tambayar Yayansa wannan yarinyar.

"Uhmmm to dama....shike nan dai, sannu."

"Kai lafiyanka kuwa?." Sai Abba ya sosa kai sannan ya ce.

"Lau nake, dama kawai kiranka na yi."

"To sai an jima........" Da sauri Abba ya ce.

"Zan tambaye kane dama." Sai General ya yi ɗan dariya sannan ya ce.

"Tuni na gano zancen, amma gaskiya Najlah is to Young, ba zan baka ita ba, ka tsufa maganar gaskiya." Ya faɗa dan ya tabbata da shin Najlah yake so ko mene.

Abba ya lumshe ido sannan ya ce..

"Ni ba aurenta na ce zan yi ba, kawai na kira na ji ne ya take."

"Hmmm shike nan, amma ka sani da Soja kake magana, sannan Najlah mun ba ta Suspension na sati guda, dan kuwa rigima ta yi da wanan mutumin, yanzu haka yana cikin mawiyacin hali, ita kuma ta samu raunuka sosai.........." da sauri Abba ya ɗan zabura yana cewa.

"Rau....raunuka!? Innalillah."

"Hmmmmm zance na ya tabbata dai, amma Mubarak yanzu yarinyar nan ce ta yi maka ?." sai ya lumshe ido.

"Eh Yaya, wallahi tunaninta hanani sukuni yake, yanzu dai ka taimaka min ka haɗa da ita a waya." Sai General ya kwashe da dariya sannan ya ce.

"Na ce maka na bata Suspension na 1 week, ta koma gida."

"Oh shit! Yanzu ya zanyi, zuwa dare zan shigo Kadunan kawai......" Da sauri General ya katsesa.

"Ba sai ka zo ba, zuwa anjima zan turo maka numberta idan tana waya, ko na mahaifiyarta." take ya sauke ajiyan zuciya sannan ya yi mai godiya yana yanke wayar.

Farin ciki ne ya kamasa, sai ya samu daman tashi ya nufa part ɗinsa, wanka ya yi sannan ya shirya zuwa office, tea kawai ya sha sannan ya ɗauki waya ya kira Marwa, tana ɗauka ya ce.

"Ku fito Ina son ganinku." Da Haka ya katse kiran yana zama.

Ba su ɗau lokaci ba sai ga su sun fito a jere, Marwa yau tana gida, Fauza kuma tashirya tsaf, sai Basma da ke sanye da Hijab har ƙasa.

Baki suka haɗa suka gaishe sa, ya amsa yana ƙare ma photocopyn matarsa Hajiya Karima, wato Basma, ranta a haɗe, sai ya murmusa sannan ya ce.

"Alhamdulillah, Autata ɗauko jakkanki mu fita tare, Basma yaushe za ki fita?." sai ta tura baki sannan ta ce.

"Yanzu zanje asibiti."

"Ok, zan sauke ki kema, ku yi sauri ku ƙara sa, dan za mu tsaya mu yi breakfast."

"No Abba, kuje kawai, zan ɗauki motata." Sai ya haɗe fuska duk da kuwa baya mai ƙyau.

Murmushi Basma ta yi sannan ta miƙe tsaye ta isa kusa da Abba, sai ta ja mai kumatu tana cewa.

"Dama ka dena baya maka ƙyau sam." ganin ta sauka sai ya matsa yana cewa.

"Karki min magana tunda ke ba za ki dena wannan halin ba." Da sauri ta kuma ja mai kumatu tana cewa.

"Abba ko a yanzu ban wuce ba, kawai na gano jiya baka yanayi mai daɗi ne, amma kalmar *Muryanta akwai sanyi* ya tsaya min a nan." Ta faɗa tana nuna zuciyarta.

"To ba zan sake ba."

"Yauwa Abba na, shi yasa nake sonka da yawa." Sai ya rungumeta yana dariya.

Da sauri Marwa da Fauza suma suka rungumesu, sun ɗau lokaci a haka sannan ya ce.

"Muje, Marwa kema shirya mu fita." Ba musu suka koma part ɗin su, Fauza ta ɗauki jakkarta, Basma kuma ta haɗa abubuwan da take buƙata ta zuba a wani jakka, suka yi waje suna jiran Marwa dake sauya kaya.

Mota suka shiga suna jiranta, can sai gata ta fito cikin wani Black Abaya, ta yi rolling Vail sai wayarta dake hannu.

A baya ta zauna, Abba kuma ya ja mota suna yi suna hira, a wani babban wajen cin abinci ya ajesu, suka zauna kowa ya ci abinda yake so, ya biya sannan suka koma mota.

"Ranar Alhamis za mu je Kaduna bikin su Aneesa, sai ku fara shiri dan sai bayan biki da kwana uku zamu dawo." Ya faɗa yana yin parking a bakin school ɗin Fauza.

"Shike nan, Bye Abba." Da Haka ta fita ta shige ciki.

Basma kuma ta hade fuska dan bata son zuwa Kaduna.

"Kunyi shiru." Ya faɗa yana jiran ya ji me za su ce.

"Shike nan Abba, Allah ya kaimu."

"Yauwa Marwa, ke fa Basma banji kince komai ba." Sai ta ja fasali sannan ta ce.

"Allah ya kaimu."

"Ameen me kama da Mom, Kuma sai ku shirya ku fito da miji, dan kun girma." ya faɗa yana murmushi.

"Abba Miji ka ce fa? Tab Ni Ko saurayi ma banda shi."

"Karya kike Basma, ko kwanakin nan ai kin kai saurayin ki station....Abba wallahi samari take da su sosai, amma ƙarshe sai su ƙare a Station." Basma dake gefan Abba ta lumshe ido tana cewa.

"Bansan sa ido, Abba banda saurayi."

"Hmmm shike nan, mun iso ma." Ya faɗa yana tsayawa, sai ta fita ta mai godiya sannan ya ce.

"Ki kula da kanki, zan zo ɗaukanki."

"Shike nan kaima haka." Da haka ta shiga cikin wani babban asibiti, sannan ya ta da motar yana cewa.

"Duk kallonku nake, kuna gama karatu aure zan muku wallahi."

"Kai Abba, to da wa za ka zauna in muka bar ka? ." sai ya yi ɗan dariya wanda iyakansa kan leɓansa, ya shafa kansa ya na cewa.

"Hmmm lokacin dai." Da haka ya sauya hirar ta su.

Bayan sun isa Company, a office ɗin Abba ta zauna, shi kuma ya fita dan aiki.

Kiran Al-hussain ta yi karo na biyar a yau amma be ɗauka ba, yasan yau tana gida, kuma irin haka gidansu yake zuwa, sai gashi yau kuma be ɗau ma kiran ba gaba ɗaya.

"Allah yasa lafiya." Ta faɗa tana jin babu daɗi, dan ya saba mata da jin sa kodayaushe...............

*Al-hassan*

Motarsa ya buɗe har zai shiga sai ya kalla Merry dake shirin shiga na ta motar.

"Merry, ki dai zo da wuri, kuma ki gaishe da kawar ta ki"

"To Ya Al-hassan za ta ji." Da haka ya shiga motan ya fita, sai da ta tabbar da ya yi nisa sannan ta fita ta dau wani hanya.

Ta yi tafiya mai tsayi kafin ta shiga wani layi ta fara bin cikin layika , can cikin wani layi ta hangi Al-hussain tsaye jikin motarsa, sai ta isa kusa da shi sannan ta faka ta fito.

"Promise."

"Promise, Promise." Sai ta yi murmushi sannan ta ce.

"Komai ya yi ready?."

"Eh, mu kawai ake jira." Sai ta koma motarta ta gyara parking sannan ta fito, motarsa suka shiga sannan ya fara tafiya a natse.

Sun kuma ɗaukan lokaci sun tafiya, sannan ya faka suka fito shi da Merry, wasu maza biyu dake gabansu suka gaisa sannan suka bashi wani makullin mota, ya amsa suka sauya mota, bayan sun shigar komai nasu a ciki.

"Haka zamu je wajen?." Ta tambaya tana kallon shigar dake jikinsu.

"Eh ai meeting ne kawai." Sai ga daga kai.

"Kafin mu isa Ni zan sauya kaya a ɗakin sauya wa, dan ba zan shiga da wannan ba." Sai ya kalla kayan na ta, Material ne Riga da wando sai gyale.

"Ok ba damuwa." Da haka ya hau kan titi tare da yin tafiya kaɗan sai ya shiga wani babban unguwa mai suna *N.P.H* yana shiga ya buɗe window ya zuƙa iskar wajen yana cewa.

"Na yi kewan iskan nan, iskan dake jingine da *Promise*. "

"Nima haka." ta faɗa a daidai in da ya yi parking.

Sannan suka fito suna kallon wajen cike da ƙauna da begen shiga dan shaƙar iskan dake cikin wajen yana ƙara musu wani natsuwa ne na musamman.

"Promise."

"Promise!! Promise!!." sai suka yi murmushi suna shiga wajen..............✍️ END.

*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:

📘 *DAGA INA TAKE* free book 📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book 📙 *BARRISTER* Paid book₦300 📕 *THE SLAVE* free book 📒 *ZAMU HAƊU* Free book 📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300 📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300 📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500 📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book 📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_ 📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_ 📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_ HIKAYOYI kuma sune : *SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥* *SARKIN MU🤣* *MOHINA DA MATSAFIYA💀* *RAMUWA💀🔥*

#LIKES👍 #SHARE👌 #COMMENTS☹️

```🔥 TALLAH! TALLAH!! TALLAN MUSAMMAN!!! 🔥 ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU 📢 Jama'a ku fito ku ji labari! Shin kun san Hajiya Safiyya Baiwar Allah? 🤔 Idan ba ku sani ba, to ku matso kusa ku saurara sosai! Ina ƴanmata? Ina matan aure? Wannan damar taku ce! 💃 ✨ Hajiya Safiyya Baiwar Allah ta kawo muku: ✔️ Kayayyaki na zamani ✔️ Masu inganci sosai ✔️ Kuma a farashi mai sauƙi 🛍️ Kayayyakin da ake da su sun haɗa da: Jakkunkuna masu kyau, launi-launi, iri-iri Zanukan gado masu kayatarwa, domin ƙara wa ɗakinku armashi 🛏️ Hijabai masu kyau da ɗaukar hankali 👗 Kayan kitchen masu ƙyau da araha 🍽️ 💥 Duk abin da kike buƙata don gyaran gida da ƙara ƙyalli yana nan a wuri guda! ⚠️ Kada ki bari wannan dama ta wuce ki! 📞 Tuntuɓi yanzu: *** 📍 Location: Unguwar Sunusi, Kaduna 💬 Ko da kuɗinki kaɗan ne, sai kin samu abin da zai burge ki!```

📢 SANARWA TA MUSAMMAN!

*Duk mai son a tallata masa hajarsa cikin tsari mai kyau da jan hankali, ya tuntubi:* 💼 ~PRETTY SK~ 📞 *** ✨ Muna yi maka tallan da zai jawo hankalin kwastomomi cikin sauƙi!🥰

★BUDURWAR ABBAN MU★ Drama&Love story

by ```PRETTY SK ✍️``` 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.